Showing 93001 words to 96000 words out of 300844 words
dai zata iya yaudarar criminals kamar wadannan in minutes ka gaya min dalilin da zai sa ba zata iya yaudarar ka ba. Ka gaya min idan har sun fada ramin data gina a cikin mintuna kai me yasa ba zaka iya fadawa ramin da take kwana take wuni tana gina maka ba?"
Hassan ya mike "ya ishe ka, ya ishe ka. My God, matata fa kake magana akai. Uwar yaya na" Hussain ya mike yace "wannan shine abinda yake rufe maka ido, ina fatan kuma ba zai makantar da kai nan gaba ba" Hassan yayi hanyar fita da sauri, Hussain yace "hey bro" ya juyo yana kallon sa bai ce komai ba, Hussain yace "Please in ka hadu da Mr Careful ka gaya masa ina bukatar taimakon sa. Cos you are no longer him".
*My Better Half*
A palo Hassan ya tarar da Ruqayyah da Sumayya suna ta hira suna dariya, suka yi masa sannu da zuwa ya amsa musu sama sama ya wuce dakinsa, Ruqayyah tabi bayansa da kallo sannan ta tabe baki tace "mutum yayi ta kumbura shi kadai kamar ana saka masa yeast? Ni wannan ban san wanne irin mutum Allah ya hada ni dashi ba" Sumayya tace "ko ma dai menene dai mijinki ne shi, kuma mijinki ya dawo gida kamata yayi ki tashi ki bishi in yaso ko ma menene yake damunsa sai kiji daga can" Ruqayyah tace "ke ni fa ba zan iya da wannan fushin nasa ba, sai inje inyi ta faman lallashinsa kamar wani jariri bayan ni ba dani yayi fadan sa ba?" Ta koma ta kwanta tace "shi da dan uwansa ne, babu ruwana ni ai ance babu kyau shiga tsakanin yan uwa. Suje su kare kalau" Sumayya ta zauna tana nazarinta tace "ya akayi kika san shida dan uwansa ne? Anya kuwa kina da gaskiya Rukayya? An ya bake kika hada su ba?" Ruqayyah ta ajiye wayar hannun ta tace "ke fa kullum kamar ba nice yar uwarki ba ba kya kyautata min zato wallahi. Ni bani na hada su ba, ni ba dashi naso in hada su ba Allah ne kawai ya kawo Hussain din ya shiga maganar".
Sumayya tayi shiru tana nazarin ta sannan tace "gaya min gaskiya Ruqayyah, menene gaskiyar abinda ya faru dazu?" Ruqayyah ta kalle ta, tunda suke bata taba boye mata kaifi idan tayi duk kuwa da tasan cewa zata yi mata fada amma yanzu anya zata gaya mata plans dinta, na farko tasan ba zata goyi bayanta ba kamar kullum, na biyu kuma yanzu bata yarda da amanar ta ba musamman saboda wannan inyamurin drivern da take ta faman yashe wa baki a waya. She can't risk her telling him.
Ta girgiza kanta "in na gaya miki gaskiya ma babu abinda zaki yi akai" Sumayya tace "dazu babu abinda ya same ki kika saka Hassan ya kai ki asibiti ko?" Ruqayyah ta juya idonta tace "idan na yi miki bayani ma ba zaki
gane ba, Please just let me be okay? Ni da wadannan tambayoyin naki ma gwara inje in rarrashi jariri na" ta mike da sauri ta tafi dakin Hassan. Sumayya tace "ki bi a hankali fa, ko kin manta doctor yace ki ke bi a hankali?" Ruqayyah ta juyo ta harare ta ta shige, Sumayya ta sauke ajjiyar zuciya a hankali tace "what are you up to sister?"
