Showing 192001 words to 195000 words out of 300844 words

Chapter 65 - Tagwaye Book 1 Hausa Novel Complete

22 Dec 2024

2697

yasa kudin da take son tarawa dan ta nemi magani suka gaza taruwa tunda duk wata sai ta fitar da kudin wancan cima zaunen ta tura masa.

A ranar da aka daura auren ne bayan tayi sallar magrib tana ta shige da fice a social media, dan yanzu nan ne gurin hirarta a nan ne kawai take ɗebe kewarta sai taga Khadijah ta saka hoton Hassan da Sumayya, a kasan hoton ta saka "Allah ya sanya alkhairi yaya H1, Allah yasa abokiyar tsufaka ce" ta tashi tana murza idonta dan ta tabbatar da abinda idon nata yake nuna mata, ko dak shima idon ya fara samun matsala ne kamar yadda kafarta da kunnenta suka samu?

Still dai hoton Sumayyan ta sake gani taci kwalliya irin ta amare tana murmushi duk da dai fuskarta ta dan kumbura kamar tayi kuka sosai, Hassan kuma a gefenta bakinsa har kunne. Ta mike da sauri, tama manta cewa yanzu bata iya mikewa tsaye sai da croches, wannan yasa ta fadi flat akan fuskarta akan tiles din falon, a take bakinta da hancinta suka kama zubar da jini amma ba shine abinda yafi daga mata hankali ba, wayar ta ta sake laluba tana kuma kallon hoton Hassan mijinta uban ƴaƴan ta da kuma Sumayya kanwarta twin sister dinta. Da sauri ta shiga comments taga mutane suna ta addu'ar fatan alkhairi, ta fita ta fara laluben accounts din sauran kannen Hassan, duk sai taga suna ta celebrating abin ba wai Khadijah ce kadai ba.

Ta lalubi crutches dinta ta mike da sauri ta bude kofar da zata sadata da valcony din dake hade da palon da take zaune a ciki, ta fita tana leken gidan Aunty sai ta ganshi a cike da motoci, mutane suka ta hada hadarsu, can da nisa ta jiyo wata ta rangada guda. Ta girgiza kanta tare da marin kanta kadan dan ko zata farka daga mafarkin da take yi "no!" Ta fada da dan karfi, it can never be, ta yaya mijinta zai auri twin sister dinta alhalin gata da ranta tana numfashi? Ta yaya haka zata kasance?

Ta juya da sauri ta dauki hanyar fita, ba zata iya kirga yawan faduwar da tayi ba kafin ta sauka palon kasa sannan ta tsare yan aikinta da suke zaune rashe rashe a kan kujeru a palo suna kallo tace "bikin wa ake yi a gidan Aunty?" Tayi maganar da karfi tana goge jinin da ya fito daga bakin ta. Duk suka kalli juna sannan suka kalle ta, wai dama bata sani ba? "Ba tambayarku nake yi ba? Bikin wa ake yi?" Saya daga cikin su tace "daddyn su Yusuf naji ance an daurawa aure dazu da safe, amma ban san wa ya aura ba" tayi kokarin damko wadda tayi maganar amma saboda cika crutch din da tayi sai ta tafi zata fadi, suka rike ta "karya kike yi kice baki san wadda ya aura ba, kuna sane baku gaya min ba, kuna sane kuka bari mijina ya auri kanwata"

Su dai yan aiki basu ce komai ba dan basu da abin cewa, wannan magana ba tasu bace ba, amma sun san wadda aka aura din dan tun satin da ya wuce ake ta tsegumin abin a tsakanin yan aikin gidajen da drivers da masu gadi, kowa yana fadar albarkacin bakinsa wasu suna ganin kamar hakan ma ba musulunci ba ne ba. Amma ganin ita din wadda aka yi wa rashin kyautawar bata ce komai ba yasa suma basu ce mata komai ba, ashe bata sani ba.

