Showing 129001 words to 132000 words out of 300844 words
ubana yafi na kowa" Ruqayyah tayi dariya tace "zama dai ki cigaba da fada har masu gidan su jiki kina cewa baban ki yafi nasu" Sumayya ta daga kai tana kallon sama tace "ai ba haka nake nufi ba, salon magana ne kawai amma shima uban masu gidan ai ina son shi" ta karasa tana daukan Aminu, Ruqayyah tace "zaki sha kwana ko?" Sumayya ta zauna tana kiran A'isha ta kawo muta ruwa. "Daga school nake, kishi na yunwa kamar zan tafi barzaq" Ruqayyah tayi dariya "ai kuwa dai baya nuna wa a jikin ki, sai wani kyau kike yi yarinyar nan kamar kece a cikin daular da nake ciki. Ninkuma gashi kullum karewa nake yi kamar kudin guzuri" Sumayya tace "ai abin ba'a daula yake ba Ruqayyah, ni babu abinda zai hana ni kiba tunda babu abinda na nema na rasa, hankali na a kwance yake, karatu kuma ina ganewa sosai kuma zuciyata fes take, lafiya lau nake bacci na" Ruqayyah ta harare ta "to me kike nufi? Waye tasa zuciyar ba fes ba?" Sumayya tace "ni fa ba wani abu nace ba, salon Magana ne kawai".
A'isha ta kawo mata ruwa da lemo, ta daga robar ta kusan shanye wa sannan ta ajiye. A lokacin Hassan yake saukowa daga sama "manya manyan yan jami'a, tun da naji gidan nan ya cika da hayaniya nasan ke ce kika zo, kin ga matata ita ba mai surutu ba ce ba" Sumayya ta ajiye robar ruwan tace "shi yasa gidan naku ai kullum yake yanayi da gidan makoki, sai nazo nake mayar dashi lively" ya karasa saukowa yana cewa "lallai wannan makarantar kullum kara kilar da ke take yi, ko kuma Adam ne yake yawar da ke?" Tayi murmushi tana dan saukowa daga kujera yayin da take gaishe shi, ya zauna yana amsawa "yasu babana da inna ta" tace "lafiya lau suke, nasan maybe da yamma zadu zo su duba oga Hussain" yace "ohh kema kin fara bin bakin Adam ko? Oga Hussain oga Hassan" ta danyi dariya, Ruqayyah tayi tsaki.
Sumayya tace "ohh har zan manta ma, Baba yace a gaya muku yana gayyatar ku walima" Ruqayyah tace "walima? Walimar menene" Sumayya tace "walimar saukar Adam" Hassan ya bude ido "sauka? Yaushe Adam din ya fara karatu ballantana har ya sauke? Allah yasa dai ba saukar zuƙu yayi ba" Sumayya tace "haba dai, Baba ne fa malamin sa, idan baka yarda ba ma zaka iya kiransa kayi masa exam da kanka" ya gyada kai yace "na yarda, tunda kika ce Baba ai na yarda kuma. Allah yasa na tsoron Allah yayi" Sumayya tace "ameen" Ruqayyah tace "kuma shine Baba zaiyi masa walima?" Sumayya tace "eh fa, Baba da kansa ya shirya masa walimar. Kunsan cewa yake yi shine babban dan Baba" Hassan yace "a'a, ki ja masa kunne ya daina shiga hurumin da ba nasa ba, wannan position din nawa ne sai dai ko ya zama shine na biyu" ya mike tsaye yana cewa "zamu zo insha Allah, kiyi masa murna inji ni, in mun hadu ma zanyi masa da kaina"