Hassan yana shiga dakinsa kofar valcony ya bude ya shiga, ya ja kujera ya zauna ya harde hannayensa a kirjinsa yana ta lissafin maganganun Hussain a ransa, amma kuma ya kasa fitar da ma'anar maganar, ya kasa tsayawa a guri daya yayi tunanin. Idan kwakwalwar sa ta jashi nan sai kuma zuciyarsa ta jashi can. A haka yaji shigowar Ruqayyah dakinsa. Ta tsaya tana kallon kofar valcony din tasan yana can amma ita har ga Allah bata son zuwa can din saboda bata son ganin gidan Hussain. Ita in tana cikin gidan mantawa take yi da gidan Hussain saboda babu ta inda take hango shi sai ta valcony din nan kuma in taga gidan ji take yi ya tsaya mata a ranta har hana ta numfashi mai kyau yake yi dan haka bata son ma ganin sa, at least not now, sai ranar da ganin gidan zai faranta mata ba wai bakanta mata ba. Sai ranar da zata kira gidan da nata.
Ta shiga tana lura da yadda bai dago kai ya kalle ta ba. Sai ta jawo kujerar da take facing dinsa wadda kuma ta juya wa gidan Hussain baya ta zauna tana kallon fuskarsa tana lura da irin tension din da take hangowa a can. Tace "Allah dai yasa lafiya kake mijina. Naga kamar baka jin dadi" ya dan kalle ta kadan yana tuno maganganun Hussain a kanta yace "lafiya ta kalau Precious, ki je kuyi hirar ku, in kina jin bacci kije kiyi kwanciyar ki ni anan zan kwana yau" ta marairaice fuska "haba dan Allah, bayan kasan bani da lafiya, bayan kasan bazan iya kwanciya babu kai ba shine zaka ce anan zaka kwana?" Ya dora hannunsa akan nata yace "kiyi hakuri Precious. Ina so zan danyi tunani ne shi yasa bana son yawan magana kinji" ta bishi da kallo a ranta tana dariyar yadda yake mata magana kamar wata karamar yarinya, sai ta gyara zamanta "ni ba zan tafi ba, nayi alkawarin ba zan ke yi maka magana ba amma nafi son in zauna a kusa da kai, kaji? Please? Nafi son kayi ta kallona kana tunanin" yaso yayi mata murmushi amma sai ya kasa, ransa yayi baccin da ba zai iya murmushi ba, ya gyara kujerar sa yadda zai ke kallon gefe sannan yayi shiru, yana ta so ya hada kyakykyawar innocent fuskar Ruqayyah da maganganun Hussain amma ya kasa, sam ba suyi kama da juna ba musamman in aka yi la'akari da gidan da Ruqayyah ta fito. Gidan malamai ne gidan tarbiyya ne.
Da safe Sumayya ce ta hada musu breakfast din soyayyen dankali da wainar kwai sai tea. Amma sai taki zama a dining din ta debi nata ta tafi daki tana ci a can. Hassan da Ruqayyah kuma suka zauna suna cin nasu anan. Suna cikin ci ya dago kai unexpected yace mata "Fatima ta musa duk abinda kika ce tayi miki, tace da Hussain sharri kika yi mata" ya tsaya yana nazarin expression din fuskarta, ga mamakin sa sai ya ga babu wani shock ko wani tsoro mai nuna rashin gaskiya kawai blank ne. Yace "me zaki ce akan hakan?" Sai yaga tayi murmushi sannan tace "wai kana expecting zata karbi laifinta ne? Dama ai cewa zata yi bata yi ba, duk hanyar da zata bi ta tsara mijinta ya yarda da ita ta kuma nuna masa nice marar gaskiya dole sai ta bita. Amma ni ina ruwana in ma mijinta bai yarda da ni ba? Ni dai tunda nawa mijin ya yarda dani ai shikenan ko?" Ta karasa tana kamo hannunsa ta rike tare da langwabe kai, yayi mata murmushi, exactly, tabbas duk abinda Hussain ya fada Fatima ce ta tsara masa, zata iya tsara masa komai dan ta kare kanta. To ma banda abin Hussain ribar me Ruqayyah zata samu idan ta yi wa Fatima sharri? It is not as if miji daya suke aure ballantana ace kishiyoyin juna ne. Sai kuma wani bari na zuciyarsa ya tambaye shi "to menene ribar da Fatima zata samu idan ta zubar da cikin Ruqayyah?"
