Showing 153001 words to 156000 words out of 294767 words

Chapter 52 - Gudun Kaddara Book 2 Hausa Novel Complete

fadi,amma shikam baiga ta inda zai hada sabganshi da ayana ba,bama ayana din ba,shi kwata kwata idan ka debe yaran gidansu bashi da wani hadi da mata,ba harkarshi bace,wannan dalilin ya sanya har yanzu laila ta kasa saito kanshi,shima kuma ya kasa sanin yadda zaiyi da ita cikin ruwan sanyi,saboda girmamawa ga iyayenta da yayanta sardauna.

***********Washegari uncle tahir da kanshi ya rakashi airport,ayana na maqale dasu don ita tayi driving nasu ma zuwa airport din.

"Don Allah yaa haidar.......kar ka manta dani,kana da number na,kayi qoqari ka kirani idan kun sauka,inaso mu fara sabawa ne tun yanzun" ta furta tana langabe kai idanunta a kansa sanda yake sanye da wata lafiyayyar suit da aka saqata da zaren vicuna. Wani irin kwantaccen kyau take hanga tattare dashi,wanda tayi imani shi kansa baisan yana dashi ba,komai nasa a tsare yake cikin aji,wanda tayi imanin muddin ta mallaki maina din Allah ya gama sallamarta cikin gidan duniya dai. Tasha ji mummynta na labarin kyan da family din MAYAK'I inda auty hamdiyyan ke aure,amma da yake ta jima basu hadu ba ba zata iya hasashen fuskarsu a zahiri ba.

"Zan qoqarta" ya amsa mata a taqaice,don gaba daya surutunta yakai masa iya wuya,dabi'ace da sam baya sonta,tana daya daga cikin abinda ya dinga hadasu fada da sultana a baya.

Sosai yayi relaxing cikin jirgin,kyawawan lion eyes dinsa a rufe,yayi nisa cikin tunani,amma kuma kunnuwansa na jiye masa 'yan surutai dake tashi cikin jirgin qasa qasa daga passengers dake magana da mabanbantan yaruka. Basu jima ba aka daidaita komai,aka kuma bada sanarwar tashin jirgin,ya jawo belt ya daurawa jikinsa ba tare da ya bude idanunsa ba.

Sanda jirgin ya daidaita a sararin subhana sai ajiyar zuciya ta kufce masa,wani sasauci yakeji daga cikin zuciyarsa,abinda bai taba hasashe ba haka kawai sai ya tsinci zuciyarsa da samun sukuni,kurkukun da yakejin kamar yana ciki sai yaji kaman an zareshi daga ita

"Alhamdulillah ala kulli haal" ya fadi qasa qasa. Wayarsa ya jawo ya bude,kyakkyawan hoton benazeer da batoul da ya mamaye fuskar wayar ya bayyana,ya saki murmushi yakai hannunsa yana shafa hoton,kewarsu sosai tana taso masa,kwana uku kacal da yayi bai gansu ba sai ya dinga jin kamar shekaru uku yayi

"Am on the way.......zan fiddoku duk inda kuke indai cikin duniyar nan ne" ya fadi cikin ransa yana sake sakin wani murmushin.



*PARIS*

*champs elysees paris*
*8th arrondissements*


Tun shigowarsu unguwar yakejin tayi masa,yanayi da tsarin unguwar gaba daya ya dace da yanayinnsa da tsarinsa. A nutse yake bin ko ina da kallo,daddy din karimi ne na gasken gaske,tsakaninsu da sardauna suhail har zuwa shi kansa da yake bare a tsakaninsu riqo daya yake musu,kallo kuma daya yakeyi musu,ba wani banbanci da yake nunawa duk qanqantarsa. Ko ba'a gaya mishi ba ya sani 8 arrondissements din na cikin unguwar masu matsakaicin matakin rayuwa qwarai da gaske,kuma daddyn duka yayi hakanne saboda shi,saboda jin dadinsa,asibitinsa da zaya fara aiki a ranar litinin yana kusa sosai da nan din,sai kuma yafi masa sauqin gabatar da komai.