Sai daya fita sannan Ruqayyah ta sauke tsakin da take ta rikewa "lallai Baba da barnar kudi, har wata walima za'a shirya wa wani kedari can? A dauri kashi ko a bata igiya?" Sumayya ta bata rai "kinga fa abinda yasa bana son zuwa gidan ki kenan kwanan nan. In dai har kinsan ba zaki fadi alkhairi a kan Adam ba dan Allah kar ki sake maganar sa. Kuma baban kike cewa zaiyi barnar kudi? Kudin ki ne?" Ruqayyah tace "ko ba kudi na bane ba ai kudin mijina ne. Ko kim dauka van san cewa duk wata yana kai wa Baba kudi ba?" Sumayya tace "still ba naki bane ba, in ya kai masa ma ai ba rokar sa yayi ba kuma ko babu kudinsa yana da aikin yi yana daukan albashi zai iya komai da kudinsa. Wai ni in tambaye ki Ruqayyah, menene matsalar ki da Adam ne? Menene laifinsa? Me yasa ba kya sonsa?" Ruqayyah tace "ba son shine bana yi ba, bana son shi tare da ke dan sam baku dace ba wallahi" Sumayya ta mike tana yin hanyar kitchen tana cewa "matsalar ki ce wannan kuma. Ni ina sonsa shi yana sona iyayena suna sonsa dan ke ba kya son sa bani da problem" Ruqayyah ta sake tsaki, dole ta sake shiri na musamman, babu yadda za'a yi ta bari Sumayya ta auri inyamurin drivern kanin mijinta.
An gabatar da walima lafiya, Adam ya gayyaci friends dinsa na gida dana school dinsu, Hussain da Hassan duk sunje sannan Hussain yayi masa kyautar zuwa aikin hajjin bana, murna a gurin Adam kamar bakinsa zai yage, su Baba suna ta taya shi godiya. Ruqayyah bata samu zuwa walimar ba saboda rashin lafiyar da take fama dashi, a jikinta ta fara tunanin ciki ne da ita dan haka tayi home pregnancy test kuma ya tabbatar mata da zargin ta, hakan yasa ta fahimci tun kafin tafiyar su Hassan India cikin ya shiga, amma sai ta boye abinta a ranta saboda tana tsoron kar ta fada ace ba za'a yi tafiyar nan da ita ba, tafi son in anje can a gane, sai ta nuna cewa itama bata san dashi ba. Ko babu komai ta samu abin nunawa Fatima.
Aka kammala duk shirye shirye, ranar tafiya tayi suka tashi gabaki dayan su Aunty, Hassan da Hussain, Ruqayyah da Fatima, Safiyyah, Khadijah, Nafisa, Zulaihat. Tunda suka je suka dukufa gurin gaya wa Allah bukatun su, babbar bukatar su ita ce ta neman lafiya ga Hussain, babban fatan su shine in Hussain ya koma asibiti a tabbatar masa da cewa ya rabu da wannan cancer din. Ruqayyah kam nata bukatun take roka babu ruwanta da wani Hussain, bata rokar masa rashin lafiya ba kuma bata rokar masa sauki ba.
Fatima ce ta fara lura da chanjin yanayin Ruqayyah kuma direct ta gaya mata cewa tana zargin tan da ciki, ta kuma raka ta asibiti kamar lokacin cikin Twins sannan kuma aka tabbatar mata da zargin ta. Kowa yayi murna da kasancewar hakan, amma kuma kirikiri suka ringa nuna wa ina ma dai Fatima ce mai cikin amma sai Hussain ya ringa basarwa duk kuwa da cewa duk sujjadar da zaiyi sai ya roki Allah ya bashi magaji kafin ya karbi ransa.
A haka suka gama azumin su, lokaci ya kuma tafiya har lokacin aikin hajji yayi, a lokacin ne Adam da Sumayya wadda Hassan ya biyawa suka taho tare da Hassana, suka hadu da sauran family din suka gabatar da aikin hajjin su sannan kuma suka juyo zuwa Nigeria. Sai dai Hassan da Hussain su ba Nigeria din suka taho ba India suka tafi inda za'a sake duba Hussain dan a tabbatar da warkewar sa ko akasin hakan.
