Showing 120001 words to 123000 words out of 300844 words
suna ciki, tayi tsaki ta shiga nata dakin, sai data yiwa twins dinta wanka ta shiryasu sannan ta fito dasu falo, still tana tunanin menene suke ta magana haka a cikin daki. Ta kira mai renon twins ta bata su tace su tafi gidan Aunty duk da tasan cewa basu gaisa da baban su ba ballantana uncle din su daya shigo, sai dai kuma ita bacci take so ta koma.
Suna tafiya Hassan ta bude kofa suka fito shida Hussain, fuskar Hassan kadai ta saka taji gaban ta ya fadi. Ya dan kalle ta yace "zamu fita, sai mun dawo" ta dan bata fuska "abinci fa? Ba ka karya ba fa" ya wuce ta yana cewa "ki ajiye min, inna dawo zan ci" shi a ransa ya ma manta da wani abu wai shi abinci. Hussain yace "sorry Madam. Na dauke miki miji ko? Aro na dauka zan dawo miki dashi in one piece". Ta bi si da kallo har suka fita a ranta tana tunanin something is up, kuma koma menene it is not good.
A ranar suka gama binciken oncologist din daya kamata Hussain ya gani, a India yake, a ranar kuma suka fara kokarin booking yadda zasu ganshi.
Ruqayyah tana zaune a palo suka kuma shigowa tare shida Hussain, gaisuwar ta kawai Hassan ya amsa ya wuce daki, Hussain ne ya dan tsaya yayi wa twins wasa sannan yabi bayan Hassan din suka shige dakin sa. Ruqayyah ta saki baki tana kallon wani sabon salo wai kiran sallah da usur sai kuma taga Hussain ya fito shi kadai yayi mata sallama ya fita.
Bata bi ta kan Hassan ba sai data gama duk abinda zata yi ta kwantar da babies dinta tayi wanka tana shirin kwanciya sannan dai tace bara ta leka shi. A kwance ta tarar da shi ya lullube har kansa kuma ya kashe acn dakin. Ta zauna a bakin gado tana dan bude shi kadan sai dai tiririn da taji yana taso wa daga jikin sa kadai ya sa ta fahimci cewa bashi da lafiya
"subhanallah. Ai zazzabi ne a jikin ka mijina" ya bude ido sa yana kallon ta, tayi kokarin daga shi "ka tashi ka sha magani, ko in kira Hussain ya kaika asibiti?" Sai ya kama hannun ta ya rike "Hussain? Bana son komai ya samu Hussain" daga yadda yayi maganar ta san magagin zazzaɓi yake yi, tace "babu abinda zai samu Hussain kuma kai ma babu abinda zai same ka, zazzaɓi ne kawai kake yi" tayi kokarin tashi sai ya jawo ta jikinsa yana cewa "babu abinda zai same shi? Thank you, ohhh thank you" ya fada yana shigar da ita cikin bargon sa tare da lullube su tare.
Washegari Ruqayyah ta tashi da murnar Hassan ya fara saukowa, a ranar ne kuma doctor din da suka yi contacting jiya ya aiko musu da email na cewa zasu iya ganin sa next week, dan haka tun a ranar suka fara shirye-shiryen tafiya.
A dakin Fatima tana zaune tana kallon Hussain da yake shirya mata maganar zuwan da zasuyi India shida Hassan saboda Hassan din da yake son ganin likita a can. Tayi kamar zata yi kuka, "kuma yanzu tafiya zakayi ka barni? Ni baka taba yin tafiya ka barni ba fa dan Allah. Ni bana son ka tafi ka barni, zan biku kaji?" Yayi murmushi yana zama kusa da ita. "Haba Princess, in nace zan tafi dake Hassan ba zai ji dadi ba tunda shi yace ba zai tafi da Ruqayyah ba, kinga babu dadi ko? Itama Ruqayyah ba zata ji dadi ba. Ki bari akwai tafiyar da zan shirya mana muna dawowa daga indiyan nan, daga ni sai ke kuma duk kasar da kike so ita zaki zaba" ta fara biga kafarta kamar me shagwaba "ni dai bana so ka tafi ka barni. To ka lallaba Hassan din mana ya tafi da Ruqayyah kaga sai mu tafi gabaki daya"
Yace "Ruqayyah tana shayarwa kin manta? Tafiyar ba zata yi mata dadi ba da babies har biyu ko?" Fatima tace "zan ke tayata rainon ai, sai in karbi daya in bar mata daya" ya hade hannayensa "Please Princess kiyi hakuri, nima bana so in tafi in barki babu yadda zanyi ne" sai yaji maganar tasa tana bada wata ma'ana ta daban wadda tasa yaji jikinsa yayi sanyi. Ita kuma sanyin da taga jikin nasa yayi ne ya sa ta sauko. "Shikenan, Allah ya kiyaye hanya. Amma dan Allah kar ku dade. Kuma kullum sai munyi video call sau biyu" yayi murmushi yace "sau uku ma zamu ke yi, safe da rana da daddare".