A nutse baturen faransan me suna Ahmad ya tsaida motar gaban gidan,a hankali ya zuro qafafunsa waje ya fito yana ambatar

"Bismillah,Allahumma anzilni munzalan mubarakan wa anta khairul munzaleen" ya qarashe fada yana shaqar fresh air din dake kai kawo a tsakanin layukan dake da wadatar tsirrai iri daban daban,idanunsa akan ginin gidan,tsarin ya masa sosai duk da bai shiga ciki ba,abinda ya fuskanta dukka gine ginen dake wajen iri daya ne,abinda ya sake qawata unguwar kenan.

Ahmad da dayan yaron daya kasance Christa su suka shiga masa da komai nasa ciki yana biye dasu a baya.

Sanda suka kammala komai sun sameshi a falon gidan,ahmad ya miqa masa muqullan ko ina yana ce masa cikin harshen faransanci

"je suis disponible quand tu as besoin de moi(duk sanda kake buqatata zaka sameni)"

"merci(na gode)" maina ya fadi yana karbar key din

"Il y a un employé qui fait le ménage et cuisine qui viendra plus tard(akwai ma'aikata masu tsaftace waje da dafa abinci zasuzo daga baya)"

"pas de soucis(ba damuwa)" ya amsa musu cikin jin dadin jigila da hidimar da sukayi dashi. Sallama sukayi masa sannan suka juya suka fice,abinda ya bashi daman wucewa cikin bedroom din daya zabi zama a ciki cikin bedroom uku da gidan yake dashi.

A gajiye yake sosai,don haka ya sabule kayan jikinsa ya fada wanka,koda ya fito zama yayi ya nema number daddy ya shaida masa isowarsa

"To Allah ya huta gajiya,ka huta sosai saboda ka samu energy din yin aiki yadda ya dace,karka shaidawa laila ka dawo,don ba zata barka ka huta yadda ya kamaya ba" daddy din ya fada yana murmushi me sauti. Kunya da kuma nauyin daddy dinne ya saukar masa,baisan ya zai kalli idanunsa watarana yace masa babu soyayyar laila ko daya cikin zuciyarsa ba,yana kunyar randa zaice masa yana mata soyayya ne kawai irin ta yaya da qanwarsa.

Sardauna ya kira bayan sun gama da daddy,sannan daga qarshe ya kira suhail. Zancan daya fara masa ya sakashi katse wayar,ya fara sansano akwai wata a qasa game da batun suhail akan sultana,wannan ya sanya zafin zuciyarsa akan batun da suhail din ya koma kashi hamsin zuwa dari,saidai yayi rantsuwa duk sanda hasashensa ya zama gaske sai suhail ya raina kanshi.

Tunawa yayi da uncle tahir,ya kamaci ace ya kirashi shima,sai ya soma duban number dinsa. Bugu biyu aka daga,saidai kuma muryar ayana ce ta fara fita daga wayar. Kanshi ya dafe da hannunsa,an riga an daga bare ya kashe,dole hakanan yayi sallama bayan ta cika masa kunne da fadin

"Hello.....hello...... who's on the line?"

"Assalamualaikum warahmatullah"

"Yes........yaa haidar?, thanks for calling,zancanka yanzu nakeyi" ta fadi da zaqewar nan tata da surutu daya fahimci baya mata yawa. Kafin wani a cikinsu ya sake cewa komai yaji uncle tahir ya karbi wayar

"Thank God" ya furta a fili can qasa qasa,sallamar uncle tahir din ya maida hankalinsa jikinsa,suka gaisa sosai ya kuma yi masa barka da hanya

"Nasan u are tired......ka huta tukunna,mamanka da ayana suna gaidaka" har cikin ransa yaji dadin hanata wayar da uncle yayi,don haka ya amsa da

"Ina amsawa,ina gaidasu sosai" daga hakan ya samu ya katse kiran yana furzar da iska yana latse wayar zuwa yanayin kasheta gaba daya,duk da yana buqatar yin magana da goumar wanda tunda ya dawo daga niamy aka ce masa yayi tafiya,bai kuma san inda yake din ba,bai samu kuma sukunin nemansa ba,amma a yanzun yafi buqatar kashe wayar don kada wani ya dameshi.

