Showing 183001 words to 186000 words out of 300844 words

Chapter 62 - Tagwaye Book 1 Hausa Novel Complete

22 Dec 2024

2079

ita bata san inda ake samo yan aiki ba dan tunda akayi bikin su Aunty ce take samo mata yan aiki har da mai girki duk ita take samo mata ita da Fatima, gashi yanzu na Fatima sun gudu saura nata kuma aikin yayi wa nata yawa dan gidan ba irin nata bane ba, duk kuwa da cewa bangaren Hussain a rufe yake.

Sai taji gida yayi mata shiru sosai, taji wani irin kadaici kamar ita kadai ta rage a duniya, wannan yasa ta kira zuwaira a waya, kawarta ce da Minal ta hada su kuma tana cikin kawayen ta da suka tsaya mata a wajen bikin su ta gaya mata problem dinta "ban sani ba ko kin san yadda zanyi in samo yan aiki? Kamar gida biyu haka masu hankali" babu bata lokaci zuwaira tace zata samo mata sannan kuma suka jajanta labarin batan Minal, zuwaira tace "ance man ke ce mutum ta karshe da kika ganta ko?" Ruqayyah tace "inji wanne munafikin? Inji wanne makaryacin?" Zuwaira tace "a'a, ni da mijinta ne yake gayamin kuma yace mijinki ne yagaya masa, ba san waye munafikin ba a cikin su ba kuma san wate makaryacin ba" Ruqayyah tayi kokarin chanja maganar "okay ban san sunyi maganar ba ai. Ki gayyato duk kawaye ku zo kuga sabon gidana" sai ta bata labarin tarewar da tayi a gida Hussain. Tun a wayar taji excitement a muryar ta, kafin a jima kuwa wajan mutum biyar a kawayen su sun kira ta aka maganar, shi kenan aka bar maganar batan Minal aka cigaba da lissafa yadda za'a ci duniya.

Wannan yasa Ruqayyah taji kadaicin taya dan ragu, sai dai tayi ta kiran wayar Sumayya amma bata shiga, taso ko ma menene zata yi Sumayya takasance a hannun damanta kamar yadda suka shirya tun suna yara amma abin ya gagara, daga dukkan alamu Sumayya tayi fushidaita amma tasan zata sauko tunda ita ba iya fushi tayi ba, dawani ma ballantana da ita yaruwarta Ruqayyah.

Sai ta bata lokaci da niyyar ta huce, kafin nan suma su Inna da Baba sun huce sai taje har gida tayi musu bayanin cewa Hassan da kansa ya dauki kudin nan ya bata ba takura masa tayi ba, wata kila ma daga nan su yarda su biyo tasu dawo gidan da zama gabaki daya. Wata kila idan sunzo ta samu nutsuwar zuciya har ta iya bacci, dan yanzu sam bata bacci sai ta sha maganin bacci shima idan ta sha a wahale take yin baccin. Wannan kukan jaririn ne yake damunta a kunnuwan ta, ko ta cire hearing aid dinta bata daina jin sa dan kamar a cikin kanta yake ba wai ta kunnen ta kukan yake shiga ba. Da zarar ta rufe idonta kuma gawar Minal take gani, bata yo mata magana sai idanuwa da take tsare ta dasu, idanuwa masu ban tsoro, in kuma ta samu tayi baccin to kuwa sai Hussain ya ziyarce ta a cikin baccin ta, kullum mafarkin kusan guda daya ne cewa jaririn data ajiye a kofar orphanage ya girma ya rikide ya zama Hussain ita kuma ta koma jaririn, so defenseless so vulnerable and so scared, shi kuma sai yazo yasa kafa ya tatsile ta, kullum mafarkin iri daya ne amma kuma kullum sai ya bata tsoro tamkar ranar ta fara yinsa.

