Showing 213001 words to 216000 words out of 300844 words

Chapter 72 - Tagwaye Book 1 Hausa Novel Complete

22 Dec 2024

2089

abinda ya samar da Da a tsakanin mu, ni kuma ban gaya masa gaskiya ba saboda bana son ya fahimci matsayin ta, dan wannan zai chanja motive dinsa na riketa. Bayan ya rufe ta sai ya zauna ya shirya min warnings akan ko da wasa in na nemi barinsa ko kuma kubutar da budurwa ta daga hannunsa to zai kashe ta ya binne ta a gidan yadda babu wanda zai kuma jin labarin ta. Ni na san shi, na san halinsa, na kuma san abinda zai aikata da kuma abinda ba zai aikata ba, dan haka nasan zai iya yin abinda yace ba tare daya ji komai a jikinsa ba"

Ba wai hakan yana nufin babana yana da mummunan hali ba ko kuma ya taba kashe wani ba, a'a, amma yaki jinin hausawa kuma ya tsani musulmai, yana kallon su a matsayin terrorist dan kullum yana iƙrarin in rigima zata tashi tsakanin kabilu zai yo iyakacin kokarin sa gurin ganin ya kashe as much Muslims as he can, "dan a rage iri". Sannan kuma abinda ya faru dani na juya wa addinin su baya da nayi ya kara wannan tsanar, kuma nasan yana sona sosai, babu abinda ba zaiyi ba saboda yaga ya zaunar dani a tare dashi"

"Yayi deleting all my social media accounts, yakuma hadani da bodyguards yadda duk inda na saka kafata nan suke mayarwa duk dan kar inyi trying guduwa ko contacting wani daga North. Amma ni ko sau daya ma ban gwada guduwar ba saboda nasan zama na ne kadai yake keeping Fatimah alive a hannunsa, kuma ko sau daya ban gwada contacting dinku ba, duk da cewa bani da numbers dinku gabaki daya, amma ban gwada nema ba, saboda ina tsoron abinda hakan zai haifar"

"Ban sani ba ko zaka fahimta, ko sauran mutane zasu fahimta, amma ni nayi gudun kar in neme ku ya fahimci na neme ku yayi mata wani abu kuma kuje ku tarar da yayi mata wani abu and that can lead to religious and tribal crisis musamman in akayi la'akari da matsayin fatima. Fatana shine ta samu lafiya sai in dauko ta mu gudu tare in kawo ta har gidan su"

"Dakin da take ciki babu wanda yake shiga sai ni, sai Mama, ita ma kuma da farko babu ruwanta da ita sai da na roke ta taimaka mata, ita ma na nuna mata cewa budurwa tace na nuna mata kamar haihuwa tayi babyn ya mutu shine an taho kaita asibiti akayi accident har kuma Daddy ya same mu a hanya. Wannan yasa ta kulata ta yi jinyar ta da duk irin abinda ya kamata ayi wa matar data haihu har ya kasance ta warke sosai. Ina nufin external injuries dinta"

"Babban tashin hankali na shine yadda na lura da halin da Fatima take ciki, farko ko sunan ta bata sani ba, sunan Hussain kawai ta sani, shima kuma dana nemo hotonsa na nuna mata sai naga bata gane shi ba sai cewa tayi "kaga wani saurayi kyakykyawa kamar kai" bata san kowa ba bata san komai ba sai ni, dole sai dai in zauna tare da ita in kuwa har na fita to zata yi ta kuka ne har in dawo. Ni kuma bansan much ba akanta except cewa yar sarkin kano ce kuma matar Hussain. Sai nayi ta nemo pictures din sarkin kano dana yayan sarkin wasu hotunan ma harda ita a ciki sai in nuna mata wai ko zata tuna amma ba abinda take tunawa sai dai ta nuna hoton ta tace "ga me kama da ni".

Adam ya girgiza kansa yace "it was hectic. I couldn't get her to remember anything. In kuma bata tuna ba ba zan iya smuggling dinta out ba dan zata tona mana asiri ne, kuma I needed her to remember saboda ta bada shaida a kaina idan munzo nan din in ba haka ba ni zan fada ciki. Ba kowa ne zai fahimta ba. I almost lost my mind ni din ma akan hakan. Zaman guri daya, rashin waya, rashin wanda zan gaya wa damuwa ta ya fahimta sai dai in saka ta a gaba muyi ta hira, inyi ta bata labarai na few of abinda na sani na rayuwar ta da kuma ni tawa rayuwar, inyi ta bata labarin ku, da labarin Sumayya" ya danyi murmushi yana shafa fuskarsa yace "how is she? Tayi aure ko?"