Yana shirin shiga wanka yana auna yadda ayana din ke zaqewa rayuwarsa da yawa,duk wani motsinta ya gama fallasa masa me takeson kutsa kanta a ciki,ya lumshe idanunsa sanda yake watsawa kansa ruwa

"Sultana" ya furta sunanta,ita daya ce matsalarsa a yanzun,ya kuma yi alqawarin zaiyi mata shigar ba zata ne,bazaiyi mata da sauqi ba wannan karon,dolen dole ta tsaya ta fuskanceshi koda bata shiryawa hakan ba,ya shiryawa komai da kowa ma. Wannan tunanin ya sakashi kammala wankansa a gaggauce,yanason ya kammala binciken da ya fara yi,bayason abun ya daukeshi da nisa,yanajin nasara cikin jikinsa,yana jin cewa tabbas addu'o'insa ba zasu tashi a banza ba.*_GUDUN ƘADDARA_*

*H U G U M A*

BOOK 02 PAGE 81



*_SULTHANA_*



**********Dukka wani mayuka zuwa qananun engines na gyaran gashi ta zube cikin bathroom dinta tana hidimar gyara dogon gashinta. Dole ta zama wata 'yar gayu ta musamman,komai nata ya canza,wani irin feleqe gareta yauqi da ya hade da wani irin aji kyau da kuma zallar kulawa na gyara da take samu. Zama da ama din ya zame mata kamar wata jami'a ta musamman,tayi naso da dabi'unta masu tarin yawa.

Tana tsaka da taje kanta ta soma jiyo hayaniyarsu,sharewa tayi taci gaba da abinda takeyi saidai kuma hayaniyar tasu kaman qaruwa yakeyi,dole ta ajjiye comb din ta dauki qaramin towel ta rufe kanta ta fito.

Tsaiwa kawai tayi riqe da qugunta tana kallonsa,harda ama,tana cikinsu,sun baje kaya masu uban yawa tsakiyar falon sunata zabe zabe. Batoul ce ta fara ganinta,tana ta dariya ta kalleta

"Guess what mummy?" Sunan mummy din data kirata dashi ya sanyata tayar da kai ta kalleta sosai. Sau daya suka taba fadi ta hanasu, w sunce daddynsu ne yace mummynsu ne,sunanta mummy not aunty. Haushinsa ya kamata a sannan,meye nashi da wani shishshigi zai sauya mata suna daga sunan da yaran suka saba kiranta

"Mummy ki canka" benazeer ta fada da qarfi tana boye abu a bayanta. Wannan yaja hankalin ama daketa tara kaya gefe guda ta waiwaya tana kallonta

"Ki canka din mana.......suna birthday month dinsu ne,saiki gaya mana date muga idan kin riqe" ta fadi tana ciro wani kwali dake dauke da wasu kids wears designers na wani kamfani ta aje gefe.

Murmushi tayi tana dan jin kunyan ama din,saita qaraso din ta zauna,sun sanyata a tunani

"Yau 25th......kaman......kaman on 28ne"

"Kaman ko kuma haka ne?"

"Hakanne ama,28 sixs years kenan?" Ta fadi cikin mamaki tana dan fidda idanu. Murmushi ama tayi,taji dadi cikin ranta,don batayi tsammanin ta riqe ranar ba

"Wanne kaya zaki saka mummy,ama zata hada mana birthday party?" Benazeer ta tambayeta cikin murna

"No......ranar da na fara zuwa aiki washegari ne zakuyi,maybe ma ina gurin aikin...... but zan bada gift na" fuska suka bata dukkansu su biyun, benazeer ta karyar da kai

"Please mummy" waiwayowa tayi ta zaro mata idanu

"Ni ko ama?,......ama ne mummy"

"Ama grandma kece mummy" ta amsa mata tana nunata da yatsa. Ama da ta kauda kai kaman bata gani dariya ya kamata,yayin da mamaki ya kama sultana sosai,wato duka yayi brainwashing yaran?. Bata gama wannan mamakin ba ta sake ballo mata wani ruwan

