Showing 39001 words to 42000 words out of 294767 words

Chapter 14 - Gudun Kaddara Book 2 Hausa Novel Complete

taimakon Allah washegari taji qwarin jikinta sukayo gida.

Sai yamma sannan suka zauna cin abinci. Cakula abincin kawai takeyi,hankalin ama duka yana kanta. Ta yaya wannan dan tayin dake manne da ita zai zama yadda akeso?,bayan kwata kwata bata wani iya cin abinci?,duk irin lokacin da ama ke kashewa tayi mata nau'ikan abinci kala kala. Bata taba damuwa da bata lokacin da takeyi ba,duk da aba kadai take kashewa lokacinta a kitchen,aah.....damuwarta na rashin cin abincin sultana dinne.

Afakaice bayan rashin cin abincin ta karanci kamar akwai damuwa boye qarqashin zuciyarta,don haka ta kirayi sunanta a hankali. Kai ta daga tana kallon ama da zugaggun idanunta da a yanzun kullum a kode suke tasss kamar danyen nama

"Banason ganin wannan damuwar sultana,zan cika miki alqawarinki......zan maidaki wajen bibinki,zan kuma karbi ko meye kika haifa,idan kinso kice ma ba kece mamarsa ba dukka na yarda......amma muddin kina son hakan ta kasance sultana sai kina sakin jiki kina cin abinci" wasu hawaye ne masu sanyi suka gangaro daga idanunta

"Basa ciyuwa abincin ama.......sai naji ko kallonsa bana sonyi,bazan iya ci ba amma yadda kikeso" sake sassauta murya ama tayi

"Shikenan,calme-toi(kwantar da hankalinki),ba lallai bane sai kinci duk abinda aka dafa din ba.....duk sanda kikaji akwai abinda kike sha'awar kici to komai rana kome dare ki gayamin ko ki gayawa tanja,zamu tabbatar an dafashi kinji?" Kai ta gyada mata a sanyaye

"Yauwa,madalla......yanzu wacce qasa kikeso mu wuce?,don banaso mukai sati uku a nan,inason na kaiki inda za'a kula dake,ba zaki sha wahala ba" har qasan ranta taji danji sanyi ya saukar mata,abinda zata iya cewa ta jima rabon da ta jishi. Ta dan lumshe idanunta tana jin yadda zuciyarta ta gamsu da tayi nesa da NIJER qwarai da gaske,tayi nesa da qawayenta dama idanun da suka santa,tayi nesa da dukkan cakwakiya,a yanzu idan ka debe bibi da aba bata qaunar ganin duk mutumin da ta sanshi a baya,tanaso ta nesanta kanta da kowa,da da halima zataso ta rayu ita kadai

"Wacce qasa kikeso?" Ama ta datsi tunaninta tana sake tambayarta. Abaya dukkan burinta shine aba ya kaita France,kullum zancanta kenan,har yana tsokanarta

"Tunda kikaje makka kikaje madeena aikin gama yawo sultanan bibi.....amma itama France din zan kaiki,amma fa sai ranar da kika gama école secondaire(secondary school),naga kuma résultat(sakamako)nki yayi kyau,zan hadaki da ama idan an dace zata shiga ta can ku tafi tare har sai kin gaji sannan ki dawo".

A wannan karon sai taji kamar an zare qasar fit daga zuciyarta,maimakon ta cewa ama itace zabinta sai ta buda baki a hankali tace

"Austria"

"Austria?" Ama ta sake tambaya,don itama France ta tsammaci zata ce. Kai ta gyadawa ama din tana me tabbatar mata,sai ama din ta sauke ajiyar zuciya tana cewa

"Très bien(ba laifi)" sai ta jawo wayarta ta kunna data ta soma danne danne.



*********Sati biyun da sukayi cikin garin kano sunyi shine cikin gida ba tare da zuwa ko ina ba,idan ka gansu sun fita din to tabbas zasu miqa sultana ne asibiti. Sultanan da ko yaushe jikinta ke qara zafi da rikicewa.

Wani irin bahagon laulayi takeyi mai bala'in zafi da wahala. Duk yadda ama tayi shekaru a duniya,taga kuma masu ciki kala kala,itama kuma tayi kalar nata cikin har sau uku ta jima bataga masifaffen laulayi irin na sultana ba. Sosai take a galabaice,bata iya komai sai kwanciya,sai kuma kuka daya zame mata tamkar sallolin farilla guda biyar.

Kullum gari ya waye rana ta fito bawa kanta mutuwa takeyi,azabar da takeji a kowacce gaba ta jikinta tana jin ba irin nau'in azabar da zakaji ka rayu bane. Ta sake zama 'yar firit da ita,sai wani mahaukacin haske da tayi,idanunta suka sake fitowa tare da yin wani irin haske me sheqi. Saidai kuma duk yawan gashin nan nata da sumar nan babu su,yanzun haka qaramin ribbon ya isa ya riqe 'yar sumar dake kanta. Bata um bata um um,kuka a yanzun ya fiye mata komai cikin rayuwarta.