Yana gama wa ya shirya ya fita sai Ruqayyah ta shirya itama tace Sumayya tazo ta raka ta gidan Hussain. Sumayya ta shirya ta bita dama tana ta so ta shiga gidan ta kashe kwarkwatar idonta. Ai kuwa tun daga bakin kofa ta fara kashe wa "wow. Ruqayyah haka gidan nan ya hadu dama?" Ruqayyah tayi tsaki, komai akayi da jaki sai yaci kara dama. Bata jira yan aikin gidan sunyi mata iso ba kawai ta kama hawan bene zuwa sama. Sai data je karshen benen kuma sannan ta rasa inda zata yi taga wadansu benayen daya yayi hagu daya yayi dama ga kuma kofofi nan ta ko ina. Dole ta nemo yarinya daya ta tambayeta inda matar gidan take, sai yarinyar ta bude mata wani guri tace su shiga bara ta kirawo ta. Suna shiga suka ga daki ne kawai da akayi masa ado da tsarin sarauta, in kana ciki zaka ke jinka kamar a gidan wani sarkin kake, anyi masa irin zanen jikin bangon nan na sarakuna sannan babu kujeru a ciki sai tintin da aka jejjera a ko ina ga lallausan carpet ga kuma lallausan kamshi. Suka zauna suna bin dakin da kallo Ruqayyah tana aiyanawa a ranta cewa ko gidan ya zama nata ba zata chanza tsarin wannan dakin ba.
Sun jima a zaune, sannan fatima ta shigo amma bata kofar da suka shigo ba, su bama su lura da kofa a gurin data shigo ba sai kawai ganin ta suka yi ta shigo din. Fuskarta babu yabo babu fallasa ta zauna a saman tintin daya ta harde kafafuwan wa irin na sarakuna sannan tace "sannun ku da zuwa, kuyi min uzuri na barku kuna jira, ina wasu aiyuka ne a lokacin da kuka shigo" Ruqayyah ta tabe baki, wai aiyuka, ko ita tunda tazo gidan hatta Bedroom dinta share mata ake yi, na Hassan kuwa bata san sanda ake gyara shi ba kuma bata san waye yake gyara shi ba kawai dai tana ganinsa a gyare. Sai ta kirkiro murmushi tace "babu komai wallahi, dama zuwa nayi in baki hakuri akan abinda ya faru jiya, dan nima kaina ba zan iya cewa mai ya faru ba wallahi. Dama tun da akayi bikin mu yana ta cewa baya son in ke shiga harkar ki waye da waye, to amma ban dauka zai dauki zafi irin haka ba. Na san baki ji dadin abinda yayi miki ba amma dan Allah ina bada hakuri on his behalf" Fatima ta bita da kallo tana studying dinta, ta saba da zama da mutane iri iri a gidan su tana kuma kyautatawa kowa zato har sai ya bata rawar sa da tsalle sannan sai tayi placing dinsa a inda ya dace, and right now ta yi placing Ruqayyah a dai dai inda ya dace da ita. Sai kuma tayi murmushi tace "it is okay, ya wuce. Zaman Hussain nake yi bana Hassan ba, duk wani abinda Hassan zaiyi tunani a kaina duk kuma wani abinda Hassan zai yarda dashi a kaina bazan damu ba saboda nasan Hussain ya sanni ya kuma san halina, yasan abinda zanyi da kuma abinda ba zanyi ba. Wannan shine abinda na damu dashi kuma na riga na samu, saura Hassan. Ba zance ba damu da abinda Hassan yake tunani a kaina ba saboda shi Hassan wani sashi ne mai girma na jikin Hussain kamar yadda Hussain yake sashe mai girma na jikina. Ba'a taba raba hanta da jini. Da sannu shima Hassan zai fahimci wacece ni kuma lamura zasu dai-dai ta a tsakanin mu. Kamar yadda na gaya wa Hussain, you are always welcome zaki iya shigowa gidan nan a duk sanda kika ga dama kuma kiyi abinda kike so ki ci arziki ki bar arziki a inda yake. Nima kuma duk sanda kike bukatar wani abu a gurina Please don't hesitate to ask, tun daga kudi zuwa shawara zuwa a listening ear duk zan baki". Ta mike tsaye tana duba kyakykyawan agogon hannun ta tace "lokacin shiga kitchen yayi, kuyi min afuwa" har ta kai bakin kofar data shigo sai ta juyo tace "Sumayya in kin je gida ki gaishe min da Inna da sauran yan uwa" Sumayya tayi mata murmushi tace "zasu ji. Insha Allah".