"Daddy fa zaizo?,uncle goumar yace zaki gayyato mana shi" ai batasan sanda ta qarasa fiddo idanun nata dukka waje ba,wannan din kuma bai hana benazeer ci gaba da zubo da surutunta ba

"Na daukama dashi zamuzo?,don Allah mummy ki gayyaceshi,we missed him a lot......ko batoul?" Tayi tambayar tana juyawa wajen batoul din. Da sauri yarinyar ta gyada kai itama,qarasa daburcewa tayi,sai kawai ta juya ta wuce ciki ba tare data samu amsar basu ba.

Guri ta samu ta zauna,ta kasa qarasawa toilet din,wai anya kuwa maina zaibar rayuwarsu yadda ya kamata?,tana tsoron faruwar wasu abubuwa nan gaba. Dukka kayan da tasan sunyi cakudedeniya dashi a nijer ta waresu guri guda,don duk wanda ta dauko babu abinda takeji a jiki sai qamshinsa. An wankesu kusan sau uku kenan,amma bata daina ji ba,kawai saita sanya kuka tana rufe fuskarta,kukan da ita kanta batasan meye dalilinsa ba.


*_MONDAY_*

Da dukka karsashi da qwarin gwiwa ya tashi ranar duk don kada yayi disappointing daddy. Ya shirya tsaf shi da sardauna da zai wakilci daddy ranan farko da za'a fara amfani da asibitin.


*_SULTANA_*


Ta bawa ranar muhimmanci me yawa cikin tarihin rayuwarta,ranar nasara kuma ranar sa'a a wajenta. Tun bayan sallar asuba bata koma ba,ta kasa zaune ta kasa tsaye,hatta da kayan da zata sanya daga gida zuwa tv station din,da wanda zata saka yayin gabatar da program din a dakin da aka tanada don buqata irin wannan.

Qasa ce ba irin tamu ba,suna matuqar bawa lokaci muhimmanci,don haka kafin cikar lokacin dukka iyalan hamdiyya abdu me kano suka isa gidan tv din don yiwa sultana rakiya a ranar farko ta kama aikinta,a matsayin cikakkiyar 'yar jarida da zata shugabanci sashen al'adu na gidan tv din.

Ama aba benazeer da kuma batoul din dukkansu,sauka ta musamman akayi musu,bayan tattaunawa a wani qaramin hall na musamman dasu ama din a matsayinsu na iyayenta,sun basu tabbacin cewa zata samu dukkan kulawa da mutuntawa data dace da addininta da al'adarta da kuma mutuncinta,uwa uba kuma sun sani tana da qananun shekarun da take buqatar hakan,daga qarshe suka rankaya tare aka sadar dasu zuwa ga office dinta.

Sam bakin sultana ya kasa rufuwa, murmushi ne zalla kwance saman kyakkyawar fuskarta,kyawawan tausasan labbanta sun fadada qwarai da mayalwacin murmushi. Madaidaicin office ne dake dauke da toilet da kuma balcony domin shan iska,ga spare din daki don changing kaya,an zuba mata komai don qawata wajen da kuma bata damar gudanar da aikinta hankali kwance.

Aqalla sun kusa awa daya wajen,aba ya mata addu'o'insa sosai ya kuma bata taqaitacciyar nasiha data ratsata sosai ta kuma sanyaya mata jiki,sannan ya fiddo key din mota ya ajjiye mata a gabanta

"Don sauqaqa zirga zirga,ranakun da kikejin qyuya kuma zaki iya bin train" hawaye ne suka fara digo mata,ta zame zuwa qasa saman gwiwarta sai ya dakatar da ita

"Tashi ki koma ki zauna,kada kicemin komai,jinin mohmoud yafi qarfin komai a wajena,rayuwarsa mohmoud ya sadaukarmin,banda Mahmoud da yanzun haka ba'a san waye hamidou bama,abu daya zakiyimin shine,ki kula da kanki,ki karemin tarbiyyarki da mutuncinki.....bazan lamunci duk wani abu da zai zama cutarwa ko cin zarafi a tattare dake ba" dan dubansa kadan ama tayi,sai taji kaman yana magana a fakaice ne akan aliyyu,amma sai ta share zancan daga ranta,tunda bai kama suna ko kwatance da zai nuna shine ba. Duka suka tattara suka tafi suka barta ta fuskanci ayyukanta,wanda sai kusan yamma sannan zata dawo gida.