Ruqayyah kuma da Hassan ya gaya mata zancen tafiyar tasu cewa tayi "yanzu daga zazzaɓi sai tafiya India? Bana baka magani ba tun a ranar kuma har ka warke" ta fada cikin zolaya, sai dai baiyi dariya ba kuma bata ga alamar zaiyi dariyar ba. Yace "bamu san tsahon lokacin da tafiyar zata dauke mu ba amma muna saka ran insha Allah ba zamu dade ba"
Ta fara kokarin kawo masa korafin cewa ya kamata su tafi tare amma a take ya nuna mata hakan ba zai yiwu ba, daga shi sai Hussain zasuyi tafiyar. Dole ta ja bakin ta tayi shiru, a ranta tana mita "ni sanda ina da ciki har na haihu cewa yayi ba za'a fita dani ba, amma da yake shine daga yin zazzaɓi har anyi booking ganin likita a India"
Babu bata lokaci suka tafi, su ka bar yan'uwa da iyalin su da tunani amma kowa ya dauka Hassan ne marar lafiyar musamman yadda a cikin kwana biyu yayi rama sosai sannan annurin fuskarsa gabaki daya ya disashe. Suna isa Mumbai suka zarce asibitin da Dr din yake suka shigar da information dinsu da komai sannan suka tafi suka kama hotel. Ranar kwana suka yi suna hirar childhood memories, irin rashin jin Hussain da kuma kaffa kaffan Hassan, farkon kafa H and H da kuma yadda tafiyar ta kasance zuwa yanzu. Sai kuma suka yi hirar future dinsu yadda suke son ta kasance, yadda suke da burin yayansu su taso tare and maybe wata rana idan har an samu wadanda suka daidaita a tsakanin su a hada su aure.
Sai bayan da suka yi sallar asuba sannan suka kwanta suka yi bacci tunda appointment din Hussain sai 12. Bayan sun tashi suka yi wanka suka shirya suka fita waje suka ci abinci sannan suka tafi asibitin, duk cikin su babu wanda yake maganar ciwon Hussain amm kuma abin duk yana ransu suna kuma tsoron sakamakon da binciken zai bayar.
A office din bayan sun gaisa da doctor din sai ya saka Hussain ya kwanta a kan wani gado ya mike kafafuwansa sosai sai doctor din ya tsaya a kusa dashi yana yi masa tambayoyi yana amsawa, sai ya dora hannunsa a kasan cikin Hussain ya dan danna da dan karfi, Hussain ya mike zaune da sauri yana damkar hannun doctor din ido a waje yace "ouch, zafi sosai fa" sai doctor din ya bishi da kallo kawai, Hassan ya mike da sauri yana rike hannun Hussain wanda lokaci data gumi ya rufe masa fuska, jikinsa har rawa yake yi.
Sai doctor din ya koma ya zauna yayi rubutu a takarda. Hassan ya koma gaban doctor din ido a bude yana tambayar, "yani zafi, me hakan yake nufi doctor?" Doctor ya dago yana kallon Hassan, ya kasa kallon Hussain yace "ba zan iya ce maka komai ba a yanzu. Zan tura ku dakin gwaje gwaje za'a yi hotuna kuma za'a dauki samples ayi gwaje gwaje. Sai result ya fito sannan zan iya cewa komai" Hassan ya karbi takardar da sanyin jiki sannan ya taimaka wa Hussain ya mike suka fita Hussain yana rike da marar sa. Wata maaikaciyar lafiya tayi musu jagora zuwa katon lab dinsu, inda aka fara gudanar da bincike sosai akan Hussain amma sai daya ja musu kunne kar wanda ya kuma danna masa marar sa, nurses din suka yi dariya suka ce ba zasu yi ba.
Har dare suna can, sai da suka yi exhausting energy din Hussain gaba ki daya sannan suka rabu dashi yana ta yi musu mita. Suka ce washegari ya dawo za'a yi mishi abinda suka kira da colonoscopy. Hassan dai ya lallaba shi suka tafi, a daren Hussain yayi ta bincike akan menene colonoscopy din sai ya fahimci zasu zura mishi micro cameras ne cikin hanjinsa ta yadda zadu ga ko menene a cikin hanjin a screen, anan zasu fi fahimtar in akwai ko babu kuma zasu san exact location din da ciwon yake da kuma stage din da yake ciki. Shi dai a ransa baya so, zuciyarsa tana ta gaya masa cewa ya hada kayansa cikin daren ya gudu ya dawo Nigeria amma yasan in ya gwada yin haka sai sunyi rigima da Hassan, kuma shi yayi alƙawarin ya daina fada da Hassan amma kuma yasan gobe za'a tabbatar masa da cewa yana da wannan ciwon, shi kuma baya son a tabbatar masa din saboda yana son ya cigaba da rayuwarsa freely har zuwa mutuwarsa, wadda yasan zata iya riskar sa gobe ko kuma nan da shekaru masu yawa, Allah ne kadai masani, akwai hikima a cikin tsarin ubangiji da ya hane mu da neman sanin gaibu dan ba zai yi maka dadi ba, ta yaya zaka iya rayuwa in aka gaya mata nan da wata biyu ko uku zaka mutu?
