Showing 117001 words to 120000 words out of 300844 words

Chapter 40 - Tagwaye Book 1 Hausa Novel Complete

22 Dec 2024

2675

cigaba da wasa da yaron sa ko ta kanta bai bi ba.

"Kayi hakuri" tace tana kakaro hawaye, "dan Allah kayi hakuri ni bana son wannan fushin naka wallahi ni sai inji gidan gabaki daya yayi min zafi, mi duniyar ma gaba daya zafi take min in kana fushi dani. Tun jiya nake ba ka hakuri fa, sai maganganu kake gaya min dan nayi kuskure sau daya" ya ajiye Yusuf yace "kin kwantar da Aminu? Kar ki bar min yaro akan kujera ya fado yaji ciwo" daga haka ya mike ya shiga toilet.

Har washegari basu dai daita ba, wannan yada bata samu damar tambayarsa zuwa gurin dinner din ba sai text din ban hakuri ta tura wa Minal sannan ta kashe wayarta dan tasan ba zata barta ta huta ba da masifa. Shi kuma Hassan, washegarin neman yadda zasu zauna da Hussain yake yi saboda ya samu ya tambaye shi abinda yake damunsa. Basu samu zaman ba har yamma, yana shigowa gidan ya gansu sun shigo shi da driver dinsa Adam.

Adam ya fito ya gaishe shi, ya amsa ba yabo ba fallasa kamar kullum, amma yau sai ya kara da "yaya karatu?" Adam ya shafa kansa yace "alhamdulillah oga" Hussain ya fito yana cewa "can you believe yaron nan First class yaje ja a school? Gashi wai yanzu har suna level two kamar fa yau suka shiga" Hassan ya kirkiro murmushi yana "good for him" sai ya juya kan Hussain "yalllabai ina son magana da kai fa, tun dazu nake neman ka kana can kana gantali" Hussain yace "ba gantali na tafi ba, napeps din nan ne aka kawo su naje gani, dama ina so mu zauna ayi shortlisting wadanda za'a bawa" Hassan ya gyada kai. Haka Hussain yake fitar da zakkar sa duk shekara, baya rabon kudi ko kayan abinci, wadannan sai dai idan normal kyauta ne amma zakka yafi son ya bayar da abinda mutum zai yi sana'a dashi. Ganin yadda Baba yake morar Napep dinsa ya sa ya yanke hukuncin zakkar bana ta Napep zaiyi ga matasa.

Tare suka jera zuwa cikin gidan Hussain sannan suka hau har samansa suka zauna a palon sa. Ya dauko takardar da aka kawo masa ta list din eligible mutane kowa da description dinsa yace "a cikin wadannan za'a zabi wadanda za'a bawa" Hassan ya karbi takardar yana noticing yawan mutanen sai ya ajiye ta a gefe yace "forget about them. Tell me about you. Me yake damunka?" Hussain ya saki baki yana kallon sa yace "ni? Me ka gani a tare da ni? Ni babu abinda yake damuna ni lafiya ta kalau" Hassan ya gyara zama yace "hmmm really? Wannan maganar da kayi ita ta tabbatar min akwai abinda yake damun naka kuma ta nuna min cewa abin is related to your health. Tunda ni dai ban yi maganar ciwo ba amma har kace lafiyar ka kalau" Hussain ya saka hannunsa a cikin gashinsa sannan ya cire yace "to mr smarty-pants, ni babu abinda yake damuna health wise ko other wise".

Hassan ya kwantar da kansa a jikin kujera yana kallon Hussain din da yake ta rarraba ido a dakin kamar yau ya fara ganin dakin. Sannan yace "is it about the fertility?" Hussain ya bata fuska yace "no. In baka yarda ba ma bara in dauko maka result din ka gani, sun ce komai lafiya lau sun kuma bamu drugs da kyma shawarwari. Ni ka tuna min ma, ya kamata in tafi gurin matata yanzu....." Hassan yace "to idan ba akan fertility bane ba akan menene?"

Hussain ya mike yace "na gaya maka babu komai, babu komai fa. Please ka bar maganar ta wuce haka nan" Hassan ya mike shima yace "bani kadai ba, hatta Aunty sai da ta lura akwai damuwa a tattare da kai. Tell me damuwarka, that's all I asked" Hussain yace "damuwata a yanzu itace yadda ka damu da abinda babu. Ni babu abinda yake damuna" Hassan ya daga kafada yace "shikenan, fine, kar Allah yasa kayi min magana din" ya juya ya bar gurin amma a ransa yana mamakin girman abinda har Hussain yake boye masa shi, mostly shine mai boye magana ba Hussain ba, Hussain zai fadi abinda yake ransa ne kawai ko a mutu ko ayi rai.

