Showing 108001 words to 111000 words out of 294767 words

Chapter 37 - Gudun Kaddara Book 2 Hausa Novel Complete

tana jin daukin ganinsa, zuciyarta na raya mata qarya batoul keyi mata. Bata iya jiran benazeer ba ta kwasa da gudu tana tattare doguwar rigarta ta nufeshi tana jin wani irin farinciki.

Da siririyar muryarta itama ta kwatsa wata irin ihu,abun tana jinsa kamar a carton da suke kalla,sannan ta diba da gudu itama tayi kansa LOKACIN tuni batoul ta dade a jikinsa,harfa fara qwallar da ita kanta batasan dalilinta ba.

Qarar batoul ita ta fara zuwa kunnenta,ta kuma ji qarar kamar daga baya wajen window din dakinta,taja qaramin tsaki,yaran sun sake da yawa,tabaransu kawai sukeyi cikin gidan,kowa soyayya qauna da kulawa yake basu,tana tsoron su sangarce da yawa da ganin yawan gatan da suke samu,saita ware dankwalinta tana daurawa da zummar idan ta fita zata kirasu taja musu kunne da kokaye kokayen banza,su nutsu cikin mutane suke. Saidai kuma bata sauke wannan tunanin ba muryar benazeer ta sake iskota. Dogon tsaki ta saki tana soke daurin dankwalin gefen kanta ta juya ta nufi window din ranta adan bace da ihun da suke sakima mutane.

Da zafin nama ta zuge labulen,saidai kuma abinda idonta ya gane matan ya kusa sanyata sulalewa a qasa. Benazeer da batoul rungume da maina,wata irin runguma dake nuna zallar shauqi da tsumammiyar qauna dake tasowa daga zukatan iyaye,ya dagasu daga jikinsa yana riqe da hannayensu,fuskarsa na fidda wani irin murmushi kaman yadda idanunsa ke jifansu da wani irin kallo na tausasawa.

Tambaya yakeson musu kamar yadda suma suka cikashi da tambayoyin,to amma sai yakejin cikin jikinsa kamar akwai wani idon dake kallonsa,tashin farko kuma idon nasa ya canki daga inda ake kallon nasa.

Sake haduwa idanunsu sukayi a karo na biyu,ko second biyu cikakke bata qara ba ta saki labulen da hanzari tana komawa da baya,zuciyarta na wani irin mahaukacin bugu kamar zata fito daga qirjinta,yayin da ranta ke mata wani suya

Meye hadinsa dasu?

Yaushe ya sansu?

Waye ya shaida masa su din yaransa ne?

Don me zai shiga rayuwarsu?

Shin ance masa suna sa buqatarsa?

Dukka tambayoyin da takewa kanta kenan a zafafe ba tare da samun wanda zai amsa mata ba.

*_muje zuwa_*

*_KWANKWASON JIMINA_*

*_TSUTSAR NAMA_*

*_AMEENATOU_*

*_GUDUN KADDARA_*

_DUKKA AYARIN LITATTAFAN KUDINSU YA KAMA KAMAR HAKA_*

LITTAFI DAYA_400
BIYU_800
UKU_900
HUDU_1200

_IDAN TA BANKI NE ZAKI SANYA KUDINKI A WANNAN ASUSUN_

6019473875
Musaa Abdullahi safiya
Keystone bank

_ANTAYA SHAIDAR BIYANKI ZUWA GA WANNAN NUMBER_

09166221261


*Masu tura katin waya ko vtu kuma kai tsaye wannan number zaku tuntuba*

09134848107

*Maqotanmu kuma al'ummar qasar nijer zaku tuntubi wannan number dinne kai tsaye don biyan naku kudin*

09033181070


*ZAFAFA FAMILY na maraba daku*🫂🫂🫂🫂🫂*_GUDUN ƘADDARA_*

*H U G U M A*

BOOK 02 PAGE 57


https://chat.whatsapp.com/IQ6XVJntkTj5FFJ66euAIR

Hey everyone.. Assalamu Alaikum. let's build our business together. join our whatsapp group, ladies only
Zamu kawo kwararru a bangaren business da zasu yi mana bayanin yadda suka samu cigaba a kasuwancin su,yaya zaka yi tallan kayan ki online ki saida online, ta ya zaki samu riba a kasuwancin ki? Yaya ake marketing da branding da sauran su.
Wanda kuma suke son fara sana'ar amma basu san taya ba, in sha Allah you will find something to start with
Lets grow together.
______________________________