Kafin Sumayya ta sauko daga dogon benen har Ruqayyah ta kai gida, bata taba jin ranta ya baci irin na yau ba. A palon ta Sumayya ta same ta tana ta safa da marwa, Sumayya tace "kiyi hankali fa, kin manta likita ya baki bedrest?" Ta jefa mata harara tare da tsaki a hade, tana jin kamar ta hada da ita da likitan da kuma Fatima ta babbaka musu wuta. Ta fara masifa "kutumar...ni matar nan zata zauna ta gaya wa maganganu har haka? Lallai ba ta san wacece Rukee ba tana kuma gab da sani wallahi. Wallahi sai tayi nadamar hada hanya dani" Sumayya ta saki baki "magana? Wacce magana ta gaya miki? Ni dai banji ba, kinje kin bata hakuri kuma tace ta yafe miki shine maganar? Ko kuma cewa da tayi mijin rabin jikinta ne shine maganar" Ruqayyah ta juyo kanta "baki ki ta ba? Baki ji ba wai har da wani cewa inje inci arziki in bar arziki a inda yake?" Sumayya tayi dariya tace "salon magana ne fa kawai. To in kika je gidan aka baki wani abu ba arziki aka baki ba? Kuma dole dai in kika fito kin bar sauran arziki a gidan. Ni banga abin tada jijiyoyin wuya a nan ba" Ruqayyah ta rike kugu tace "dama ai ke ba zaki gani ba, tunda ke din ba sosai idanuwan ki da kunnuwan ki suke miki amfani ba. Ki kuwa naji kuma na gani kuma sai na rama. Tana so ta nuna min wato ban isa in hada ta da mijin ta ba ko? To mu zuba mu gani. Ita ce a tsaye a gurin da nake bukatar tsayawa dan haka dole ko tana so ko bata so dole ta matsa ta bani guri" Sumayya tace "guri? Wanne gurin kike magana akai Ruqayyah? Ji nake ke da ita kowa mijinsa daban, dan haka gurin tsayuwar ku daban daban menene zaki yi a gurinta bayan kema ganaki gurin nan?" Ruqayyah ta bata rai, bata so tayi subutar baki ba a gaban Sumayya dan tasan ko bata tona mata asiri ba zata bita da nasiha ne, ta juya tana cewa "wannan kuma ba abinda ya shafe ki bane ba" ta wuce sama ta shige dakinta.
Sumayya ta zauna akan kujera tana tattauna maganganun Ruqayyah a zuciyarta. "Ya Salam! Me yarinyar nan take so ta zama ne mai kuma take shirin aikatawa? Ko ma menene akan Fatima ne, that nice Fatima. Ai gwara ka zalunci wanda ya ke azzalumi ne akan ka zalunci wanda ya ke kyautata maka.