Suna zuwa aka sake yin wani colonoscopy din aka dauki sample daga hanjin Hussain sannan aka tura shi lab dan gwadawa. Fir Hussain yaki zama ya jira result din yace sai dai a aiko masa ta email dan haka kwanan su biyu a India suka bi iyalinsa zuwa Nigeria.
Yana zuwa Nigeria ya tarar Fatima babu lafiya, wai tun a jirgi ta fara amai kuma har yanzu yaki tsayawa. Da kansa ya dauke ta zuwa asibiti "wato da banzo ba zama zakiyi tayi ba zaki je asibiti ba ko Princess?" Tace "ni bana son allura" amma a ranta tsoron ta daya, tana ta saka ran cewa ciki ne da ita tana jin tsoron kar a gwada ta ace babu, wannan heart break din take tsoro, shi yasa duk yadda Aunty tayi da ita akan zuwa asibitin taki yarda.
Tashin farko PT aka rubuta mata, aka yi mata kuma aka bata result sai dai ta kasa budewa, idonta har hawaye ne ya taru a ciki, ta mikawa Hussain tace ya bude, shima tsoron budewar yake yi sai ya mika mata yace ta bude. Doctor din yayi dariya yace "to ni ku bani in bude tunda naga kamar tsoron takardar kuke yi" suka mika masa sannan suka zauna suka zubawa juna ido, doctor din ya karanta yana murmushi sannan yace "to a bani goron albishir da kuma ladan karantawa. You are going to be parents in the next seven months"
Basu san sanda suma tashi suka rungume juna a gaban doctor din ba, Fatima sai kuka, Hussain yana dariya, doctor yace "kar a manta da goron albishir dina" Hussain ya juyo yana kallon sa yace "just name it, ko me kake so in dai ina dashi ya zama naka".
A ranar kaf gidan babu wanda bai san da labarin cikin nan ba, hatta masu gadi sai da suka sani dan aljihunsu sai da yayi nauyi, rabon kudi har mutanen waje sai da suka samu nasu.
A ranar ne kuma e-mail ya shigo wa Hussain daga doctor.
"Dear Hussain Aminu Abdullahi, we regret to inform you that the operation performed on you was not successful in eliminating the cancerous tumor, it has regrown. We suggest performing another surgery as soon as possible"
Ya rufe e-mail din sannan ya rufe system din tare da kwanciya ya rufe idonsa, mintuna kadan sannan ya bude su ya mike ya dauko diary dinsa da biro ya fara rubutu.
Dear baby .
A yaune aka tabbatar min da cewa kana nan kan hanyar ka ta zuwa duniya, a yaune kuma aka tabbatar min da cewa ni kuma ina kan hanyata ta barin duniya. Tunani na daya shine "ko zan ga fuskar ka kafin in tafi?"
Wannan littafin na siyarwa ne, idan kika ganshi a wani gurin na sata ne, in kina son ki karanta halaliyar ki kiyi min magana through WhatsApp ta wannan number din 08067081020
*The News*
Ya rufe diary din da sauri dan ji yayi kamar zuciyarsa ba zata iya cigaba da rubutun ba, sai ya koma ya kwanta yana mai dora diary din akan kirjinsa tare da rufe idonsa yana tunani, Fatima ce ta fara fado masa a rai, tunda doctor ya karanto musu result din PT dinta har yazu ta kasa rufe bakinta dan murna sai yaji baya son ya katse mata murnar ta da wannan mummunan labarin, baya son ya katse mata murnar ta har abada. Zai so ace murmushin da yake kan fuskarta zai dore ne har karshen rayuwarta.