Yanayin sultana din ya sake cirewa ama nutsuwa,tausayinta takeji kamar kamar me,inda tana da iko da kuma me yiwuwa ne da tuni ta fidda cikin daga jikinta ta dawo dashi nata jikin ko zata samu hutu koda na kwana daya ne tak.


*_AUSTRIA_*
*VIENNA*

*_VIENNA INTERNATIONAL AIRPORT_* _(flughafen whien_schwechat VIE)_


A nutse suke saukowa daga jirgin Ethiopian airlines wanda yayi jigilarsu daga kano ta dabo suka yada zango a Addis ababa,daga addis ababa din suka sauka London,daga london kai tsaye zuwa Austria babban birnin Austria din wato Vienna.

Hannun sultanan wadda tayi wani dan qaramin kyau cikin wasu skirt and blouse da suka dace da jiki da kalar fatarta,sai headscarf data nannade kanta dashi,wanda hakan ya bayyana fuskarta data bayyanar da rama quru quru.

Backpack bag ne a kafadarta guda daya, sauran duka luggage dinsu yana hannun tanja. Shima ita ta dage kan zata iya amma aman hanata tayi.

Hannunta cikin na aman,wadda ke saye da wata doguwar riga me rubi biyu beig color saqar qasan oman,sai rufaffen takalmi data saye qafarta dashi. Qwayar idanunta lullube da wani sun glasses baqi da ya qara mata kwarjini ainun. Kana kallonta kaga classy maama,muddin baka santa ba ba zaka taba tsammanin ita ta haifi saurayi haka kaman aliyyu ba, zakayi tunanin almu shine yaronta na fari. Tana da kyan jiki,tana da son ado,idan akace ado ado me aji wanda bai fiya daga hankali ba,irin adon da duk wanda ya kalla zao burgeshi ya kuma ga cewan ya dace da age dinta.

Duk da ba kasafai ta fiya zuwa Austria ba,to amma abune na aiki da ilimi,don haka tun kafin su tsoma qafarsu cikin qasar hatta da inda zasu zauna tsahon wadannan watannin ta gama dashi,don haka suna sauka taxi suka dauka kai tsaye suka wuce masaukinsu.



*_SECOND DISTRICT Leopoldsdadt_*

Unguwace dake da wani irin tsari me kyau tare da saukar da nutsuwa, nutsuwar da tunda suka shigo unguwar har qasan rai da zuciyar sultana taji yanayin unguwar yayi mata. Suna da wasu irin jerarru kuma tsararrun Street da aka cikasu da bishiyu dake bada wadatacciyar iska da inuwa me kwantar da hankali.

A nutse suka isa second floor,inda anan apartment nasu yake. Babban falo ne yalwatacce dake dauke da dining area,budadden kitchen,balcony daga gaban gininsu da zai baka daman samun iska me kyau da ganin yanayin ginin unguwar,sai dakunan bacci guda uku madaidaita dake manne da toilet kowannensu. Yanayin ginin gini ne me matuqar tsari wanda ama tayi amanna zai dace da tsarinsu,komai an zuba,hatta da kayan abinci basu da abinda zasu buqata.

Tun daga daren har zuwa wayewar gari ama bata zauna ba. Kwanaki biyu tayi a tsaye,sai data tabbatar duk wani da zai zamewa rayuwarsu tilas na su nemeshi ta gama da matsalarsa a tsahon shekara guda da take sanya rai zasu kwashe a qasar. Tun daga booking na asibitin da sultana zata dinga zuwa anti natal,tayi mata register da wani center na bawa mata masu juna biyu kulawa da kuma shawarwari,ta sake mata register da cikakken likitan dake lura da matsaloli da qwaqwalwa kamansu depression anxiety da sauransu. Center ce me kyau data jima tana bin qwaqwafi da bincike a kanta,tanason duk wani damuwa ya gushe daga zuciyar sultana din,tana sha'awar taga sultana ta fuskanci rayuwa da kyau,tanaso ta haihu successful ba wani matsala da zata shafeta ko ta shafi abinda ke cikinta. Ta canza layukan wayarta,ta kuma canza dukka accounts nata da take amfani dasu,kama daga Facebook page dinta,instagram dinta da watsapp dinta,daga ita har sultana suna buqatar nutsuwa,suna da buqatar su manta da kowa da komai na wani dan lokaci.*_GUDUN ƘADDARA_*

*H U G U M A*

BOOK 02 PAGE 21

Hutun sati guda kacal sukayi duk wani abu data biyawa sultana din tayi qoqari taga ta fara zuwa. Duk da zuwan nata sai ya zamana asha ruwan tsuntsaye saboda yanayin jikinta na yau lafiya gobe babu.

