Showing 66001 words to 69000 words out of 300844 words

Chapter 23 - Tagwaye Book 1 Hausa Novel Complete

22 Dec 2024

2636

zai zamanto obstacle dinta kamar yadda gidan sa ta toshe mata ganin ta. Ya kuma tsaya mata a zuciyarta.

Har an fara fita ana shiga motocin da zasu tafi dasu airport sai Aunty ta kira Hassan dakinta suka tsaya tace "nace ka sallami Ruqayyah kuwa?" Yace "sallama kamar yaya?" Aunty tace "eh mana, zaka bata kudi sanoda liƙi da sauran abubuwa" ya zauna akan kujera yana dafe kanta "Aunty ita tace miki tana bukatar tayi liki? Shin wai ma menene amfanin yin likin? Yana daga cikin sharudan biki?" Aunty ta hade rai "to mu dai ko kayi mana wa'azi dai sai munyi, ya zamu je gidan biki gidan fitar kunya kuma na tabbatar za'a yi kida sannan kace ba zamu fita muyi wa amarya da ango liki ba? Ita kuma ya kake so tayi? So kake ta zauna ta zuba tagumi tana kallon mu muna yi?" Yace "Aunty, ke kinfi kowa sanin dalilin da yasa tuntuni naki auren yayan masu kudi saboda bana son macen data saba da barnar kudi da saka kaya masu tsada da sauran su, saboda a hala zata tarbiyyan tar da yaya na, a haka family na zasu tashi. Kuma babu wanda yasan abinda gobe zata zo mana dashi. Ni daban Hussain daban, kudi na daban na Hussain daban. Ranar da bani dashi kuma yaya zanyi dasu aunty? Shi yasa nayi murna da Allah ya hada ni da Hassana saboda background dinta da kuma halayyar ta sannan da yarintar ta yadda zanji dadin tarbiyyan tar da ita akan tsarin rayuwa ta ita kuma ta tarbiyyan tar da yaya na. To yanzu idan kuma na fara nuna mata zubar da kudi a kasa a gurin biki dole ne me akayi kenan? Ai anyi ba'a yi ba ko?"

Aunty tace "to mister smart, komai sai ka nuna wa mutane kai kamar ka fimu iyawa. Wannan dai biki ne, kuma har yanzu bikin ku ne ba'a gama ba, ka dauko kudin liki ka bata tun muna shaida juna ni da kai" yayi ajjiyar zuciya yana shafa aljihun sa sannan yace "i don't have cash on me, in na fita zan samu sai in bata" ta nuna masa kofa, "jeka daki ka dauko ka kawo mata ina nan ina jiran ka" yayi murmushi yana karya wuya, tace "ai na fika wayo, ni na haife ka fa ba kai ka haife ni ba". Dole ya tashi yana murmushi ya tafi tsohon dakin sa, ya bude drawer ya dauko kudi yana jujjuya, ya gama plan din abinda zaiyi da kudin nan, yayi tsaki sannan ya mike ya fita.

