Showing 75001 words to 78000 words out of 300844 words

Chapter 26 - Tagwaye Book 1 Hausa Novel Complete

22 Dec 2024

2656

ta, ta girgiza kai sai ya mayar nasa bakin yace "to shikenan, bara in cinye abata amma kuma duk abinda ya biyo baya ke kika siya da kudin ki" tayi saurin dawo da hannunsa baya tana saka ayabar a bakinta tana ci a hankali idonta a cikin nasa har ta gama cinyewa sannan tace "na cinye to" ya dauko cinyar kaza yace "saura wannan" tayi kamar zata yi kuka "ni ayaba kawai kace min ai" yace "ai ba rantsewa nayi ba". A haka sai data ci kazar, shima kuma yaci. Tace "to na koshi, ka sake ni to" yana murmushi yace "ai ba rantse wa nayi ba" sannan ya juyo da fuskarta zuwa gare shi, ta rufe idonta, ya dora bakin sa akan nata.

A part din Hussain, a cikin Bedroom dinsa. Fatima tsaye a gaban mirror tana cire ear rings dinta. Hussain yana zaune a kujera yana amsa waya yana ta dariya, tana kallonsa ta mirror fuskarsa tana reflecting farin cikin da yake zuciyarsa. Tayi murmushi itama tana jin zuciyarta wasai. Bata da wani tension bata da pressure din komai sai farin ciki da annashuwar cikar burinta na zama matar Hussain. Rabin ranta. Ya ajiye wayar yana cewa "Time to switch off the phone, duk wanda bai kira ba yayi missing, duk kuma wanda bai zo ba shina yayi missing" ya karaso bayan Fatima ya tsaya yana tayata cire sarkar wuyanta yace "duk wanda bai ga kyalliyar Fatima ta yau ba yayi missing" tayi murmushi tana juyowa suna facing juna sannan ta mika masa hannunta yana cire mata awarwarayen ta tace "wanne mai missing din ne ya kira ka? Nasan duk wanda ya bar gidan nan yanzu ba zai kira ka ba" ya kamo yatsunta yana cire zobuna guda biyu da suke yatsun yana ajiye su a gefe yace "Sadiq ne, dan banza, bayan yaki zuwa bikin kuma shine zai kira ni yana min dadin baki" tayi murmushi tace "the prince of Abuja kenan. Shalelen Sarki Abdallah. Ina zai iya tahowa daga america ya bar his Arabian girlfriend?" Hussain yayi dariya yace "sai na gaya masa kina tsokanar sa" ta durkusa tana cire masa socks din kafarsa, sai ya kamota ya dago da ita yana kallon fuskarta yace "kinsan me yace min" ta girgiza kanta idonta a kasa, ya jawo ta zuwa jikin sa sannan ya kai bakinsa dai dai kunnen ta yace "yace wai insha strawberries before I kiss you, so that I will taste like a strawberry to you" ta danyi dariya tana sunne fuskarta a kirjinsa. Yace "kinsan amsar dana bashi?" Ta girgiza kanta ba tare data kalle shi ba, ya saka hannu ya dago fuskarta amma sai ta rufe idonta sai dai ta kasa daina murmushin da take yi, yace "nace masa ba zan sha din ba, cos when I kiss you, I want you to taste me, to taste Hussain not strawberry".



Nasan ba yawa, ayi hakuri


Tun da ta shiga motar bata ce masa komai ba, hankalin ta yafi karkata ga halin data baro yaruwarta dan taga babu alamar Hassan zai bata kofar da zata kubuce masa. Ta lumshe idinta a ranta tana fatan Allah ya huci zuciyar Hassan ya rangwantawa Ruqayyah, duk da dai tasan ko da Ruqayyah ta samu kafar zamewa to kuwa tabbas Hassan zai diga mata alamar tambaya, wannan zai kawo doubt a rayuwar aurensu, zargi kuma zaizo ya shiga ciki, daga nan komai zai rushe. Dan zargi yana lalata aure komai karfin soyayyar da aka gina auren a kai.

