Showing 141001 words to 144000 words out of 294767 words
Chapter 48 - Gudun Kaddara Book 2 Hausa Novel Complete
aba ba'a huce yake ba,itama ama din haka" siririyar iska ya fidda daga bakinsa. Me yasa ake masa hakan?,kamar dai ya saci diyar mutane?,ko kuma ya dauki diyar da ba muharramarsa ba?,bai manta bafa har yanxu,ba wanda ya bari ko a sannan ya biya mishi sadaki,da kudin school dinsa ya biya sadakinta...... Me yasa suke manta wannan?. Gefe guda kuma goumar din masoyi ne,yasan yana cikin masu sonsa cikin gidan,kome zaiyi yana yine saboda kawo gyara da daidaito,don haka ya sassauta fushinsa ya amsa shi a gajarce
"Okay" kai goumar din ya jinjina
"Na gode da fahimta" sai ya sauke wayar.
Yana takawa zuwa dakin yana ji a ransa inama zasu gansun su fusata da hakan?,shi kam da yafi kowa jin dadi,yafiso su fahimta ma da kansu shikam bazai taba iya yi musu abinda sukeso ba idanma kora da hali suke masa a kanta.
Wannan karon a dakensa ya shiga dakin,ya kuma kasa ya tsare da tsukakkiyar girar nan tasa da idan baiso ba yake juyewa wata irin fuska me ban tsoro. Abincin ya jawo ya bude yace kuma ta taso taci,kaman yasan me ta qudurta yi ya dora da
"Duk musu daya da zakiyi kuma dai dai yake da kwananmu nan wajen,dama kudin kwana din na biya,choose wisely.....but zanfi so kiyi taurin kan" ya qarashe maganar yana buda dukka hannayensa ya dora saman makarin kujerar yana yakuma yi relaxing bayansa jikin makarin kujerar bayan ya miqe qafafunsa sosai.
A yadda yayin ta tabbatar ya fadi ne har cikin zuciyarsa. Dole taja abincin ta kuma juya masa baya taci spoon uku da qyar. Data maida masa sai daya mula don kansa sannan ya miqe ya tattara komai da yasan nasa ne sannan ya bude dakin ya fice ta bishi a baya tana jin kamar tayi tsuntsuwa ta ganta a gida.
Shuru ne ya ratsa motar,shi da ita din babu me cewa komai. Itakam ko qwaqwaqwaran motsi batayi,ta gama yarda maina kawai ya qaro ta'addanci ne,a yanxun idanunsa sun sake soyewa fiye da baya,ta tabbatar zai iya aikata komai,koma dai meye Allah ya kusa nesantata dashi.
A nutse kuma hankali kwance yake tuqinsa,yasan yau din ya samawa kansa memory masu dadi,duk wani motsi laushin fatarta da kuma qamshinta ne yake dawo masa sabo,zaqin da laushin labbanta sai yakejin kamar a duniya babu wani abu da yakai lips dinta sulbi.
Cikin qwarewa ya sauka daga saman titin ya gangara layin nasu dake shimfide da tsararriyar kwalta. Dai dai qofar gate din mansion house din nasu ya tsaya ya kuma danna horn daya tak saiga daya daga cikin security na gidan ya bayyana tamkar dama dawowarsa ake jira.
Tsaf ya wangale qofar,hasken fitilar gaban motar da ya sanyata a full light ya haske masa farfajiyar farko ta gidan da kuma mutanen dake tsaye a wajen. Shi da ita dukkansu zubawa wajen idanu sukayi,tata zuciyar ta tsinke ta fara luguden bugu cikin firgita,yayin da tashi zuciyar take a nutse tamkar ma baiga komai ba,ya sanya hannunsa saman steering din ya soma murzashi a nutse kuma cikin qwarewa yana sanya hancin motar cikin gidan game da rage kaifin hasken motar.