Yau dai sai ga Ruqayyah da Sumayya a jirgi. Ruqayyah ta maze wai dan kar tayi kauyanci ayi mata dariya amma lokacin da jirgi zai tashi ji tayi kamar dodon kunnen ta ne ya fashe a cikin kunnen, amma taki tabawa dan kar wani ya gani yace tayi kauyenci, ta kankame rigarta cike da tsoro amma fuskarta babu ko alamar tsoro a ciki. Ta shanye kayanta. Suna sauka suka tarar an aiko da motocin da zasu tafi dasu gidan sarautar kano, suka shiga aka kaisu sannan akayi musu jagora har masaukin su, daga nan aka shiga hidimar kawo musu abinciccika na alfarma irin na sarauta, wani kalar abincin ma Ruqayyah bata taba ganin sa ba. Nan take bayi da hadiman gida suka fara saving dinsu, daga kinyi motsi za'a ce "me kike so? Me za'a karo miki? Ko kafafuwan ki sun gaji a tausa miki su?" A haka har sai da aka tabbatar kowa is fully satisfied sannan aka yi musu jagora zuwa wani katon palo da yafi kama da hall din taro amma yasha shimfidu da kujeru na alfarma. Anan Ruqayyah take tambayar kanta ko wannan ce fadar? Amma kuma bata ga karagar sarki ba, sai taga an nuna musu kujerun suka zazzauna sannan sai ga matan gidan suna isowa daya bayan daya ana gaisawa dasu cikin mutunta juna da karramawa. Duk inda Aunty zata je hannunta yana rike dana Ruqayyah, duk Wadda suka gaisa kuma zata nuna mata Ruqayyah tace "ga daya ƴar tawa, matar Hassan ce, jiya aka kawo ta" nan da nan sai taga an jata an rungume "ga yar uwar Fatima" "Allah ya baku zaman lafiya" "Masha Allah, kyakykyawa daita kuwa, ya sunan ki?" A haka a haka har laasar tayi, Ruqayyah tana cewa "wato ita ogar ba zata fito ba ko?" Bakin cikinta kawai kar kwalliyar ta ta karasa lalacewa ba tare da Fatima ta fito ta ganta ba, kar ta raina ta, tunda taji ance first impression matters alot.

Ba'a fito da Fatima ba sai da suka je suka yi sallar laasar, dole Ruqayyah ta wanke kwalliyar ta tunda zata yi alwala amma duk da haka sai Nafisa ta dan gyara mata fuskar dai dai gwargwado kuma ta mayar mata da head dinta. Sannan suka koma suka zazzauna side daya dangin ango daya side din kuma dangin amarya, akayi ta rabon snacks da drinks daga can gefe kuma ga masu kidan kwarya nan suna yi . Sannan sai ga amarya nan an fito da ita lullube da alkyabba fara tas mai adon golden, ko tafin kafarta ba'a gani, aka zaunar da ita akan kujerar da aka tanada musamman domin ta sannan kawayenta suka zagaye ta duk sun sha ankon lace kalar zaren da akayi dinkin alkyabbar ta dashi. Kasanta kuma bayinta ne a jere duk sunyi ankon riga da zani na atamfa mai hoto da sunan ta a jiki. Hannayensu rike da shantu suna kida da cinyoyinsu sannan suna rera waka, a cikin wakar taji an ambaci sunan gimbiya Fatima, sannan ne ta fahimci wakar ma musamman saboda ita aka shirya ta.

Nan take guri ya tashi da sowa da tafi, wasu kananan yammata suka fito suma a jere hannayensu rike da mahutai wadanda side dinsu daya tambarin masarautar daya side din kuma hoton gimbiya fatima, suka jeru suna rawa gwanin ban sha'awa. Mutum biyu ne aka nema daga dangin ango suka je suka bude fuskar gimbiya sannan suka feshe ta da turare, duk da haka sai ya zamanto rabin fuskar ne kawai a bude idanuwan ta da goshinta still suna rufe, amma duk da haka zaka iya hango tsantsar kyawunta ta bakinta da yake dauke da murmushi da kuma dogon hancinta da yake tsaye chas. Ruqayyah tayi tsaki a ranta. "Ashe ma na fita hasken fata" ta fada a hankali tana hararar iska. Sai dai ita kanta tasan koda tafi Fatima haske to kuwa kulawar da fatar fatiman ta samu ba zai bar hasken Ruqayyah ya haska ba.

