Showing 57001 words to 60000 words out of 300844 words

Chapter 20 - Tagwaye Book 1 Hausa Novel Complete

22 Dec 2024

2091

wanke fuskarta maganganun Sumayya ciwo suke kara wa kanta. Tana fitowa daga toilet din bata kalli inda Sumayya take ba ta wuce palo.

Sumayya taji zuciyarta tayi babu dadi, ta jima a zaune a gurin hannayenta tallafe da kuncinta sannan tayi ajjiyar zuciya ta mike ta tafi palon itama. Abin mamaki sai ta samu Ruqayyah kace kace cikin kaya tana ta bubbudewa ita da Suleiman da ya shigo yanzu. Inna tana gefe tana kallon su. Tan fitowa Ruqayyah ta kira ta. "Zo ki taya ni zaben wanda zan saka ranar kamu, kina ganin wannan lace din yayi?" Sumayya ta zauna tana karbar lace din tace "too heavy, kamu ai atamfa ya kamata ki saka. Wannan kuma kya saka ranar yini. Yauwa ga wani yadi can sai ki hada dashi. Kai! Kinga wani takalmi? Amma ya shiga da lace din nan" Ruqayyah sai murmushi take yi tana lissafa irin kyan da zata yi. Gimbiya Fatima is in for a surprise.

Da daddare Hassan yazo zance, kamar yadda suka shirya tare suka fita gurinsa. Suna gaisawa da Sumayya yace "mutumin ki fa yayi zuciya, ya tafi kuma bana jin zai sake dawowa" Sumayya ta bude ido tace "me ya faru? Lafiya?" Ya daga kafada yace "maybe na fadi abinda baiji dadi ba I don't know, maybe I was unintentionally rude to him amma ki kirashi ki ba shi hakuri on my behalf please, ina da interest akansa sosai and I like him a lot. I found out something about him da baya son a sani and it pissed him off, ni kuma abinda na samu din shine ya kara min karfin guiwa a kansa. Tell him that dan Allah and make him come back to my office" Sumayya ta dan bata rai tana kokarin hasashen abinda ya hada su amma Sai kawai ta bar maganar saboda bata son Ruqayyah ta shiga ciki amma sai da ta shiga. "Wait, you two, wai maganar me kuke yi ne? Maganar wa kuke yi wanda ku biyu kuka sanshi amma ni bn san shi ba?" Hassan yana kallonta yace "saurayin Sumayya ne,tace kuma kar in gaya miki ban kuma san dalilin ta ba amma zan rike mata amanar ta, it is her call, ita ya kamata ta gaya miki" ya juya yana kallon Sumayya yace "amma zan rike amanar ne daga nan zuwa bikin mu, in akayi biki to I can't promise cewa zan iya boye wa matata wani abu kuma" ya kare maganar yana murmushi, Ruqayyah ta sunkuyar da kanta tana murmushi a ranta tana cewa "you better not".

Sumayya ce ta shigar masa da maganar biki, ta tambayeshi plans dinsa, sannan tayi masa bayanin kayan da Aunty ta aiko musu dashi takuma yi godiya. Ya gyada kai yace "yeah, Aunty ta gaya min dazu da naje gida. Ina ganin ku shirya duk abinda kuke son yi ni amma personally babu abinda nake shiryawa gaskiya, akwai dai dinner da zamuyi gabaki dayan mu ranar Sunday bayan an dauko Fatima, dinner ce for dukkan couples din uku da friends din kowa da kuma family din kowa. To ita kadai zanyi attending gaskiya, sai daurin aurarrakin duk ukun. So, in kuka tashi sai ku shirya abinku da friends din ku kawai".

