Showing 273001 words to 276000 words out of 300844 words

Chapter 92 - Tagwaye Book 1 Hausa Novel Complete

22 Dec 2024

2096

irinsa a cikin ku " Hussain ya girgiza kansa yace "babu, shi din na daban ne, special ne" ya kuma goge hawayen ta "ya jima yana neman ku, me yasa baku neme shi ba sai yanzu?" Yusuf yace "rashin sani Baba, bamu san yana raye ba da ko gida gida zamu bi a abuja sai munbi mun nemo shi" Baba Asabe ta kuma cewa "bata gaya muku ta yar dashi ba kenan, wannan wacce irin muguwar uwa ce haka? Amma dai ku baku yi kama da mugaye ba, amma dai ba ita ta raine ku ba ko?" Hussain yace "ba ita bace ba, ba kuma ita ta haife shi ba, sace shi tayi daga hannun wadda ta haife shi ta kawo shi nan ta yar".

Sai gurin yayi shiru, gaba daya jinjina girman laifin Ruqayyah suke yi, "ina yake yanzu" Abdulrahman ya sake tambaya yana kallon Madam Merry, ta jawo wani file gabanta tace "akwai address dinsa anan da phone number dinsa da komai, duk sanda ya kawo donation muna rubutawa" Hussain ya mika hannunsa da sauri amma sai ta janye file din tace "amma ba zan baku ba" gaba-daya suka hada baki "why?" Tace "saboda haka dokar mu take, for security purposes, ba wai bamu yarda da ku ba dan kamannin ku kadai sun tabbatar mana cewa ku yanuwansa ne, amma still we gave to be careful" Yusuf yace "to amma in baku gaya mana inda yake ba ta yaya zamu same shi?" Tace "a ka'ida sai mun nemi izinin sa kafin mu gaya muku komai a kansa, shi zai yanke shawarar in yana so ya ganku ko kuma in baya so ya ganku" Hussain yace "amma kince last week ma yazo nan yana tambayar ko anzo neman sa, meaning yana son ganin mu kenan"

Tace "still dole mubi protocol" sai ta dauko wayarta tana dialing number, duk zuciyoyin suna bugawa da karfi sanin cewa number dinsa take dialing, suna jin karar ringing din daga inda suke har suka ji karar wayar ta katse bai dauka ba, ta sake kira still bai dauka ba. Hussain ya gyara zamansa "zamu jira, in yaga kiranki ai zai kira back ko?" Tace "eh zai kira" Abdulrahman yace "then we will wait"

Sai Yusuf ya juya yana kallon Baba Asabe yace "ki bamu labarin sa mana, ya yake? Ya Rayuwar sa take tafiya? Ta danyi murmushi tace "fitinanne ne, baya jin magana" sai suka yi murmushi gabaki daya, Madam Merry tace "he had had a rough life, a good life kuma" Baba Asabe tace "har zaman gidan kangararru yayi. Amma kuma america yayi karatun sa tun daga secondary har masters" Hussain yace "america?" Tace "eh. Ai shekaru hudu kawai yayi a tare damu anan, sarkin Abuja ne ya dauke shi daga hannun mu, ya gada shi tare da jikansa ya rike su tare" Yusuf yace "sarki Sadiq?" Tace "aa babansa, babansa, shi yayi masa yanka ai kuma ya saka masa sunansa" Hussain yace "Abdullah" he just can't wait ya bawa Fatimah duk wadannan labaran. Bai ma san ta inda zai fara bata labarin ba, ko kuma ya bari sai shi wanda aka kira da Amir din yaje har gabata sai ya bata labarin da kansa? Yes, haka shine ya dace.

Abdulrahman yace "amma yanzu how is he?" Madam Merry tace "very good. Yayi aure, yana running a private company" sai duk sukayi murmushi hankalin su yana kara kwanciya, at least sun san cewa bai tagayyara ba, at least yana yin rayuwa mai kyau duk da dai sun san cewa abinda Ruqayyah ta dauke a cikin rayuwar sa ba zata taba iya dawo masa da shi ba.