Tsananin hasken ne yana hankulansu dukka zuwa bakin qofar,ama ce tsaye sai aba da goumar kusa dashi,sai kuma oncle issoufou da alamu ke nuna yanzun nan suka suka shigo gidan shi da aba. Idanu dukka suka zuba musu,har zuwa sanda ya isa da motar parking lot na gidan,ya daidaita ya kasheta ya zare key din. Juyowar da zaiyi sai suka hada idanu da ita,hawaye ne kwance cikin idanun nata,ta kuma zuba masa ido kafin ta janye kallonta ta maida gefansu inda su ama ke tsaye,kuma dukkansu hankulansu suna kan motar kamar masu jira suga wanda zai fito daga ciki.
Ya fahimci me take nufi,wani murmushi ya taso masa daga qasan zuciyarsa,shi kam wannan incident din yake da buqata ako da yaushe,sai ya dage mata dukka girarsa biyun yana tambayarta da idanunsa
"Kaga irin abinda zaka janyomin ko?,yanzu me kakeso nace musu?,waye zaice ba nice na bika ba?,wanne irin shiga haqqine wannan?" Ta jefa masa tambayar muryarta yana rawa kukan da takeson daqilewa ya fara yin kansa da kansa.
Hannayensa dukka biyu ya daga yana kallonta da zagayayyun idanunsa daya fiddo waje
"No.....kinga kada ki sake shafamin baqin jini banda wanda na diba......idan suka qaraso yanzun kuma sukaga kina kuka,ba rape zasuce nayi miki ba tunda sunsan an riga na wuce wajen tunda ga result nan kin basu......i think wannan karon kidney dinki zakice musu naje na saida ko?" Haushi kaman ta dora hannu ta rusa ihu,amma ba zata iya hakan ba don batason asan tana ciki tare dashi,don haka idanunta sai suka zarme da jefa masa harara cikin maqurar bacin rai
"Gyara kallonki babe.....if not wallahi zakisha mamaki a gabansu...... okay har kin manta dokan dana kafa miki saboda kin dawo gaban masu sangartaki ko?" Ba shiri ta janye idanun nata saita maida bakin qofar,still suna tsaye saidai magana aba yakewa ama wanda batasan me yake ce mata ba. Kafin ta ankara ya bude murfin motar ya fita,ta zaro idanu saboda data lura da kyau handbag dinta na hannunsa,baiko waiwayo ba,hakanan kuma ko a jikinsa yake takawa yana nufarsu. Fitowar tasa taja hankulansu,shi kuma ya basar yana takowa dai dai har ya iso dab dasu.
"Ama barka da dare" ya fadi a ladabce yana rusunawa
"Yauwa" ta amsa shi a taqaice. Ya waiwaya wajen aba ya buda baki da zummar gaidashi sai yayi hanzarin juyawa yana duban almu da ya iso wajen yanzu
"Ka bude bayan motata ta fiddowa bibi cukui kakai mata"
"Attah......kaima sultana handbag dinnan nata tana fitowa yanzu" maina ya fadi da biyu cikin dan taqaicewa,don bayason aba yabar wajen baiji abinda ya fada ba.
Sarai aba din yaji abinda yace din,amma sai yaci gaba da takawa yana wucewa ciki baiko waiwayo ba. Yana miqawa atta jakar ama ta bita da idanu,sai suka hada ido dashi,nauyi yaji yadan saukar masa,ya sanya tafin hannunsa yana shafa kwantaccen sumar dake qeyarsa yana dan basarwa. Itama nata idon ta janye,daidai sanda sultana ke takowa wajen,don dole saita wucesu zata isa qofar sassan ama din ko sassan bibi.
Dukka idanunta qasa suke kalla,don batasan yadda zata iya hada idanu da ama din ba duk da tana jin idanunta a kanta,haushi takaici da baqincikin maina ya kamata,cuta yau kam ya riga ya gama da ita ya kuma cuceta,amma daga yau ai zata yiwa tufkar hanci,da wanne ido zata kalli ama?,da kuma wanne baki zata yi mata bayanin yadda suka hada tafiya da maina?.