Cikin nasara da taimakon Allah sannu sannu tana zuwa ganin likitanta sai aka fara samun sassauci,don an samu ci gaba tayi katari da irin abincin da takeso a wata fita da ama tayi dasu cikin unguwarsu. Street food ne da sukeyi a wani kebantaccen waje,ama din bata taba tsammanin sultana zata iya cin abincin ba,don har ta kira waitress tace a maida,sai ta buda baki da muryar nan tata data zama sasaanya tace

"Ama ni zanci" a mamakance take kallonta,cikin harshen German tace su ajjiye. Kaman wasa ta koma da baya ta zubawa sultanan idanu,sannu sannu sai gashi ta tashi dashi. Abun ya yiwa ama dadi,sai suka maida wajen gurin zuwansu duk dare,don acan ne kadai sultanan ke iya ci ta qoshi,koda zataci tayi amai,amma tanaso,hakanan ana samun wani yana zama a cikinta.

Kaman yadda taci burin sadaukar da komai nata ta sadaukar din,don lokutta da yawa tanja na girmama girman qaunar data karanci ama na yiwa cikin dake manne jikin sultana,ko kadan batajin kudin dake fita a jikinta,duk da cewa ita din ahalin abunne,ta tara da yawa an kuma tara mata,amma saidai daga qasar har zuwa unguwar da suke zaune din tana cikin nau'in gurare masu tsadar rayuwa a duniya,amma tanja bataga alamun hakan sam sam yana damun ama ba.

Sannu sannu suka kwashe watanni uku a Austria......daidai watannin cikin sultana shida cif,ba labarin gida a kunnuwansu kamar yadda gida basusan wacce duniya AMA TANJA DA SULTANA suke ba.....bare maina da tun daga wancan ranar ko me kama dashi basu sake gani ba,basu sake jin komai da yayi kamanceceniya dashi ba..... tun uncle abdulhakeem suna cigiya har gwiwoyinsu ya sare.......tun suna cigiyar maina kadai har suka koma hadawa da cigiyar ama......tun hankalin aba bai tashi da yawa ba,yana ganin kamar adadin Tex naban haqurin da yake tura mata yana riskarta......girman soyayyar dake tsakaninsu zata hanata yin nisan zango.......zata kuma waiwayeshi.....har ya sare ya fara tunanin ta ina zai nemo hamdiyya?,ta yaya zai maidowa da bibi farincikinta?. Duk wani kuzari da walwala na family din MAYAK'I yayi nasa guri sai abinda ba'a rasa ba. BA MAINA BA AMA BA SULTANA wadannan abubuwa dasu suke kwana kuma dasu suke tashi cikin zuciyar duk wani ahalin mayak'i.

********K'arfe takwas na dare agogon qasar Austria,daidai lokacin da ama ke tsaye gaban cupboard din sultana tana zaqulo mata kaya.

A qalla kayan dake zube saman madaidaicin gadon sultana din sun kusa kala ashirin,saidai kowanne a ciki sultanan ta gaya mata baya shigarta.

Daga qarshe hannunta ya damqo wata free size gown,golden brown ce da ratsin baqi,ama ta dagata tana kallonta hadi da sauke ajiyar zuciya.

K'ofar toilet din dakince ta bude,sultana ke takowa a hankali daure da babban towel.

Idan a watanni biyun baya kaga sultana a yanzun zaka iya rantsewa ba ita bace,ko kuma kace
"Wanne irin ci takewa abinci haka?" Zaka kuma iya qaryata duk mutumin da yace maka baqar wahala takesha,bata iya bacci da dare sosai,bayan dukka 'yan kwanaki sai ta ziyarci likita ya qarawa jijiyoyinta ruwa.

Kamanninta tun daga jikinta zuwa fuskarta sun dauki hanyar bacewa. Tana takowa gaban ama ama din na kallon idanunta

"Kuka kikayi cikin bandaki sultana?" Ta jefa mata tambayar data sanya sultana ala dole kauda kanta. Kukan tayi,kukan data kwan biyu batayi irinsa ba saboda rashin qwarin jikinta. Fuskarta ta kalla taga yadda ta koma,gaba daya kaman ba sultanan bibi ba?,me yasa ama ta tilastata akan tabar cikinnan?,me yasa bata yarda da shawarar bibi ba?,kullum rana ji takeyi kamar ruhinta zai fita daga gangar jikinta,wani lokaci ma sai taji numfashi kamar na mata wahalar shaqa,wani abu ya yiwa cikinta qabe qabe,yayita mata motsi kuma yana dukan bangon cikinta,wani lokaci ta tashi ta zauna a firgice cikin dare,wani lokaci ta dafe gurin ta saki kuka me tsuma zuciya.

