Showing 267001 words to 270000 words out of 300844 words

Chapter 90 - Tagwaye Book 1 Hausa Novel Complete

22 Dec 2024

2033

da babu hearing aid dinta yace "na yafe miki Hassana, na yafe miki duniya da lahira ba dan halayenki ba sai dan Allah. Ina fatan nima Allah ya yafe min kurakurai na ni da iyalina" Sai yaji ta saki hannun

Ya juyo a dai dai lokacin da Abdulrahman da Abdulrahim suke shigowa palon da sauri, fuskokin su cike da tashin hankalin abinda idanuwan su suke gani, ya kalli Abdulrahman yace "she is alive, do something" nan take Abdulrahman da yake a matsayin likita ta tafi gurin Ruqayyah, sannan ya dauko wayarsa yana kiran ambulance din asibitin da yake aiki. Abdulrahim da yake shine mai karyayyiyar zuciya a cikin su sai ya tsaya a gaban gawawwakin yaran hankalin sa a matukar tashe, hawaye yana zuba daga idonsa, innalillahi wa inna ilaihir rajiun, so innocent. Basu saba sosai da yaran ba saboda basa shigowa nan babansu ya hana su suma kuma yaran basa shiga nasu gidan saboda mamansu ta hana su, amma suna haduwa a waje kuma suna haduwa a gidan Baba, ya tuna Sa'adatu duk inda ta ganshi sai ta gaishe shi, har wani abokin sa ya taba tsokanar sa cewa budurwar sa ce shi kuma yace ba zai iya budurwa da mai kama da mommyn sa ba. Ya tuna Sa'ad kullum suka hadu sai ya roke shi kudi ko kuma ya nuna masa wani abu yace ya siya masa. They were his cousins, they were his s family. Sai yaji a ransa kamar abinda ya faru dasu fault dinsu ne gaba ki daya.

Yace yana rufe wa Sa'adatu idonta "wanne marar imani ne ya aikata wannan abin? Wanne mara imani ne zai kashe uwa da ƴaƴan ta ba tare da sunyi masa komai ba? Kawai saboda abin duniya? Abin duniyar da ba zasu iya hanaka dauka ba dan basu da karfin hanawar. Allah wadaran dan fashi" sai wannan yaron gidan da ya kawo towel yace "a'a yallabai, basu suka harbe ta ba" gaba-daya suka juyo suna kallonsa da alamar tambaya, sai ya nuna kofar da take shiga part din ma'aikatan gidan yace "da yawa daga cikin mu witnesses ne, su suka harbi yaran, ita kuma mai gidan ne ya harbe ta bayan ya saka ta saka masa hannu a wata takarda"

Hassan ya kalli Abdullahi da sauri, kafin yayi magana har ya dauko wayarsa ya fara waya yana describing Lukman da motar daya fita a ciki da address din daya gidan nasa. Yana gamawa police suna zuwa kusan a tare da ambulance, police din ne suka ga maigadi a dakinsa an buga masa wani abu aka ya suma, aka dauko shi shima aka hada da Ruqayyah, Abdulrahman ya bisu a baya, Abdullahi kuma ya shiga cikin police suka fara karbar report, Hassan kuma ya koma gidan sa yana tunanin ta inda zai fara bawa Sumayya da sauran yara wannan labarin.

Kafin gari ya waye labari yaje duk inda ya kamata yaje. Sumayya a asibiti gari ya karasa waye mata hannun ta rike dana Ruqayyah har aka gama shirya ta aka shiga da ita dakin aiki aka yi kuma nasarar fitar da bullet din ya samu gurin zama a makogwaronta. Sai dai tun kafin a shiga daita aikin doctors din sun warning Sumayya cewa ba lallai ne a samu sakamako mai kyau ba "the most da zamu shine ranta, bayan haka bamu yi alkawarin komai ba"