Ta karanci fuskarta fes,don haka tun kafin takai ga isowa sai ama din ta juya abinta ta wuce ciki itama,wannan ya sauqaqa tsananin nauyi da kunyar da takeji din,kallonsa kuma sai ya koma kanta,yana kallonta tsaye kallon tsaf,yadda take takawa cike da kunya sai abun yaji ya masa,ta masifar tafiya dashi gami da burgeshi,kamar ya dauketa su kuma suci gaba da kasancewa tare kaman dazun,koda ba zata buda baki tayi masa magana ba,koda zata masa tsiwa ne,koda masifa zatayi masa
"Ki tafi a hankali mana please" ya furta a tausashe sanda take giftawa ta gabanshi. Ji tayi kaman ta sanya abu ta tureshi ya fadi,a sanda ya hada wata cakwakiya me zafi sai yasan yadda ya zame kanshi,sai yasan yadda ya maida komai ba komai ba,yasan duk yadda zai sauke laifi duk girmansa izuwa qaramin mataki.*_GUDUN ƘADDARA_*
*H U G U M A*
BOOK 02 PAGE 74
Sassanyan murmushi ya saki yana furzar da iska me sanyi daga bakinsa,ba qaramin dadi yaji ba da ganinsun da aba da ama sukayi,wani abu ya darsu a ransa sanda yake wucewa zuwa sassansa yana sake sakin qaramin murmushin,yakai hannunsa ya shafa lallausar sumarsa yana cije lips dinsa na qasa. Nishadi da farincikin da zuciyarsa ta samu wunin yau kawai ya wadatar dashi lafiyayyen bacci a daren yau me cike da kwanciyar hankali.
Kai tsaye ya fidda kayan jikinsa bayan isarsa bedroom dinsa,ya hada ruwa me zafi ya shige cikin bathtub dinsa yana rufe idanunsa,dumin ruwan yana ratsashi zuciyarsa na masa haske.
Koda ya fito a nutse ya sharce kansa ya kuma shirya cikin wata cotton doguwar riga ta maza maras nauyi saqar qasar india,kewar benazeer da batoul yakeyi sosai,yasan kuma ko su din sun nemeshi,yanzun haka yana da tabbacin sunyi barci,to amma kuma bazai iya kwanciya har zuwa safiya bai gansu ba,don haka ya zura wasu slipper nashi masu taushi off-white kalan rigar yana fita a dakin.
Daga sassan bibi har na ama suna da dakunan kwanansu a ciki da komai da komai,ko ina suna iya kwana cikin gidan,don haka ya rasa wanne sashe suke. Daga bangaren ama harna bibi din ba wanda yakeson shiga,sassan ama yana dan jin nauyin abun dazu ne, sassan bibi kuma bayason ya taras da suhail a can,ko yaya yayi misbehaving masa yasan sai bibi ta tanka,don ya fuskanci ta karbeshi hannu bibbiyu.
Kamar an jeho masa saddi,ya tako a hankali ganin yayan nasu tsaye a wajen,yadan rusuna cikin ban girma yana fadin
"Barka da dare"
"Barka saddi,BB fa?"
"Suna sassan ama" ya amsa masa yana masa nuni da sashen da yatsansa
"Yayi jeka abunka" ya furta yana nufar sashen.
