Showing 249001 words to 252000 words out of 300844 words

Chapter 84 - Tagwaye Book 1 Hausa Novel Complete

22 Dec 2024

2111

jiya zuwa yau gabadaya rayuwarta tana kokarin ta koma upside down, to wai wanne tsautsayin ne ma ya kawo ta Nigeria yanzu. She thought she was running away from something bata san cewa she was running toward it ba. Tace "umma ta, dan Allah kiyi masa magana, please make him understand, am not ready" Hajiya Ummah tace "sai yaushe zaki zama ready? Sai kin shiga menopause tukunna? Ko ba kya son ki haihu kema ki ga ƴaƴan ki a duniya? Bara in gaya miki wani abu Fatima, duk da nasan ba zaki ji dadin sa ba. Kinga marigayi Hussain? Mutumin kirki ne duk mun yaba da halayyar sa kuma muna fatan Allah yaji kansa da gafara, amma da ace kece kika mutu shi yana raye bana jin zai shekara biyar ma ba tare da ya sake wani auren ya haifi wasu ƴaƴan ba ballantana shekara goma. Ko da ace kuna raye kuma tare da ke da shi a matsayin mata da miji to baki da guarantee din cewa Ku biyu zaku yi rayuwar ku ba zaiyi miki kishiya ba. Fatima, ten years is enough. Gaki nan ras dake, tas abinki, you deserve a chance at happiness, ba wai dan mijinki ya mutu shikenan hakan yana nufin kamar kin tashi daga matsayin mace ba, na tabbatar kina da bukata kema kamar kowa, kina kuma son ki samu lada ki samu aljanna ta hanyar aure. Dan menene ba zaki yi ba? Shi fa wanda ya mutu ya riga ya mutu Fatima, Hussain ya mutu, ko kinyi aure ko baki aure ba babu abinda ya dame shi a yanxu, wadanda suka mutu damuwar su daban take da mu wadanda muke raye. In fact, idan da za'a taso shi yanzu da zai so ya ganki cikin farin ciki ba wai kina kunshe a daki kina kuka ba".

"Sannan kuma wannan yaron da kike riko, no matter how much you love him ba dan ki bane ba, ba dan mijinki bane ba, ba dan yan uwanki bane ba, babu wata alaka ta jini a tsakanin ki ke da shi sai dai shakuwa, shin ba kya so ki haifi naki? Ki haifi dan da zaki kira da naki?"

Fatima ta dora hannun ta akan marar ta tana missing feelings din being pregnant. Hajiya umma tace "kuma ki sani, ba ko wanne miji ne da zaki aura zai yarda ki tafi da yaron ba, dan wan tsohon mijinki wanda kike ruko saboda yana kama da tsohon mijinki" Fatima ta girgiza kai, "Adam ba zai ki daukan sa ba" Hajiya umma ta harare ta "Adam din da kika ce ba zaki aura ba? Ji nake abinda kika ce kenan"

Fatima tace "Adam saurayi ne umma, budurwa yake bukata wadda bau kowa a zuciyarta sai shi kadai. Ya dauki lokaci mai tsaho a rayuwarsa yana sacrificing abubuwa da dama saboda ni, bana son yayi sacrificing rayuwar aurensa saboda ni" Hajiya umma ta zauna kusa da ita tace "shi saurayi ne tabbas, ke kuma gimbiya ce darajar ki ta dara ta duk wata budurwa da za'a bashi. Kuma ina ganin ai shi yafi kowa sanin cewa ke ba budurwa bace ba tunda shine yayi jinyar ki sanda kika haihu, shi yafi kowa sanin kin haihu, amma kuma ya furta yace ke yake so" Fatima ta dago kai tana kallon ta, sai Hajiya umma ta gyada kanta tace "munyi waya da Maryam dazu, ta gaya min dalilin tahowarki gida. Kin taho ne saboda Adam yace yanason aurenki. Shin kina da wani dalili na kin aurensa bayan fadin da kika yi cewa shi saurayi ne ke bazawara?"