A gida ya tarar Ruqayyah ta shirya masa abinci, taci kwalliya da shigar kananan kayan da tasan yana so. Yana hawowa sama ta mike da twins are both arms dinta tace "sannu da zuwa mijina. Muna nan muna ta jiran ka ni da boys" ya karaso yana pinching cheeks din yaran da suke ta kokarin miko masa hannu. Yace "yauwa sannunki, ya gida?" Ba tare da ya jira amsar ta ba ya zagaye ta zai wuce, cikin muryar kuka tace "wai kai ba zaka hakura bane ba, na baka hakuri na baka hakuri, nayi kuka nayi kuka, kuskuren da nayi guda daya amma ba zaka yafe min shi ba"

Ya juyo yana kallon ta, yana kallon hawayen da take matsowa daga idanunwanta, sai yaga kukan nata yayi masa kama da kukan karya, hawayenta yayi kama da crocodile tears, sai ya samu kansa da tambayar kansa in wannan shine irin kukan da take yi masa all the times kuma me yasa bai taba lura da cewa ba kukan gaskiya bane ba sai yau? Ya dawo ya karbi Aminu daga hannunta yace "ni bance miki ba zan yafe miki ba ban kuma ce miki ban hakura ba kawai dai ina bukatar tume alone to process things, am surw zamu dawo kamar yadda muke ada ko? Besides, love concurs all"

Ta dan yi murmushi tana goge hawayenta tace "yes, love. Shine abinda na sani, abinda na sani shine ina son mijina sosai bana kuma son bacin ransa. Kaga fa yau ake yin dinner din Minal amma saboda bana so in tambayeka ranka ya baci shi yasa ban ma tambaya ba ballantana inje" ya karasa share mata hawayen yace "good girl. In ba kyason bacin raina ba dinner din Minal ce kadai ba zaki je ba, harka da Minal din gabaki daya nake so ki daina. Yes, nasan childhood friend dinki ce saboda makotan ku ne and all, but ni kuma yanzu mijinki ne kuma nace bana son harkar ki da ita" ta sunkuyar da kanta sannan ta gyada kai da sauri, yace "good" ya juya zai tafi daki tace "ga abinci fa, abincin da kafi so shina dafa maka" ba tare daya juyo ba yace "zan ci, sai nayi wanka na huta tukunna".

Har sati ya zagayo Ruqayyah bata gane inda Hassan ya dosa ba, tayi amfani da hawayen, tayi amfani da kalaman, tayi girkin, har sanitation din dakinsa tayi masa amma sai ya gyada kai yace mata "Nagode" yayi tafiyar sa. Shi kuma Hassan ba wai case din Ruqayyah bane ba kadai a ransa, da akwai case din Hussain, tunda ya dawo ya kasa gae kansa yanzu ma gani yayi kamar yana avoiding dinsa baya son su zauna su biyu a guri daya sai dai in da third party Saboda yasan suna kadaicewa zai dame shi da tambayar menene problem dinsa. Shi kuma akan sa Hussain ya ki barin zuciyarsa tayi processing abinda doctor din ya gaya masa, ya san cewa akwai chances na cewa doctor din is wrong but tunda maganar ta daki kunnensa yaji a jikin sa cewa gaskiya ne maganar.

Tun da yayi hankali, kullum zuciyars tana kan mutuwa, kullum gani yake ba zai kai gobe ba zai mutu kuma bai taba jin cewa hakan ya dame shi ba, but he always thought about sudden death, accident da sauran su. Sannan kuma abinda yasa maganar ta taba shi sosai shine rashin Da, yaci burin ya haihu kafin ya mutu, yadda sunan sa ba zai taba ba, blood line dinsa zai cigaba da tafiya a duniya. Amma kuma sai da yake tsaka da neman haihuwar sannan wannan labarin zai riske shi.

Wannan shi yasa ya gudo daga America, saboda baya son ayiasa test din ballantana a tabbatar masa da abinda likitan ya fada, ya fi son ya cigaba da rayuwarsa without having to go through all that cancer treatment processess sai dai in mutuwar tazo kawai ya tafi. Ya san babu mai kara masa ko da numfashi guda daya ne akan wanda aka riga aka rubuta masa.

But.......ten days after.

Ya tashi da safe ya gama using toilet sai yaga jini, and his heart sank. A kasan toilet din ya zauna ya dafe kansa da hannayensa biyu yana lissafo rayuwarsa tun daga wayonsa zuwa yanzu da yake jin tana crashing down on him. So yake yaga mistakes dinsa ko zai iya gyarawa, so yake yaga abubuwan da yake so yayi kuma bai yi ba dan yayi kokari yayi su yanzu. Ba mutuwar ce damuwar sa ba sam, rabuwa da loved ones dinsa ne damuwarsa. A wanne hali zasu kasance bayan babu shi? Wacce irin damuwa zasu shiga ta rashin sa a tare da su?