Duka a rude take sanda ta wucesu,ta rasa ina zata dosa wajen ama ko bibi?. Idan ta tafi wajen bibi hakan yana nufin fa kenan ya tabbata ita din me laifi ce,amma kuma zuwanta wajen ama din kuma fa?,kunya takeji yau din matuqa, tilas ta hadiye tunda tana jinta aba me laifi ba tayi sassan ama din,ta bude dakinta ta tura ta shiga. Sai data maida qofar sannan ta fidda numfashi tana jinta safe,ta soma tariyo abinda ya faru dukka wanin yau din,sai taja dogon tsaki
"Bazan sake bashi daman da zai ganni ba bare ya rainamin hankali haka ba" ta fada tana jin zafin walagigi da ya dinga yi yau din da ita. Wanka ta shiga itama don gaba daya kayanta da jikinta taji sun fita mata a rai,don ba abinda sukeyi sai qamshin wannan mayataccen turaren nasa,tana ciresu ta jefasu a laundry basket ta fiddashi qofar dakinta,tasan me hada musu kayan wanki zuwa gobe da ssfe zata iso tayi gaba dasu zuwa laundry room dinsu.
Tsaye tayi gaban madubi,lallausan gashinta da yaji ruwa ya kwanta mata lambas a goshinta zuwa wuya,ta goge fuskarta da qaramin towel sannan ta jawo cream dinta ta fara matsa tana shafawa. Sanda tazo daidai bakinta saita tsaya tana zagaya yatsunta akai,turo lips din tayi gaba ta kuma jan qaramin tsaki tana dauke ido daga saman kyakkyawar fuskar tata. Sai yanzun takejin wai yama akayi ta tsaya yayi mata dukka irin wadannan abubuwan kaman me jin tsoronsa?,ya raina mata wayo da yawa, sa'a dai kawai tasan ya taka,amma tabbas nan gaba ko meye zaiyi mata bazai sake samun dama a kanta irin haka ba.
Wasu pink pyjamas ta zaqulo masu hade da cap ta sanya,ta taje gashinta da kyau ta nannadeshi ba tare da ta sanya band ba saboda batason abinda zai takurata idan zata kwanta,tabi dukka jikinta dukka da sassanyan body body mist me qamshin strawberry,ta zauna daga saman stool ta dauki wayarta da zummar turawa aminata da yasmine apology tex akan rashin xuwanta,sai benazeer da batoul suka fado mata a rai. Zura wayar tayi cikin dan qaramin aljihun pyjamas dinta dake maqale ta qasan rigar,kwana biyun sai takejin wani sabuwar qauna da kewar yaran,ta sanya takalmanta ta rage hasken dakinta ta fito. Ta tabbatar suna sassan,don yawanci irin wannan ranar sunfi kwana sasssn ama,don itama a sassan take kwana,ba kasafai ta fiya zuwa sassan aba ba a irin wannan ranar,su kuma sunfi son su kwana idan tana cikin sashen.
Ba kowa falon ama din har ya ratsa ya isa dakin yaran,ya murza handle din ya tura ya shiga,dim light ne duka dakin,ya gauraye da sassanyan qamshin da kusan ya kama jikinsu da ma dakin zuwa sassan ama gaba daya. Makunnin babbar fitila ya laluba ya kunna. Tarwai fuskokinsu suka fito,ruqunqume da juna cikin duvet kamar wadanda aka ce za'a rabasu. Murmushi ya subuce masa,qaunarsu da alfahari da yaran yana ratsashi,a yadda yake ganin sun damu matuqa da al'amuran juna da tsananin kama da juna da sukeyi yana kyautata zaton a mahaifa daya suka rayu.
A nutse ya qarasa ya haura saman gado,tsakiyarsu ya zauna sosai,ya miqa hannu yana shafa fuskarsu sannan ya gyarawa kowacce kwanciya,ya hada hannayensu biyu waje daya ya musu addu'o'i ya shafa musu. Hannunsa saman kan batoul,yana jin wata soyayya tana sake ratsashi. Shi kadai yasan me yaji sanda ya fahimci mamansu na dauke da cikinsu,a lokacin da bashi da iko ko daman taimaka mata da komai,a lokacin da kowa ke masa kallon ya gudu ne da gangan,a lokacin da kowa ke kallon yayi komai ne akan bada qarfi,ba wanda ya kalli K'ADDARA cikin lamarin.