Fatima tayi shiru kanta yana kasa amma bata ce komai ba, shin tana da dalili? Hajiya umma tace "babu wanda zai matsa miki ki aure shi, ko ba shi ba ko wani ne, amma duk kan nin mu zamu so kiyi aure, ko baki auri Adam ba dole ki auri wani. In yaso shi kum Adam din sai ya samu wata yayi aurensa" Fatima ta bude ido da sauri tana fasalto maza da yawa a zuciyarta, da yan lukutaye da sirara da tsofaffi da masu mata biyu ko uku tana jin kamar zata amayo abincin da dama bai gama sauka a cikin ta ba. Sai yanzu take kara realising din issue din da yake gabanta, ko Adam ko wani. Shima kuma Adam ko ita ko wata. Zabi ya rage nata tunda dai shi ya fadi nasa zabin.

Ta sake girgiza kanta da sauri, "uhm uhm. I can't" Hajiya umma tace "you can, and you will. Sai dai in baki bawa kanki dama ba, sai dai in baki bawa wanda zaki aura dama ba. Nawa akayi kuma? Mata nawa ne mazajensu suka mutu kuma suka same aure? Wata ma bata shekara take kara wani auren. Amma ke kinyi goma, goma is very much okay, dan ma biyar din farko ba'a gida kika yi su ba da babu yadda za'a yi a barki kiyi goman"

Sai ta kara zuba mata wani abincin ta mika mata "ki ci kiyi wanka ki huta, zuwa anjima sai kije ki fuskanci Takawa, ki kuma shirya wa yadda zakuyi da shi". Fatima bata kara ko loma daya abincin ba, abinda take ta lissafawa a ranta shine; ko Adam ko wani, shima kuma Adam ko ita ko wata.

Allah ya taimake ta Takawa bai nemi ganin ta ba sai dare, a tsahon lokacin ta gama lissafe lissafenta. Idan ta tata ne, idan ta son zuciyarta ne, zata zabi Adam a cikin ko maza dari ne aka jera mata. Dan tasan in ta barshi ba lallai ta samu mai nagartarsa ba. Bata taba ganin mutum mai gaskiya irin sa ba, bata taba shakuwa da wani, ko da kuwa a cikin siblings dinta bane irin yaddata shaku da Adam ba, babu wanda ya santa ciki da bai kamar yadda Adam ya sanya. Ta tuno rayuwara su a imo, babu irin abinda baiyi mata ba, har abinda mace ce ya kamata tayi mata amma Adam yayi mata kuma ita dai a cikin abubuwan da zata iya tunowa bata taba tuno ranar daya taba gwada taking advantage of her ba, ko da gwaji bai taba ba, wanda kuma hakan abu ne mau matukar girma a gurinta musamman a matsayin sa na balagaggen namiji mai jini a jika. Sannan ga kyau, Adam kyakykyawa ne, irin kyan da duk kushen mai kushe sai dai yayi shiru amma ba zai iya aibatawa ba. Ga gayu, a lokuta da dama gayunsa yana tuna mata da Hussain, they have almost the same taste na yadda suke dressing da kuma yadda suke tafiya da zamani. Matsayin iyayen sa, da kuma kabilar sa, basu taba damunta ba a zamanta da shi.

Amma kuma in ta cire selfish interest din ta sai kuma taga cewa gwara ta zabi wani akan Adam, saboda tana ganin bai dace da ita ba. Tana ganin ba zata bashi kulawa da kuma soyayyar da yayi deserving a rayuwar aure ba. Sai take ganin kamar in taki zaben nasa shi ta taimakawa, sai dai amma wa zai aura kuma? Sai taji bata son sanin wadda zai aura din.