Ta tashi ita ma ta tafi saman gurin Ruqayyah ta tarar da ita zaune a bakin gado har yanzu tana huci, ta zauna tace "ko ma menene kike shirin yi ina tuna miki da cewa ba dai dai bane ba, matar nan bata yi miki komai ba. In fact tare ma kika gansu ke ce outsider a cikin su. In baki gode taimakon su a gare ki ba kuwa ai bai kamata ki zamar musu kadangaren bakin tulu ba" Ruqayyah tace "taimako? Kina nufin taimako na suka yi da Hassan ya aure ni? Ni dana taimake shi na tseratar dashi daga mutuwa kuma fa?" Sumayya tayi murmushi tace "in kin manta Ruqayya bara in tuna miki, shi rai Allah ne yake hurawa mutum shi kuma shi yake cire shi a lokacin da ya ga dama. Da ace Allah yayi Hassan zai mutu a ranar da babu ta hanyar da zaki bi ki cece shi. Shin bakya tunanin cewa Allah ya hada ku a ranar ne a matsayin jarabawar ki? Dan yaga yadda zaki yi da haduwar taku? Think about this please" ta mike ta sauka kasa ta fara hada yan kayanta da tazo dasu. Ba zata iya cigaba da zama a gidan nan ba kar bakin cikin yar uwarta yayi mata illa amma kuma tana tsoron tafiya ta bar ta ita kadai tare da wannan muguwar zuciyar tata mai kissima mata abubuwa iri-iri. Sai ta ajiye jakar tata a kasa ta zauna a bakin ttare da yin tagumi tace "oh Allah. What should I do?"
Kamar amsar tambayar ta sai gashi Hassan ya dawo yana ce mata ya hadu da Baba a office ya kuma roke shi a kan ya bar ta ta dan yi musu kwana biyu saboda Ruqayyah bata jin dadi "duk da cewa da akwai masu aiki a gidan, amma nata ke bukatar wani a kusa da ita sosai yadda ko wani abun zai faru za'a yu saurin taimaka mata" sai Sumayya taji tausayin sa, shi duk ya damu Ruqayyah bata da lafiya bayan kuma karya take yi lafiyar ta kalau, shi duk ya damu da Ruqayyah bayan Ruqayyah bata damu dashi ba ko kadan, ita wani abin take hange na daban.
A hankali sati ya zagayo, babu wanda ya kuma neman wani a tsakanin Ruqayyah da Fatima, Hassan da Hussain kuma babu wanda ya kuma tayar da maganar sun maida hankalin su kan bikin bude kamfanin da yake gaban su, har ranar tazo kuma aka gabatar da bikin successfully komai ya tafi yadda aka shirya, sannan da daddare suka gabatar da dinner ga friends and families dinsu.
Da farko Hussain yayi niyyar samun gurin da za'a yi a can, amma sai Fatima ta bashi shawarar tunda dai dinner din ta mutum dari ce very close friends da kuma immediate family members why not a mayar da ita informal kawai ayi a gida? Akwai filin da swimming pool dinsu yake, katon guri ne zai dauki duk mutanen. Shawarar tayi masa dan haka aka kira masu decoration suka zo suka gyara gurin aka saka kujeru da tables aka shirya komai tun two days to day din. Abinci kuma tace tunda informal dinner za'a yi home cooked meals zai fi dacewa akan ayo order. Amma duk da haka sai da tayo hayar wasu chefs gida biyu sannan suka hadu har ita da kuma kannen ta biyu da suka zo ga kuma su Khadijah duk da suka shigo ga kuma yan aiki nata dana Aunty duk aka hadu a katon kitchen dinta ana tayi. A soya wancan a dafa wannan a yanka wancan. Nafisa ce ta fita zuwa part din Hassan ta gaya wa Ruqayyah cewa ana aikin abinci fa a gidan Hussain ko zata leka ayi da ita? Tana dariya tace "duk da dai nasan yadda kike ta laulayin nan ba wani taya mu aikin da zaki yi amma dai ai ayi hira a dan wataya ko?" Ruqayyah ta tabe baki tace "kin san