Adam ya kalleta sannan yayi ajjiyar zuciya yace "ni bani na kar zomon ba, ratayar ma kuma ba'a bani ba amma an daura min laifi" ta juyo tana kallon sa tace "wato bayan magana da yaren hausa har karin magana ka iya ko?" Yace "ina cin A+ a hausa language sanda ina school" ta danyi murmushi ta sake yin shiru. Yace "what's wrong? Ko har kin fara missing sister dinki ne?" Ta girgiza kanta da sauri, sai kuma taji hawaye ya taho mata. Tayi saurin gogewa kar ya gani amma da yake hankalinsa yana kanta ya gani din, yace "subhanallah. Kuka Sumayya?" Sai ya sauka gefen titi yayi packing duk kuwa da cewa babu motoci sosai akan titin. Ta sake goge idonta tana kokarin kirkiro murmushi tace "babu komai fa, mu tafi kawai, maybe kamar yadda ka fada ɗin ne, maybe missing Ruqayyah na fara tun yanzu" yace "is that right? Ni kuma a fuskarki banga haka ba, fuskar ki tafi kama da wadda take jin tsoron something will happen, ko kuma ma ya faru din" tana girgiza kanta tace "am just scared for Ruqayyah, ina tausaya mata rayuwar da zata yi a gidan Hassan" Adam yace "tausayi kuma? Ruqayyah fa oga Hassan ta aura, kin san kuwa kudin da mutanen nan suke dashi? She will never lack anything a rayuwarta" Sumayya tace "and that's the problem Adam. Kudi sune problem din. Babu wanda ya san halin Ruqayyah Kamar ni a duniya kuma ni din babu wanda nake zama muyi hirar Ruqayyah dashi dan ita din tamkar wani barin jiki na ce da bazan iya butulcewa ba. Ruqayyah bata taba zama satisfied a rayuwarta, Ruqayyah bata taba murna da abinda ta samu, abinda bata samu ba shi take so. Na san kaddara ce ta hada Hassan da Ruqayyah amma aurensa da tayi, tayi ne saboda kudinsa, saboda tana tunanin kamfanin sa ne, yanzu da akayi auren ta fahimci na dan uwansa ne ina tsoro abinda zata aikata akan hakan" sai ta bashi labarin haduwar Hassan da Ruqayyah, dan brief soyayyar su, furtawar da Ruqayyah tayi da bakinta cewa Hussain yafi Hassan kyau, nuna wa da tayi tafi son gidan Hussain akan na Hassan, kin zama ta kalli kayan lefen gimbiya, da kuma abinda ya faru a gurin siyan baki. Bata san me yasa ta iya sakin bakinta tayi masa wannan zancen ba maybe dan abin yayi mata yawa a ranta ne, maybe kuma dan dadin ac da comfort din motar ne, maybe kuma it is something else.

Bai yi mamakin maganganun Sumayya ba saboda shi dama yasan Ruqayyah bata da kirki, but bai san how deep rashin kirkin nata ya kai ba sai yau. Ya fahimci yaudarar Hassan take yi, ya fahimci kuma she is a danger to that nice lovely family. Amma kuma babu abinda zai iya yi akai, shi dai ba zai tafi gurin Hassan yace masa "matarka yaudarar ka take yi ba" in yayi haka yasan bayan aikinsa da zai rasa maybe har a cell sai ya kwana. Sannan babu wani problem din da hakan zaiyi solving dan Hassan din ba yarda zaiyi ba.