Bai gudun ba ya zauna, ranar da sassafe suka je suka zuwa akayi preparing Hussain aka yi masa allurar bacci, sai Hassan yaji zuciyarsa ta karye dan haka doctor din ya amince masa cewa zai iya shigowa ayi a gabansa. "It is not a surgery, we are just going to view the tumor on a screen and classify it. Then take a sample, that's all".
Hassan yana zaune rike da hannun Hussain aka gama procedure din, doctor din yana nuna masa abinda yake gani yana kuma yi masa bayani, ya nuna masa ciwon da idonsa ya gani ya kuma gaya masa tun jiya da yayi wa Hussain manual exam ya fahimci cewa akwai ciwon da gaske, ganin hankalin Hassan ya tashi sosai sai ya kwantar masa da hankali ta hanyar gaya masa cewa ba wani problem bane ba tunda an yi detecting da wuri kuma akwai means na neman magani babu wani problem, ya gaya masa kuma yayi iyakacin kokarin sa na ganin ya kwantar wa da Hussain hankali dan lokuta da dama tashin hankali shi yake kashe patient ba wai ainahin ciwon ba. Ya kuma jaddada masa muhimmancin jin surgery da wuri "ita cancer tana spreading ne, tana kara yaduwa, in aka barta zata ci gaba kuma ba zata tsaya a hanjin kadai ba zata taba wadyu vital organs din da suke cikinsa. Dan haka I suggest ayi surgery as soon as possible. Daga anyi surgery an cire tumor din sai kuma a kashe surrounding area din da radiotherapy yadda in akwai saura ma zata mutu" Hassan ya gyada kansa yana assuring doctor din cewa kafin su bar kasar za'a yi surgery din. Ba zai bar kasar ba sai da healthy Hussain.
Sanda Hussain ya farka, Hassan ya gani a gefensa rike da hannun sa ya kwantar da kansa a jikin gadon da Hussain yake kwance idonsa a rufe. Hussain ya dago hannunsa ya dan taba fuskarsa yace "hey bro" Hassan yayi saurin bude kumburarrun jajayen idanuwan sa ya dora akan Hussain, sai yaga Hussain din yayi masa dariya yace "have you been crying?" Ya sake dariya "sai na gaya wa Ruqayyah mijinta rago ne" Hassan ya harare shi ya tashi ya shiga toilet ya wanke fuskarsa ya fito sai ya tarar dashi yana kokarin tashi zaune sannan ya zare drip din da aka saka masa. Ya kamashi yana kokarin kwantar dashi amma yaki kwanciya ya tashi yana cewa "ni yunwa nake ji wallahi, kamar anyi min sata a hanji na" sai kuma ya bude ido yana kallon Hassan yace "gaya min gaskiya, ko har sun yanke hanjin ne?" Sai kawai yayi dariya ya kama hanyar fita.
Hassan ya bishi amma yaki dawowa, sai da ya tuna masa da cewa rigar asibitin ce a jikin sa sannan ya dawo briefly ya mayar da kayansa ya kuma fita. A dole Hassan ya dauko takardun su da kuma wayoyin su ya biyo shi a baya. Sai da suka je gurin cin abinci suka zauna suna ci sannan Hussain yace "na san abinda doctor yace, you don't have to tell me, na riga na gaya maka dama kai ne baka yarda ba. Yanzu tunda ka yarda can we please go home? I have to get back to making that baby you know?"
Hassan ya dauke kansa gefe yace "babu wani home da zaka tafi, you are going to have a surgery next week. Na riga nayi filling takardu har na biya kudi" Hussain ya bude ido cikin mamaki yace "no, na riga na gaya maka am not going to go through that" ya ajiye spoon din hannunsa ya mike ya fice daga gurin. Hassan ya biya bill da sauri ya bishi a baya. Ya tarar dashi a hanya suka jera yana cewa "Hussain Please, doctor din nan fa yayi min bayani, ya nuna min komai a screen na gani ba wai wani guri ne mai yawa ba, yace da zarar sunyi surgery sun cire shikenan sai......." Hussain yace "sai ayi radiology a kashe gurin sannan chemotherapy dan a tabbbar komai ya mutu, after three months kuma sai in dawo a sake wani colonoscopy din a gani idan bata yi regrowing ba, idan kuma tayi sai a sake going through that same precess, a haka har sai hanjin ya kare yadda babu abinda za'a kuma yankewa, ko kuma in ta taba wani vital organ din, sai kuma abar mutum ya karasa mutuwa, yes I know about all the process and no am not going through that. Na gaya maka tun acan".