Ruqayyah taji tamkar ya kwada mata mari, taki gaya wa friends dinta maganar auren su saboda tana son tayi showing dinsa up a bikin su, amma yana ce mata ba zaiyi attending komai ba, ita kadai zata je ba miji, kamar wadda akayi wa auren dole?" Sumayya tace "it is okay" Ruqayyah tayi saurin juyowa tana kallon ta tana jin kamar ta makure ta, it is definitely not okay. Ita da ta kirawo ta saboda ta taya ta fighting shine zata yi saurin giving up? Yace "duk abinda kuke so fa ku fada kar ku boye min. Zan aiko muku da kudin da zasu ishe ku komai, in na baku kuma ko bai ishe ku ba ku gaya min sai in kara muku, ai nasan ba zakuyi abinda bashi da muhimmanci ba ko Hassana?" ta gyada kanta da sauri tana kirkirar murmushi, ba haka taso ba amma sai zuciyarta, har dark heart ta hana ta yin magana, a take kuma ta kitsa mata abinda zata yi.

Washegari kuwa sai ga sakon kudi ya aiko musu dashi, kudade ne masu yawa a idon Sumayya da Inna Ade da sauran mutanen gida, but as usual a gurin Ruqayyah taga kankantarsa duk kuwa da cewa bata taba rike kudi masu wannan yawan ba, ita kawai position dinsa take hangowa tana ganin yafi karfin wannan kudin. Sai ta saci jiki ta shiga daki ta dauki wayar Sumayya ta rubuta masa sako kamar haka.

Assalam. Yaya Hassan ina yini? Munga min gode sosai Allah ya kara arziki. Sai dai muna so ko za'a karo mana wasu dan ina ganin kamar wadannan din ba zasu ishe mu ba, kawayen mu suna da yawa, zamu yi arabian night da bridal shower kuma zamu basu soveniers gashi muna so muyi musu anko kala bibbiyu. Ruqayyah tace a barshi kawai amma sai nace bara ni inyi maka magana tunda kace in basu isa ba a gaya maka. Nagode
Sumayya


Ta tura masa sannan ta goge message din ta juya tayi kwanciyar ta. Ba'a jima ba ya kira wayarta, ta dauka ta gaishe shi sannan tace "munga sako dazu, mun gode sosai. Nace amma wadannan kudaden ai kamar sunyi yawa ko? Me zamuyi da kudi har haka, da rabin su ma ka bayar ai da sun isa" sai taji ya yi dariya, muryar sa cike da farin cikin da zuciyarsa take ciki, yace "dariya na baka ko?" Yace "nooo ba ke kika bani dariya ba, zuciyata ce cike da murna da farin cikin samunki a matsayin matata, a yanzu haka bani da buri illa inga ranar da za'a daura auren mu in ganki a gida na a matsayin matata, gaskiya daga ranar banajin ina da sauran wani buri a rayuwa dan nasan with you by my side my life will be completed" murya can kasa tace "so will mine".

Yace "yanzu na samu sako daga Sumayya, tana zancen wai kudin ba zasu ishe ku ba" Ruqayyah tace "what? Amma lallai wannan Sumayyan...." Yace "it is okay. Kowa dama ai da halinsa da kuma kalar tunanin sa. Sumayya kanwa tace dan haka ba zan watsa mata kasa a ido ba saboda nasan duk danke take yi sannan kuma yarinta ma tana damunta wai harda cews za'a yi wa kawayen ku anko kala bibbiyu" ya sake yin dariya, "babu wani abu, zan sake aiko da wasu kudin but kiyi monitoring dinta kar tayi almubazzaranci da yawa" Ruqayyah ta karya murya "ni wallahi da ka barshi ma. Wannan ai ni ta bawa kunya wallahi" yace "kunya, mijin naki kike jin kunya?" Tayi dariya, yace "kar kiyi mata maganar,kar ma ki nuna mata nace bata yi dai dai ba, dan mu take yi kinji? For you, I will do anything" tace "nagode. Allah ya bar mu tare har abada" yace "ameen, ni har gaban abada ma nake so muje tare. In naje office gobe zan aiko da sakon".