Ya juyo yana kallonta yace "now, what do you propose we do?" Tace "ban sani ba nima. Ni dai nasan sanda Ruqayyah tana gida ina yin iyakacin kokari na wajen ganin duk sanda zata yi ba dai dai ba na hanata. Ko da kuwa zata yi fushi dani. Amma yanzu bama tare babu kuma wanda zai ke bata shawara acan inda take, duk abinda yazo mata zuciyarta shi zata yi, wannan shine tsorona" yace "still you can do something" ya juyo sosai yana kallonta yace "na fahimci cewa ta yarda dake tana gaya miki dukkan sirrinta, to kiyi kokari ki yi keeping that relationship a tsakanin ku, ki ringa bibiyar ta kina jin abinda take ciki ta yadda zaki san plans dinta, ke kuma sai kiyi kokarin ganin kin dakatar da ita ko kuma in abin yafi karfinki ki gayawa wanda zai iya dakatar da ita. Kin fahimce ni?" Ta gyada kai. Yayi murmushi yace "and you stop worrying about her, yes ku twins ne kina son sister dinki and all that but still you have to put yourself first, rayiwarku daban daban kar ki zama so caught up a ta ta rayuwar ki manta da taki rayuwar, musamman yanzu da ba kwa tare, find something to enjoy, someone to love, someone like me" ya karashe maganar ta sigar wasa yana nuna kansa, tayi murmushi tana hararar sa, yace "ha! Finally tayi murmushi, you have no idea yadda murmushi yake yi miki kyau. Please don't ever let something stop you from smiling" ya mayar da motar kan titi suka cigaba da tafiya a hankali, har yanzu da murmushi a fuskarta tace "enough about Rukee, tell me about you. Who is Adam?" Yayi ajjiyar zuciya, yes ya gaya mata secrect dinsa amma har yanzu baya son yin maganar fast dinsa, not now, sai yayi kokarin chanja maganar yace "Adam is going back to school this session" ta bude baki cikin mamaki tace "really?" Proudly Yace "yes ma" tayi dariya "amma naji dadi wallahi na taya ka da murna kuma. But wait...wai har ka tara kudin" ya girgiza kai yace "nooo. Oga Hussain ya tambaye ni abinda yasa ban koma school ba sai nayi mishi bayanin plans dina and he said da zarar am fara siyar da form inje in siyo zai biya komai" Sumayya tace "Masha Allah. Allah ya biya shi da alkhairi" yace "ameen. Yana da kirki sosai, ni dai zan iya cewa ban taba haduwa da mutum mai kirkin sa ba, kowa kuma a gidan haka yake fada, daga haduwa ta dashi zuwa yanzu ba zan iya lissafa alkhairan da yayi min ba, kuma ba wai kyautar ce mafi muhimmanci ba, a'a yadda yake treating mutane shine abin so" Sumayya tayi murmushi tana tuno fuskar Hussain, bata tunanin ta taba ganin sa babu murmushi a fuskar sa.

Adam yace "yanzu sai inje in siyo mana tare ko?" Ta bude ido "noo. Kar ma ka fara" yace "why not?" Tace "baba ba zai yarda ba, in dai har ina karkashin sa ba zai bari wani ya dauki nauyi na ba" Adam yace "okay, sai mu dauke ki daga karkashin nasa ai, ki dawo karkashina" ta sunkuyar da kanta kasa tana wasa da fingers dinta, a hankali kamar mai magana da kansa yace "ban ma san ta yadda hakan zai kasance ba but ina son ya kasance din, ya ilahi see me through" ta dago kai tana kallonsa yace "I want to marry you amma ban san ta inda zan fara ba" suka hada ido briefly, tayi saurin sunkuyar da nata idon kasa dan bata da amsar da zata bashi.

Sai da yayi packing sannan ta dago kai tana kallon kofar gidan nasu, tayi ajjiyar zuciya tace "nagode sosai Adam. Sai da safe" yace "kar kiyi saurin yi min sallama, go and knock ina nan ina jiran ki. Know that in Baba ya dake ki I will feel it here" ya nuna kirjinsa, ta kalli kofar gidan sannan ta kalli agogon motar, 12:32. Ta ja numfashin tsoro tana bude ido sannan ta fita da sauri taje ta fara knocking kirjinta yana bugawa. Ba'a jima ba aka bude mata. Allah ya taimake ta yan uwan su da suka je dinner duk suna nan dan haka ba'a yi bacci ba ana ta hira ana mayar da magana. Ta juyo tana kallon cikin motar da Adam yake zaune suka hada ido sai yayi kissing hannun sa yayi mata blowing, ta dauke kanta tana blushing, hoping wanda ya bude mata kofa bai gani ba. Sai da ta shiga ta rufe kofa sannan ya juya motar ya bar layin, sai a lokacin ya lura cewa bata dauki jakar kayan sawar ta ba.

