Showing 225001 words to 228000 words out of 294767 words
Chapter 76 - Gudun Kaddara Book 2 Hausa Novel Complete
tsam a qirjinta,sautin muryarsa ta dinga yi mata amsa kuwwa a kunne. Tattausar muryar nan me dauke da wani irin sauti me dadi.......lallausar muryar nan da yake iya bada tsoro da ita a duk sanda yaso yin hakan..... muryar nan da a baya koda bacci takeyi take farkar da ita koda bata shirya hakan ba.......muryar nan data zauna daram cikin rayuwarta,ta shiga kowanne motsi na second da mintuna na rayuwar tata.
A hankali a hankali tun tana goge qananun hawaye har hawayen suka soma ja baya,fuskarta ta bushe sarai,ta dinga sakin ajiyar zuciya kamar yaron daya gaji da neman mamarsa,a hankali har bacci ya dauketa.
Koda ta tashi da asuba jikinta da zuciyarta dukka taji sauqinsu,saita samu kanta da duba wayarta,ta rasa meye take nema?,kira ko saqo,amma daga wajen wa?,itama bata sani ba. Tun tana dubawa har ta gaji,ta maida wayar ta ajjiye tana tura baki gaba gami da kwantar da kanta saman cinyoyinta a hankali,a haka bacci yayi awon gaba da ita ba tare data sani ba.
Hayaniyar benazeer da batoul ne saman kanta ya tayar da ita,ta bude idanunta a hankali tana kallonsu. Ama ce ta aikosu su tasheta hakanan ta samu abinci taci sai suka buge da fadan waye zai fara tashinta a cikinsu.
"Ku matsa daga kaina kada ku sakamin ciwon kai" ta fadi tana korarsu.
Miqa tayi sosai tana duba lokaci,har sha daya da rabi na safe,ta shafa cikinta saboda yadda taji wata wawuyar yunwa tana sakadar cikinta. Bandaki takeso taje ta fara yin wanka amma sai taji ba zata iya jurewa ba,don haka ta jawo hularta ta saka,ta maida kimono din sleeping dress din jikinta tana wucewa kitchen,cikin ranta fal mamakin me ya sameta haka?,don tunda take bata taba jin yunwa kaf rayuwarta irin na wannan lokacin ba.
Ta samesu sunyi dama dama da kitchen,anata soya awara suna cinyewa. Mamakin inda suka samo awara a qasar ya kamata,tabi goumar da kallo wanda ya cika plate da miyan source na vegetable ya saka benazeer a gaba da batoul sunata kaiwa cikinsu
"Wannan nasan aikinka ne,saboda qwalama a qasar nan sai daka zaqulo awara?" Ta fadi yawunta yana tsinkewa,saidai kuma tana tsoron taci,don ta fuskanci duk sanda taci wani abu solid sai ya dawo mata.
"Bakisan awara tayi matsayi a duniya ba?,ba inda ba'a santa ba,suna nan suna saidata a supermarket matar babban yaaya" ya qarasa fada yana cika bakinsa da awarar.
Harara ta balla masa,yanason bata kunya gaban ama da zai dinga kiranta da wannan sunan?,sai ta matsa kawai tana cirar cup saboda hango kunun gyada da tayi fari qal da yayi masifar tsinkar mata da yawu. Gefan ama ta tsaya ta soma gaidata saboda sanda ta shigo kitchen din waya takeyi,a dan mamakance ama ta waiwayo tana dubanta tana kuma amsa gaisuwar,saidai kuma nazarinta takeyi cikin mamaki,wanne irin ciwo ne wannan?,jiya a galabaice harda zuwa asibiti qarin ruwa?,yau kuma gata har kitchen da qafafunta
"Ya jikin naki?"
"Da sauqi alhamdulillah" ta bata amsa tana miqawa tanja cup din ta cika mata da kunun gyadar.
Waje daya ta samu ta zauna sai gata ta tashi dashi,ta sake cika cup din shima ta tashi dashi. Ta ajjiye tana daukan ruwa ta Kora,take taji ta soma ganin daidai,tayi hamdala tana mamakin yawan kunun da tasha.