Har ta zame tabar wajen bai daina kallon window din ba,shi kadai yasan me yakeji a zuciyarsa game da ita,yadda tausayinta yayi shekara da shekaru yana masa didibniya cikin zuciyarsa shi kadai yasan yadda ya luguiguta shi,ya kuma yi masa kyakkyawan kamun da zuciyarsa tayi wani mugun laushi. Takun goumar shine ya ja hankalinsa yadan dauke idanunsa daga wajen ya maida ga goumar din,suka hada idanu sai goumar din ya sakarwa maina murmushi,murmushin dake nuna tsananin farincikin dake kwance qasan zuciyarsa da dawowar dan uwansa cikin ahalinsa

"Ya maina....bansan a irin wannan lokacin ka shirya dawowa ba ai,da banyi nesa ba,da na zama mutum na farko da zan dauko ka na kawoka cikin gidan.

Harara ya jefeshi da ita da lion eyes dinnan nasa,dole goumar yadan dauke dubansa daga cikin nasa saboda yadda idanun sukayi masa kwarjini

"Kayimin dukka qoqari goumar,amma kuma daga qarshe ka yanke alaqata dakai,ka barni ni kadai ins fakan fakan.......ba uwa ba uba ba mata......ka hanani ganin fuskar yaro na fafur......ko sunansa ka hanani sani bayan ina cikin asibitin ranar da za'a fiddoshi daga ciki" idanu goumar ya dora kansu benazeer,da alama har yanzu bai samu masaniyar sune 'ya'yan nasa ba,sune wadanda cikinsu yazo cikin gagggawa zazzafan rabo wanda ko cikin tarihi ba'a fiya samun irinsa ba,yaji dadin hakan,zai kuma ci gaba da wasa ba hankalinsa har sai yaji ciwo cikinnzuciyarsa shima,yanason a ranar da zai san su benazeer yaransa ne yasan hakan yana jin ciwon shekarun da ya dauka yana mutuwar sonsu ba tare da yasan mallakinsa bane su

"Yanzun tunda ka dawo ai zaka san komai ba?"

"Ina d'ana goumar?,inason ganinsa,na tabbatar duk gidan nan babu me yimin maganarsa,kai kadaine nake da fata a kanka" tsaiwarsa goumar ya gyara yana harde hannunsa a qirjinsa

"Yaronnan baya cikin gidan nan yanzu haka, infact ma banjin yana nijer gaba daya"

"Nigeria suka kaishi?" Ya jefawa goumar tambayar cikin damuwa,har hakan ya bayyana qarara saman fuskarsa

"Ban sani ba,but amma zan tambayi ama naji" miqewa tsaye maina yayi,har yanzu suna riqe da hannun juna shi dasu benazeer

"Alright......akwai maganganu da yawa da nakeso mu tattauna,inason nasan abubuwa da yawa bayan wadanda na sani akan sultana"

"Saboda me?" Goumar ya jefa masa tambayar. Kallon da maina din ya jefa masa ya sanyashi shiga taitayinsa,ya kuma tuna cewa har yanzun fa shine din dai ALIYYU MAINA HAIDAR ba abinda ya canza daga wancan halin nasa,don haka ya gyara zancansa cikin basarwa

"Sanin komai akan sultana yana da tsada matuqa,nawa ne farashin?"

"Daga million daya har million goma kayi requesting......zaka sameta cikin account dinka" yayi maganar yana fidda wayarsa saboda shigowar kira. Goumar yana dariya shi kuma dukka hankalinsa yana kan wayar.

