Showing 102001 words to 105000 words out of 300844 words

Chapter 35 - Tagwaye Book 1 Hausa Novel Complete

22 Dec 2024

2065

tana yi sai tayi sallar azahar sannan ta koma kitchen din ta tarar sun kusa gama abincin. Sai ta dawo sama ta kunna tv tayi kwanciyar ta akan kujera tana danna wayarta. A lokacin ne taga an saka ta a sababbin groups, ta kuma fahimci aikin Minal ne, taga wata ta aiko a bata shawara akan uwarmijinta da ta sako ta a gaba, mutane kowa yana fadar albarkacin bakinsa wasu suna bata shawarar da hatta ita Ruqayyah ta fahimci ba dai dai bane ba wasu kuma suna bata shawarar dai dai, masu cewa tayi addu'a kuma suna ta fada. Tayi shiru tana ta lissafi, tabbas social media guri na na samun abubuwa da yawa, alkhairi da sharri dukka, ya danganta da menene a zuciyar mutum.

Tana nan a zaune yan aikin suka hawo da abincin suka shiga dashi dining room sannan suka tambayeta in akwai wani abu kuma, da hannu tayi musu alamar suje kawai, har laasar tayi sannan ta tashi ta koma daki tayi sallah tana jin anya kuwa zata iya cigaba da jiran Hassan dan ita yunwa take ji already, sai ta tunawa kanta da cikin da yake jikinta dan haka tana fitowa ta tafi gurin abinci ta bude zata zuba. Kallo daya ta yiwa tuwon tasan bai tuku ba, tana saka shi a plate kuwa ya fara tarwatsewa. Tayi tsaki tana jin ranta yana baci, ta tuno da tuwon da taci ranar nan a part din aunty wanda ko kwayar shinkafar baka gani a ciki. A bude miyar taga babu laifi a ido, ta dan zuba tana ci taji gishiri yayi yawa. Ranta bai kara baci ba sai data bude farfesun. Gaba ki daya kazar ta narke romon kuma yayi ruwa tsululu. Ta zauna ta zuba tagumi, yanzu ya zata yi kenan? Ita da taso in abincin yayi dadi ta nuna masa kamar ita ce tayi? Wannan ai ita suka bawa kunya.

Kamar daga sama taji sallamar Hassan, tayi kokarin kirkirar murmushi dan ta tare shi amma sai ta tuna cewa fada fa suka yi kuma har yanzu basu shirya ba, dan haka ta bata rai ta koma ta zauna tana cika tana batsewa. Taji motsinsa ya shiga dakinta sannan ya dawo palon sannan ya taho dining din, ya tsara yana kallonta ita kuma ta maze tan cigaba da jujjuya abincin gabanta. Ya jawo kujerar kusa da ita ya zauna yana kokarin leka fuskarta sai ta dauke kai gefe, ya danyi murmushi mai sauti "haba my Precious wife, wai fushin ne har yanzu vaki gama ba?" Ya kama hannunta tayi kokarin kwacewa yace "look. Nasan abinda na fada jiya ya bata miki rai, but dole ce ta saka na fada. Kinga munyi aure ne ba tare da mun fahimci halayen junan mu ba, dama nasan dole watannin farkon auren mu a going to be rough on us, tunda a lokacin ne zamu fahimci kanmu, ina son duk abinda nayi miki, ko menene wanda kika ga ba kya so dan Allah ki fada min dan in san cewa ba kya so kinji? Ni ma kuma in kika yi min abinda bana so zan gaya miki kinji? Kamar jiya, na gaya miki bana son jin magana marar dadi akan Hussain saboda bana so din, idan kuma ban gaya miki ba ai ba zaki sani ba ko? I know I was harsh a magana ta but kiyi hakuri raina ne ya baci saboda abinda kike fada kina kara maimaita wa. Na sani Hussain dan Adam ne kamar mu, kowa kuma yana da bangaren sa mai kyau da marar kyau dan haka duk wasu halaye na Hussain na sani bana bukatar ki gaya min su. Kinji?" Ya saka hannu ya juyo da fuskarta da take zubar da hawaye yana kallo sannan ya girgiza mata kai yace "ya isa haka, ko nima so kike inyi kukan?" Ta turo baki "ba kai ne kace baka sona ba wai kafi son Hussain a kaina" yayi dariya "ohh kukan kishi ne ashe kike yi. To bara in gaya miki Hussain side dinsa daban a zuciya ta kema haka. Kin san wani abu? Sai da na aure ki ne fa na zama complete mutum, Hussain yana tare da ni tun a ciki amma ba zai iya completing dina ba sai ke ce kika iya. Kin gane banbancin?" Ya kamo ta yana dawo da ita cinyarsa, ya dora kansa ya wuyanta yace "ga kuma babies zaki bamu, abinda Hussain ba zai taba iyawa ba. Kuma bara kiji, kamar yadda nayi defending Hussain a gabanki haka zanyi defending dinki a gaban Hussain idan ya taba ki because you are my precious wife". Tayi kokarin tashi ya dake riketa, "Please ki ce min kin hakura komai ya wuce kinji? In ba haka ba tuwon nan ba zai iya wucewa cikina ba"

