Showing 246001 words to 249000 words out of 300844 words

Chapter 83 - Tagwaye Book 1 Hausa Novel Complete

22 Dec 2024

2044

da amsa ba amma sai ta dora wa Fatimah wayar a kunnenta. Yana jiyo sheshshekar kukan ta. Ya zauna akan kujera yana dafe kansa "ba na baki hakuri bane wai Zahra, menene kuma? Na janye magana ta yinda ba kya sona, please kiyi imagining cewa it never happened. Idan da nasan it will hurt you this much da ko maganar zata zama ajalina ba zan furta ta ba"

Yayi shiru yana ci gaba da sauraren yadda take rera kukan ta. Wata zuciyar tana gaya masa cewa ya dauki key din mota ya koma gidan yaje ya lallashe ta, the same zuciya da ta saka shi ya furta mata kalaman inda first place, amma yasan zuwan nasa ba zaiyi wani amfani ba tunda shine sanadin kukan nata, duk kukan kiyayyar sa ne wannan take yi da takaicin kamar sa yace yana son kamar ta. Yaji zuciyarsa ta yi nauyi a kirjinsa yace "nasan ban isa ba, it was an insult to you, I am sorry Fatimah me zan ce ne kuma ki daina kukan nan haka?"

Cikin karyayyiyar murya tace "stop talking like that. You are hurting my heart". Yaji wani sabon arrow wanda aka fara narka shi da wuta ya sauka a zuciyarsa. Yace "shikenan. In dai Adam ne ya daina yi miki magana balle ya bata miki rai. Kiyi hakuri". Sai ya kashe kira sannan ya saka wayar a flight mode ya ajiye ta sannan ya kwanta rigingine akan kujera, shi kansa bai san tunanin da yake yi ba. Amma yasan cewa tunanin Fatima tana can tana kuka shine a saman zuciyar sa. Sai kuma ya mike ya shiga daki ya jawo akwatin sa ya fara zuba kayan sa a ciki, he is going to take a break, dole zai dauki hutu a makaranta ma dan ko yaje ba gane mai akeyi zai ke yi ba.

Sai daya gama sannan ya dawo ya dauki wayar sa yayi booking next flight to Nigeria.

Kamar yadda yayi tunani Fatima kusan kwana tayi tana kuka da kunan zuciya. Har sai da Aunty Maryam bayan ta yi ta kiran wayar Adam har ta hakura bata shiga sai da tayi tunanin kiran likitan da Fatima take gani a garin, sai ya bata shawarar cewa ta rabu da itata barta tayi kukanta amma kar ta barta ita kadai a daki, ta saka su kwana tare da wani. Wannan yasa ta turo mata Firdausi, budurwar yarta tace su kwana tare, sannan ga little Hussain Wanda dama tare suke kwana.

Sai da tayi kukanta ta gama sannan ta tashi ta wanke fuskarta, a lokacin har Hussain ya gama nasa kukan yayi bacci a jikinta, ta gyara masa kwanciya sannan ta jawo akwati ta fara zuba kayan ta a ciki, she is going to take a break, Nigeria zata ta fi ta dan sha iska kadan. Amma a zuciyarta tana lissafin can she really spend some days ba tare da ganin Adam ba? Ba tare da ji daga gare shi ba? Dan tasan yayi fushi, daga jin yadda yayi mata magana yayi fushi ba lallai ne ya kuma yi mata magana ba ma in ta duba yadda ta rufe ido tayi turning down proposal dinsa, kuma ta fahimci irin fahimtar da yayi wa answer din tata, gani yake yi dan bai isa bane ba, ita kuma ta san ya isa in every way kawai dai she can't.

Tun ranar da ta tabbatar da mutuwar Hussain da kuma bata jaririnta ta riga ta tsayar da zuciyarta akan cewa ba zata cigaba da rayuwa ne kawai dan dai bata da ikon katse rayuwar ta, zata jira har lokacin da kwanakin ta na duniya zasu kare ta tafi gurin mijin ta da ɗan ta. Dan haka ita ko a zuciyarta bata taba kawowa zancen soyayya ba ballantana aure, bata taba tunanin cewa wai ko tana son Adam ba ko kuma wai shima yana son ta. Sai yanzu, sai daya fada mata three words din, sannan ne tayi realising abinda yake faruwa. And her heart hurts, ji take yi kamar zata tarwatse.

Taji ta tsani kanta akan abinda tayi wa Adam amma kuma wani bari na zuciyarta yana gaya mata cewa it is for the best. But can she? Ita ba zata iya moving on ba dan rayuwarta ta kare a ranar da aka saka Hussain a kabari amma dole tasan shi Adam zaiyi moving on komai daren dadewa, amma kuma wani part na zuciyarta baya so yayi din. And she hates herself for being so selfish.