Sumayya ta samu ta shige cikin mutane, amma bata buyar wa Inna Ade ba dan sai data yi mata magana "Sumayya ke kuwa me yasa kika taho da daren nan haka? Ba suna da dakuna a gidan ba ba sai kiyi kwanciyarki ba in yaso da safe sai ki taho?" Sumayya tace "Inna kawai ji nayi ina son in taho gida, shine suka saka driver dinsu ya kawo ni har gida" Inna tace "nan gaba kar ki sake tahowa da irin wannan daren, gwara ki kira wayar baban ku ki gaya masa dare yayi zaki kwana, karkarinta yayi miki fadan me yasa kika bari dare yayi miki amma ba zaice ki taho da daren ba" Sumayya tace "insha Allah Inna" sai kuma ta fara tambayarta yadda ta baro Ruqayyah "bata kukan ko? Ranar nan ance min kuka tayi tayi" Sumayya taji wani abu ya taba ranta, Allah sarki uwa, ita bata san Ruqayyah duk ba wannan ne a gabanta ba, tace "ta daina kukan Inna".

Ruqayyah kam ta gaya wa yan garinsu a hannun Hassan, dan sam bai daga mata kafa ba duk kukan da take masa, a take ta yanke a ranta cewa shi din azzalumi ne bayan kasancewar sa solobiyo, ba wai nadamar aure kadai tayi ba, sai data yi nadamar taimakon sa dan bata san wannan shine sakamakon ta ba. Shi kuwa oga Hassan bakinsa har kunne dan exactly abinda yake so shi ya samu a gurin Ruqayyah wannan ya saka yaji duk sauran gurbin da bata gama cikewa a zuciyarsa ba yanzu ta cika shi taf. Sai yazo kuma ya fara aikin rarrashi, shine rarrashi shine gyaran gado shine jinya. Yawan kukan da tayi ya saka mata ciwon kai da zazzabi, da kyar ya samu ya lallabata ta sha paracetamol sannan ta kwanta ya lullube ta. Amma kuma sai ta saka masa rigimar cewa ba zai kwanta a kan gadon ba dan kar ya kuma tabata haka yana ji yana ganin lafiyayyen gado da lafiyayyar shimfida ga kuma matarsa a kai amma dolensa ya saka pillow a kasa a gaban gadon ya kwanta ya rufe idonsa saboda ya lura idonta yana kansa, sai daya tabbatar tayi bacci sannan ya hau kan gadon ya jawo ta jikinsa ya lullube su yana ajiyar zuciya. Me yafi aure dadi? Da murmushi a fuskarsa bacci ya dauke shi.

Da safe ma bata chanja zani ba, zaman jinyar ya cigaba dayi. Anan akan gado taci abincin safe da na rana, sallah kawai take tashi tayi itama sai ya fita tukunna wai dan kar yaga yadda take tafiya yayi mata ɗariya. "Ba zanyi dariya ba fa" ya fada yana kokarin gimtse dariyar, ta saka kuka "wallahi gashi nan dariyar zaka yi, gashi nan na gani bakinka yana abin dariya" dariyar ta kubuce masa yayi, tace "ba ga shi nan kana dariyar ba" ya rufe bakin yace "na daina, bara in fita in baki guri" ya fita yana cigaba da dariyar yarintarta.