A gida kuma Inna Ade da Baba su suka wanke kuma suka suturta jikokin su, sannan akayi musu sallah aka kuma kai su gidan su na gaskiya. Dama can Allah bai rubuta cewa masu tsahon kwana bane ba, ya kuma karbe su tun kafin su loda wa kawunan su zunuban da zasu halakar dasu, rayuwar su gabaki daya da kuma mutuwar su ta kasance aya ce akan Ruqayyah.
Daga nan kuma sai suka tafi asibiti dan duba lafiyar Ruqayyah, wadda da kyar likitocin da suka yi mata aiki suka cire bullet din da Lukman ya saka a makogwaronta. Sai dai ana gama aikin ta fara convulsing, sannan kuma ta shiga coma. Coma din da har sai da yan uwa suka fara fitar da ran zata tashi sannan ta tashi, bayan watanni. A cikin watan farko police suka tsinci gawar lukman a cikin motarsa, gefensa da jaka cike da kudin da yayi withdrawing using check din da ya saka Ruqayyah tayi masa signing. Ya gama shirinsa kaf har da passport dinsa ya cikin aljihun sa yana niyyar barin gari.

Bayan dogon zama da Ruqayyah tayi a asibiti, wanda a cikin sa ne yayanta manya suka dawo cikin rayuwarta da dukkan karfinsu, suna fatan wannan kulawar da zasu yi mata zai zamanto sanadiyyar kankare zunuban da suka dauka ada na watsar da rayuwar ta da suka yi. A lokacin ne kuma akayi bikin Hussain da gimbiya Fatiman sa.

Problem din Ruqayyah shine, ta zamanto tamkar mutum mutumi, dama already doctors sunce tayi loosing her ability to talk, amma sai ya zamanto ta koma emotionless, tamkar jikinta ne kawai a duniya amma ruhinta is somewhere else, bata motsi, ko yatsunta sai dai a motsa mata su. Ko kayi mata magana ba zata yi responding ba ko da kuwa an saka mata hearing aid dinta. Sau da yawa sai dai kawai kaga hawaye yana zuba daga idonta, wannan ne kadai alamar da suke gani wanda yake nuna musu cewa she is there, amma Allah ya dauke komai daya bata.

Ganin babu wani sauran abinda asibiti zasu iya yi mata ya saka aka tafi da ita gida, Baba da kansa yace a kaita gidansa duk da dai bata shiga da kafafuwan ta ta roki gafarar su ba kamar yadda yayi mata kwadayi, sai dai duk da hakan ma shi da Inna gabaki daya sunce sun yafe mata duk hawayen da ta saka su zubarwa, fatan su shine Allah ma ya yafe mata. Anan gidan Baba ta zauna, Hussain ya dauko mata kwararriyar maaikaciyar jinyar da aikin takawai shine kula da Ruqayyah, dan Inna Ade ba zata iya ba saboda jikin tsufa. Babu irin addu'a da ayoyin Alqur'ani da Inna bata rubuta ta bawa Ruqayyah ba, amma laifin Ruqayyah ba tsakanin ta da ubangiji bane ba, dan haka shi ba zai taba yafe mata ba.

Bayan lokaci mai tsaho Ruqayyah tana a wannan hali sai Allah ya dauki ran Baba, a kwance akan gadon sa bayan yar karamar jinya, rasuwar Baba ce ta kawo Adam gari, sai a lokacin ya ga Ruqayyah kuma kallo daya yayi mata yace shi kam ya yafe mata duniya da lahira, ya kuma yi alkawarin zai yiwa Fatima magana akanta, but shi kansa bai san ta inda zai fara yiwa Fatima din magana ba, yana fara kame kamen sa akan maganar ta daga masa hannu tace "har abada ba zan taba yafewa Ruqayyah ba" daga ranar bai sake yi mata maganar ba amma sai yaji yana jin kunyar Hussain sosai, uwa ai uwa ce, ko yaya take kuwa.

Rasuwar Baba da yan watanni Inna Ade ta bishi. Wannan ya tashi hankalin gabaki daya yayansu musamman Sumayya, sun zama kamar Hassan, babu uwa babu uba, gwara shima yana da aunty, karin tashin hankalin Sumayya kuma shine yadda taga Ruqayyah tamkar bata san anyi mutuwar ba, duk kuwa da cewa likita ya tabbatar musu da cewa tana sane da duk abinda yake faruwa, bata da ikon nunawa ne, bata da ikon yin komai.