Ta sake daukan wayarta ta kuma kira, still babu ansa, sai kuma data kuma kira taji a kashe. "Dan Allah" Hussain ya roketa, ki gaya mana inda zamu same shi" ta yi shiru tana binsu da kallo daya bayan daya tana deciding ko da karya doka a kansu. Fuskokin su cike da dokin ganin dan'uwan su, sai ta jawo wata takarda a gefe tayi rubutu a ciki ta mika musu. Yusuf ya karba yana dubawa, e-mail address ne a jiki, tace "e-mail dinsa ne, kuyi contacting dinsa, shi zai yanke shawarar in yana son ganin ku or not"

Hussain ya fara kokarin nuna kin amincewa da hakan, shi gani yake tunda gasu a Abuja kuma shima ance yana abujan nan me zai saka su tafi gida basu ganshi ba? Amma sai Yusuf yayi musu bayanin da cewa hakan is the best, sun san yana nan kuma yana lafiya, sun kuma samu e-mail address din sa, that's more than abinda suka saka ran samu. In suka je gida suka hadu da iyayensu da sauran yan'uwa sai suyi maganar best way da zasu yi contacting din sa.

Bayan sun bar orphanage din suka je gidan Aminu, wanda shi yana Kaduna a lokacin amma iyalin sa suna nan suka ci abinci suka yi sallar sannan suka kira waya Kaduna suka bada labarin information din da suka samu. Sai dai sunyi shawarar kar a gaya wa Hassan "zai iya dauko mota yanzu ya taho Abuja har fadar sarki ko ya fara bi yana knocking gidajen mutane yana neman mai suna Amir" Hussain yace "that's not a bad idea though, muje fadar, a can zamu samu duk bayanan sa da muke bukata, ko kuma ma mu ga shi a can din, yanzu haka ma maybe yana can as muna wannan discussion din" Yusuf yace "I know, but kamar yadda matar nan ta fada, mu fara contacting dinsa first mu kuma nemi iznin ganinsa daga gurinsa tukunna, mu bi komai a sannu insha Allahu zamu samu maslaha" haka suka dauki hanya suka koma Kaduna.

Suna isa Kaduna suka sake wani zaman, yanzu harda Sumayya da Hassan suka kuma fayyace musu duk abinda suka yi finding a Abuja. "Maybe ba shi bane ba. Tunda basu rike date din ba kuma babu file" Hassan ya fada, wata zuciyar tana gaya masa ya tafi a Abuja a daren nan yaje ya makure wannan Madam din har sai ta kai shi inda dan Hussain yake. Hussain yace "Daddy shine, yadda matar nan tayi reacting kadai ya tabbatar mana da cewa shine" Hassan ya juya kan Sumayya yace "har yanzu bata kuma rubuta komai ba?" Tace "bata rubuta ba" suka mika masa e-mail din. "Yanzu abinda ya kamata muyi shine mu aika masa da sako mu nemi yazo nan ko kuma ya bamu izinin zuwa can mu same shi, anan zamu tabbatar da cewa shine ko kuma ba shi bane ba"

Hassan ya kalli Hussain yace "kar ka gaya wa Fatima komai" ya gyada kai cikin fahimta. Sannan Hassan ya mike da takardar a hannun sa ya hau sama. Ranar ko saukowa kasa cin abincin dare bai yi ba. Sumayya ita ma ta samu ta ja jikinta ta bi mijinta dan taga alamar su yaran ba yanzu zasu tashi daga zaman ba, da plans kawai suke tayi na irin taryar da zasu yi masa idan yazo da yadda zasu yi ta yawo dashi suna nunawa mutane.