Zamannan da yayi a tsakaninsu sai yaji tamkar yana hira ne a tsakanin zukata biyunsu da tashi zuciyar,tamkar yana gaya musu damuwarsa wadda kowa ya kasa fahimtar sa,kowa yaqi bashi uzuri tamkar su din suna fahimta suna kuma tayashi alhini.
Bude idanunsa yayi a hankali,cikin jikinsa yakejin kamar tana tahowa dakin saboda yadda bugun zuciyarsa ke qara yawa,sai ya miqe tsam,ya tafi bayan qofa yayi tsaiwarsa,don ya tabbatar muddin ta ganshi ba zata qaraso ba,shi kuma yana da buqatar ganinta da gaske,ganin da zai zame masa dan rakiya har zuwa gadon baccinsa.
Can qasan maqoshinta tayi sallama da siriryar muryarta duk da tana da tabbacin sunyi bacci
"Ya akayi sukabar wuta akunne kuma?" Ta fadi da tattausar muryarta tana takowa zuwa ciki. Fes yake qare mata kallo cikin pyjamas din da suka fidda shatin bra da kuma pant dinta, yalwataccen gashinta nata sheqi a hasken qwan dakin,qamshin strawberry body mist dinta ya gauraye dakin duka ya sauya masa qamshi.
Wani yaarr taji yaji tun daga yatsun qafarsa har tsakiyar kwanyarsa lokacin da take takawa a nutse tana nufar bed din yaran. Kowanne sashe na jikinta motsawa yakeyi da salon tafiyarta tamkar wadda takeyin tafiyar a qididdige ko kuma take motsa jikin nata da gayya. Baby sultanansa ta bude sosai ta zama babbar mace,irin isassun matan nan da qirar jikinsu keda wahalar samu,duk da kusan a rurrufe yake ganin komai har yanzu,amma shi din a yanzun ba yaro bane qarami,yayi yawo a duniya yaga halittan mata kala kala,uwa uba likita ne shi din dake mu'amala da kowanne irin jinsi ko yare. Wani irin kishi ya taso ya saukar masa,maza nawa ne sukaga irin haka a tattare da ita?,ko dai abinda suhail ya gani din kenan ya rude masa har haka a kanta?, tambayar data ida rikita mode dinsa gaba daya,yaji kaman zai fita hayyacinsa saboda wani irin kishi daya sauko masa,hakan ya sanyashi kulle idanunsa yana zuqar iska sosai don takai hunhunsa, rufe idanun da suka sanya har ta musu nata addu'o'in ba tare da tasan yayi musu ba ta sake rufesu ta juyo zata bar dakin bai sani ba,sai da tazo dab da qofar ya shaqi qamshinta da kyau ya miqa hannunsa a tausashe ya fusgota zuwa inda yake tsaye din.
Bata zaci haka ba kwata kwata,don haka abin ya matuqar tsoratar da ita,ta kira sunan Allah da qarfi abinda ya saukar mata da nutsuwa kenan nan da nan. A tare suka ware idanunsu akan juna,cike da zafin nama ta sanya hannu zata turasa baya,ya nuna mata namiji gaban mace yake ta hanyar kamo qugunta ya riqe sosai,ya kuma janyota jikinsa ya hade qugunsa guri guda,abinda yayi sanadiyyar daukewar numfashinta na wucin gadi saboda saqon daya aika mata a fakaice. Dukka jikinta ya soma rawa kamar wadda aka tsoma cikin ruwan qanqara,tsoratar tata sai ta sake qarawa idanunta kyau a idonsa,ya saki boyayyen murmushi don yasan saqon da yakeson ya aika din ya isa,ya gyara tsaiwarsa da kyau yana duban tsakiyar idanunta suna musayar numfashi
"Ina roqonki..... please..... please,daga yau ki dinga saka jilbab