Hassan ya dauke kai gefe yace "she is fine. Ya akayi kuma kuka fito?" Adam yace "rana daya, a farkon wannan shekarar, na shiga da magazine ina nuna mata hotunan celebrities wai ko zata gane wata ko wani a ciki, sai kawai taga hoton wata da ciki, and that was the switch, sai ta fara neman cikinta wai ina cikin ta yake? Ina babyn cikin ta? Daga nan kuma sai aka fara samun improvement ta fara tuna abubuwa kadan kadan, little at a time, amma kuma tumawar sai ya saka ta koma very emotional, kullum cikin kuka, kullum cikin tunani, ta fahimci ita wacece ta kuma fahimci cews bata gida yanxu. A ranar data tuna da labarin mutuwar Hussain naga tashin hankali, sai da na nemo allurar bacci nayi mata duk da ban iya ba sannan ta samu nutsuwa."

"Daga nan ta tuna abubuwa da yawa, yarintarta tashinta da komai amma banda accident din su banda kuma haihuwarta. Wannan shi ya tayar mana da hankali, muka hada kai ni da ita muka nemi solution. Solution din kuma da muka tsayar shine mu nemi taimakon Mama na, kasan tsakanin Da da uwa sai Allah, na nuna mata in bata taimaka mana ba zamu gudu da kan mu kuma komai zai iya samun mu. To ita ma dan zaman da tayi da Fatima ta shaku da ita, she forged an ID card for us yadda zamu iya tahowa ta jirgi, and jiya she used kissar su ta mata ta kawar da hankalin Daddy da guards dinsa daga kan mu sannan muka taho tare"

Maybe ba zaka yarda ba, and maybe wasu mutanen ba zasu yarda ba amma wannan labarin dana baka to the best of my knowledge, shine gaskiya. In akwai wani abu da na manta ban gaya maka ba in na tuna zan gaya maka. Ina fata kuma ina saka ran ko kowa bai yarda dani ba kai zaka yarda dani"


Forgive the typos please


*She Smiles*

Hassan ya dago kai yana kallon sa, yana lura da yadda damuwa take bayyane a kyakykyawar fuskar sa, ya fahimci damuwarsa da ba kowa ne zai dauki uzurinsa a matsayin uzuri ba, sai mai zurfin tunani musamman akan yadda alaka take a tsakanin kabilun guda biyu. Idan sanarwa ta fita cewa an samu gawar gimbiyar kanawa wadda aka rasa ta shekara da shekaru a gidan inyamuri a garin owerri, wannan ba karamar magana ba ce ba, wadda zata iya jawo asarar rayuka masu yawa a cikin kabilun. A lokacin kuma babu wani bayani da Adam zaiyi wanda za'a fahimce shi, laifin zai zamo kidnapping, enslaving, maybe a hada da sexual assualt da kuma murder.

Ya fahimci cewa kokarin Adam shine ya dawo da Fatima gida alive and in one piece, kuma alhamdulillah ya dawo da ita din a hakan. Wannan kadai ya isa a jinjinawa rikon amanar sa, idan wani ni ko blinking eye ba zaiyi akan ta ba musamman idan ya fahimci ta yi loosing memory dinta. Ko kuma ma ya taimaka wa baban nasa gurin assaulting din ta, kuma yanzu he risked his life, and his mother's life dan ya dawo da Fatima gidan su.

But still.....

"Na fahimce ka Adam, really na fahimce ka, but you could have done something, you could have contacted me ta hanyar wayar either mamanka ko one of your sisters. You could have at least warn me cewa you two are alive amma ga halin da ake ciki in yaso sai mu hada kan mu muyi finding solution ba tare da wani ya sani ba. You should have contacted Sumayya, ta damu sosai da rashin ji daga gare ka, sau biyu muna zuwa kano gidan ku dan neman labarin ka"

Adam ya bude ido "but how? Ya akayi kukayi tunanin nemana a gida? Na dauka zaku dauka na mutu ne, grieve and just move on?" Hassan yace "Ruqayyah. She admitted cewa ita ce ta sanar da mahaifinka cewa ga inda kake, I guess shi kuma ya ringa binka har ya same ka kai kadai ya kamaka" Adam ya dafe kansa yace "Ruqayyah! I thought as much duk da cewa shi kansa ya nuna min bai san wacece ba but ita nayi zargi dama. Ban san me na tsare wa Ruqayya a duniya ba"

Hassan yace "babu abinda ka tsare mata, bata sonka ne kawai, and that's what she did to mutanen da take iƙrarin tana so ma ballantana kai data ambata cewa bata son ka. You should be grateful to Allah daya kasance a haka kawai ta barka bata illata ka ba" yadda ya fadi maganar da daci ya saka Adam ya kalle shi, yana tuna irin son da yake yiwa Ruqayyah da kuma yadda yake tsayawa a bayanta akan komai. Ko ya fahimce ta ne yanzu?