Ta bata rai tana kara kwanciya a jikinsa tace "tuwon ma babu dadi ai" ya jawo plate din yace "me ya same shi?" Tace "har na shiga kitchen din zan fara girkin kuma amai ya hanani, bana son mixed kamshin abubuwan girki, shine na barwa yaran nan suyi kuma gashi bai yi dadi ba" ya ture plate din yana cewa "it is okay, bara in samo mana wani abun ko a gurin aunty ne" tace "aunty kuma? Kar ka takura mata mana" ya mikar da ita tsaye shima yana mikewa yace "no, babu wani takura ai tasan baki da lafiya, daga nan ma sai ce ta samo mana cook mai tsafta sosai tunda dai babies sun hana maman su girki" ya karasa yana tsokanar ta sannan ya fita, ta zauna tana jin kalmar maman babies tana bata mata rai, sai kace ita ce Inna Ade da ake cewa uwar biyu.

Sumayya bayan ta shiga gida su Inna suka yi ta mamakin ganin ta haka da sassafe, sai tace musu kawai tayi kewar gida ne shi yasa ta dawo, amma Inna Ade ta lura da damuwa a fuskarta. Sai data bari ta shiga daki tana gyara kayanta sannan ta bita ta zauna tace "ya kika baro su Ruqayyah? Jiya da dare da muka ganta naga tayi girma sosai, kamar hankalin ta a kwance yake ko? Bata da damuwa ko?" Sumayya ta ajiye kayan hannunta ta dawo kusa da Inna Ade ta zauna tace "bana jin Ruqayyah tana da damuwa Inna, ki kwantar da hankalin ki, mijinta da surukan ta suna da kirki sosai kuma suna son ta sosai" sai kuma ta dan yi shiru idanunta a kasa, Inna Ade tace "sai dai kuma me? Akwai magana a bakin ki ki gaya min mana wani abun ya faru ne?" Sumayya tace "kawai dai ina tsoro ne Inna, kin san halin Ruqayyah tun tana gidan nan, yanzu kuma tayi aure ga kuma irin gidan da tayi auren a ciki, cikin yan kwanakin nan da auren nata har idanunta sun kara budewa sosai, ta kara chanjawa sosai, ina tsoron nan gaba kar ta kauce hanyar da kika dora mu akai Inna, so nake kiyi tayi mata addu'a Inna" Inna Ade tayi ajjiyar zuciya tace "ko sau daya ban taba cire wannan tunanin daga zuciyata ba Sumayya, kullum ina yi muku addu'a gabaki dayan ku kullum dare sai na tashi nayi muku addu'a neman tsari daga shaidan, mutum da kuma aljan. Kuma na tabbatar ubangiji ba zai jiyar da addu'a ta ab saboda yayi alƙawarin amsar addu'ar uwa akan ƴaƴanta. In sha Allah yar uwarki ba zata tabe ba. Xan kara wata addu'ar akan wacce already nake yi kullum.