Yana fita yaji mutane suna shigowa da sallama, ya sauka yana amsawa. Yan uwansu ne kaf dinsu da suka zo daga Gombe suka shigo, daga alama sallama zasuyi musu. Ya kara fadin murmushin sa yana karasa saukowa sannan ya gaida manyan ciki yaran kuma suka gaishe shi. Suka zazzauna shima ya zauna dattijan ciki suna tsokanar sa wai yana kyallin goshi. Ya shafa goshin nasa kamar mai son gogewa yana dariya, ya kasa daina dariya. Wata a ciki tace "ina amaryar to? A kira mana ita mana muyi sallama" ya shafa kai yace "tana sallah amma ban sani ba ko ta idar yanzu" Zulaihat data rako su ta mike tace "bara in dubo" ya bita da kallo kehar ta hau saman, a ransa yana tunanin irin dramar da za'ayi da Ruqayyah a gurin saukowa daga bene. Daga nan suka cigaba da hirar su shida yan uwansa, kawai sai jin muryar Ruqayyah yayi a bayansa, tana gaishe da mutanen gurin, suka amsa da amarya bata laifi ko ta kashe dan masu gida. Sai da ya waiga sannan ya lura cewa a tsaye tayi gaisuwar, yaji babu dadi a ransa amma sai ya bata uzuri da ciwon da jikinta yake yi, ai tayi ma kokari data iya saukowa daga stairs din. Yace "Zulaihat tashi ki kawo musu ruwa" nan take suka ce "a'a alhamdulillah, yi zamanki Zulaihat ba zamu iya sha ba" "ni cikina kamar zai fashe saboda koshi" "kayan gara muka samu a gidan Hussain, Fatima tayi ta loda mana wai sai munci, sai da kyar ta rabu damu kagan su can ma tray guda ta aika mana dashi gurin Amina wai ma ci a hanya in munji yunwa" Hassan yace "ta kyauta, kamar ta san ummah (kanwar kakarsu) dama da cikin zani, bata koshi" tace "ko ma cikin menene dani ci zanyi, dama zubi na daban tayi min kuma tace kar in bawa kowa in ajiye a firji in na koma gida" Ruqayyah tace "can kuka fara shiga kenan?' Yadda tayi maganar yasa duk suka juyo suna kallonta tana tsaye a bayan kujerar da Hassan yake kai, Ummah tace "eh, can muka fara zuwa, shine a farko ai" kadan ya rage Ruqayyah bata bata amsa da cewa ai Hassan ne babba ba, sai kawai ta rabu da ita saboda Hassan yana gurin amma a zuciyarta tana tunanin ba suyi dai dai ba, ai Hassan ne babba dan haka gidan sa ya kamata su fara zuwa ba wai suje gidan Hussain sannan su zo suna basu labarin abinda suka ci a gidan ba, wannan gaskiya a ganinta rashin adalci ne da nuna bambanci.

Shirun da gurin yayi ne ya saka suka fara mikewa daya bayan daya "to mu zamu tafi, Allah ya sanya alkhairi, sai mun dawo suna kuma" suka fada cikin tsokana, Hassan yayi murmushi sannan ya bisu a baya zaiyi musu rakiya, Ruqayyah kuwa ko ci kanku bata ce musu ba ta juya ta komawarta sama.

Kwanaki suka wuce suka samar da sati biyu A cikin sati biyun nan kowane amarya da ango sun ci amarcin su son ransu. Hussain da gimbiya suna ta zuba lafiyayyiyar tsadaddiyar soyayyar su irin ta wayayyun ma'aurata. Duk yawon Hussain a wannan satin babu inda yaje in banda gidan Aunty. Amma fa shi nasa gidan kullum a cike yake da mutanen sa da mutanen gimbiya wadanda suke zuwa ganin gida da kuma cin arziki, duk kuma wanda yazo ɗin to sai yaci arzikin ya kuma bar arzikin a inda yake. Dan ita ma Fatima budadden hannu ne da ita babu yadda zaka shiga gidanta ka fito ba tare data baka wani abu ba, in ka hadu da Hussain shima ya kara maka. Kullum daga gidan aunty ake yin girkin safe rana da dare a kai gidan Hassan da kuma gidan Hussain, bayan yan aikin da Aunty ta basu kowa bibbiyu duk da cewa Fatimah ta taho da

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login