Yana jin nauyin yaqi daga wayarta amma kuma ya rasa me yasa ta gaza fahimtar take takensa ta yiwa kanta fassara ba tare data wahalar da kanta har haka ba?. Daddy da sardauna mutanene da bazai taba iya butulce musu ba......bazai kuma taba iya wulaqanta jininsu ba,don haka ya danne zuciyarsa da duk wani emotion nashi ya daga kiran


"Hello.......Yaa maina kana jina?" Ta furta daga can bangaren murya can qasa

"Ina jinki laila.......ya akayi?" Zamewa tayi sosai ta kwanta daga can inda take tana narkewa,iya sautin muryarsa kadai yana tafiyar da dukka damuwarta ya qara mata walwala da kuzari,yana da wani irin husky voice dake ratsa zuciya qwarai da tunani,wani lokaci recording takeyi na taqaitacciyar hirarsu tayita kunnata tana saurara duk sanda take tsananin kewarsa kaman haka. Ta fahimci yana cikin jerin sahun mazan da su baki lokacinsu abune dake musu wuya,duk da ta bayyana kanta bata tsaya boye boye ba,amma hakan bataga ya canza wata mu'amala a tsakaninsu ba,abinda har kullum yake sanyata kokwanto

"Ya akayi kuma yaa maina?,bayan ka wuce nijer ka manta dani?,last wayarmu kace zaka kirani amma shuruuu" boyayyar ajiyar zuciya ya sauke,bata qaunar saba alqawari ko kadan,amma shi sam ya manta ma sunyi zaiyi kiran nata. Yanayin da yake ciki yanzu yana buqatar lokaci da kuma nutsuwa,don haka ya gyara tsaiwarsa

"Afwan na saba alqawari,amma ina cikin wani muhimmin aiki dana tabbata sardauna zai iya dan gaya miki muhimmancinsa a taqaice,ina tare da family na muna kashe wani issue......amma in sha Allah idan na zama normal zamuyi waya" sosai maganar tasa tayi mata wani iri,amma da yake ita din me yawan bada uzuri ce sai ta gyada kai

"Tou yayi...... Allah ya taimaka,i missed you"

"Thanks,but......kina iya kira duk sanda kk buqatar hakan" ya fadi don ya sassauta mata abinda ke yawo a zuciyarta,don ya fahimci kaman maganar batayi mata dadi ba

"Na gode da wannan karramawar"

"U r welcome" ya sake fada yana katse wayar ya jefata a aljihu.

Idanu suka hada da goumar,sai yadan dauke kai kaman baiji wayarsa ba

"Yaran waye a family dinnan?" Ya jefawa goumar tambayar da baiyi zato ba. Idanu kadan ya zuba masa yana tunanin amsar da zai bashi,sai kuma ya janye yana cewa

"Ba zakasan waye mama da babansu ba saina zauna na maka bayani,kuma qilan ka manta fuskarsu ma yanzun.......zan wuce dasu na maidasu kada ayita nemansu ansan tare muka fito" ya fada yana riqe hannun batoul da tafi kusa dashi. Idanu ya sakawa goumar din yana jin kamar maganar tasa bata hau ma'auni ba,tunani ne iri iri cikin kansa,don haka ya ture wannan,ya durqusa a tausashe yayi kissing goshinsu daya da daya sannan ya dubesu yana murmushi

"Zan shirya zan fito..... anjima akwai shan ice cream?" Ya tambaya yana kallon fuskar benazeer. Qaramin ihun murna ta saki tana tsalle,sai batoul itama tabi sahu,don itama wannan karon sosai takejin dadin ganin uncle haidar din,har bataso yabar inda suke. Tare suka wuce da goumar sunata bashi labarin haduwarsu a makka,tausayinsu su dukka ya dinga ratsashi,ya dinga jin kamar ya koma ya bayyana musu gaskiyar su din waye wa junansu?,amma kuma sai yaji bai kamata yasan yaran su waye a wajensa ta cikin sauqi ba.

Ya samu kira daga wajen najjashi mutumin da sardauna ya hadashi dashi don ya masa hidima yana tambayarsa ko yana buqatar breakfast ko wani abu me kama da haka?,yace masa a'ah,don ya samu almu ya shirya masa breakfast din,komai da komai,yayi tsaye yana mamakin yadda almu zai iya shirya abinci sosai kaman haka,amma kuma daya dinga qarewa salon jera kwanukan kallo da kuma yadda aka shirya abincin sai yaji jikinsa yana bashi tabbas daga hannun ama aka aiko dasu.

Ya debi abincin yaci sama sama don bai fiya cin abu me nauyi da safe da kuma dare ba,ya wuce bandaki yayi wankansa na kusan minti talatin yadda ya saba,sannan ya fito ya shirya.