A nutse ya maida qofar ya rufe yana ajiyar numfashi,baro mutanen da wajen hayaniyar da yayi sai yakejin kamar ya tserewa wani mugun abu. Kwata kwata baya son hayaniya ko surutu me yawa,yanzunne kanshi zai fara yi masa ciwo.

A hankali ya zare suit dinsa na saman ya maqale,ya wuce toilet ya daura alwala ko zaiji mode dinsa ya daidaita,kasancewarsa kuma mutum da baya rabo da zama da alwala(hakan yana da matuqar muhimmanci,don tana bawa mutum kariya sosai daga dukkan sharrin wani abu me sharri mutum ko aljan).

Saman sofa din da aka shirya daga wani sashe daban na office din ya zauna,yayi relaxing sosai yana fidda numfashi da kyau,har sai da yaji ya fara komawa dai dai. Qafafunsa ya sauke yana lissafa adadin kwanakinsa a paris,yana ganin kamar yayi nawar gano inda ama suke,don haka ya sanya hannu cikin zafin nama ya jawo system dinsa dake aje saman table ya bude.

Aiki sosai ya shiga yi da ita,lokaci lokaci yana magana ta wayarsa,sau biyu ana masa knocking yana neman excuse akan wani aiki yakeyi me muhimmanci.

Kimanin awa guda da wasu mintuna kusan arba'in din kafin hannunsa ya tsaya cak saman board din system din,yana duban sunan qasar dake yawo saman screen din. A fili fuskarsa shimfide da wani shauqi da farinciki,zuciyarsa fari tas ya furta

"Paris!" Sunan ya fita tar a bakinsa da wani irin accent tattacce.

Baya ya koma ya jingina sosai da kujerar yana tallafe da qeyarsa,wani sassanyan abu ke masa yawo cikin zuciyarsa,ama benazeer da batoul dinsa dukka suna Paris?,suna qasa daya?,jaha daya?,wannan shine dalilin da ya sanya yakejin raguwar qunci kenan daga zuciyarsa tunda ya sauka a qasar?,wannan shine dalilin da yasa ya dinga jin ya nutsu sosai da qasar?.

"Komai yazo qarshe,zai kuma zo da sauqi" ya furta a fili yana jin kaman ya gansu ya gama.

Knocking da akeyi shine ya katse masa tunaninsa,sai kuma kira ya shigo daga wajen sardauna

"Am done.....yallabai a daure a budemin qofan" ya fada da sauqin kan nan nasa har sai daya bawa maina dariya,ya aje wayar baice komai ba ya tashi ya nufi qofar.

"Done and dusted" sardauna ya furta yana saluting maina. Murmushi ya sakeyi,ya miqawa sardauna hannu

"Daddy ya kamata ka bawa wannan salute din sardauna...... he's our mentor"

"Harda kaima haidar......mafarkan daddy na shekara da shekaru dana gaza cika masa su yanzun ka zama silar cikarsu........ thanks for coming into our lives" jijjiga hannun sardauna yayi ya jashi zuwa kujera

"Kowacce kaddara da silarta sardauna.......sanda duk wani abu ya sameka qila sila ce kuma ta samuwa ko faruwar wani abu ga rayuwarka,Allah shine abun godiya" kai sardauna ya jinjina

"Haka maganar take......kunyi waya da suhail"

"Karka ambatarmin shi,tunda ya bini ciwon kai kawai yake bani,na rantse saina ragargaza maka dan uwa watarana" dariya ya kubcewa sardauna,ba kasafai maina yake biyewa suhail ba,amma kuma duk randa ta hadosu to da zafi zafi abun


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login