Har ga Allah su tausayin ta suke ji dan aganin su karshen rashin adalci anyi mata, saboda ta zama musaka sai mijinta ua sake ta ya raba ta da yayanta sannan ya auri kanwarta? Wannan wanbe irin rashin adalci ne?

Jin sunyi shiru yasa Ruqayyah ta tabbatar da maganar, ta tabbatar kuma sun sani, sau ta kwace daga hannun su ta zauna a kasa ta dira hannu aka ta fara rusa kuka da duk iyakacin karfin ta, tasan waye ya kulla wannan abin, tasan Baba ne,dama ai ba tun yanzu yake ikirarin aurawa Hassan Sumayya ba saboda ita baya sonta ya tsaneta, saboda ya fi son Sumayya akan ta, wannan kawai shine dalilin sa ba wai wani abu ba.

Ba zasu kyale ta da bakin cikin shakulatin bangaro da suka yi da rayuwar ta ba a matsayin su na iyayenta duk da cewa sun san tana bukatar kulawar su a halin da take ciki amma shine zasu yi mata bi ta da kulli da wannan mummunan lamarin? Ita kuma Sumayya, munafuka, bayan alkawarin da tayi mata shine ta karya ta aure mata mijinta? Wanny shine dalilin da yasa tayi blocking dinta a waya saboda tana busy yaudarar Hassan da nuna masa cewa ita ta Allah ce kamar yadda ta saba yi tun suna yara.

Shi kuma Hassan, munafiki, dama can watakila yana som Sumayyan shine ma dililin da yasa yayi sauri sakin ta kuma har saki uku a lokaci daya dan yaje ya hada baki da Baba ya auri kanwarta. Wallahi basu isa ba, sai ta yi maganin su gaba ki daya, sai ta hana su zaman lafiya, wannan auren ba zasu zauna ba.

Ta sake jiyo wata gudar, kamar kuma a gidan Hassan, wato gyaran data lura ana tayi a gidan kenan? Ita da taga ana aikin ta dauka siyar da gidan zaiyi shima ya sake yin wata sadakar ashe munafikin aure zaiyi, auren ma kuma twin sister dinta.

Tana son ta fita taje ta tara musu mutane akan su kowa ya fahimci irin cin amanar da akayi mata amma kuma bata son fita a yanayin da take ciki, tunda ta sami nakasa ta rasa self confidence dinta, bata son shiga mutane dukda cewa dama can ita ba mai son mutanen bace ba, yanzu kuwa sai take ganin kamar duk wanda suka hadu dashi kallon yamusashshiyar kafarta yake yi.

A gidan Hassan kuwa gida ya cika makil da mutane, kowa sai fadan albarkacin bakinsa yake yi a game da irin chanjin da gidan ya samu, ba zata taba cewa wancan gidan bane ba dan komai an chanja masa tsari. Yanuwan Hassan sunje sun dauko Sumayya wadda tasha nasihohi da adduoi da kuma tarin albarka daga gurin iyayenta da duk yanuwan da suka san gaskiyar abinda ya faru.

Zuciyarta wata iri take jinta tayi mata wani irin nauyi saboda kukan da tasha, tun safe take kuka har dare, sai dai bata tare da bakin ciki, ita kanta tasan biyayyar da tayi insha Allah ubangiji ba zai barta ta tabe ba, tasan Allah zai sanyaya mata zuciyarta ya cire mata son Adam ya saka mata son mijinta wanda ita kanta tasan shi din already ya fara sonta saboda yadda ta lura yana lallaba ta.

Kamar yadda Aunty da hajiyan kano suka kamo Ruqayyah haka suka kamo Sumayya wannan karon ma, karkashin rakiyar gwoggo Habibah da matar kawu Sama'ila har zuwa gidan mijinta, suna shigowa duk da chanjin da akayi wa gidan sai da Sumayya ta tuna da ranar da aka kawo Ruqayyah, ta tuna da kukan da tayi a ranar da yawon da Adam ya tafi da ita har sai da ya ga tayi murmushi sannan ya dawo da ita gidan, ta tuno da yadda ta shigo ta tarra Ruqayyah tana ta gursheken kukan bakin cikin gidan Hussain yafi na Hassan kyau.