A haka har tayi sati daya agidan ita kadai kamar mayya, wanda zata yi magana dashi ma babu sai yan aikin da ba wata sabawa sukayi ba balle suyi hira, a lokacin ne kuma kawayenta suka kawo mata ziyara ta zagaya dasu duk suka ga gida suna ta yabawa. A ranar ne kuma alert ya shigo wayarta na ribar data samu a kamfani a cikin wannan satin. Ta rike baki tana mamaki hade da murna, da gaske Hassan yake kenan, da gaske wannan kudin duk nata ne. Lokaci yayi da zata je gida ta yiwa su baba bayani ta kuma lallabasu su dawo gidan ta da zama ko ta danji dadi a ranta, dan ita har yanzu data ga alert din kuɗin bata ji dadin da take tunanin zata ji ba. Zuciyarta a kuntace take, maybe in suka zo zata ji dama dama.

Ta shirya ta ja kafa ta sauka kasa ta aika aka kira mata drivern data bari a matsayin nata ya jata zuwa gida, ta ja kafa cikin murna ta shiga gida amma tun a soro Baba ya dakatar da ita "me kika zo yi gidan nan?" Tace "Baba ina wuni? Nazo muyi magana ne" yace "maganar me? Innar ki bata gaya miki sharadin dana kafa ba? Amma na ganki da mota? Cewa nayi ki ajiye duk abinda kika san a gidan Hassan kika same shi ki taho ke kadai kamar yadda aka kai ki ke kadai, idan ba haka kika yi ba kar ki shigo min gida na" ta fara girgiza kanta "Baba shi ya bani da kansa matsa masa nayi ba, kaso ya bani a cikin kamfanin su, da kuma gidan daya gada na danuwansa, yanzu duk nawa ne, zuwa nayi ku binimu tafi can zai fi nan dadin zama sai......" Ya daga mata hannu "duk ya gaya min abinda kika yi wanda yasa har ya baki wadannan kudade, bama son ko kwandala a cikin su, ke kadai muke so, in kina son mu ki jiye masa kudinsa ki dawo gare mu, in kuma kinfi son kudi ki koma ga kudi mu ki barmu"

Ruqayyah ta zabi kuɗi.....ko cikin gidan Baba bai barta ta shiga ba....ko Sumayya bata samu ta gani ba.....

Tun a mota ta fara kuka, kuncin zuciyarta yana karuwa. Tana som family dinta tabbas kuma zata iya zabensu akan kudi idan da ace bata samu nakasa ba, amm yanzu she can't even imagine herself a matsayin kurma, gurguwa, bazawara kuma talaka. In tana cikin wannan nakasar kuma tana cikin kudi ai da sauki ko? Sai ta samu kanta da questioning choices dinta, shin me yasa ma tayi abinda tayi ne? Me yasa kuma ta tona asirin ta ga Hassan har ta kai shi ga sakinta har kuma ta kai iyayenta suka sallama ta? Yes, tana son kudi, kuma koda yaushe tana yin dogon tunani akan hanyar da zata sami kudin amma yanzu me yasaya zamana kamar kanta ya toshe ne?

A haka ta koma gida ta cigaba da rayuwa, ta tashi ta jawo jiki zuwa palo tayi kallo taci abinci ta koma daki ta kwanta ta kasa bacci ta kuma dawowa palo ta zauna. Sai in ta gaji ta kira kawayenta suzo suyi ta mata hir ta dauki kudi ta basu du tafi. Shikenan. Hatta wayarta takan wuni batayi kara ba. A cikin wata daya sai da loneliness din ya zamanto kamar zai kasheta da ranta. Ta rame tayi duhu kuma ita kanta tasan rashin bacci ne. Tsoro da fargaba dan ko kofa aka taba sai taji kamar zuwa za'a yi ace mata ga Fatima nan ta dawo.