Tunda uwarta ta haifeta bata taba jin ana motsi cikin mutum ba,a ranar data fara ji din kusan haukacewa ama tayi da kuka da firgici. Ita sa tanja sai da suka kusa kwashe awa guda suna mata bayani suka kuma kwatanta mata kafin su samu ta sassauta,saidai har yau idan cikin zai motsa to yana motsawa ne da wani irin miki a zuciyarta.

Ganin tayi namijin shanye damuwarta sai ama din bata kuma tuhumarta ba,ta zauna tana miqa mata kaya tana shiryawa. Gaba daya girman cikin ba zakace na haihuwar fari bane,bayan haihuwar fari ma ace cikin yarinya kaman sultana?. Duk da a yanzun wani girman dole yazo mata,ta cika ta zama mace,amma idan ka qare mata kallo tsaf idan kana da nazari zakazan yarinya ce danya shataf.

Ko a jiya sai da sukayi zancan girman cikin da tanja

"Next month zamu koma ganin likita,zan masa complain naji me zaice" ama ta cewa da tanja

"Amma hajiya anya baki tunanin tagwaye ne a cikin nan na sultana?" Sai da gaban ama ya fadi

"Tagwaye a cikin sultana kuma?,ina zata kaisu?" Ta tambaya da fargaba,sai kawai tanja tayi murmushi

"Shikenan,Allah dai ya raba lafiya kawai zamuce cikin amincinsa"

"Allahumma ameen" ama ta amsawa tanja,saidai cikin ranta tana nazarin maganganun tanja din

A nutse ta gama shirinta tsaf sannan ama ta sanyata a gaba suka fito. Yau din tanja tace zata zauna cikin gida,ita ta soma gajiya da kallon masu jajayen fatar nan. Sosai maganar ta bawa ama dariya,sultana kuwa murmusawa tayi qasan zuciyarta ba tare da fuskarta ta nuna ba.

Hakan kaman qa'ida ya zamewa ama tun sanda likitan ya basu shawarar fita strolling da sultana din saboda sake samun qarin lafiya da kuma gujewa qaruwar hauhawar jininta. Tare suka jero ta layin unguwar da yafi kama da titi sabooda shimfidaddiyar kwalta data maye gurbin qasa da mu muke fama dasu cikin layukanmu. Idan ka hangesu daga nesa zakayi tunanin yaya ce da qanwarta,idan suka kusance ka kuma sai kaga UWA da 'YA sak.

Yau din shuru ne ya soma ratsa tafiyar tasu,har sai da ama tayi gyaran murya

"Yau bakison kowanne labari ne?" Ta fadi tana dan satar kallon sultana,wadda tun sanda ta fara zuwa center din data mata register ake samun sauqin wasu abubuwan,koda ba zaka ganta tana dariya ba amma a qalla akwai raguwar dakuwa kaso sittin cikin saba'in data dawwamarwa fuskarta,to amma yau din da alama akwai wani abu da ya taba zuciyarta

"Inaso" ta fadi a taqaice,sai ama ta dage dukka kafadunta

"Shikenan,zan baki labarin qasar Germany,sanda mukaje da abbana duka duka shekaruna goma sha hudu......amma saikin gayamin meye yake damunki,karki manta......munyi alqawari dake kin daina boyemin komai" ama ta fada taba nuna fuskar sultanan da dan yatsa.

Duk yadda taso jurewa saida hawaye suka taru a idonta,tasa bayan hannunta ta matsesu sannan bakinta yana dan rawa tace

"Na gaji da cikin ama,don Allah yaushe zai baki na huta?" Tausayi da dariya dukka suka kama ama din,amma tausayin ya rinjayi dariyar. Tsabar sangarta da gata batasan ma wata nawa ne ciki yakeyi a jikin mace ba kafin ta haihu,tsabar qanqantar shekarunta ma batasan yadda zatace Mata yaushe zata haihu ba,sai ta kama hannunta suna dab da wani shop na Shan coffee da snacks don haka suka qarasa. Kujera taja mata ta kalleta,ko batayi magana ba tasan me take nufi,don haka sai tayi taku biyu,ta isa gaban kujerar ta zauna,fararen idanun nan a narke.

Murmushi ama din ta sakar mata,ta daga mata yatsanta guda sannan ta shiga shop din. Da kallo sultana ta bita harta bace cikin shop din,sai ta zuqi numfashi wanda yakai mata har tsakiyar hunhunta. Da sauri tare kuma da wani irin gaggawa ta saki numfashin hadi da fesar dashi waje tana zare idanunta.

Cikin kowacce kafa ta numfashita.....cikin kowanne sasanni na shiga da fitar numfashinta qamshin yakai. Qamshin da


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login