Sai ta daga kanta tana kallon gidan Hussain, tana jin a ranta cewa yanzu twin sister dinta kuma tsohuwar matar mijinta tana cikin wannan gidan, zasu yi kuma zaman makotaka, a matsayin su na wadanda suka hada miji a mabanbanta lokuta kuma a matsayin su na tagwaye.

Aka shigar da ita da kafar dama da bismillah zuwa gidan ta, da fatan sai mutuwa ce zata fitar da ita daga gidan. A palo aka zaunar da ita akan kujera, Yusuf a hannun ta na dama Aminu a hannun ta na hagu ga kuma Hussain akan cinyarta, fuskarta da jikinta gaba ki daya katon farin mayafin ta. Yan uwa ana ta daukan hotuna da ita, masu nasiha nayi masu saka albarka nayi.

A lokacin ne suka ji kururuwar Ruqayyah ta shigo, muryarta har ta dashe saboda kuka, "wallahi baku isa ba, karya kuke yi munafukai, azzalumai, maciya amana, almurai, wallahi kunyi kadan ku yi min wannan cin mutuncin" a bakin gate take amma har cikin gidan ana jiyo ta. Nan take jama'a suka dunguma suka fita kwallon ta, masu kokarin bata hakuri suna yi masu tsegumi suna yi. Kokari take lallai sai ta shigo ana riketa, yan uwan Baba dana Inna Ade ne masu kokarin riketa su hana ta shiga ciki yayinda yan uwan Hassan suka zama yan kallo, ita kuma ga babu kafa, ga masifa tana cinta, so take ta shiga ciki ta kalli idon Sumayya, ta kalli idon munafuka.

Sumayya tana jin ta amma bata ko motsa daga inda take zaune ba kuma bata bar yaran sun motsa ba suma, amma duk abinda Ruqayyah take fada tana ji, kuma munanan kalaman ta suna taba har cikin zuciyarta. A lokacin ne ta jiyo murya kamar ta Hassan, ita bata san ma yana gidan ba ko kuma kirawo shi akayi ya taho oho.

"Ki kama hanya ki fitar min daga gida Hassana, kar ki sake ambaton matata da wata kalma marar dadi idan kuma kika sake wallahi sai na yi miki marin da zaki rasa idanuwan ki bayan rashin kunne da kafa. Waye yaci amanar ki? Ke kika ci amanar kanki, ke kika zabi kudi a madadin ni mijin ki da yayan ki da iyayenki da yan uwanki. Bakin cikin abinda kika yi ya saka babanki ya bani kanwarki ita kuma ta karba saboda ta faranta zuciyoyin iyayen ku da kika riga kika bata. Kin zabi kudi, na baki kudi, me kuma ya rage a tsakanin mu? Menene kuma abinda ya rage wanda zaki zo ki karba a hannuna?"

Hassan ya kula ta yabata amsa ne saboda yana son ya wanke Sumayya dashi kansa a idon mutane, yana so ya gaya wa mutane ita ta zabi kudi a kansa ba wai dan ta nakasa bane yarabu da ita ba.

Ta yi kokarin kamo hannunsa "mijina, kar kayi min haka, ni na hakura da kudin da Allah kar ka auri kanwata, dan Allah Hassan, wallahi ina sonka, na hakura da kudin ka mayar da ni dakina dan Allah, na gaji da wannan rayuwar Hassan ka tausaya min dan Allah. Yanzu bana son kudin, bama ni nake cin kudin ba dan Allah ka saurare ni mijina. Wai ina son da kake yi min ne? Ta fada cikin matsanancin kuka

Yace "so? Wanne irin so kike magana akan shi? Ni wadda naso kuma nake so ba ke bace ba, I fell in love with halayen da nayi tunanin naki ne ashe ba naki bane ba, ashe na yar uwarki ne kika ara kika yafa wa kanki, sai yanzu na fahimci dama can ashe Sumayya nake so bake ba, rabo ne yahada ni da ke kuma rabo ya kare tsakanin mu".