Ta koma gidan su har sau biyu amma ko tsakar gida bata taka ba, kamar Baba yanzu ya daina gadin kamfani ya koma gadin kofar gidan sa. Sai a lokacin ta tuno da malamin duban Minal, sai a lokacin ta samo amsar tambayar da take yiwa kanta na dalilin da yasa ta aikata abinda ta aikata din, abinda malamin duban nan ya gaya mata shine dalili, wannan kudin daya kwadaita mata shine tabi ta kuma dauki zabin da take ganin shi zai kaita ga kudin, kuma ya kaita din. Amm kumaa cikin duban nasa bai gaya mata cewa zata zama musaka ba, ko bai ga wannan ba? Ko kuma ya gani bai fada mata ba?

Sai ta ya ke shawarar komawa gurinsa.

Bata manta gidan ba, ta kwatantawa drivern kuma ya kaita har kofar gidan sannan t fita tana jan kafa ta shiga ta aika aka gaya masa yayi bakuwa kamar yadda taga Minal tayi ranar nan. Akayi mata iso ta shiga har palon da suka zauna ranar nan, kamar babu abinda ya chanja amma komai ya chanja, babu Minal, babu kunnuwan ta babu kafarta guda daya.

Tana zaune ya fito fuskarsa da murmushi ya zauna yana kallon ta "Hajiya Ruqayyah barka da zuwa. Har na fara tunanin ko kin manta da alkawarin mu ne" ta bata fuska tace "alkawari kuma? Wanne alkawari muka yi da kai?" Yace "alkawarin idan aikina ya tabbata zaki zo ki biya ni kudin aikina" tace "ni babu aikin dana saka ka ballantana in biya ka. Ni sanda nazo gidan nan bansan kai malamin duba bane ba da ba zanzo ba ma. Sanda ka yar da charbin ka bansan duba zakayi min ba shi yasa na dauka, da na sani da......" Yace "and yet, you believed what I said" ta tsaya ta saki baki tana kallon sa, ya daga kafada yace "eh, mana. Idan har Abinda kika fada har cikin zuciyarki ne me yasa da na gaya miki maganar kika yarda da ita har kuma kika yi amfani da ita? " Tayi shiru ta kasa magana, a lokacin ta fahimci cewa wannan shine kuskuren ta a wannan bangaren, yarda da abinda malamin duba ya gaya mata, da bata yarda ba da ba lallai ta kawo idea din yarda jaririn a ranta ba, da bata yarda ba da ba zata yi tunanin wasu options guda biyu ba har ta zabi daya, da bata yarda yaron ba kuma da ba zata hadu da wadannan masifu da suke ta samun ta a jere ba, da bata hadu da masifun ba kuma da ba zata zama frustrated da har zata gaya wa Hassan maganganun da zasu saka ya sake ta iyayenta kuma su sallamawa duniya ita ba.

It all starts here.........duk da dai ya tarar da hali.

Ta mike tana jan kafa zata bar gurin yace "baki sallame ni ba har yanzu" ta juyo a fusace "me zan baka ne wai ni? Ka barni da masifun da nake ciki mana kar ka kara min da naka masifar kuma. Wallahi kwandala ba zan baka ba kuma babu abinda zance maka sai Allah ya isa tsakani na da kai" ta sake juyawa sai yace "ina kawarki Amina? Har yanzu ba'a tono gawarta ba ko?" Ta juyo da sauri ta zube idanuwan ta akansa, yayi murmushi yace "yar uwarta tazo nan gurina akan in duba musu ko zanga inda Amina take, na duba kuma na gani, naga mutuwarta, na kuma ga inda aka binne ta" Ruqayyah ta dauke numfashin ta tana jiran mai zai ce sai kuma yace "amma ban gaya musu ba, ina jiran sai kinzo tukunna" tace "abinda ka gani karya ne, in da gaskiya kana ganin badini me yasa baka gayawa Minal cewa ga abinda zai faru da ita ba? Me yasa baka gaya min cewa ga masifun da zasu same ni idan nabi kudi ba?" Yace "ba komai nake gani ba sai abinda Allah Ya banj ikon gani, in kuma na gani din ba komai nake fada ba, ina fadar abinda zai saka mutum ya sake dawowa gurina ne ba wai abinda zai saka mutum ya daina zuwa ba. Idan da ace na gaya miki zaki zama kurma kuma gurguwa ai da ba lallai ki bi hanyar da nake so kibi ba, kinga kuma da ba zaki dawo yanzu ba" ta dafe kanta tana jin hawaye yana cika idonta, sai yace "wannan da jaririn yana nan lafiya kalau, mahaifiyar sa ma kuma tana da rai" ta bude idon tana kallon sa, bakin ta ya kasa budewa balle har tayi masa magana, sai ya dauko wata takarda ya ajiye a gabanta yace "account number dina ce, da kuma adadin kudin da nake so kike turo min duk wata a cikin account din, in ba haka ba zan gayawa yan uwan Amina exactly a inda gawarta take zan kuma gayawa Hassan a inda dan danuwansa yake in kuma bashi labarin yadda akayi yaje gurin. Wannan karon in ya shake ki sai ya kai ki lahira. Sannan Inna da Baba su biki da tsinuwa har cikin kabarin ki. Zabi ya rage naki".