Sumayya taji dadi kuma taji hankalin ta ya dan kwanta, tasan babu abinda addu'a ta bari dan karfin addu'a yakan iya chanza kaddarar mutum gabaki daya.

Cikin kwana biyu Ruqayyah ta kuma dawo da mijinta gare ta, ta kuma fara shiga cikin yan uwansa kamar yadda Minal ta bata shawara. Idan ya fita itama sai ta shirya ta tafi part din aunty tayi zamanta acan, ba zata dawo ba sai yayi mata waya yace gashi nan zuwa sannan zata debar musu abinci ta tafi can ta kuma shirya tayi masa kwalliya kafin ya dawo. Wannan yasa shima ya wanke zuciyarsa gaba ki daya akan waccan maganar yake enjoying matarsa.

Motocin su da Hussain ya siya musu ita da Fatima sun iso kuma Ruqayyah tayi murna sosai dan bata dauka haka motar ta hadu ba sai da tagan ta kiri kiri sannan ta kuma fahimtarta. Hassan ne yayi suggesting ya kamata ta shirya taje gida ta nuna musu motar dan tun da suka dawo bata je gidan ba. Dan haka ta dauki kayan tsarabarsu sannan shima kuma ya dauki kudi masu kauri ya bata yace ta kai musu, sai ya hada ta da driver yace ya kaita tunda bata fara koyon motar ba tukuna. Dan haka hankalin ta kwance ta tafi a zuciyarta tana plan din daga can zata biya ta gidan su Minal suje gurin malamin nan mai addu'a.

Tana shiga soron gidan taga Adam yana fitowa daga dakin su Sulaiman. Yana shafa kai yace "welcome Madam" ta watsa masa harara tare da jan dogon tsaki ta wuce cikin gidan sai yayi murmushi kawai ya fita. Tana shiga Zunnur yana ta murnar ganinta amma ita da fada tafara "me wancan kedarin yake yi a gidan nan? Duk ya cika masa gida da warin karti" Sumayya da take daki suna waya da Adam yana gaya mata ya gama zai tafi ta fito tana kashe wayar ta nuna ta "kar ki kuma, wallahi Ruqayyah ki fita daga idona na gaya miki" Ruqayyah tace "in na kuma nace sai me? Me zakiyi min? Wallahi sai ya daina zuwa gidan nan ai badan irin su Hassan ya sai gidan ba" Sumayya tace "to maza, yi mana gorin cewa mijinki ne ya siya mana gida, dan ma dai ba rokar sa mukayi ba kuma daya siya din ba ke ya siya wa ba Baba ya siya wa dan haka baki da iko da gidan" Ruqayyah tace "amma dai saboda wa ya siya? Saboda ni ya siya baby girl amma ina da say akan waye zai ke shiga gidan nan yana fita kuma wancan katon kedarin baya daga cikin su"

Inna data rike baki tana kallon su tace "to kuyi dammara ku daku a gaban kannen ku kunji. Akan saurayi zaki yi fada da yar uwarki Sumayya? Ke kuma akan wata akida taki ta daban zaki yiwa yar uwarki damu iyayenki gori cews mijin ki ya siya mana gida? Ruqayyah? Har kin kai haka? Har kin yi girman da zaki yi mana gorin gida Ruqayyah?" Ruqayyah ta zauna taa magana kasa kasa "ni ba gori nake muku ba inna, ni kawai mutumin nan ne bana son yake zuwa gidan nan wallahi. Na tsane shi bana son ganin sa" Sumayya ta bude baki zata yi magana sai kuma ta kalli Inna ta juya ta koma daki tana rufo kofa. Tana ragawa Ruqayyah akan komai amma ta rasa me yasa bata iya raga mata akan Adam. Ko da wasa bata son Adam yaji irin maganganun da Ruqayyah take fada akan sa, babwai dan tana son sa a matsayin saurayi ba sai don tana sonsa a matsayin sa na wanda yayi loosing everything for islam.