A duk tsahon shekaru goman nan da Hussain yayi a kabari babu wanda ya taba yi mata zancen aure har iyayenta, dan haka ita gabaki daya a ranta ta gama saddakarwa cewa kowa ya fahimci manufarta. And then Adam came with his three words. "Darling, I love you" he said. Ta zauna tanadafe zuciyarta, the words remind her so much of Hussain, sai taji kamar shi yake fada mata. Wannan kuma shi ya dawo mata da mutuwar sa sabuwa a zuciyarta. Dole ta tafi kano, maybe ganin iyayen ta ya danyi cooking dinta down, kuma ta fara practicing rayuwa without Adam.

But his ring is soooo beautiful, his words soooo touching. Poor Adam..

Sai data gama hada kayan ta jaka daya na little Hussain a wata jakar sannan ta dauko wayarta tayi booking next flight to Nigeria.

Da sassafe ta tashi, tayi wanka ta tashi little Hussain tayi masa wanka tana cikin taimaka masa gurin shiryawa Aunty Maryam ta shigo dan ganin yadda ta kwana. "A'a Fatima? Unguwa zaku je ne haka?" Fatima ta zauna tana kallon ta da kumburarrun idanuwan ta tace "zamu je Nigeria ne Aunty" Maryam ta zauna tana kallon ta "lafiya? Tafiya lokaci daya? Me za kuyi a gidan? Wani abin ne ya faru Fatima?" Sai Fatima ta zauna a bakin gado, hawayen ta na jiya suna sake dawowa, Maryam tace "ikon Allah, Fatima lafiyar ki kuwa" ta fada tana tura Hussain waje dan su samu suyi magana

"Gaya min, me ya hada ki da Adam jiya, lafiya lau kika fita raka shi kuma kika dawo kina kuka?" Fatima ta share hawayen ta, a hankali tace "cewa yayi yana sona wai, wai zai aure ni yace" Maryam ta zauna a kusa da ita tana dafa kafadar ta, "shine dalilin wannan kukan Fatima? Har kika saka yaron nan ya zauna shima yayi ta rusa kuka kamar ance babansa ya mutu? To ai ni na dauka already kun gama wannan maganar da Adam din ai" Fatima tace "wacce maganar?" Maryam tace "maganar auren mana, ni ai na dauka karatu yake jira ya gama ko dai wani abu daban" Fatima ta rike fuskar ta tace "aure fa Aunty? Aunty aure fa kike cewa kin dauka zanyi? Ni ya zanyi inyi aure kuma?" Maryam ta bude baki cikin mamaki "to ke me kike nufi da? Kina nufin haka zaki yi ta zama ba zaki yi aure ba? To shi Adam din da duk bata masa lokaci kike yi ko me?"

Fatima tace "Aunty babu komai fa a tsakanin mu wallahi" Maryam tace "babu komai a tsakanin ku kuma kika ce yace zai aure ki? Sannan kuma kika zo kika zauna kike kuka saboda yace yana sonki? Fatima, you are just confused. You don't know what you want. Bazan ce na fahimce ki ba saboda ban taba shiga irin halin da kike ciki ba a yanzu, amma abinda na sani shine abinda kike cewa bazai taba jiyuwa ba, wai ki zauna ba tare da kin kara aure ba, kin san wannan ba zai yiwu ba Fatima, ba za'a taba barin ki a gida ba. Yanzu ma da kika ga anyi shiru an saka miki ido to duk saboda ana saka ran cewa zaku daidaita da Adam ne, mu jira kawai muke yi kuce mana kun shirya mu saka rana"

Fatima ta mike ta fara zagaya dakin "ba zan iya auren Adam ba Aunty, ki taimaka min kiyi musu bayani a gida, ba zan iya auren Adam ba dan Allah" Maryam ta mike itama tana kallon ta da mamaki "saboda me? Me yayi miki da zafi haka? Mu muna ganin cewa babu wanda ya dace da auren ki sama dashi" Fatima ta tsaya a tafiyar da take ta juyo tana kallon Maryam "Aunty, babu abinda yayi min Adam, he is just too good for me, I don't want to hurt him. Duk wanda na aura will end up heartbroken, I don't want it to be Adam".

Sai Aunty tayi murmushi tace "shi yasa nace, you are just confused" sai ta mike, "ba zan hana ki tafiya gida ba, amma Hussain ba zai biki ba, yana school, in kin dawo kafin suyi hutu to, in kuma baki dawo ba in anyi hutu sai a turo miki shi". Ta juya ta fita.