Daga nan sai taga an fara shigowa da kaya ana jere wa a tsakiyar gurin wai kayan gara ne, amma abin mamakin shine ba wai kayan abinci bane ba kamar yadda tasan ana yin gara aa wannan kayan suttura ne kawai, akwati akwati, jaka jaka. A al'adar gidan sarauta duk wadda aka yiwa aure a gidan sarauta idan wani gidan sarautar aka kaita to kuwa hatta bayin gidan sai an yi musu suttura kuma an basu kudi albarkacin ta, idan kuma ba gidan sarauta bane ba to kuwa za'a binciko duk dangin angon na nesa dana kusa sai kowa ya samu rabonsa albarkacin gimbiya, yan uwansa shakikai kuwa da iyayensa da gwoggonninsa nasu na musamman ne, sai an yi musu kamar wani karamin lefe. Haka akayi ta kiran sunan tun daga iyayen Hussain dangin uwa da dangin uba har zuwa kan dangin dangarere, wasu ma basa gurin, wasu ma ko kadunan basu je ba ballantana kano amma an kira sunan su kuma an basu rabon su, kowa aka bashi kaya kuma sai an hada da kudi, maza da mata.

A cikin rabon sai taga na Hassan, sunanshi na biyu daga Aunty sai shi, akwatin sa guda mai cike da dangin shaddoji masu tsada, da yar karamar jaka ita kuma takalma ne a ciki da huluna da turaruka na maza. Tunda babu maza a ciki dan haka ita aka ce taje ta karbo masa, ta taka kaje har gaban gimbiya, ita bakin cikinta kenan wai sai anje gaban gimbiya, ta tsaya a gefen gimbiya akayi musu hoto sai mai hoton ya yi mata magana da cewasai ta sunkuya saboda ita gimbiyar a zaune take, ita kuma Ruqayyah a ganin ta in da sunkuya kamar gimbiyar ta sunkuyawa amma ganin mutane suna kallo dole ta sunkuya din tana kirkirar murmushin karya aka sake daukan wani. A lokacin da zata bar gurin ne taji gimbiyar ta riko hannunta tayi mata alamar data sunkuyo, bakin ciki ya toshewa Ruqayyah makogwaro, amma dole ta sunkuya sannan ne suka hada ido, da murmushi a fuskar gimbiya fatima, ga wani fitinannen kamshi yana tashi daga jikinta tace "ban san dake aka zo ba ai, da tun dazu na aika an kawo min ke gurina, ke bakuwa tace ai bata mutan gida ba" Ruqayyah tayi yake "yeah right" sannan ta zare hannun ta ta bar gurin, ko ta kan kayan bata bi ba. Ita sunkuyawar da tayi wa gimbiya shi yafi komai kona mata rai. Tana dawowa ta fara sansana kanta dan taji ko tana irin kamshin da gimbiya fatima take yi?

Abin takaici sai gashi tana zama an sake kiran sunanta again, wannan karon kuma nata kayan taje aka bata, exactly zubin da akayi wa Hassan irin sa akayi mata kawai dai nasa na maza nata na mata. Wannan karon da akace taje suyi hoto cewa tayi ai tayi, tayi tafiyar ta.

Sai da aka kwashe kayan gara sannan su kuma dangin ango suka shigo da lefe, tun Ruqayyah tana lissafa akwatunan har taji kanta ya fara ciwo ta kwanta a jikin kujera ta rufe idonta, bata son ma ganin kayan ciki tunda ance kazantar da baka gani ba tsafta ce. Sumayya ta kama hannayenta, ta juyo ta kalle ta sai tayi mata murmushin kwarin guiwa, sai taji har Sumayyan ma haushi take bata. Gabaki daya mutanen gurin haushi suke bata, ranta zafi yake yi, zuciyarta ciwo take yi. Ta mike da sauri tana daukan jakarta. Aunty ta riko hannun ta "ina zakije Ruqayyah?" Ruqayyah ta langwabe kai "Aunty kaina yake ciwo wallahi, zuwa zanyi in dan kwanta kafin a gama" Aunty tayi murmushi "Akwai ciwon kai kam, nima kaina ciwon yakeyi, amma zaki iya gane hanya kuwa" Ruqayyah tayi shiru, ita wadannan sorayen da suka wuce ina zata iya gane su? Aunty ta waiga ta kira wata a cikin wadanda ta lura bayin gidan ne tace "dan Allah raka su inda aka sauke mu".