Mutuwar Inna ta saka yaran suka hadu da niyyar zasu mayar da Ruqayyah gidan Aminu a Abuja, amma sai Sumayya taki yarda tace ba zasu raba ta da yar uwarta ba, bisa amincewar Hussain sai aka dawo da ita gidan da take da, aka cigaba da biyan masu kula da ita sannan Sumayya tana shiga ta dan zauna da ita in Hassan baya nan, in kuma yana nan Amatullah tana shiga ta zauna da ita. A lokacin Sumayya ta fara farautar duk wanda tasan Ruqayyah ta zalunta tana rokar mata yafiya a gurin su. Wannan sun hada da iyaye da tsohon mijin Minal, duk da Sumayya bata tabbatar da abinda ya faru a lokacin ba, cikin ikon Allah Maman Minal tana nan da ranta sai dai babanta ya mutu, mijin ma yana nan sai tsufa daya saukar masa tunda ko a lokacin ma ba karami bane ba, kuma albarkacin Sumayya da kuma ƴaƴan Ruqayyah sai duka zo har gida suka ga halin da Ruqayyah take ciki kuma suka ce sun yafe mata.

Bayan sun tafi ne Sumayya ta zauna tana rike da hannun Ruqayyah a cikin nata kamar yadda take yi a duk sanda suke tare, sai ta tuna itama tana daga cikin wadanda Ruqayyah ta zalunta one way or another, sai tace "Ruqayyah, bansan dalilin da yasa ubangiji yake hukunta ki haka ba, ban kuma san ko hukunci ne yake yi miki ko kuma jarabawar ki ce haka ba. Amma nasan bazan bar ki ba har sai mutuwa ta raba mu, ko ke kin tafi ko ni na tafi. I will always be by your side kamar yadda nayi miki alkawari. Ni dai a bangarena na yafe miki duk abinda kika yi min da wanda na sani da wanda ban sani ba. Kuma zan cigaba da bincikawa duk wanda nasan kunyi alaka dashi zan nemar miki yafiyar sa. Na fatan Allah yaji kanki ya dauki ranki haka nan ko kuma ya baki lafiya"

Ga mamakin ta sai taga Ruqayyah ta motsa hannunta, hawaye yana fita daga idonta ta yi rubutu da yatsanta akan bedsheet kamar haka

"Alive"

Sumayya ta gane mai ta rubuta, cikin zakuwa tace "yes, Ruqayyah you are alive, gaki nan da ranki, yanzu ma alwala zanyi miki kiyi sallah" sai ta kuma rubuta wa

"He is alive"..

Gaban Sumayya ya fadi, waye He din? Wa Ruqayyah take nufi da he is alive? Mutum daya ne ya fado mata a rai, dan Hussain. A mike da sauri taa dafe kirjinta, dama tun a lokacin har kuma zuwa wannan lokacin bata taba jin cewa Ruqayyah zata iya kashe jaririn ba kamar yadda Hassan da Fatima suka dauka, amma ita kanta ta girgiza da cewa wai yaron yana raye kuma Ruqayyah ta sani tayi shiru duk wannan shekarun. Lallai ba karamin so ubangiji yaje yiwa Ruqayyah ba.

Da sauri ta fita tana tunanin abinda zata yi da wannan bayanin, Hassan ta kira a waya ta roke shi yazo suyi magana a gidan su. Amma da yazo sai kunnuwan sa suka kasa gaskata masa abinda yaji Sumayya ta fada "You are not sure" ya fada dan baya son getting hopes dinsa up, "maybe tana nufin someone else, maybe bata san ma abinda ta rubuta din ba" Sumayya tace "maybe, maybe not, Allah ne kadai ya sani, ba zamu sani ba kuma sai mun bincika maganar" yace "bincikawa? Bayan duk binciken da mukayi a da da binciken da court tayi wanne kuma zamuyi?" Tace "I don't know. Amma mu munyi namu ne, mu bar wa yaran nan ragama yanzu suma suyi nasu".