Sai ya dauki wayarsa ya fita valcony tare da rufe kofa, ya kira number din doctor din daya duba shi a Indiya, doctor din was so sympathetic yana kuma jaddada masa muhimmancin komawa a sake yin wani aikin. Bai musa ba ya nuna masa zai dawo as soon as possible amma kuma sai ya roke shi wata alfarma guda daya, alfarmar ita ce yana so ya sake turo masa wani email din stating cewa ya warke completely daga ciwon da yake damunsa "my wife is pregnant, and I don't want to break her heart" da farko doctor din kin yarda yayi saida Hussain yayi ta nace masa ya kuma tabbatar masa da zai dawo sannan ya amince, washegari da safe kuwa sai ga wani e-mail din da sa hannun doctor din da logo din asibitin da komai amma a ciki an yi bayanin cewa Hussain ya warke completely babu sauran trace na Cancer a tare dashi. Hussain yana samun wannan sai ya koma baya ya goge wancan da aka fara turo masa dashi. Sannan sai ya dauki system din ya tafi dakin Fatima da murmushi a fuskarsa. A palonta ya same ta tana saka turaren wuta, tun daga nesa ya hango annurin fuskarta ya kuma san tun na jiya ne, tun na albishir din doctor ne. Yace "hey princess" ta juyo tana kallonsa tare da kara fadada murmushin ta, sai ta ajiye incent burner din hannunta ta taho gurin sa da sauri. Kafin ta karaso yace "albishirinki" sai ta dakata zuciyarta tana ayyana mata albishir din da zaiyi mata dan ita yanzu bayan sakon doctor na jiya to wani sakon doctor din ne kadai zai faranta mata maybe ma fiye da wancan, dan lafiyar Hussain ta fiye mata komai yawan yayan da zasu haifa. Ta fara kokarin studying fuskarsa dan ta tabbatar da abinda yake mata albishir din akai, sai ya gyada mata kai kamar mai kokarin tabbatar mata da zargin ta sannan ya juyo mata da screen din system din da take hannunsa "read this".
Da sauri tayi yawo da idanunta akan screen din, tana taking information din at ones sannan tayi tsalle tana rufe baki, idonta kamar zai fado daga fuskarta, haka ma zuciyarta. "Ka warke! Hussain ka warke. Oh my love, ohh Allah na na gode maka, Alhamdulillah" ya ajiye system din yana kokarin rike ta amma taki rukuwa, farin cikin da take ciki yafi karfin tsayawa a guri daya sai ta fara zagaye a palon tana tsalle yana binta har ya samu ya kama ta ya daga ta sama yana zare mata ido "ke! Garin murnar mijinki ya warke kuma shine zaki je ki sabauta shi?" Bata kula fadan da yake mata ba sai ta kama fuskarsa da hannayenta sannan ta fara kissing duk inda ta samu a fuskar, sai shima ya fara dariya a ransa yana hoping ina ma inama? Ina ma farin cikin su mai dorewa ne.
Haka yayi ta juyi da ita a palon sai da suka gaji sannan ya zauna da ita a kan cinyarsa yana nishi "yarinyar nan fa nauyi ne dake wasa wasa" tayi dariya tana juya idonta "kasan dai bani kadai bace ba yanzu ko? Dan haka nauyin ba nawa bane ni kadai" ya dora hannunsa a marar ta "ayyah, bawan Allah za'a yi masa sharri dan anga bashi da baki ko?" Sai ya kai fuskarsa kusa da cikinta yace "hello angel, this is your father speaking, maman ka tana yi maka sharri tace kai dan lukuti ne kamar ta" ta dago kansa tana hararar sa "wace lukutar?" yace "wai da" sai ta dauki pillow ta fara dukansa dashi, ya tashi yayi daki da gudu ta bishi.
A ranar labari ya kai wa duk wanda ake tunanin ya kamata a gayawa cewa result din Hussain ya fito kuma ya warke tas babu sauran abinda yake damunsa. Aunty da kanta ta shirya musu dinner gaba ki dayansu to celebrate the news. Ta ai kawa kowa sakon azo part dinta a ci abincin dare, har Hassana da mijinta da kuma Jabir wanda sati uku ya rage bikin su da Safiyya. Da kuma Ruqayyah da Hassan.