Da dare tana falon Hajiya Fulani taji sallamar sa zai shigo, sai taji kamar zata tashi ta bar gurin, ta lura da yadda shima ganin ta ya saka yayi kamar zai koma da baya amma dai sai ya shigo din ya durkusa ya gaishe da Hajiya Fulani yayi godiyar irin saukar da akayi masa sannan yayi mata sallama. "Zan dan je Kaduna ne in kwana biyu" tace "kwana biyu na bahaushe ko kuma kwana biyu na lissafi" ya dan shafa kai "na bahaushen dai Hajiya, ban san dai kwana nawa zanyi ba gaskiya. Sai an ganni dai kawai, suna ta korafin bana zuwa ne"

Hajiya tace "Allah sarki, ka kyauta sosai kuwa, gidan su yarinyar nan ne ko? Wama sunan ta" "Sumayya" ya fada "sunan ta Sumayya" ta gyada kai "haka ne. To Allah ya kai ka lafiya ya dawo da kai lafiya. Ka gaishe da su sosai. Allah yasa dai ba zaka yo laifi a gurin aikin ka ba, ga kuma makaranta kana fama ita ma" yace "na dau leave a office, school kuma dama thesis nake yi, babu wani problem insha Allah" tace "Allah ya yarda. Allah kuma ya kiyaye hanya" yace "ameen, Nagode sosai. A huta lafiya"

Ya mike ya dauki hanya fita daga gurin without a single glance at side din da Fatima take zaune, duk kuwa da cewa zuciyarsa tana ta tunxura shi akan ya kalleta ko da sau daya ne, sai da ya kai tsakiyar falon sannan Fatima da tun da suke magana da Hajiya kanta yake kasa, amma tunda ya tashi kuma ta bi shi da ido, tana jin babu dadi yadda yayi ignoring dinta. Tace "adawo lafiya, Allah ya kiyaye hanya" ya dakata sannan ya waigo yana kallon ta, sannan yace "ameen Nagode" then ya juya ya karasa fita.

Fatima ta bishi da kallo kamar yadda Hajiya ita kuma take kallon ta.

Bai jima da fita ba jakadiya ta shigo tana yiwa Fatima iso cewa mai martaba sarki yana nemanta yanzu. Ta tashi ta nemi babban mayafi ta dora akan doguwar rigar jikinta sannan ta tafi. A bakin kofa jakadiya ta sannan Fatima ta shiga ita kadai, yana zaune a an kujera Hajiya Ummah tana zaune a kasa saga gefenta, Fatimah tana ganin Hajiya Ummah sai gabanta ya fadi, tana ganin cewa bata rike mata alkawari ba. Ta durkusa ta gaishe shi cikin biyayya, shi kuma ya amsa mata cike da kauna da kulawa. Sannan ya tambaye ta "ya kika baro yaruwar taki da iyalinta?" Tace "suna nan lfy lau Allah . Sunce ayi musu gaisuwa sosai" yace "madallah. Allah yayi muku albarka baki daya" Hajiya Ummah tace "ameen".

Sai Fatimah taji tana son tashi, duk da dai bata gama ganin mahaifin nata ba amma sai taji tana son tashi tun kafin yayi mata maganar da bata so, maganar kuma da take ji a jikinta cewa zaiyi mata. And it is rude ka tashi daga gaban manya ba tare da sun sallame ka ba. Sai yace "Adam yayi min sallama dazu wai zaije Kaduna ya kwana biyu a can, kunyi maganar da shi?" Ta sunkuyar da kanta kasa tana wasa da hannunta tace "eh munyi maganar ran sarki ya dade" yace "da safe zai tafi, na dauka ko zaki so zuwa ki gaishe da Hajiya Amina" ta girgiza kanta da sauri, "zan je, amma nafi son in dan kwana biyu a gurin ku in gama ganin ku tukunna"