*Her New Life*

Ta fara girgiza kanta hawaye yana zuba tana cewa "karya kake walllahi, kai baka isa kayi blackmailing dina ba karya kake wallahi, babu abinda ka sani, kawai kame kame kake yi dan ka mayar dani saniyar tatsar ka amma karya kake babu abinda zaka iya yi min" yace "da gaske? To ki gwada ki gani mana. Nan zuwa karshen wata kar inji alert a waya ta kin ga a lokacin zaki tabbatar da gaske nake ko karya nake yi, zaki tabbatar na sani din ko kuma kame kame nake yi" ta zauna a hannun kujera saboda yadda taji tana neman faduwa tace "azzalumi, mugu, in Allah ya yarda ba zaka gama da duniya lafiya ba" yace "ni wanne zalunci nayi? Ni ban dauki jariri daga jikin uwarsa na jefar dashi ba, kuma ban boye mutuwar aminina ba, dan haka tsakanin ni da ke za'a warware waye azzalumi. Ni sana'a nake yi, wannan aikin duban shine sana'a ta dashi nake samun kudi kuma dashi zan cigaba da samun kudi ta wajen ki, ban jawo kafarki na kawo ki gurina ba da kanki kika zo, da kanki kuma kika aikata abinda kika aikata ni ko shawara ban baki ba, sannan kuma da kanki zaki ke biya na kudi duk wata" bata ce komai ba har ya mike, yana kallonta yace "kar ki manta da takardar in zaki fita" sannan ya koma ta kofar daya shigo.

Ta jima a zaune a gurin tanajin hawayen ta yana zuba akan rigarta, sannan ta saka hannu ta dauki takardar tana karanta amount din kudin daya rubuta sannan ta girgiza kanta da sauri, inaa, ba zai yiwu ba, wato kura da shan bugu gardi da kwace kudi? In dai har zata ke bashi wannan kudin duk wata sannan zata ke biyan maaikatan data dauka a gida albashi plus kayan abinci da sauran house maintenance to babu abinda zata tsira dashi ita din. Tunda ta fara ganin alert daga H and H lissafin ta shine ta tara kudi ta nemi hanyar da zata bi ta dauko likita daga waje yazo ya duba mata kunnen ta yadda zata iya hawa jirgi ta tafi neman lafiyar kafar. Yanzu kuma gashi wannan yallaban yace shi zata ke bawa kudin, wato ita kuma ta cigaba da zamanta a matsayin musaka har karshen hargitstsiyar rayuwarta? Gaskiya da sake wai an bawa mai kaza kai.