Washegari sai ta zama alert, tasan zai aiko da sakon kuma bata son wano ya rigata karba, dan haka a hannunta dan aiken ya danka envelope din. Ta wuce daki ta kirga taga dai dai yawan wadancan ne, sai ta bude cikin kayanta ta dauko wadancan kudin da take ta ajiiyar su na wajen Hussain ta hada da wadannan a ranta tana cewa, "in kasan wata ai baka san wata ba. Dole in tara kudi ko dan in kankarowa kaina mutumci a gurin yan uwanka da sauran mutane".

Sau ta debi kadan ta bawa Sumayya tace "inji Hassan, wai ko zaki yi wani abu" Sumayya tace "ni me zanyi? Duk abinda zanyi ai tare dake zamuyi. Shi dai kawai ya fiya kirki". Next zuwan da Hassan yayi suka hadu da Sumayya yace "sako na yazo miki ko?" Ta yi murmushi tace "yazo fa, na gode sosai" yace "asha biki lafiya".

Tun ranar da Hassan ya gaya wa Sumayya yadda suka yi da Adam take neman layinsa amma yaki dauka, sai bayan kwana biyu sai ta tura masa text

"In na sake kiran ka baka dauka ba ba zan sake kiran ka ba"

Mintuna kadan bayan nan sai gashi ya kira ta, tana dauka yace "why? Me yasa ba zaki sake kirana ba? Saboda abin da ya gaya miki a kaina ko?" Tace "me ya gaya min a kanka? Ni babu abinda ya gaya min a kanka kawai dai yace kayi fushi in kira ka in baka hakuri on his behalf, yace kaje ka karbi aikin" taji yayi ajjiyar zuciya sannan yace "naki daukan wayarki ne saboda bana son inji kalmomin daga bakin ki, na dauka ya gaya miki, na dauka kin kira ni ne kiyi robbing abin a fuskarta" tace "wanne abin kenan? Menene abinda baka so in sani?" Ya danyi shiru sannan carefully yace "ba wai bana so ki sani bane ba, ina tsoron yadda zaki yo reacting ne idan kin sani ɗin" tace "idan nasan me? Ba zaka gane ya zanyi reacting ba har sai ka gaya min tukunna" murya can kasa yace "reacting to the fact that I am a religious convert. I was a christian before..." Ya rintse idonta tare da kwanciya akan gado. She suspected as much, amma tafi son ya furta mata da bakinsa.

Tace "you said it yourself, you said the word "before' before yana magana akan past, past is in the past, you are a muslim now, and that's all that matters. Kaje ka karbi aikinka, yace it doesn't matter" yace "I don't care about the job, I care more about you, zaki iya cigaba da kula....zaki ke kula....." Ya kasa fadan kalmar sai tace "kula musulmi? Idan ban kula musulmi ba wa kake son in kula Adam?" Ya lumshe idonsa ya bude "but my parents are still......" Tace "your parents are not you. Kai daban su daban, ba'a taba judging wani a bisa laifin wani. It doesn't matter who you were, what matters is who you are. And you are a muslim, you are Adam. And I like you" ya sauke ajjiyar zuciya mai karfi yana dora goshinsa akan stirring motarsa. Tun ranar nan, ranar daya saka kafafuwansa cikin masallacin nan ya karbi kalmar shahada bai taba jin wani ya gaya masa wadannan kalmomin da sune abinda yafi so yaji fiye da komai ba, cewa his past doesn't matter, kowa nuna masa yake yi kamar past dinsa wani rubutu ne a goshinsa da ba zai taba gogewa ba. Shi kuma tun kafin ya karbi addinin a dan ilimin da yake dashi akan Islam yasan cewa duk wanda ya musulunta tamkar sabon jariri yake, duk abinda ya aikata ya wuce kamar bai taba yi ba, an bude masa sabon littafi. But nobody made him feel like that, sai yau, sai Sumayya. Yace "thank you" yadda yace thank you din kawai yasa ta fahimci daga can wani lungu na zuciyarsa ya fade ta. Taji itama maganar ta taba tata zuciyar.