Yayi murmushin "mun ganki ai, munji dadin ganin ki kuma, mun fahimci lafiya ta same ki sosai yanzu alhamdulillah. Amma mu ba haka muke so ba, ba so muke muyi ta ganin ki haka ba kin taho daga gidan yayarki kin kwana biyu anan kin kuma komawa gidan yayarki. So muke mu ganki a gidan mijinki kema, idan har Allah ya bamu yawan rai ma muna so muga yayanki kamar yadda muke ganin na yanuwanki. Ba zamu matsa miki ba saboda munsan irin abubuwan da suka faru dake a baya, amma kuma ba zamu barki haka ba ba kuma zamu zabar miki miji ba, ke zaki zaba da kanki namu shine mu baki shawara mu kuma tabbatar da nagartar duk wanda kika zaba din"

"Amma abinda zan tuna miki shine, mu lokacin mu ya tafi, mun gama zamanin mu mutuwa kawai muke jira" ta rufe baki cikin rudani "Takawa!" Yace "ai mun gode ubangiji, yayi mana komai alhamdulillah, rayuwa kuma ai mun mora, fatan mu dai kafin mu tafi mu tabbatar cewa dukkan ku mun barku cikin rayuwa mai kyau. Mun aurar da ku mazan ku da matan ku idan da rabo ma munga yayan ku. Ke da yaruwar ki Asma'u ne kadai kuke a gida, ita ma kuma an saka ranar ta wata biyu suka rage mata a gida, ke kuma yau shekara goma da Allah ya karbi ran mijinki dan haka muna umartarki ki fitar da wani mu sake aurar dake. Kije kiyi tunani kuma kiyi addu'a, sannan sai ki sanar damu zabinki mu kuma sai mu karasa sauke nauyin da Allah ya dora mana"

Fatimah ta dago kai tana kallon Hajiya Ummah wadda ita ma ita take kallo sannan tace "tashi kije kiyi abinda aka umarce ki dashi. Allah yayi miki albarka yayi miki jagora" tace "ameen. Na gode. Allah ya ja min da ranku" sannan ta mike ta koma cikin gida tana harhada hanya, ta tuna da lokacin da aka kira ta aka vata irin wannan umarnin na cewa ta fitar da miji. A lokacin zuciyarta fara kal ta fito daga gaban mahaifinta tana zuwa daki kuma ta kira Hussain tayi masa albishir. A lokacin bata yi tunanin za'a kuma bata irin wannan umarnin. Lallai mutuwa mai yankan kauna, mutuwa mai tonon asiri.

Bata tsaya ko'ina ba sai dakin ta, wanda yake part guda ne a gidan wanda mai martaba sarki da kansa ya saka aka shirya mata shi tun dawowarta gida, duk da dai ba sosai take amfani da gurin ba dan ba zaman kasar take yi ba, in tazo kuma tafi son zama tare da hajiyan ta ko kuma tare da Ummah. Amma yau sai ta tafi can, an riga an gyara mata shi da niyyar ko zata yi amfani da shi, dan haka ta wuce cikin bedroom ta kwanta akan gado rigingine tana kallon ceiling. Maganar data fi tsaya mata a rai a cikin maganganun Takawa shine na mutuwa da yace zaiyi, ya kuma gaya mata cewa burin sa a yanzu shine ya aurar da ita kuma yaga yayanta kafin mutuwa ta riske shi. Sannan a karshe ya bata umarnin ta fito da miji. Duk da bai gaya mata limit din lokacin daya bata din ba.

"Oh Hussain, oh Mi Amour, what should I do?" Sai ta rufe fuskarta da hannunta ta fara kuka.

Sai kuma taji tana son yin magana da Adam, shine kullum a kusa da ita in tana bukatar a shoulder to cry on. Bata jin a cikin shekaru goman nan akwai wata magana da aka taba fada mata ba tare da ta gaya masa ba, ballantana wannan maganar mai girma haka. Amma wannan dole zai zamanto na farko a tsakanin su.

Washegari da wuri ya fita, kasancewar yana son fita da wuri ne ya saka tun jiya yayi sallama da kowa, sannan ba tare da ko breakfast yayi ba ya dauki hanyar Kaduna. Bai samu Baba a gida ba sai Inna da Zunnur, wadanda suka yi masa sauka ta musamman kamar yadda suka saba yi masa a duk sanda ya samu damar zuwa gidan.