Fatima ta tsaya tana bubbuga hannayenta together, wai da gaske maganar maganar Aunty na cewa duk family sun dauka aure zasuyi da Adam gaskiya ne? Ta sake girgiza kanta. She can't, she can't marry Adam. Yadda tayi breaking heart dinsa ma jiya kadai ya isa ba sai ta cigaba ba, he doesn't deserve that. He doesn't deserve her. Saboda ita zuciyarta a cike take taf kuma a rufe take da padlock..

Bata fasa tafiyar ba duk da Aunty tace ba zata tafi da Hussain ba, amma kuma tana tunanin yadda zata iya zama a Nigeria babu Adam babu Hussain. Ta dan je airport late, saboda rikicin da Hussain ya saka cewa ba zata tafi ta barshi ba. Tana zuwa ta karbi boarding pass dinta taga seat number 25b, ta tafi da sauri ta shiga tunda already passengers din sun kusa gama shiga, ta duba seat dinta blindly va tare da ta lura da waye a seat din kusa da ita ba ta zauna tae da sauke ajjiyar zuciya tana rufe idonta.

Adam ya dago kansa daga karanta jaridar da take hannun sa saboda kamshin turare da yaji irin na Fatima a kusa dashi. Ya kalli side din da yaji alamun an zauna, and there she is, ya ajiye jaridar "Fatima?" Ya fada cikin mamaki, ta juyo da sauri saboda jin muryar sa da tayi tana kallon sa "Adam? Me kake yi anan?" Yace "me nake yi anan ko ke me kike yi anan?" Tace "gida zan tafi in dan huta, kai fa?" Yace "nima gida zani in huta" suka yi shiru, sai yace "so... saboda ba kya ma son ganin fuskata shine zaki bar gari ko? Da kinyi zamanki ma, ni zan bar miki garin. Abinda na fada jiya shine abinda yake cikin zuciyata tabbas babu kuskure a ciki. Kuskuren shine furta miki da nayi, kamata yayi in shigaba da rikon abina a raina har zuwa kabarina. Once again am sorry. Zaki iya sauka kafin su rufe kofa"

Tana girgiza kanta tace "ni zan baka hakuri Adam, laifi nane ba naka ba. Ni ce mai matsala ba kai ba. Ina kuma ba ka hakuri akan yadda matsala ta ta shafe ka. Kayi hakuri Adam, Please kayi hakuri" ta fada a lokacin da jirgin yake tashi dasu, bai ce mata komai ba har sai da jirgin ya daidaita a sama sannan sai ya mike, ba tare da yace mata komai ba ya bar gurin. Ita a tunanin ta rest room ya tafi dan haka sai ta mike ta dauki jakarta da ta bar seat din da niyyar in ya dawo ya tarar bata nan. Shi kuma Adam niyyar chanja seat dama yayi, sai ya hango wani seat da babu kowa na kusa dashi ma babu kowa, sai ya tafi can dan baya son ya zauna a kusa da wani yayi masa magana, so yake yaji da ciwon da zuciyarsa take yi masa, musamman saboda ganin ta da ya sake yi. Ya zauna tare da reclining seat din sannan ya cire hular kansa ya rufe fuskarsa da ita tare da rufe idonsa.

Bai fi minti daya ba ya kuma jin kamshin taa kusa dashi, ya cire hular yana kallon gefen sa da sauri, ita ce a zaune tana waigen seats din da suka baro. Yayi murmushin takaici "are you following me?" Ta dan zabura kadan tare da kallon sa, sai kuma ta fara hawaye, haka take kamar baby, magana daya kuka musamman duk sanda take emotional. "Wallahi ba binka nake yi ba, can seat din na bar maka na dauka zaka koma can ne" a lokacin wata attendant tazo, tana kallon Fatima da take share hawaye tace "are you okay Madam?" Adam yayi saurin cewa "she is fine. Thank you" matar ta gyada kai sannan tace "what will you like, tea or coffee" yace "tea for her and coffee for me".

Sai data tafi sannan yace "kiyi hakuri ki daina kukan nan haka. Zan bar miki nan din ma. Kiyi zamanki anan kinji?" Ta goge hawayen ta. "Kar ka tashi, ka zauna Please. Ina so muyi magana dan Allah. Ina so mu fahimci juna Adam bana son yadda na fahimci tunanin ka ya karkata akan maganar nan, you are making it harder than it should be" ya karbi drinks din da aka kawo musu ya kurbi coffee dinsa yace "menene nake tunanin ke kuma me kike nufi" tace "bansan cewa abinda ka dauki alakar mu ba kenan Adam, da na sani da tuni na gaya maka cewa ni ba haka na dauke ta ba. You mean so much to me Adam. But I can't marry you"