Ya tuna Hassan, he is going to be broken to pieces but with time zai yi surviving saboda yana ga kakkarfar zuciya duk kuwa da yasan ba zai taba komawa dai dai ba, saboda su biyun kowannen su tamkar sashi ne na ruhin danuwansa dan haka rayuwar Hassan will take a sharp change without him, sai dai yayi masa addu'ar Allah ya bashi strength din da chanjin zai zama for the better.

But halin da Hassan zai shiga bai yi breaking heart dinsa ba kamar halin da Fatima zata shiga. His poor innocent princess. Sai yaji kamar bai yi mata adalci ba daya aure ta, ya cika ta da soyayyar sa ya mayar da ita karamar bazarawa without even a child to look at and remember him. Auren Fatima is the best thing that happened to him and rayuwar da yayi da ita so far are the best days of his life. Looking at his life sai yaga his only regret is not having a child of his own, someone to carry on his name tunda dai duk yadda yake da Hassan babu ta yadda za'a yi yayan Hassan suyi bearing sunansa.

Ya fara lissafin abinda ya kamata yayi yanzu, shin ya tara family dinsa ne gabaki dayan su ya gaya musu halin da yake ciki su taya shi da addu'a ko kuma ya barsu sai mutuwar ta zo sa sani?

Ya tashi ya shiga shower ya kunna wa kansa ruwa, kafin ya fito ya yanke shawarar abinda zaiyi. Bai samu Fatima a dakin ba, ya san tana kitchen tana shirya masa abinda zai ci. Poor sweet thing. Da sauri ya shirya ya fita ta hanyar da yasan ba zasu hadu da Fatima ba dan baya son ta ganshi a wannan yanayin dan zata iya karanto wani abu a fuskarsa. Yana so yaje ya samo wa kansa strength dan haka inda zai samu ya tafi.

A palon kasa ya tarr da Ruqayyah daga dukkan alamu aiki take yia kitchen, ta saki baki tana kallonsa da mamaki sai kuma ta gaishe shi, ya amsa yana tanbayarta Hassan tace yana daki, "bara ayi masa magana" ya dakatar da ita "no, yi aikin ki kawai, bara inje" daga nan ya wuce ta ya hau saman. Ta bishi da kallo, tana jin motsinsa har taji ya bude kofar Bedroom din Hassan ya shiga, ta tabe baki, "yau kuma wani kuturin wulakanci ne ya tashi za'a shigar min har dakin miji?"

Hussain ya shiga dakin yana karewa tsarin dakin kallo, it has Hassan written all over it, tas tas komai a arrange kamar yadda yake a kowanne dakin sadaya sani. Babu ko digon datti a kasa. Ya zauna a bakin gado yana jin kewae Hassan already tana ra tsa zuciyarsa. Sai ya jawo pillow ya kwanta ya kifa fuskar sa a kai.

Hassan ya fito daga toilet da robe a jikin sa hannunsa kuma rike da towel yana gige ruwan kansa. Ya tsaya yana kallon Hussain da sakakken baki, yace "kai! Me kake yi min a kan gadon aure na?" Hussain ya dago kansa yana kallon sa da lumsassun idanuwa yace "kar ka yi min gori Malam, nima ina da gadon auren a gidana, klin kana son ka rama kaje ka kwanta kaima akai" Hassan yace "ni ai ina da hankali, ba zan kwanta a gadon matarka ba. Kuma wannan pillown na Ruqayyah ne ba nawa bane ba" Hussain yayi jifa da pillown ya jawo dayan, Hassan yayi dariya yana cigaba da goge kansa.

Hussain yace "ka tuna sanda nake baro dakina in taho naka in kwanta in ce acn dakina bata da sanyi?" Hassan yace "kuma in kazo ka takura min kace sai akan pillow na zaka dora kanka wai yafi laushi" Hussain yayi dariya yace "har zuwa kake ka siyo min pillow dan in bar maka naka, ka saka aka zo aka gyara min ac amma duk ban dai na zuwa ba" Hassan yace "ai dama babu abinda ya samu acn, kawai dai kana so ka takura min ne ka hana ni jin dadin bacci"