Inna ta jima tana yiwa Ruqayyah fadan abinda tayi sannan kuma ta koma yi mata nasiha, daga nan kuma sai suka shiga hira. Su Sulaiman da suka tafi dauko kaya daga mota suka suka dawo suna baje kayan anan tsakiyar palo kowa yana diban nasa. Ruqayyah ta dauko na Baba ta bawa Inna ta ajiye masa sannan ta bata nata itama. Ta ware na Sumayya gefe tace "ita kuma wannan inntaga dama ta fito ta dauka to in kuma tayi fushi in kinyi bakuwa inna ki bayar" Sulaiman yayi dariya yace "babu wanda zai shiga tsakanin ku dan duk wanda ya shiga to kuwa zai ji kunya" duk suka yi dariya amma ita Ruqayyah bata ga abin dariya a cikin fadan su da Sumayya ba, ita bata san me yasa suke daukan lamarin Adam for granted ba. This is very serious issue amma su suna dariya akai.

Sai daga baya Inna da kanta ta aika aka kirawo mata Sumayya ta fito suka cigaba da hirar si tare, Ruqayyah tana ta nuna musu hotunan guraren da suka je da kuma abubuwan da suka yi, sannan tace "ohh ni na manta ma, ga mota can Hussain ya bani kyauta. Tana waje" sai murna da ihu. Suka fita waje gabaki daya har da Inna, suna ta gani suna saka albarka, Ruqayyah ta saka drivern ya dauke su ya dan zaga dasu unguwa sannan ya dawo dasu.

Anan Ruqayyah ta kusan yini har laasar, sai da Baba ya dawo ta gaishe shi sannan ta fara shirin tafiya. Inna tace "da wuri haka zaki tafi?" Tace "yace kar in kai dare ne, yace in koma gida kafin ya dawo kuma karfe biyar yake dawowa" Inna Ade ta gyada kai tana jin dadin yadda Ruqayyah take wa mijinta biyayya. Ta dauko kudin da Hassan ya bayar ta ajiye musu sannan tayi musu sallama suka raka ta har bakin mota, Baba yana sakawa motar albarka.

Suna fita daga layin ta saka driver ya dauke kan motar zuwa gidan su Minal, ta dauko waya ta kira ta ta gaya mata gasu nan zuwa dan haka suna zuwa ta fito ta shiga motar suka tafi. Basuyi wata tafiya mai nisa ba suka zo gidan malamin, sai Ruqayyah tayi mamakin ganin hadadden gida ba irin gidan malam Shehu ba dan tasa ran ganin dan karamin gida mai dakin almajirai a soro da kuma malami a zaune akan buzu a kofar gidan amma sai taga an bude musu gate sun shiga hadadden gida drive in, suka fito daga motar kamar zasu shiga cikin gidan sai Minal ta kira wani a gurin tace a gaya wa Malam sunzo.

Sannan ta juya gurin Ruqayyah tace "dama tun ranar da muka yi magana dake na gaya masa ta WhatsApp cewa zamu zo" Ruqayyah tayi dariya "wai kina nufin malamin ne yace WhatsApp?" Minal tace "to me za'a fasa, na gaya miki fa ba irin wadanda kike jin labarin su bane ba. Mu shiga ciki zaki kara tabbatar da abinda na gaya miki" suka shiga cikin wani palo suka zauna, Ruqayyah tana ta mamaki "yanzu dama ana samun irin wannan kudin a harkar malinta shine malam Shehu yake zaune a gidan kasa? Duk ilimin sa?" Minal tace "shi ya zaba. Kinga shi fa wannan yan siyasa suna zuwa gurinsa yayi musu addu'ar nasarar zabe, a haka ya gina wannan gidan ya kuma sayi motoci har biyu, ko da yake dayar ance min kyautar ta aka bashi"