Haka suka yi ta fama har suka je hotel din da suka sauka, suna ziwa Hussain ya fara hada kaya yana zubawa a jaka Hassan kuma yana kashewa yana mayar wa gurin ajjiyar kaya, "waye ya gaya maka zata sake regrowing? Dan ta wasu tayi that doesn't mean taka ma zata yi. Doctor din fa yace tana stage 2, he is 90% sure cewa zai iya cire ta completely" Hussain yace "I am sorry but I don't believe him. Tunda za'a bashi kudin sa ya karbe ai zai fadi haka dama. Ni ba zan bari likitoci su mayar dani lab animal dinsu ba".
Hassan ya koma ya zauna yana kallon Hussain, he have been stubborn and strong headed tun suna yara, anty ma da kanta ta sha ba da labarin irin taurin kansa da yadda yake bata wahala kafin ta juya shi, in yasa kansa abu to kuwa sai da dabara kafin a iya hana shi. Sai ya dauko wayarsa yace "shikenan tunda kaki jin magana ta, bara in kira Fatima in gaya mata halin da ake ciki watakila in ita tayi maka magana zaka ji" sai Hussain ya tsaya daga hadan kayan da yake yi yana kallon Hassan yace "you won't do that, ai amana na baka maganar nan, kana nufin zaka karya alkawarin da kayi min na cewa ba zaka gaya wa kowa ba?" Hassan ya daga kafada yace "yes of course, idan har hakan yana nufin saving life dinka ne zanyi. Kuma try me ka gani idan ba da gaske nake ba" Hussain ya tsaya yana kallonsa, baiga alamar wasa a fuskarsa ba sai ya ajiye kayan hannunsa ya hau kan gado ya kwanta, sai kuma ya tashi ta shiga toilet yayo alwala ya fito ya tayar da sallah.
Hassan ya mike ya mammayar da kayan da Hussain ya baza, sannan shima yaje yayo alwalar ya fito ya tayar da tasa sallar.
Hussain ya hakura ya yarda za'a yi masa aiki amma sam babu walwala a fuskarsa, sai Hassan ya fahimci kamar aikin yafi damunsa a kan ciwon ma gabaki dayansa. A haka har aka gama preparation ya zama saura kwana daya ayi aikin sai suka tafi asibitin zasu kwana acan, a lokacin ne zuciyar Hassan ta karye yace da Hussain "ina ganin a fasa aikin nan Hussain, ni bana jin dadin yadda kake reacting to it ka ƙi kwantar da hankalin ka bayan kuma kai ba mai yawan tayar da hankali akan abu bane ba, ni duk sanyaya min jiki kake yi wallahi, na kasa fahimtar if am doing the right thing or not. Please bro, ka gaya min cewa ba wai takura maka zanyi ayi maka aikin nan ba, dan Allah ka gaya min" sai Hussain yayi masa murmushi yace "ba wai ka takura min bane Hassan, ba kuma na yarda bane saboda kayi threatening cewa zaka gaya wa Fatima ba, na yarda ne saboda kai, saboda ina so in faranta maka, saboda ina so kaji cewa you did your best kar kayi feeling cewa ka gaza gurin kula dani. But ina so kai ma kayi mini wani alkawari Hassan. Ina so kayi min alkawarin cewa wannan shine surgery na farko kuma na karshe da zaka saka ayi min akan wannan cutar" Hassan ya sunkuyar da kansa kasa, Hussain ya dago fuskarsa yana kallon idonsa yace "say it. Kace kayi min alkawari" Hassan ya karbe fuskarsa sannan yace "nayi alkawari. Kuma nasan ma wannan aikin akwai nasara a cikin sa, mun gaya wa Allah kuma ya dubi kokarin mu. Zamu samu nasara am sure" sai Hussain yayi murmushi yace "good" . Sai ya koma ya kwanta ya rufe idonsa har aka zo aka tafi dashi.
The surgery took 3 hours. A cikin 3 hours din nan Hassan sai da yayi nadamar da basu gaya wa kowa ba, at least da an taya su addu'a, dan ji yake yi kamar bakin sa shi kadai yayi kadan a addu'ar. A cikin awa ukun nan har wata irin rama yayi.
Yana tsaye aka fito da Hussain, aka tura shi recovery room, inda kuma anan ne zai cigaba da karbar treatment dinsa.
*The Email*
Washegarin da akayi aikin aka fara yiwa Hussain chemotherapy treatment tare kuma da radiation therapy, at the same time kuma