A zaune ta tarara da Hassan ya saka computer a gaba amma hankalin sa baya kanta, sai da tayi waving hannunta a kusa da fuskar sa sannan ya juyo yana kallon ta, ta zauna a kusa dashi tana matsa masa hannun sa tace "shi yasa su ka ƙi gaya maka maganar nan tun jiya, sun san tayar da hankalin ka zakayi akan maganar" yace "dole in tayar da hankali na Sumayya, kin fi kowa sanin matsayin yaron nan a gurina. Gidan marayu fa akace ya tashi fa Sumayya, dan Hussain, his only son, the sole heir to H and H" ta girgiza kanta tace "amma kuma sai suka ce ya tashi a gidan sarautar Abuja, yayi karatu a america, yanzu kuma yana running private company" yace "not his father's company" yace "haka ne, amma ba'a titi yake yana bara ba, ko a bola yana shaye shaye. Bana son kana saka damuwa a ranka, in kana cikin damuwa gabaki dayan mu ni da yara ba zamu kasance cikin farin ciki ba" ya kirkiri murmushi yayi mata yace "na sani, kuma na gode Allah da duk ni'imomin sa gare mu da kuma gare shi shima. Ina tsoron kawai kar ya zamanto bashi bane ba, bana jin zuciya ta zata iya dauka" tayi murmushi tace "Habibi, zuciyarka is stronger than you think, ta dauki abubuwa da dama a lokacin da kake tunanin ba zata iya dauka ba. Amma insha Allah, wannan ba zai zama daya daga cikin su ba" sai ya bude takardar yace "me zance mishi?" Ta karba tana dubawa tace "ka bar min, ni zan tura masa da sakon, zan san abinda zan gaya masa" ya gyada kai yace "shikenan, na gode Sumayya, Allah yayi miki albarka".

Da kyar ya samu yayi bacci a ranar, amma ita kuma bata yi baccin ba tana ta tunani akan maganar, akan wannan yaron da aka kira da Amir da kuma irin girman laifin da Ruqayyah ta aikata masa. Bata jin hakkin sa zai bar Ruqayyah tayi kwanciyar kabari lafiya ballantana kuma in an tsaya hisabi a tsakanin su, tana so ta taimakawa yar uwarta in any way that she can indai har taimakon nata ba zai kaucewa iyakar ubangiji ba. Menene ya kamata tayi?

Tabbas dawowar Amir gida wani abu ne da zai rage nauyi daga cikin nauye nauyen da suke kan Ruqayyah, amma babu guarantee din in ya dawo din zai yafewa Ruqayyah, but she is going to try, duk da bata san halinsa ba bata san irin zuciyarsa ba amma tasan Hassan yana da zuciya amma ganin irin yadda Allah ya matar da Ruqayyah kawai ya saka yace ya yafe mata da bakinsa ba tare da kowa ya matsa masa ba. Maybe, just maybe shima wannan yaron ya kasance haka. Maybe in ta samu hanyar da zata fara hada shi da Ruqayyah first, ya fara jin labarin Ruqayyah da laifin data aikata gare shi da kuma irin sakayyar da Allah ya fara yi masa tun few minutes bayan ta aikata masa laifin da duk irin masifun da ta ringa gamuwa dasu through out all these years, maybe hakan ya sanyaya zuciyarsa a kanta.

In yaji labarin ta kuma sai ya ganta a zahiri, yaga yadda Allah ya mayar da ita saboda hakkinsa......................,waya sani ma ko ya taimaka gurin bawa Fatima hakuri? Amma ita kanta tasan she is asking for too much. Amma tausayin yaruwarta take yi, tun ranar data rubuta he is alive da hannunta take kwana ta wuni taba hawaye, yau ma wuni tayi tana hawaye, sautin kukan ma babu, hannun da zata share hawayen nata dashi ma babu, tayi ta tambayarta inda ta ajiye babyn tana kuma lura da yadda take stressing kanta gurin kokarin fada, gurin kokarin rubuta wa da hannun ta amma ta kasa.