Sai kuma Inna Ade ta fara yi masa zancen da yasan dama dole zata yi masa "Adam har yanzu babu aure ko? Ko mangofak kake so ka zama?" Yayi dariya, "a'a fa Inna, lokaci ne dai kawai bai zo ba amma babu ruwan karatu" tace "to Allah ya nuna mana lokacin, ya kamata dai ayi kokari ayi, shi aure ai shine cikar mutum, duk shekarun mutum duk hankalin sa idan bashi da aure to tamkar rabin mutum yake" ta cigaba da nasiha akan aure, a inda ta tsaya anan Baba ya dora da yazo gidan bayan Zunnur ya kira shi ya gaya masa zuwan Adam. "Ni na dauka ma maganar aure ce ta kawo ka?" Yace "Baba zuwa nayi fa in gaishe ku in kuma ganku ku ganni"

Baba yace "mungode munji dadin ganinka amma munfi so ace ba kai kadai kazo ba, ace tare kazo da matar ka da yayan ka sai kuyi mana sati a nan" Adam yayi murmushi yace "watarana Baba, insha Allah" Baba yace "Allah yasa. Amma dan Allah ka kara himma kaji? Ni bani da sauran yaya mata da na baka, da ace ina da yar budurwar ya a gaba na da tabbas bata da miji idan ba kai ba dan kuwa duk wata nagarta da ake nema a gurin miji ina ganin kana da su malam Adamu" Adam yace ya gode, yana kokarin chanja maganar dan baya son ta kunan zuciya take kara saka shi. Amma Baba bai bar maganar ba sai yace "amma ida ka amince, idan kuma babu wata a ranka a yanzu, ni zan samo maka mata a cikin yayan yan'uwa na" sai Adam yace ya amince din, na farko saboda ya faranta ran Baba, na biyu kuma dan abar maganar, amma shi yasan zai bi duk hanyar da zaibi dan ganin ya kubce daga wannan tarkon.

Daga nan kuma sai suka kama hirar abinda ya shafe su, Baba ya bashi labarin halin da Ruqayyah take ciki a yanzu shi kuma yayi alƙawarin zuwa duba ta kafin ya bar garin, sai kuma suka yi hirar Hassan da irin daukakar da yake samu yanzu, Baba yana bawa Adam labarin yadda yake kula dashi sosai. "Ya dage sai na bar gadin nan, ni kuma bana son inzo gida inyi ta zama a daki kamar mace shi yasa na ke son aikin, amma dole yanzu na hakura dan in faranta masa, tare da Sulaiman, shima lallai so yake in daina" Adam yace "nima kuma na kara roko akan nasu, lokaci yayi da za'a huta Baba, tunda Allah ya raya zuria kuma yayi musu albarka ina ganin a zauna a gidan a huta shi yafi" Baba yace "kash, zaman gida ai kashe jiki yake" Adam yace "to me ake so ayi yanzu in an var wancan aikin da bama so?" Baba yace "makarantar islamiyya nake sha'awar budewa in ringa koyar da yara da kuma manya karatun Alqur'ani, wannan shine burinsa.

Dai Adam yaji yana fatan Allah ya bashi iko ya cikawa Baba wannan burin nasa. Amma yanzu addu'a yake so ayi masa akan abinda yake damunsa. Yinin ranar gabaki daya haka yayi ta babu dadi, ya kasa tuna lokacin da ya shiga cikin kuncin zuciya irin na wannan lokacin. Bama ya son yaga wayarsa dan zuciyarsagaya masa takeyi ya dauka ya kira ta, yana son ganin ta , yana kuma son jin muryar ta amma yasan kiran a waya ba zai taba haifar masa da Da mai ido ba, shida ya tahoda niyyar ya rarrashi zuciyarsa ta manta da ita, tabbas in ya kira ta zai bata


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login