Sumayya duk tana jin su, hawaye yana zubowa daga idanunwanta yana sauka akan rigar Hussain da yake kan cinyarta. Bata taba jin Hassan yana fada ba sai yau, ashe dama fada ne dashi haka? Tana ji har hayaniyar ta lafa daga alama an fitar da Ruqayyah daga gidan amma ita tasan this is not the end but the beginning, tafi kowa sanin hali da kuma masifar Ruqayyah tasan tabbas zata dawo ko ba yau ba ko gobe ne.

Gwoggo Habibah ta kira Baba ta gaya masa abinda ya faru ta roke shi ida ya yarda su taho da Ruqayyah gida sai yace "itace tace zata taho? Ta amince da duk sharudda na? Idan ba haka ba ko kofar gida na ban amince ta zo ba"

Ruqayyah taji Abinda Baba yace, sai ta saki hannun gwoggo Habibah ta shige gidan da take kira da matsayin nata a ra ta tana mamakin karfin hali irin na Baba da har bayan wannan abinda yayi mata sannan yace wai ta koma gidan shi, ba san cewa ita a yanzu hanyar da ake bi aje gidansa ma ba zata bi ba. Lissafin da take yi na komawa gida in ta samu lafiya ma yanzu babu shi, sun gama nuna mata karshen kiyayya dan haka su rike soyayyar su ita kuma xata rike rayuwarta. Duk wani ragowar string da take ji yanarike da dangantakar da take tsakanin su yanzu ya tsinke.

Da ta shiga gidan ma bata iya ta hau sama basai tayi zamanta a kasa, kukan ma ta daina yi sai kunan zuciya, bata taba tunanin tana son Hassan ba sai yau, sai data ga shi a matsayin mijin wata, watan ma kuma twin sister dinta. She just can't imagine, zuciyarta ba zata iya daukan tunanin Hassan da Sumayya a matsayin ma'aurata suna yin duk irin abubuwan da ita da Hassan din suka yi a da ba, the bedroom things, yanzu kuma sai yayi da Sumayya?

Da tace ba zata iya kisa ba, now she is not sure .........

Sumayya tana zaune har mutane suka yi ta mata sallama suna tafiya, yanzu duk wanda bai san dalilin rabuwar Hassan da Ruqayyah ba ya sani ko ma ba'a san complete dalilin ba amma an san ita ta zabi ya bata kudi ya sake ta. Hussain already yayi bacci a cinyar ta, sai ta dauke shi a kafadar ta ta tafi dashi sama ita da Zulaihat, sauran kawayensu duk sunyi musu sallama sun tafi musamman saboda ganin dan hargitsin da aka yi sji yasa basu tsaya siyan baki ba.

Sumayya ta saka Zulaihat ta nuna mata dakin yara a saman, ta nuna mata sannan ta nuna mata nata. Ta shiga tana kallon tsarin dakin, sam baiyi kama da na Ruqayyah ba, kayan Ruqayyah sunfi tsada amma ita a idonta sai taga nata kayan sunfi kyau kuma sun dace da ita sosai. Ta kwantar da Hussain akan gado ta sannan ta koma da niyyar tahowa da Aminu da Yusuf sai Zulaihat tace mata "a ina kike tunanin zasu kwana? Wannan din ma ba lallai Aunty ta bar miki shi ba. Sai kin gama cin amarci tukunna za'a kawo miki shi" ta fada da sigar tsokana.

Sumayya ta marairaice "dan Allah kinga yayi bacci, kar a tashe shi kansa yayi ciwo ki tafi dasu Aminu kawai, a barshi shi yayi baccin sa anan" Zulaihat tace "ni dai babu ruwana, zan tafi dasu amma in aunty ta lura baya can na san zata aiko a dauke shi" Sumayya tace "ba zata lura ba ma" a haka sukayi sallama Zulaihat ta kama hannun twins suna ta bacin rai su a gurin mommy zasu kwana, suka tafi.