Bata da sauran hanyar da zata bi gurin neman gafara, sai dai mutum in ya ganta shi da kansa imani ya saka yaji ya yafe mata kamar yadda Hassan yayi, dan haka ita Sumayya zata zama bakinta, ita zata nema mata gafarar ko da kuwa zata kaita ga durkusa wa ne ko kuma birgima a kasa. Ta tashi ta koma kan study table din Hassan ta kunna reading lamp, sannan ta jawo drawers din da suke gefe ta binciko wani littafi sabo babu rubutun komai a kansa, ta dauko biro tana jujjuya shi a hannunta sannan ta fara rubutu.

"Sunana Ruqayyah, wannan shine labari na".........

Tun daya yarintarsu ta fara bayani, da kuma abinda ta sani na daga yarintar su Hassan da Hussain. Labarin haduwar su da Hassan da kuma labarin aurensu. Komai har zuwa mutuwar Hussain da kuma accident din da sukayi, haihuwar da Fatima tayi a gurin accident din da kuma yar da babyn da Ruqayyah tayi. Sannan ta dora da labarin abubuwan da suka faru bayan nan.

Har saida aka fara kiran sallar asuba sannan ta tashi, ta rufe littafin ta boye, bayan Hassan ya fita masallaci sai ta tashi tayi sallah itama sannan ta dauko wayarta ta shiga e-mails ta saka address din Amir sannan ta aika masa da sako kamar haka

"Assalamu alaikum wa rahmatullah. I may be wrong but I think you are the person am looking for. Ina da labarin da zan baka, a story concerning your parents"

Sai ta saka address din gidan da Ruqayyah take sannan ta tura masa.



*The Book*

Amir ya je ya dauko Aisha kamar yadda ya fita da niyyar yi, sai dai yau din ya lura da chanje chanje a tare da ita, na farko yau malamin ta da tace ba saurayin ta bane ba, wanda ya saba rako ta kullum zuwa mota yau bai zo ba. Na biyu kuma ya lura gabaki daya kamar yanayin ta bashi da dadi, shima kuma nasa yanayin babu dadi dan haka tafiyar tasu ta zama shiru, sai daga baya yayi breaking silence din ta hanyar tambayarta abinda yake damunta sai kawai ta kama yi mishi kuka, ta tsaya a gefen hanya ya barta ta gama kukan ta sannan ta fara yi masa bayanin irin problem din da take ciki na rashin matsaya akan wanda ya kamata ta tsayar a matsayin miji. Ta bashi labarin dukkan maneman ta da rawar da kowanne ya taka a cikin rayuwar ta.

Sai yaji tausayin ta, yaji cewa kamar neman aurenta da yake yi suima wani karin nauyi ne a gurinta tunda yasan tana ganin mutuncin sa sosai, maybe shi yasa har yau ta kasa bashi amsar tayin soyayyar da yayi mata. Sai yaji a ransa kamar tana gaya masa haka ne dan ya fahimci cewa ba zata iya karbar tayinsa ba, and for some unknown reason sai yaji hankalin sa ya kwanta da decision dinta. Amma daya tambaye ta game da malamin ta da yake rakota mota sai ta ce masa kawai friend dinta ne tun na shekara da shekaru, da haka ya kaita gida, cikin palace, gidan abokinsa Sultan inda anan ne take zaune a lokacin. Suka yi sallama ta shiga ciki shi kuma ya koma da niyyar zuwa asibiti gurin Dr Maimoon matar Sultan kamar yadda yayi niyya, sai daya je kofar asibitin sannan ya fara neman wayarsa zai kira ta sannan ya fahimci cewa wayar bata tare da shi, maybe a office dinsa ya barta. "Damn it" ya fada yana dan dukan stirring kadan, ya fita ya shiga asibitin sai aka tabbatar masa da cewa ta koma gida tun dazu, dole ya sake kunna mota ya koma office dinsa, a nan ya tarar wayar har ta mutu, maybe anyi ta kiransa ne shi yasa battery din yayi running down.