Suna zuwa can Ruqayyah ko ta kan Sumayya bata bi ba tayi kwanciyar ta, taji karar wayarta ta dauko ta taga ten missed calls daga Hassan, hayaniya ce ta hana ta ji. Tayi tsaki ta mayar da wayar cikin jakarta sayi kwanciyar ta.

Sumayya ta bita da kallo sannan ta tabe baki tace "kin dorawa kanki aiki. Babban aiki ma kuwa" a kara gyara fuskarta Sannan ta juya ta koma gurin taron. Ita ba zata iya zama tayi tagumi ba bayan ga shagali can ana yi.



Wannan littafin na siyarwa ne, idan kina so kiyi min magana ta WhatsApp ta wannan number 08067081020


Sai magrib aka tashi daga taron, daga nan duk aka dawo masauki aka yi Sallah masu son yin wanka suka yi sannan aka fara shirin tafiya dinner, sai a lokacin Ruqayyah ta tashi tayi sallah sannan itama ta shiga tayi wanka, suka zo suka fara shiryawa, kayan ta data zubo a jakar Sumayya ta dauko, daya daga cikin kayan da aunty ta siya mata ne na fitar biki, tayi kwalliyar ta tsaf ta shirya duk da cewa bata cika make up da yawa ba amma tayi kyau sosai. Sumayya ma tayi wanka ta chanja kaya, suka yi sallar isha i sannan suka fita suka tafi inda sauran mutane suke, ana ta yin make up da daurin dankwali, Aunty ta tambayi Ruqayyah ko tanaso ayi mata amma tace a'a, sai daurin dankwalin ta kawai aka gyara mata. Zuwa karfe takwas aka ce su fito za'a tafi. Sai a lokacin ta dauko wayarta ta kira Hassan, har ya gaji da kira ya hakura. Ring daya ya dauka. "Har na dauka ko an sace min amaryata" ta danyi dariya, "sace wa kuma sai kace kai" yace "ohh abin harda tsokana? To zan rama ne nima zan zo in sace ki kinga munyi one one" tace "ai ni bani na sace ka ba" yace "yeah, ke kika dawo dani gida, and I am never going to forget that" tace "me too". Yace "nayi ta kiranki ne dazu dan in gaya miki mun karaso muma, an kaimu masauki tare dasu Hussain and I was lonely nace bari in kira matata tayi min hira" tace "muna gurin taron can, and the place was so noisy shi yasa banji ka ba, sai yanzu dana dauko wayar sannan na gani. Sorry" yace "it is okay dear. Gamu nan muna shirya wa yanzu zamu tafi dinner" tace "muma haka" yace "okay, I will see you there angel"

Tayi murmushi tana kashe wayar. Sai yanzu taji dadin zuwansa garin, ita sam bata son zuwa gurin dinner din nan dan bata ga abinda zata je ta gani a can ba. Sai yanzu kuma take kara gode wa Allah da Sumayya tayi dabarar sallamar kawayenta da sun biyo ta kano ai da ansha abin kunya. A cikin palace din za'a yi dinner amma sai da aka dauke su a motoci aka kaisu gurin saboda girman palace din, kamar wata duniya suka je.

Suna shiga suka tarar da gurin already da mutane, taji ana zancen harda governor da matarsa ne zasu je gurin. Yanayin tsarin gurin kadai ya isa yasa mutum kamar Ruqayyah ciwon kai. Sumayya sai kalle kalle take tana daukan hotunan yadda akayi arranging tables din gurin da kuma kujerun amarya da ango, ta dauki hoton high table, wannan lallai sai ta nuna wa Inna Ade dasu Sulaiman, wannan lallai sai ta nuna wa Adam.