Suna nan zaune malamin ya fito, middle age mutum ne mai kamala da komai, ya saka manyan kayan sa da babbar riga hannunsa rike da charbi yana ja ya zauna suka gaishe shi yace "Ruqayyah ko? Amina ta gaya min zaki zo. To madallah Allah yayi albarka. Yanzu mu fara yiwa Annabi salati kafa goma tukunna" suka yi salatin nabiy a tare kafa goma sannan yace su karanto sunayen Allah 99 a tare, suka karanta sai ya jefar da charbin sa a gaban Ruqayyah yace ta miko masa, ta dauko ta miko masa sai ya rike gefe da gefen inda ta taba ya kirga adadin beats din da suke gurin sannan ya kalle ta yayi murmushi yace

"Amina ta gaya min bukatar ki, dukiya ce ta kanin mijinki ke kuma a ranki kina so ta zama ta mijin ki. Shine kike so ayi miki addu'a Allah yayi miki jagora akan wannan kudiri naki" Ruqayyah ta gyada kai tace "haka ne"

Yace "to ai malama Ruqayyah ni dai abinda na gani a tattare dake shine arziki, naga dukiya fiye da wadda kike saka ran samu, na ga budi, indai kudi ne wadanda ake kira da kudi na gansu. Amma kuma naga kadaici. Zabi ya rage naki Ruqayyah, nan gaba kadan wata damazata same ki wadda zata barki da zabi guda biyu, ke da kanki zaki zabi rayuwa cikin dauka marar iyaka ko kuma rayuwa a karkashin masu daula marar iyaka. Zabi ya rage naki. Idan kin je gurin zaki fahimci abinda na gaya miki kuma sai a lokacin zaki biya ni kudin aikina da kanki ba tare da wani ya tuna miki ba" Ruqayyah ta mike da sauri tana jin uneasiness, wannan ai duba yake yi, malamin duba ne Minal ta kawo ta gurinsa. Ba tare da tace komai ba ta yi hanyar waje, tana zuwa bakin kofa yace "Allah ya sauke ki lafiya Ruqayyah. Ki gaishe min da Hassan da Hussainin da zaki haifa".

Babu shiri ta karasa fita tana hada hanya, tana shiga mota bata jira Minal ba tace da drivern su tafi, gabanta yana ta faduwa amma maganganun malamin suna ranta kamar yayi zane akan dutse.


*The Twins*

Sai da ta kusan zuwa gida sannan kiran Minal ya shigo mata, tana dagawa ta fara yi mata bala'i "shine dan kuturun wulakanci zaki tafi ki barni ko? Wato ke ga mai mota ko? Laifi nane ni da na dauko ki na kawo ki inda za'a taimaka miki. Kuma kinyi da yar halak in dai ni Amina kika yiwa haka wallahi zaki gane kim wulakanta ni a gaban mutane" Ruqayyah tayi ajjiyar zuciya tace "kiyi hakuri Minal, wallahi ba zan iya bane ba tsoro nake ji, kema ki daina zuwa gurin sa duba yake yi. Ko waye ya gaya mishi ina da ciki har zai gaya min abinda zan haifa? Ki bashi hakuri kawai ki ce ba zan iya ba" ga mamakin ta sai taji Minal tayi dariya tace "bai ji haushi ba ai. Yace in gaya miki kiyi kokari ki aiko masa da date of birth na Hassan da Hussain da kuma na Fatima, rana da wata da shekara, da su za'a yi amfani gurin yi miki adduar" Ruqayyah ta girgiza kai tace "ni fa babu abinda zan bashi, ban sani ba kuma ko na sani ba zan gaya masa ba. Ke da jin wannan kinsan malamin tsibbu ne irin su kuma sunfi boka hadari" Minal tace "if you say so bazan yi miki musu ba, ni dai nasan bai bani komai na binne ba kuma bai bani komai na barbada ba. Dan


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login