But bai tambaya ba sai Hassan ya kuma cewa "zuwan mu na farko mun samu mai gadi, shi ya tabbatar mana da cewa kana tare da iyayenka, amma ko kadan bai gaya mana wani abu daya danganci Fatima ba, zuwa na biyu kuma muka samu kanwarka, she told us kana lafiya tare da girlfriend dinka and that ka koma school." Adam ya dago kai yana kallon sa a hankali yace "and Sumayya heard that?" Hassan ya dauke kai yace "taji mana. And wannan ne ya saka har yanzu nake ganin saka cin ka. You should have told us cewa kana raye ko da kuwa baka gaya mana zancen Fatima ba"

Adam yace "in Sumayya ta san ina raye she won't move on, zata dage cewa in dawo gare ta abinda ni kuma ba zan iya ba, in taga ban dawo ba kuma zata yi tunanin bana son ta ne ko dama yaudarar ta nayi. Nafi son in bar good image of me a ranta. Nafi son tayi aurenta ta haifi yayan ta, I sacrificed my love for Sumayya saboda Fatima" Hassan ya gyada kai yana kara fahimtar sa yace "not just for Fatimah, for something much more than Fatimah. Na yarda da kai Adam, na fahimce ka da manufar ka, kuma zanyi iya kacin karfina in ga cewa iyaye da yan uwan Fatima suma sun fahimce ka insha Allah kuma zasu yi saboda mutane ne masu ilimi ba gidadawa ba ne ba".

Sai ya mike a lokacin da Adam yake cewa "how is she?" Hassan ya juyo yana kallon sa, ya gane wace "she" din da yake magana akai amma sai yayi shiru har sai da Adam ya sake cewa "tayi aure ko?" A cikin muryar sa yana jin hope, hope din cewa maybe har yanzu bata yi aure ba. Sai ya gyada masa kai ba tare daya kalle shi ba yace "tayi aure, ta haihu ma last year" Adam yayi shiru yana jin haushin kansa da ya saka ran cewa Baba zai barta a gida har tsahon shekara biyar ba tare da yayi mata aure ba.

Ya danyi murmushi, irin murmushin nan mai ciwo yace "Allah ya sanya alkhairi, Allah kuma ya raya abinda aka samu. Ni kuma Allah ya hada ni da wadda zata zame min alkhairi fiye da Sumayya" sai dai shi kansa daya fadi maganar yana tunanin anya kuwa zai samu wadda tafi Sumayya? Shi gani yake Sumayya ta hada komai da yake bukata a gurin mace. Sai dai tunda Allah yace, yasan tabbas Allah babu abinda ba zai iya ba. Tabbas soyayya Sumayya is the biggest sacrifice da yayi for Fatimah.

A lokacin ne aka shigo akayi musu iso zuwa inda aka gabatar musu da breakfast daga nan kuma aka shigar dasu inda zasu hadu suyi magana.

A cikin gida kuma tun sanda su Aunty suka shiga komai ya rikice, sunga Fatima sun kuma tabbatar ita din ce ba wata ba, sai dai ganin Fatima ya tayar musu da mikin mutuwar Hussain, dan babu wanda bai yi kuka ba a cikin su musamman ita ma Fatima din da sai da suka gama nasu kukan suka koma rarrashin ta. Ita tana tambayarsu ina baby su suna tambayar ta labarin baby. Lamarin daya daga dukkan hankulan su baki daya, dan daya kamata ace ya kasance mafi soyuwa a gurin su baki daya shine kuma dan da basu san inda yake ba, hasali ma basu ma san ko yana da rai ko bashi da rai ba.

Da kyar aka samu suka dan ci abinci kadan, sannan ne kuma aka raka Fatima gidan baki dan su gaisa da Hassan, sai dai kuma zuwan nata sai ya kasance sai da akayi nadamar yinsa, dan ganin Hassan ya saka gabaki daya ta nemi ta fiya daga hayyacinta a dole aka dawo da ita zuwa gida babu shiri, shi kansa Hassan duk da jaruntar sa da dauriyar sa da kuma karfin zuciyarsa amma ganin Fatima sai da saka yaji tamkar yau ne ya binne Hussain.

Sai da komai ya nutsa sannan aka samu aka zauna gabaki daya, tun daga kan yanuwan Fatima da ita kanta Fatimah zuwa Hassan da Aunty da yanuwansa da Sumayya, sai Adam wanda yau aka shigar dashi cikin maganar sannan kuma da Maman sa wadda tun jiya Fatima da kanta ta saka aka dauko ta daga inda akayi mata masauki aka dawo da ita bangaren Hajiya fulani inda ita fatiman take. Mai martaba sarki ne kawai da matansa basa gurin, amma suma suna dakin da yake jikin nan kuma suna ji suna ganin duk abinda ake yi ta hanyar Camera.