Ta dauki takardar ta saka a jakarta ta koma mota suka fita daga gidan, a zuciyarta tana tambayar kanta dalilin daya dawo da ita zuwa gurin dan duban, duk dadai tasan in yaso blackmailing din nata zai iya binta har gida ya gindaya mata sharadin sa. Amma wannan sharadin sam ba zata iya binsa ba ba zata iya zama baiwar sa ba. Ita da zunubin, ita da rashin iyaye, ita da nakasa, ita da rashin miji sannan kuma shi da samun kudi? Wannan sam ba zata yiwu ba.

Tana zuwa gida ta wuce cikin bedroom ta jawo akwati ta fara zuba kayan sakawarta, gida zata koma ta zauna, gwara ta mayar wa da Hassan dukiyar sa kamar yadda Baba ya bukata, gwara ta bi sharadin Baba wanda ya haife ta ya kula da ita har girmanta akan ta bi sharadin wani kazamin mutum da yake kiran kansa da Malami. Ai dai tasan Baba ba zai hana ta daukan kayan sakawarta ba tunda dai ya'ya uku maza ta haifawa Hassan ai kuwa ta ci lefenta. Gwara taje ta zauna a matsayin musaka, bazawara, talaka amma kuma tare da iyayenta akan ta zauna anan a dukkan wadancan matsayin amma kuma babu iyayen. Sai data cika akwayi biyu da kayan sannan ta fita da niyyar kiran nai aikinta ta fitar mata da kayan bakin gate sai kuma wani tunani yazo mata, yanzu in ta mayar wa da Hassan dukiyar sa ba zata ke biyan mai duba ba, in kuma ba ta biya shi ba zai iya aikata abinda yace zai aikata.

Ta tuno da Fatima da matsayin ta da matsayin mahaifinta da irin tarin son da yake yi mata, me zaiyi idan yaji labarin cewa gawar daya binne ba ta Fatima bace ba, in yaji cewa Fatimah tana raye amma ba'a san a inda take ba, sannan kuma danta, jikansa an jefar dashi cikin kaskanci a gidan marasa gata? Tasan in ya fara daure ta har sai igiya tayi saura kuma babu wanda zai taimaka mata tunda ita a yanzu bata da kowa. Ta tuno irin zuciyar Hassan kuma da irin son da yake wa Hussain, idan yaji abinda ta aikata ga da daya tilo na Hussain in ya shake ta tabbas sai ta dangana da lahira. Idan haka ta faru sunayenta zasu karu daga kurma gurguwa bazawara talaka zuwa yar prison, ko kuma worst, matacciya. Ita kuwa bata shirya tafiya lahira yanzu ba dan tasan bata aikata abinda can din zata yi mata kyau ba.

Ta zauna akan kujera tana dafe kanta, ita kanta tasan cewa rayuwar ta ta kare tun kafin ma ta soma. Ita da kanta ta dauko biro da takarda tayi signing contract da shaidan shi kuma ya zuga ta ta haka rami da kanta ta shiga sannan malamin duba ya binne ta da ranta. Menene kuma yayi mata saura?

Babu abinda ba zata iya bayarwa ba a yanzu dan ta dawo da hannun agogo baya. Dan ta dawo da rayuwarta ta baya, dan ta dawo da alakar ta da Hassan. Ta tuno da irin son da Hassan yake yi mata da yadda yake tsayuwa akan dukkan al'amuran ta, da ace suna tare ne da wannan mai duban bai isa yayi blackmailing dinta ba Hassan sai ya kwato mata yancin ta. Ta tuno Sumayya, da irin yadda suke open to each other, babu abinda ba zata bayar ba a yanzu dan ta samu Sumayya ta gaya mata halin da take ciki ko zata bata shawarar yadda zasu bullowa lamarin. Ta dauki wayar ta for the nth time ta kira number din Sumayya amma ko ringing ba tayi ba ta katse kamar yadda take yi kullum alamar an yi blocking layinta kenan. Wai Sumayya ce tayi blocking dinta, kuma tasan akan Adam ne. Ita a ganinta taimakon Sumayya tayi data rabata da


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login