Tace "kaje ka karbin aikin Adam, you need it" sai ta danyi dariya tace "kuma kasan me? In ka karbi aikin we will be closer tunda Ruqayyah zata yi aure a gidan" yayi dariya shima yace "you mean zan ke ganin ki ba tare dana yi dogon wuya ba" suka yi dariya a tare.

Adam yaje gurin Hassan, ya kuma karbi aikin personal driver na Hussain. Kallo daya Hussain yayi masa yace "he is strong, young and handsome. I like him" daga nan ya shiga daki ya kwaso masa kayan sawa jaka guda da takalma da huluna yace "a cigaba da gayu daga inda aka tsaya"

Lokaci ya tura, satin biki ya kama. Tun farkon satin yan'uwa da abokan arzikin Inna Ade da Baba suka cika gidan, da yawa sunzo ne dan su kashe kwarkwatar idonsu akan zancen da suka ji na wanda Ruqayyah zata aura. Ita kuma Ruqayyah sai da ta tabbatar duk wanda yazo gidan nasu, ko a kawayen data gayyato ko kuma a yan'uwa ya san wa zata aura."CEO ne na H & H group of companies" daga nan sai ta bi sakakkun bakunan su da kallo tana jin cewa she have made it in life. Ruqayyah duk tayi abubuwan da take son yi da First kudin da Hassan ya bata, ta zabi friends na fita kunya, most of them ma ba kawayen ta bane ba kawayen Minal ne. Suka shirya bridal shower dinsu a gidan Aunty Hafsa yayar Minal aka ci aka sha aka yanka cake akayi hotuna, shigar da Ruqayyah tayi kowa sai ya tabbatar da abinda take fada akan mijin da zata aura, kowa ya tabbatar shi din ne dai.

Akayi yini anan gidan su ranar Alhamis, a ranar ne kuma aka kawo lefen Ruqayyah. Hatta ita kanta Ruqayyah duk abinta sai data yadda cewa tabbas anyi mata lefe, dan bata taba ji ko ganin lefe irin nata ba. A hankali a hankali take jin burikanta na rayuwa suna cika.

Ranar juma'a da safe aka daura auren Hassan Aminu Abdullahi da Ruqayyah Yusuf Mu'awiyah. Farin ciki a gurin ango da amarya ba zai misaltu ba, kowa da abinda yake zuciyarsa, kowa da sirrin da yake zuciyarsa. Sai dai muyi mudu fatan zaman lafiya da zuriya mai albarka.

Gobe zamu kai amarya dakinta insha Allah, daga nan kuma sai muje kano mu dauko daya amaryar.

Wannan littafin na siyarwa ne, duk wanda yake so ya neme ni through WhatsApp ta wannan number din 08067081020

Twenty : Shattered Dreams 2

Yinin ranar nan murmushi ya kasa daukewa daga fuskar Ruqayyah, kowa in ya ganta sai yaga ta burge shi ga kyau, ga kwalliyar da ta ci ta gani ta fada, ga gyaran jiki da taje ta kashe kudi aka yi mata sannan ga farin ciki lullube da zuciyarta da kuma fuskarta. Yau ce ranar da burikanta suka fara cika, yau ce ranar data taka wani matsayi wanda zai zamo mata jagora zuwa ga matsayi na gaba a rayuwarta.