Daga nan sai ya saka phone din a charge sannan ya sake fita ya nemi abinci yaci, har lokacin lunch ya wuce amma shi ko breakfast bai yi ba, abincin ma babu dadi, ko dan zuciyarsa babu dadi ne? Sai daya gama sannan ya dan karasa aikin da yake gabansa a office din, akwai fita field daya kamata yayi amma sai yaji ba zai iya ba maybe sai gobe, dan haka ya tattara abubuwan sa ya dauki wayarsa ya fita, yana tunanin abinda zai tarar a gida, wata zuciyar tana gaya masa ya tafi palace kawai gidan Sultan yayi zamansa a can sai dare ya koma gida, ya samu ma Dr Maimoon ta duba shi a can, amma kuma sai yaga hakan ba dai dai bane ba tunda Aysha ta sauko ta bashi hakuri kuma ya kamata shima yayi meeting dinta halfway sai du bawa juna hakuri, amma sai ya tabbatar cewa ba zata kuma gaya masa magana irin wannan ba ko ba da shi ba ko dan ƴaƴan su, kar ta fada watarana a gaban ƴaƴan su.

Yana packing ta fito bakin kofa ta tsaya, hannunta na dama dauke da Afnan hannun hagu kuma rike da Sultan. Duk sunyi kyalliya sunyi kyau abinsu kuma sun taba zuciyarsa sosai amma sai ya maze yana muzurai irin shi mai gidan nan, Sultan ya taho da gudu ya tare shi yana masa sannu da zuwa sannan yace "Abhi munyi maka cake ni da Ammi, mun rubuta maka we are sorry a jikin cake din" yace "kun kyauta, yayi kyau" sai kuma yaron ya tambaya "laifin me muka yi maka ne wai Abhi da muke baka hakuri?" Sai ya samu kansa da yin murmushi tare da rije kugu yace "kai baka san kayi laifi ba amma kake bada hakuri?" Aysha ta karaso inda suke tsaye tace "ni ce nayi laifin, ni nake bada hakurin, shi kawai taya ni yake yi ban sani ba ko zanci albarkacin sa?" Ta karasa tana langwabe kai, ya kankance ido yana kallon ta ita kuma ta sunkuyar da kai, sai ya mika mata jakar hannun sa, ta karba da sauri shi kuma ya karbi Afnan yana manna mata kiss a lips dinta, suka jera zuwa cikin gidan tana cewa "ka hakura?" Yace "tukunna dai".

Haka suka matsanta masa sai da ya yanka cake duk da ba birthday dinsa bane ba kuma anniversary din auren su bane ba, kuma dole sai da suka saka shi yayi dariya, shi dama mutum ne da ba wai iya hade rai yayi ba. Sai da yayi wanka ya kwanta ya dan huta sannan suka fita masallaci suka yi sallar magrib shida Sultan sannan ya dawo ya tarar tana setting table, ya zauna kenan Afnan ta fara rigima, ya tashi ya dauko ta yana rocking dinta a hannayensa, sultan yana kallon su sai ya kwashe da dariya, Aysha ta juyo tana taya shi dariyar, Amir ya tsaya yana kallon su "wa kuke yiwa dariya?" Ta rufe baki "ni babu ruwana fa, Sultan ne" ya juya kan Sultan "wa kake yiwa dariya?" Ya sake dariya "yar fara na gani da ɗan baƙi" Amir ya dan bata ransa yace "kai! Waye baƙin? Kasan dai nafi Ammin ka fari ko?" Tana aikinta tace "a hakan dai aka gani akace ana so"

Sai yayi murmushi, ita kuma taji dadin murmushin da yayi. Ta gama shirya komai sannan tazo ta karbi babyn daga hannunsa ta zauna tana feeding dinta shi kuma ya fara cin abinci shi da Sultan suna ta hirar su kamar abokai. Sai daya


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login