Cikin wata shegiyan danyar gezna off-white ya shirya kansa,sai maiqo take da daukan idanu,dinkin babbar riga wanda da 'yar ciki,hular daya sanya a kansa baqa ce wadda ta dace da rufaffen baqin takalmin qafarsa me matuqar kyau da jan hankali qirar kamfanin WEITZMAN,fatarsa kawai idan ka kalla zakasan ba qananun kudi ne suka mallaka masa shi ba. Sassanyan turarensan nan daya kasa rabuwa dashi tsahon shekaru......sai kamfani kawai daya sauya amma da dsame qamshin shi ya fesa,yana fesawar yana kallon fuskarsa cikin mudubi. Tabbas shekaru ba qarya bane,a yanzun fuskarsa kadai ta zama cikakkiya wadda ke bayyana zuwan gejin girma da hankali a tare dashi,ya ajjiye turaren yana qoqarin daura agogon fatar kamfanin blancpain sai yaji muryoyi a falonsa. Ko bai fita ba yasan cousins nasa ne,daga bangaren aba da ama gaba daya. Baima gama tunanin ba yaji ana knocking qofan bedroom din. Muryar attahir ne,ya lumshe ido yana murmushi kana ya budesu saman madubi,attahir sunsan juna kaman yadda sukasan yunwar cikinsu,abokin fadanshi abokin adawarsa,shi fushi da zuciya attahir kuma tsokana,haka zasuyita bugata saidai idan baije nigeria ba,d'a ne ga uncle abdulhakeem babban d'ansa ATTAHIR ABDULHAKEEM ME KANO.

"Malam kada ka balla min qofa fa?" Ya fada yana gyara zaman agogon a hannunsa

"Idan kaqi fitowa tsaf zamu balla qofar......." Muryar bilal ya ratsa ta attahir. Dole murmushi ya subuce masa,ya zari handkerchief ya fito.

Dukkansu cousin nasa ne kaman yadda yayi zato daga bangaren aba din da ama,kuma dukkansu sa'anin haihuwarsa ne da kusan tare aka taso. Dukkansu kaman dai shi,sun zama cikakkun samari,wasu a cikinsu ma basu jima da angwancewa ba. Rudu iya rudu suka hada a falon nasa,don ma dai shi din ba gwanin magana bane amma duk da haka sai da sukayi yadda suka saba,sannan daga qarshe suka fice can masallaci suna takawa da qafafunsu domin shaida daurin auren. Kafin sukai ga fita din haka ya dinga bi yana gaida kowa,kowa kuma barka da dawowa yake masa,a haka suka isa masallacin suka kuma hade da tawagar angwaye suka tsaya karbar daurin auren.


*_KWANKWASON JIMINA_*

*_TSUTSAR NAMA_*

*_AMEENATOU_*

*_GUDUN KADDARA_*

_DUKKA AYARIN LITATTAFAN KUDINSU YA KAMA KAMAR HAKA_*

LITTAFI DAYA_400
BIYU_800
UKU_900
HUDU_1200

_IDAN TA BANKI NE ZAKI SANYA KUDINKI A WANNAN ASUSUN_

6019473875
Musaa Abdullahi safiya
Keystone bank

_ANTAYA SHAIDAR BIYANKI ZUWA GA WANNAN NUMBER_

09166221261


*Masu tura katin waya ko vtu kuma kai tsaye wannan number zaku tuntuba*

09134848107

*Maqotanmu kuma al'ummar qasar nijer zaku tuntubi wannan number dinne kai tsaye don biyan naku kudin*

09033181070


*ZAFAFA FAMILY na maraba daku*🫂🫂🫂🫂🫂*_GUDUN ƘADDARA_*

*H U G U M A*

BOOK 02 PAGE 58


Kusan duk inda suka gilma sai sun debi kallon jama'a,kana ganinsu zakasan samari ne masu jini a jika wadanda ilimi da hutu suka ratsasu,amma duk da hakan daban maina ya fita a cikinsu,saboda yadan fisu tsaho da kauri hakanan sumarsa tafi tasu nannadewa,kaman yadda fatarsa ta dara tasu gogewa.

Cikin qasa da minti talatin aka kammala siga aka daura aure,sauran hidimomi ne suka biyo baya kafin daga bisani a wuce babban hall na gidan da aka ginashi musamman saboda lokaci irin wannan. Reception sukayi a ciki wanda family din MAYAK'I suka shirya,kusan duk biki suna yiwa dangin ango wannan karramawar komai wadatarsu kuwa. Daga nan cikin gidan suka yi don gaida iyayen amarya.