Ta koma sama dakinta ta shiga ta zauna a kan gado ta saka Hussain a gaba tana kallon sa, amma ba wai shi take kalla ba zuciyar ta tana saka mata urin rayuwar da zata yi a gidan nan tare da Ruqayyah a matsayin makociyarta, da kuma rayuwar da zasu yi da Hassan a matsayin miji da mata.

Bata an kara ba taji an bude kodar dakin an shigo, ta dago kai tana kallon Hassan shima daya tsata yana kallon ta, ta sunkuyar da kanta kasa tana shafa kan Hussain daya sauke ajjiyar zuciya ya cigaba da baccin sa, Hassan yace "ina kawayen naki?" Tace "sun tafi. Kai ina abokan ka?" Yace "sun tafi" sai ya karaso ya zauna akan side drawer yana kallon ta, ita kuma bata kalle shi ba sai kirjinta da yake dukan tara tara.

Ya kalli Hussain yace "shi wannan me yake yi anan?" Ta kara jawo Hussain jikinta tace "yayi bacci ne, shine nace a bar min shi ya kwana anan" ya girgiza kai, "ki ce in koma in bude kofar gida kenan, dan na tabbatar Aunty sai ta aiko an dauke shi" Sumayya tace "ba zata lura ba, dan Allah ka barshi ya kwana anan dan Allah" ya bita da kallo, a tsorace take sosai, sai kara kankame Hussain take a jikinta kamar zata tsaga kirjinta ta saka shi a ciki.

Sai ya mike tsaye yana kallonta yace "shikenan, in kwanan nasa anan zai faranta miki" ya danyi faking hamma yace "sai da safe"

*The Sixth Wave*

Kanta yana kasa tace "Allah ya bamu alkhairi" tana jin sa har ya fita ya rufo mata kofa sannan ta dago kai tare da sauke ajjiyar zuciyar da take ta rikewa. Ta tashi tayi locking kofar sannan ta dawo ta dauki Hussain ta kaishi toilet sannan ta dawo dashi ta kwantar dashi itama tayi shirin kwanciya duk da tasan ba bacci zata iya yi ba, kukan Ruqayyah dazu ya taba ta, ta tina rabon da ta ganta tun ranar da Hassan ya sake ta and she ca only imagine abinda Ruqayyah take ji a zuciyarta yanzu. Duk da tasan ba son Hassan Ruqayyah taje yi da gaske ba amma still dole auren su da Hassan sai ta taba zuciyarta sosai.

Ta kwanta tana tuna Adam, sai kuma ta daina tausayin Ruqayyah dan ita ta jawo komai, idan da Adam yana nan da babu yadda za'a yi Baba ya hana shi ita ya bawa Hassan dan tasan Baba yana son Adam kamar yadda yake son Hassan. Ruqayyah ce tayi sanadiyar rabuwarsu dan haka this will be her price to pay.

Ta dauko wayarta tana going through hotunan su kamar yadda take yi kullum, sai data gama gani sai kuma ta koma farko tayi marking all sannan ta danne delete tana jin zafin abin a ranta amma tasan hakan shine dai dai hakan shine zai kara taimaka mata gurin cire shi daga zuciyarta. Bayan ta gama gode hotunan sai ta koma kan messages dinsa da take ta ajjiyar su suma ta goge su sannan ta shiga contact ta goge number dinsa, tasan ko zai dawo ma he won't be using that same number again.

Sai data gama sannan ta tashi tahe ta dauro alwala tazo ta tayar da sallah, tana gayawa ubangijin ta bukatar ta, and for the first time tun bayan rabuwar su da Ruqayyah sai ta samu kanta da yi mata addu'a tana neman Allah ya shiga lamarin ta ya huce zuciyarta ya daidaita tsakanin su.

Sai da taji bacci yayi mata nauyi har bata iya bude idonta sannan ta


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login