A daren suka tara taron yayansu kaf har Amatullah, aka kira Hussain a Skype sannan Sumayya tayi musu bayanin abinda Ruqayyah ta rubuta da kuma ita abinda take tunanin hakan yana nufi. Tace "I may be wrong. Amma ina son ku hada kawunan ku a guri daya ku bincika maganar dan mu tabbatar da gaskiyar ta ones and for all" Hassan yace "Please, if he truly is alive, find him and bring him home" sai kawai ya kwanta a jikin kujera hawaye yana bin fuskarsa, abinda yayan basu taba gani ba.

Washegari Hussain yayi shiri ya taho Nigeria, sannan suka kuma haduwa sukayi bitar maganar kowa yana kawo shawarar sa ta yadda yake tunanin za'a yi, yayin da Sumayya kuma ta sake komawa gurin Ruqayyah da fatan ko zata kuma yi mata wani sign din amma babu, abinda Allah ya bata ikon yi kenan for now. Sauran aikin kuma nasu ne.

Abdullahi ne ya karbo musu police record na accident din, Aminu kuma a matsayin sa na maaikacin environment sai ya binciko musu dai dai spot din da akayi accident din, suka shirya gaba ki dayan su suka tafi gurin, da kyar suka samu an kaburburan duk sun shafe saboda shekaru, sai gwangwanin motar da suka gani a gurin wanda sun san da a cikin gari ne da tuni yan gwangwan sun dauke shi. Suka dauki gps din gurin sannan suka koma gida. Daga nan kuma sai suka satellite image na location din, suka saka gps din ya nuna musu exact spot din da suka je, sannan suka tuna cewa according to record din court, Ruqayyah tayi awa daya bayan anyi accident din kafin ta kira Hassan. A jikin satellite image din nasu suka yi mapping area din da za'a iya zuwa a kafa a dawo a cikin awa daya. A wannan area din ne Ruqayyah zata iya ajiye yaron ta kuma dawo gurin accident din kafin ta kira Hassan.

Bayan sun dauki circumference din gurin, sai suka fara bin features din da suka fada cikin cycle din nasu one after the other suna tattauna possibility din kasancewar a can aka ajiye shi. Mostly gurin daji ne sai duwatsu, sai wani kauye can da nisa wanda suka dauke shi a matsayin suspected point dinsu, har zasu rufe system din kuma sai suka lura da wani gini da yake can karshen circle dinsu, Hussain ya saka hannunsa yayi zooming hoton building din, sannan Yusuf ya karanta sunan da yake saman gate din. "National Orphanage......"

Bai karasa ba ya dago yana kallon yan uwansa, orphanage, of course orphanage is a perfect spot da za'a batar da jariri, babu wanda zaiyi cigiyar sa tunda kowa ya ganshi a kofar gurin abinda zaiyi tunani kawai shine uwarsa ce tayi cikin shege ta haife shi ta kawo shi nan ta ajiye.

Basa son su tayar da hankalin babansu dan haka basu gaya masa ba suka bar maganar a tsakanin su da niyyar gobe zasu tafi Abuja suje orphanage din gabadayan su zasu binciki maganar, duk da dai sun san in ma can ne aka ajiye shi to tabbas yanzu baya can din, koma a ina yake indai yana raye to yanzu ya zama cikakken mutum, maybe ma yayi aure, maybe ma ya haihu......

A ranar babu wanda yayi bacci a cikin su.......
Kamar yadda a ranar Amir ya kwana bai yi bacci ba saboda mafarkin da yayi........


*The Email*

Yayi juyi yana shafa empty space din kusa dashi sannan yayi tsaki. Sai yanzu ya tuno dalilin da yasa yayi wannan mafarkin, dalilin da yasa yayi mafarkin mahaifiyar sa. Da dare kafin ya kwanta sunyi rigima da matarsa, rigimar da ta saka har suka raba gurin kwana, abinda basu taba yi ba tunda suka yi aure kullum tare suke kwana in dai har suna gida daya.