Sumayya kuma tunda aka gama daura auren taji jikinta yayi sanyi matuka, ita kawai lissafin rabuwa da yar uwarta rabin jikinta take yi, bata jin tun da aka haliccesu sun taba rabuwa ta cikakken kwana daya amma wai yau Ruqayyah zata tattara ta koma wani gidan da zama kachokan. Tsakanin su sai dai ziyara, ziyarar ma tasan Baba ba barinta zai ke yi tana yi akai akai ba kamar yadda bata ga alamar Hassan zai zamo mai barin mata tana yawo koda yaushe ba. Sai data shiga toilet tayi kukan rabuwa da yar uwarta, amma ita yar uwar tata ko a jikinta, hirarta kawai take yi a cikin kawayen aronta suna ta dauke dauken hotuna tare da shirin dinner din da za'a yi ranar Lahadi da daddare. Already dama Hassan ya kawo mata cards na mutum hamsin, wanda sai da suka yi rigima da Sumayya dan boyewa tayi ta hana yan uwansu da suka zo biki "zuwa zasuyi wallahi su tsinka ni a cikin mutane, wasu fa ko cin abinci da chokali basu iya ba, gwara mu aro mutanen da zasu je a matsayin yanuwana shikenan mun huta. Mu dan dauki kudi mu basu sannan mu basu kudin liki" amma Sumayya taki yarda, dan me bayan ga yan uwanka sannan zaka tafi kaje kayi hayar yan uwa? Ita bata ga logic a cikin maganar ba. Ta gayawa Inna Ade ita kuma ta kira Ruqayyah tace mata "bani katinan" dole ta dauko ta miko mata tana kunkuni. Inna Ade ta bata guda ashirin na kawayenta sannan sauran ta rabawa duk wanda take ganin in ya dace yaje yaci arziki ya bar arziki a mazauninsa.

Juma'a din tunda yamma aka fara shirye shiryen kai amarya, Ruqayyah ta hada kayanta kaf a guri daya, ita bata yi wani alkunya ma ba na kin hada kaya ta bar Sumayya ta hada mata a'a tare suka hada ɗin, tana tunawa Sumayya akan duk abinda ta manta. Ita bata ga wani abinda zai saka ta bata ranta ko tayi wani kuka ba a ranar da ya kamata tayi farin ciki fiye da wanda take yi a kowacce rana, a ranar data yage rigar talauci ta lulluba ta arziki?

Tun da yamma Inna Ade ta aika aka kirawo Hassana zuwa dakin Baba, suka tafi tare da Sumayya, tun kafin suje Ruqayyah ta riga tasan dalilin kiran, tasan fada ne za'a yi mata a kan zaman aure ita kuma tana ganin kamar bata lokacin su zasu yi su kuma bata bakin su, su fa irin zaman auren talakawa suka sani dan haka akan irinsa zasuyi ma ta fada, wannan kuwa aure na na masu abin hannunsu wadanda basu dawata sauran damuwa a duniya sai dai suci mai kyau su sha mai kyau su kuma kwanta a mai kyau. Ita tuntuni ta gama yiwa kanta fada akan yadda zata yi wannan zaman auren, ta riga ta kama bakin zaren Hassan ta fahimci cewa ba zata iya yi masa musu ba saboda yayi mata kwarjini dayawa amma zata iya cigaba da lullube kanta da hijabin daga riga ya santa dashi sannan tana jan zaren sa a hankali ta karkashin kasa kamar yadda tayi masa a lokacin karbar kudin hidimar biki. Let someone else take the fall, someone else, in dai har ba ita bace ba. Anyone.

Suna shiga dakin sai taji Baba ya fara tsokanar ta, abinda ta jima bata ji yayi ba, da alama shima yana alhinin rabuwa da yar tasa ne. Sai da ya saka su duk yi dariya gabaki dayan su sannan ya fara magana.

"To Hassana, alhamdulillah, gashi kamar yau Allah ya bamu ku keda yaruwarki amma gashi cikin kudirarsa yau zaki bar gidan nan zuwa gidan mijin ki. Babu abinda zamu cewa Allah sai dai godiya tunda munsan kudirarsa ce kawai ta hada ku keda Hassan sannan ta saka soyayyar ki a zuciyar Hassan din. Dan girman Allah Ruqayyah kar ki bamu kunya, ina tsananin ganin girman yaron nan wallahi kuma in da zaki bi ta ta shi na tabbatar ba karamin zaman lafiya zaku yi ba tunda yana son ki sosai. Da farko shi aure bautar ubangiji ne, ita kuma bauta ita ce abinda ake yi dan


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login