Tana idar da sallar azahar houda na sanyo kai cikin dakin

"Ki fito za'a yi hoton family......ama tace nayi kiranki" kusan hoton hotone me muhimmanci ga dukkan dan gidan,don ana maidashi enlargement ne a ajjiyesu,kuma kowanne biki kusan sai anyi hakan.

"Kice mata bana danjin dadi....."

"Kinsan Allah saikin fito, bazanje na gaya mata ba" houda ta fadi kanta tsaye tana jawo mata mayafinta. Ko kadan bata qaunar fita farfajiyar gidan saboda dalilai biyu na farko bata son ta ganshi sam sam,duk da tana ji a jikinta zai wuya ta sameshi a wajen saboda shi din bamai shiga ire iren wadannan abubuwan bane,na biyu kuma bata qaunar kallo,ta rasa wanne irin kallo ne mutane ke binta dashi haka?,kamar ita daya ce Diya cikin dangin?.

Gaban madubi ta tsaya ta shafa powder ta maida lipgloss din da houda ta matso mata,sannan ta maida daurinta ta lulluba mayafinta a saman ka

"Kin saje da amaren ai wannan" houda ta fadi tana dariya,harara ta balla mata

"Zan fasa wallahi"

"Na tuba" ta maida mata amsar dai tana dariya. Plate shoe ta saka wanda ya dace qwarai da kayan jikinta,ta fito suka jera da houda din.

Duk inda ta gifta sai an Mata magana,wasu sunata mamaki dama tana ciki?,tana amsa musu da eh ta tashi ne yau bata jin dadi,da haka da haka sannu sannu har suka fara fita qatuwar harabar gidan. Tanata raba idanu taga benazeer ko batoul amma babu wanda ta gani a wajen,harma ta haqura ta koma hirar da houda ke mata tana biye mata.

Qoqarin saita tsarin hoton akeyi yana daga zaune saman kujerun dake wajen yana maidawa suhail reply din saqon daya turo masa,yana gaya masa yana sanya ran shigowa NIJER nan da kwana uku. Ya san suhail din nada family a nan amma ba masu yawa ba,to sai bai saki jiki sunyi wani hirarsu ba saboda bayason Susan daga wanne yanki ya fito,yasan kuma zaiyi wahala ya ambaci family dinshi suhail din bai sani ba duk da ba wai yana yawan shigowa bane. Har tsakiyar kansa yake jin hayaniyar tana damunsa,banda son ya farantawa su bibi da aba dake wajen da tuni ya fice yabar wajen,don kwata kwata kanshi baya iya daukar hayaniya haka.

Shigowarsu wajen sai ya zamana kamar sun taho da daukewar surutun dake tashi a wajen. Baya ga shirun da baisan meye ya haifar da shi ba,cikin jikinsa ya dinga jin wani baqon yanayi,tilas yadan dauke idanunsa daga fuskar wayar yana maidashi cikin farfajiyar wajen.

Gani daya biyu ana uku idanunsa suka fada kanta. Dan mitsitsin bakin nan dake dauke da wasu irin pink lips......bakin daya saba da tsiwa a baya yana motsawa a hankali tamkar bataso,ta zube fararen idanunta akan fuskar houda da alama wani magana suke me muhimmanci a wajensu.

Wani irin zuzzurfan kallo ya samu kansa da yi mata,yana karantar kowanne motsi nata. A nutse ta jingina da wata qaramar bishiya dake a wajen ta kuma goye hannayenta a qirji, kyawawan fararen idanun nata nata da abaya yasan ta qware wajen yin fari dasu idan tana jin rashin kunya a yanzun sun rusuna qwarai,sun zama wasu irin lumsassun idanuwa dake qawace da eyelashes,sun kuma qara girma kewayayyun idanun masu dauke da fararen qwayar idanuwa. Kwantaccen gashinnan da ya sani a gefe da gefen kunnenta zuwa gaban goshinsa ya sake qawata fuskarta qwarai,ya sake cika da sake kwanciya luf luf abinda ya zame mata kamar wani adon dawisu.

Yadda ta nutsu tana sauraron houda kadai ya isa ya gaya maka tarin nutsuwa da rayuwarta ta samu,zallar aji da kamala dake tattare


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login