Farko an fara gabatar da addu'a sannan kuma aka yi bitar abubuwan da already kowa ya sani, sai kuma ka koma kan abubuwan da ba'a sani ba. Adam aka fara tuntuba akan ya fadi nasa side din, sai ya bayar da labari kamar yadda ya bawa Hassan dazu. Sai dai bayan ya gama, kamar yadda yayi tsammani sai ya fahimci fiye da rabin mutanen gurin suna binsa da kallon rashin yarda kuma idanunsu cike da tambayoyi, ai kuwa tambayoyin suka yi ta jera masa yana amsa musu dai dai da sanin sa, sai dai wani abu da ya burge Hassan shine ko kadan babu alamar tsoro ko rashin gaskiya a fuskar Adam sai dai takaicin cewa an kasa fahimtar sa.

A karshe Umar yace "ni har yanzu na kasa gane cikakken dalilin da zai sa ka dauki shekaru biyar ba tare da ka sanar mana da cewa yar uwar mu tana hannunka ba". Maganar da Fatima tayi ne ya saka duk suka dawo da hankalin su kanta, tace "ba zaka fahimta ba yaya Umar, ba zaka taba fahimta ba babu kuma wanda zai fahimta sai wanda ya ke a matsayi irin wanda Adam yake ciki. Sai wanda ya kasance a tsakanin kabilu guda biyu masu kiyayya ga junan su, sai wanda ya kasance tsakanin addinai guda biyu masu rigima da junan su, sai wanda ya kasance dukkan bangarorin biyu sunyi rejecting dinsa sannan kuma kuskure daya idan yayi zai iya tayar da rigimar da Allah kadai zai iya kwantar da ita, wannan shine kadai zai gane cewa Adam yayi iyakacin kokarin sa"

"Adam ya gaya muku duk abinda ya kamata ya gaya muku, abinda kawai ya cire daga cikin maganar bai gaya muku ba shine ba wai memory na kawai nayi loosing ba, nayi loosing har da sanity dina. I was crazy. Kuma nasan yaki fadar haka ne kawai saboda kada ya bata image dina, saboda yana so ya kyautata min dan shi din ya kasance mai kyautatawa ne sosai a gare ni"

"Adam yayi min abinda ba kowa ne a cikin ku zai iya yi min ba, ba kowa ne zai iya kula da marar lafiya irin rashin lafiyar da nayi ba har na tsahon shekaru biyar ba tare da ya gaza ko ya nuna gazawa ba. Farko ya taimaka min, ya dauke ni daga dajin nan wanda da ya ga dama zai iya bin babansa su tafi su barni anan, ko da ban hadu da mugaye sun azabtar ko kuma kashe ni ba to da yanzu watakila ina can ina yawon hauka a kauyuka. Daga nan kuma yayi sacrificing dukkan rayuwarsa for me, his freedom, his choices, his love" ta fada tana kallon Sumayya, wadda ta sunkuyar da kai hawaye yana zuba a fuskarta.

"A duk tsahon shekarun nan Adam shine uwata, shine ubana, shine brothers and sisters dina, shine friend dina, shine doctor na, shine maid dina. Kuma he did duk wadannan roles din perfectly. Adam har allura ya koya kuma yake yi min a duk lokacin da bani da lafiya. He cried and laughed with me. Duk abinda ya fada, wadanda na tuna haka suke babu gyara, wadanda ban tuna ba kuma na yarda da abinda yace hundred percent saboda banajin a rayuwata na taba haduwa da honest man irin Adam"

Sai ta taso daga inda take zaune tazo gaban Adam ta durkusa tace "bayan na dawo hayyacina, bana jin na samu damar gode maka, hankali na gabaki daya ya tafi ga cewa in dawo gida in tabbatar da labarin rasuwar Hussain sannan kuma inji labarin dana, that was so selfish of me, kayi hakuri. Nagode Adam. Allah ya saka maka da mafificin alkhairi dan ni nasan ba zan iya saka maka akan abinda kayi min ba. Allah ya biya ka da gidan aljanna Adam"

Sai yayi murmushi yana kallon cikin idonta yace "Allah, ya bamu aljanna gabaki daya. And thank you too for standing up for me".

Daga nan babu wanda ya kuma bude bakinsa yayi questioning Adam.

Sai kuma Hassan ya fara nasa bayanin, bai rufe komai ba akan tsohuwar matarsa Ruqayyah da kuma karyar da tayi akan wadda ta mutu da kuma zarginta da yakeyi a yanzu da yaji komai na cewa tana da masaniya akan jaririn Fatima. "Sanda Adam ya ganta ta haihu, meaning a gurin da suka yi hatsarin ko kuma a kusa da gurin ta haihu, babu wanda yake witness sai Ruqayyah tunda ita kadai ta tsira sauran sun mutu, sannan kuma boye


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login