Ya lumshe idonsa tare da sake karanto addu'ar bacci. Amma baccin da bai koma ba kenan. "What if it is not a dream but a memory?" Memory na ranar da mahaifiyar sa ta yar da shi. Memory na ranar da aka haife shi. Yayi ta kokarin ganin ta tuno da fuskar matar daya gani a mafarkin sa amma ya kasa.

A haka har assuba ta riske shi

Yayi juyi, tare da jan dogon tsaki. Ba zai iya tuna ranar da ya kwana tun daren Allah har safiyar Allah ba tare da ya ko da rintse idonsa da sunan bacci ba sai yau. Haushin A'isha yake ji dan yana ganin duk itace silar mafarkin sa. Me yasa? Me yasa zata yi masa haka? Me yasa zuciya take baci sosai idan wanda ta rike abin so ya kasance wanda yake bata mata?

Jin kiran Sallah ya saka shi ya mike ya zauna a bakin gado tare da dafe kansa da hannu bibbiyu, sara masa kan yake yi goshinsa yana barazanar tsagewa kwakwalwar sa ta fito. Jikinsa gabaki daya ciwo yake yi saboda kwana da yayi yana juyi,

Why?

Ya tambayi kansa a karo na babu adadi kuma duk da yasan cewa shi dai bashi da amsar tambayar tasa, bashi da amsa kuma bai san wanda zai amsa masa ba bai kuma saka ran cewa zai sami wanda zai amsa masa din ba.

Tunda ya bude idonsa a duniya ya fahimci shi din yana da bambanci da sauran yara amma bai fahimci menene bambancin ba. A lokacin da hankali ya fara shigar sa a lokacin ya fahimci banbancin ya samo asali ne daga bambancin asalinsa dana sauran yara amma kuma bai san asalin nasa ba ballantana ya gane a inda banbancin yake. Sai daga baya sannan kalmomin suka fara sinking a cikin kansa, gidan marayu, Maraya, dan tsintuwa, yasashshe, shege, marar asali, tsintacce. Wadansu kalmomin ma karamar kwakwalwar sa alokacin kasa dauka tayi sai daya hada da tambayar wadanda suka girme shi suka yi masa bayani inda a karshe suke hada wa da "kamar dai kai kenan"

"Amir in akace marar asali a na nufin wanda ba asan iyayensa ba ko kuma wanda ba'a san daga inda iyayensa suke ba, kamar kai kenan"

"Kalmar yasashshe tana nufin wanda iyayensa suka yar dashi saboda basa sonsa, misali jaririn da aka haifa sai uwarsa ta yar dashi ta gudu, kamar kai kenan"

"In aka ce shege Amir ana nufin wanda aka haifa ba tare da iyayensa sunyi aure ba, irin wadannan yaran ba'a san su dan sau da yawa akan jefar dasu dan gudun abin kunya, kamar dai yadda aka jefar da kai"

A lokacin abinda kansa yake dauka kawai shine duk wadannan kalmomin suna da dangantaka dashi. Sai da ya kara girma sannan takanas yaje office din shugaban orphanage din wanda yayi masa bayani sosai har ya fahimci cewa shi din uwarsa ta yar dashi ne a ranar data haife shi ba tare data ko tsaya ta yanke masa cibiya ba, ta hada dashi da mahaifarsa ta yar a kofar gidan marayu tsirara ko zani bata saka ta lullube shi ba.

Wannan ya saka dole yake amsa wadancan sunayen da ake kiransa dasu. Dole, tunda iyayen sa sun riga sun zabar masa Wadannan sunayen duk da cewa basu samu damar zabar masa sunan yanka ba.

Tun daga ranar daya fahimci wannan sai ya saka a ransa cewa yana son sanin dalili, ya saka a ransa yana son sanin iyayen sa dan ya kalli cikin idanunsu ya tambaye su "why?" Me


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login