Hussain ya danyi shiru yana kallon wani hoton su a cikin karamin frame a gefen gado, da uniform din secondary school a jikin su duk kanin su suna murmushi, ya tuno ranar da aka dauki hoton ranar da suka yi wani match ne kuma suka yi winning, a lokacin Hussain cewa yayi footballer zai zama tunda yaga suna saurin yin kudi, ya juyo yana kallon Hassan yace "ba wai dan in takura maka bane nake zuwa dakin ka ba, ina zuwa ne dan ina son ka, bana son rabuwa da kai" Hassan ya tsaya da towel din a hannunsa yana kallon Hussain amma ya kasa cewa komai, Hussain yace "promise me idan na mutu kullum zaka ke zuwa kabarina kana yi min addu'a" Hassan ya saki towel din hannunsa yace "stop it" amma bai ga alamar wasa ko murmushi a fuskar Hussain ba, sai ma yaga murmushin da yake masking damuwarsa da shi ya gushe sai damuwar ta bayyana gabaki dayan ta. Ya bude baki a hankali yace "I am dying bro"

Hassan yace "No!" Da kakkaurar muryar da sai da dakin ya amsa. Sannan ya tako zuwa gaban Hussain fuskar sa babu ko digon annuri ya nuna shi yace "don't ever say that again". Hussain ya juya fuskar sa gefe yace "ko da hakan ne gaskiya? Baka son in fada maka gaskiya? Ni da nazo da niyyar in samu kwarin guiwa daga gareka sai kuma ka satar min da guiwa ta? Zuwa nayi fa dan ka bani courage, dan bani da inda zan je inda yafi nan gurin ka"

Hassan ya zauna a kusa dashi yana juyo da fuskarsa yana so ya karanto alamar wasa a idonsa amma ya kasa karantowa yace "yau ba 1st of April bane ba, ka tuna ranar da kayi min April pool kace min dakina ya kama da wuta? You are fine brother, you look good, very good even." Hussain ya dan yi murmushi yace "Cancer ce Hassan, colon cancer" Hassan yana girgiza kansa da sauri ya sake cewa "no! Karya suke, duk likitan daya gaya maka karya yake yi, he is a crook doctor da yake using fake machines"

Sai Hussain ya bashi labarin yadda suka yi da likitan daya duba su shida Fatima a america, sai Hassan yayi murmushi yana jin sanyi a ransa yace "you see? Kana tayar da hankalin ka a banza kana kuma tayar min da hankali Hussain. Ta ya fertility doctor zai diagnosing Cancer? Karya yake yi, he is wrong, he is very wrong" Hussain ya girgiza kansa yace "he is not wrong bro" sai ya bashi labarin jinin da ya gani yayi a toilet.

Murmushi Hassan yabace sai kuma ya sake yin wani yace "that doesn't mean anything, zata iya yiyuwa basir ne ko rana ko wani abu na daban. Wannan zaman da kake yi a jirgi ma ba dole basir ya kamaka ba?" Hussain ya girgiza kansa cikin raunanniyar murya yace "Hassan Please, don't give me false hope mana" Hassan bai bashi amsa ba sai ya mike ya dauko wayar sa da take jikin chargi ya kira family doctor dinsu yace "ina so dan Allah ka bincika mana best oncologist ko a wacce kasa yake kayi mana booking din ganinsa"

ya ajiye wayar yana kallon Hussain daya koma da baya ya kwanta a kan gadon yace "zamu je ayi wannan test din daka gudo baka tsaya anyi maka ba. Anan zan tabbatar maka cewa likitan is wrong" Hussain yace "what if he is right?" Hassan yace "then zamu ne mi magani, babu wata cuta da bata da magani Hussain. You will have the best care in the world" Hussain yayi murmushi yace "you are beginning to sound like me. But you are forgetting something, even the best doctor in the world ba zai kara min second daya a cikin lokacin da Allah ya kayyade min ba a duniya. Ni ba mutuwa ce problem dina ba, dan haka ba zan yi going through wannan procedure din ta doctors ba, that chemotherapy treatment and those surgeries da ba zasu kare ni da komai ba. Ko so kake in koma kamar aljani kafin in mutu? So kake doctors su ringa gutsirar hanji na piece by piece har sai ya kare sannan su barni in tafi? In zan mutu Hassan na fi son in mutu in one piece. At least nafi son in mutu looking my best ba wai kwarangal da kai babu gashi ba" ya karasa maganar yana murmushi.

Hassan yace "wannan ba abin wasa bane Hussain. Look, dan Allah yace ka yarda da kaddara ba ya na nufin in ciwo ya kamaka kayi folding hannunka ka jira mutuwa ba. Promise me zaka bini mu tafi" Hussain yace "zan bika muje dan ayi maka confirming abinda ni na riga na sani. But I will not go through those cancer treatment processess".

Wannan littafin na siyarwa ne, in kika ganshi a wani gurin na sata ne, in kina son karanta halaliyar ki ki yi min magana through WhatsApp ta wannan number din 08067081020


*The Surgery*


Tun Ruqayyah tana zuba idon ganin saukowar Hussain har ta hakura ta hau saman, ta ga kofar dakin a rufe tasan kuma


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login