Yace "saboda me?" Duk da a ransa yaji baya son jin amsar, duk kuwada cewa daga jiya zuwa yau ya lissafa dalilai kusan cikin charbi na abinda ya sa Fatima ta ki shi. Amma sai yaji ta tsallake duk wadancan dalilan nasa tace "saboda bana jin zan iya samar maka da farin cikin da ka yi deserving a rayuwa. I am not the one for you. I can't replace Hussain with you, it is not fair for both of you" yace "and I don't want you to replace Hussain with me. I can't replace him no matter how much I try, saboda ni ba Hussain bane ba and I can never be, ni Adam ne. Kowa a cikin mu daban yake. Bance ki cire shi a ranki ki saka ni ba, ban kuma ce ki dora ni a space dinsa ba, abinda kawai nake so, nake roka a gurin ki shine ki bani nawa space din a zuciyar ki komai kankantarsa, in dan samu in rakube ko ba zai ishe ni zama ba zan iya tsugunnawa in dai har a cikin zuciyarki ne" ta girgiza kanta "but it is not fair, you don't deserve that. Kana bukatar fresh zuciyar da babu kowa a cikinta inda zaka kafa kingdom dinka ka sake kayi abinda kake so kai kadai. Ita kake bukata ba tawa ba"

Sai yayi murmushi yace "kin manta da cewa da Adam kike magana ne? Adam din daya ajiye iyayensa da dukiya da motoci da karatu for something da zuciyarsa take so? Ya tafi yake squarting a dakin abokai yana driving taxi saboda ya samu abinda yake so. Ke nake so, and that's all that matters to me" ta sake girgiza kai "ba zaka fahimta ba Adam, yanzu kake tunanin haka amma ba haka bane ba, ba zaka fahimta ba, sai nan gaba zaka fahimci cewa you deserve someone better than me. Please Adam don't make this harder than it already is, please accept my decision"

A haka suka iso Nigeria.

Ta riga tayi waya gida an san da zuwan ta, dan haka tana sauka ta tarar da mota tana jiranta, ta shiga suka tafi amma Adam sai yaki shiga ya dauki taxi, a ransa yana jin cewa ba zai zauna ma a fadar ba, daga yaje ya gaishe su zai tafi Kaduna gidan Baba yayi zamansa a can. Dan ya daina ganinta yayi wannan tafiyar amma kuma gata yadda ta kasance, ba zai ke tubka tana yi masa warwara ba dan in dai har yana ganinta to cire ta daga zuciyarsa zaiyi masa matukar wahala.

Amma sai dai ana sauke ta shima yana shigowa, dan haka ganin natan dai da baya son yi sai da yayi din. Sai yayi zamansa a mota yaki fitowa amma duk da haka bai dauke idonsa daga kanta ba har sai data shiga ciki sannan ya fito shima ya bayar aka shigar masa da kayan sa ciki.

Fatima tana shiga gurin Hajiya Fulani da murnar ta ta gaishe ta sai tambayeta "ina Adam din? Ki kira shi yazo yaci abinci ko waje za'a fitar masa dashi?" Sai tayi shiru a ranta tana mamakin yadda automatically Hajiya tayi tunanin tare suke da Adam, ba zata iya tahowa ita kadai ba sai tare da shi? Taso ace ba taren suke ba dan ta ga reaction din hajiyan, amma kuma yanzu sai Tace "yana waje, maybe yana gurin da yake sauka in yazo. Sai dai a aika masa" daganan taga Hajiya ta saka an fara hidimar shirya masa abinci, ita ko abincin ma baay bata ba.

Takaicin wannan ya saka ta mike ta tafi part din Hajiya Ummah ta gaishe ta. A can ta samu ta zuba abinci taci ta koshi, amma still sai taji Hajiya Ummah ita ma tace "ina Adam? Ya karatun nasa? Na ga dai alama sai yaga karshen biro da takarda tukunna za'a yi auren nan"

Let's rest here for today....

Team Adam and Fatimah together ina gaisuwa
Team Adam and Fatimah seperated I salute you


*Re-Married*

Ta bude baki "aure kuma Ummah? Auren wa kike fada?" Hajiya umma ta juyo tana kallonta tace "in ina maganar Adam auren wa nake nufi kenan? Sai na fito nace auren Fatima sannan zaki gane?" Ta ajiye chokalin hannunta. "Ummah! Ni bansan waye yace aure zamuyi da Adam ba, ni ban san waye yace aure zanyi ba" Hajiya umma ta bita da kallo "ba aure zaki yi ba me zaki yi kenan? Zancen banza kenan kike yi ai. Dan kinga Takawa ya daga miki kafa to wallahi alkunya yake yi miki sosai da sosai saboda yana ganin irin abubuwan da kika yi going through amma shekara goma Fatima ba kwana goma bace ba, duk cikin mu babu wanda ma yayi tsammanin za'a barki ki shekara goma ba tare da kin sake aure ba"

Fatima ta ajiye spoon din hannunta. Daga

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login