Ruqayyah ta ja Sumayya zuwa can extreme end din hall din suka zauna, Sumayya tace "nan ai ba gani zamu ke yi ba, Please ki tashi mu koma gaba" Ruqayyah tace "ke da kika zo gani kenan, ni kuma zuwa nayi a ganni and I really don't want to be looked at, dan haka nan zanyi zamana. Ke ma kuma sai ki zaba, gurina kika zo ko gurin bikin gimbiya? The choice is yours" Sumayya tayi ajjiyar zuciya ta zauna tana ta daga kai, sai daga baya ta lura a gefen su ma akwai katon screen da kake iya hango can gaba kamar a gabanka akeyi, just like kana kallon TV. Shikenan Sumayya ta gyara zaman ta da niyyar shan kallo tana yi tana recording as much as she can. Basu jima da zama ba guri ya cika, sai ga Hassan yana kiran Ruqayyah, "kuna ina ne? Ga guri an tanadar mana" ta yamutsa fuska "mun samu guri mun zauna ma, kuyi zamanku kawai" yace "noo, ni ba zan iya zama ni kadai babu ke ba, common ki na ina inzo in taho dake inda nake" ta kwantar da murya "ni ba zan iya zama a can ba, dan Allah ka bar ni inyi zamana anan" yayi ajjiyar zuciya, he thought as much, yaso a rabu da yarinyar nan tayi zamanta a gida aunty tace lallai sai an taho da ita, ita bata saba da irin wadannan abubuwan ba dan haka dole zata jita a takure. Yace "kina ina? Ni sai inzo inda kike" ta gaya masa. Mintuna kadan sai gashi nan yazo, yaci kwalliya kamar babu gobe dan ita kanta tasan yayi kyau. Tayi masa murmushi shima ya mayar mata yana jan kujerar kusa da ita ya zauna. Sumayya ta gaishe shi yace "su Sumayya an samu abinda ake so ko? Biki dai ayi ta hidima dai" tayi dariya tace "eh mana, biki ai lokaci daya ake yinsa daga an gama shikenan" yace "Allah ya kaimu baki bikin to, mu sha shagali har mu gode Allah" ta sunkuyar da kanta tana murmushi. Yace da Ruqayyah "muna shigowa ai Hussain ya kira ni wai gimbiyar sa tana ta nemanki, tana so wai ko zaki shiga cikin friends dinta and I said no, baki san su ba ba zaki ita zama a cikin su ba" Ruqayyah bata ce komai ba sai kira ya shigo wayarsa ya dauka yayi magana sannan ya mike "excuse me ladies, zan je zamu shigo da Hussain. Reserve my seat please dan anan zan zauna"

Bayan fitarsa da kadan sai akayi sanarwar amarya da ango zasu shigo, kowa ya mike tsaye kamar wani president ne zai shigo, suka shigo suna taku dai dai abokan ango da kawayen amarya suna take musu baya, camera tana daukan su ta kowanne angle ana turo hotunan a manyan screens din da suke a gurin saboda wadanda ba zasu iya gano wa ba. Mai video yana dauka tun daga kan takalman gimbiya har zuwa kan sarka da dan kunnen ta, haka shima Hussain aka dauko shi, ba kuma wai shigarsu ko kuma kyawun surar sune abin burgewa ba, a'a, soyayyar junan su da take kwance akan fuskokin su. Kowa ya gansu ya san a cikin farin ciki suke. Ruqayyah ta kifa kanta a jikin table din gabanta tana rufe idonta kamar mai bacci, wannan abin shine abinda tayi ta mafarki zata samu a bikinta tun lokacin data hadu da Hassan. Mutane irin wadannan, governor, ita da mijinta su shigo kowa yana kallon su cike da sha'awa, amma ita nata mijin ma cewa yayi ba zai je kowanne event dinta ba, in dai bai je ba kuwa mutanen sa ba zasu je ba, shi yasa bata yi komai ba saboda baya ga amfanin yin ba tunda so take yayi introducing dinta ga mutanensa a matsayin matarsa ita kuma tayi a matsayin mijinta kuma ceo of h and h group of companies. Now she is just a guess a bikin ceo na H and H group of companies. Jama'ar amarya da ango suna wucewa ta mike ba tare da tace komai ba ta bar cikin hall din ta fita waje, a can gefe taga wata doguwar veranda da kujeru a ciki sai ta tafi can ta ja kujera daya ta zauna sannan ta zubawa


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login