Lokacin da Hassan ya shiga gida baki har kunne yana nunawa Ruqayyah email din da Hussain yayi masa forwarding zuwa wayarsa, a daki ya same ta a kwance dan wannan cikin kasala yake saka ta ba kadan ba, ya jawo ta ya rungume ta "Hassana Hussain ya warke, ya warke ya warke, Hassana ki taya ni murna Hussaini na ya warke" farko bata ma gane me yake cewa ba, ta dan bata rai tana ture shi saboda bata son kamshin turarensa tace "me kake cewa? Me ya samu Hussain din?" Ya sake ta yana murmushi, idonsa yana kyalli "babu abinda ya same shi babu abinda zai same shi likitoci sunce ya warke" ta danyi shiru tana digesting maganar "wait, what? Ya warke fa kace, dama ana warkewa daga cancer ji nake yi bata da magani" ya danyi dariya "babu ciwon da bashi da magani Ruqayyah, ita cancer maganin ta shine ayi aiki a yanke bangaren da yake da ciwon sai kuma a kashe gurin yadda ciwon ba zai dawo ba balle ya yadu, in dai akayi nasara a wannan to shikenan mutum ya rabu da ita, akwai mutane da yawa da suka warke daga cutar cancer kuma Hussain yanzu is one of them. I am so happy, I was so scared cewa wani abun zai iya samunsa" tayi sauri ta mike ta shiga toilet pretending as if amai ne ya taso mata. Ta rufe kofa sannan ta jingina da jikinta. Daga inda take tana iya hango katangar gidan Hussain ta tagar toilet dinta. Ta runtse idonta tana tuno mugun labarin da jiya ya cika gidan na cewa Fatimah tana dauke da ciki, kuma a yadda Nafisa take gaya mata wai cikin har yayi wata biyu ma'ana banbancin wata biyu ne tsakanin nata da na Fatima. Wannan wacce irin bakar rana ce? Dukkanin mafarkanta sun tarwatse a cikin kwana daya. Fatima ta samu ciki sannan Hussain ya warke.
Ta tari ruwa a hannunta tana wanke fuskarta, a zuciyarta tana jin haushin kanta data daina shan pills dinta har ta kai ga samun ciki a hope dinta na rike gidan ta hanyar amfani da ƴaƴan ta, gashi yanzu gimbiya zata haifi nata, guda dayan da zai doke dukkan nata guda ukun tunda ubansa shine mai kudin gidan. Ta tuna da irin celebrating din da akayi tayi a gidan tun jiya bayan ita sanda ta samu nata cikin farin babu wanda ya ko da daga murya ne da sunan murna. Wannan ciki kuwa ko maganar sa ma ba'a yi, wani abin haushin shi kansa uban yayan sanda ya fahimci tana da cikin sai da yayi mata magana, a lokacin suna Saudiyya . "Ina pills din da doctor ya baki" tace "suna Nigeria, ban taho dasu ba" ya bata rai "ai dama ba nan nake nufi ba, ai ba anan aka samu cikin ba, a Nigeria din nake nufi ba kya sha dama" ta bata rai "ina sha mana, wasu kwayar magani sun isa su hana mutum haihuwar abinda Allah ya riga ya rubuta sai an haifa. In baka so ka gaya min kawai ba sai kana boye boye ba" ta fara hawaye, ya kamo hannunta, ya zanyi ince bana so Hassana? Ko ya'ya nawa zan haifa ai duk Allah ne ya bani kuma duk ina so kawai dai jariran can nake tausayawa wallahi, kin ga basu yi wani kwari ba yanzu suke kokarin fara rarrafe" tace "ai dama suna shan madara, sai su cigaba da shan madarar su kawai ni kuma su barni in ji da kaina" daga nan kusan babu wanda ya kuma yin maganar cikin nata a zaman nasu na Saudiyya, su duk sunfi mayar da hankalin su akan addu'ar samun sauki gun Hussain. Gashi yanzu addu'ar tasu ta karbu ita kuma sun barta a tasha.
Ta tuna da