Duk kuma sai ya kashe mata jiki,tanason zama cikinsu amma ta kasa,idanunta suka dinga lumshewa,kasalar nan tanason dawo mata. Dukka ama na ankare da ita,gaba daya zaren tunaninta ya gama kuncewa,duk yadda taso kawar da tunaninta kan abinda zuciyarta keta bata amma hakan ya gagara. Saidai kuma taqi gasgata tunanin nata,saboda abu ne a duqunqune da zai zamo da zallar firgici da kuma ayar tambaya
"Ki wuce ki kwanta sultana" ama ta fadi ganin yadda ta dafe goshinta tana qoqarin amsa surutansu benazeer,amma kuma launin idanun nata ya sauya,hakanan muryarta ma tayi laushi sosai. Murmushi kawai ta yiwa ama tanason dakewa,a haka a daddafe ta bari qarfe daya na rana tayi,ta wuce daki tana layi saboda tsabar bacci. Tasan muddin ta sake ta kwanta tofa ba lallai ta samu sallar azahar ba akan lokaci,don haka ta fara shiga toilet tayi alwala tayi sallar azahar din tata tunda mukhtari ya shiga.
A nan inda ta idar ta zube,tanata qoqarin cijewa tanason gama addu'o'inta amma kuma bacci yace baisan wannan ba,bata tsinci kanta a ko ina ba sai a duniyar bacci.
*_ABUN B'OYE_*
Tun k'arfe biyu na rana goumar ya sanya tanja ta shirya benazeer da batoul don zuwa airport. Dukkansu cikin shiga iri daya. Wandon jeans da rigar chiffon da tayi matuqar dacewa da wandon. Sosai tanja ta qware itama wajen gyaran gashinsu,idan ka gani zaka dauka me gyaran gashi na musamman ama ta aje musu. Takanas tanja din ta zauna ta koyi komai da komai,wannan yana daya daga cikin abubuwan da ya sanya tanja ke sake shiga zuciyar ama Bibi dama sauran 'yan gidan,komai da ake da buqata daga wajen 'yar aiki tana qoqarin ganin ta koyo,zuwa yanzun tanja ta wuce me aiki a wajensu,saidai su kirayeta kakarsu tamkar ama,a wajen sultana ma kuwa uwa ce dungurun gum.
Cikin tashi shigar ta shirt da trouser ya iso falon,yayi fes dashi yana fidda salon nashi qamshin.
"Sai ina kuma sarakan yawo?" Murmushi ya saki yana sanya maballan hannun shirt dinsa
"Kin manta daddyn twins zai dawo?"
"Oh..... okay" ta furta tana gyada kai
"Allah ya tsare hanya" ta musu addu'a sanda suke fita. Sai da suka bacewa ganinta ta dawo da dubanta cikin falon tana sauke ajiyar zuciya. Addu'a takeyi sosai cikin ranta, addu'ar data kwana da ita ta kuma tashi da ita cikin ranta.
Basu jima da fita ba taji ana danna bell,ta tashi ta duba,sai taga aba ne tsaye. Mamaki yadan kamata,saboda yau din suna da tafiya daya daga cikin state din dake France.
Buda masa qofar tayi da sauri da dan mamaki saman fuskarta. Ta miqa hannu tana karbar briefcase dinsa
"Barka da dawowa"
"Yauwa hamdeee......kina mamaki ko?" Ya tambayeta yana murmushi
"Fargaba dai aba,Allah yasa lafiya"
"Lafiya qalau,anyi cancel flight dinne......sai jibi in sha Allah tafiyar"
"To alhamdulillah,Allah yasa hakanne yafi alkhairi,da sun shaida maka ma da baka sha wahala ba......"
"Laifi nane,tun tura ta email hankalina ya dauku kan wani aiki ban samu damar dubawa ba" ya bata amsa yana wucewa hanyar da zata sadashi da dakinsa.
Har zai shiga ya dakata yana dubanta
"Gidan shuru,ko sarkin yawo ya debesu?" Murmushi ama tayi,sam ba dama aba din ya shigo gidan yaji baiji su batoul ba ya dinga tambaya kenan,idan kuma har ya jima ciki basu dawo ba ya soma qananun mita da qorafi kenan har sai an nemosu duk inda suke sun dawo gida
"Yanzun nan suka fita..... amma yau ba nisa sukayi ba" ta bashi amsa a dunqule ba tare data masa zancan dawowar maina ba. Tuni tayi cancel din yi masa batun maina,kwata kwata ta daina masa magana kan duk wani abu da ya shafeshi. Dan dubanta kawai yayi,kaman zaiyi magana sai kuma ya sanya kai ya wuce ciki. Ya lura akwai maganganu da yawa data daina yi dashi,ta daina hira dashi kan abubuwa masu yawa,tanason fadi masa abubuwa da yawa nan ma ta daina.....har yanzu yana tunanin akwai wani side nasa da bata gama sani ba,abinda bata sani ba,shi din komai na iyalinsa kusan akan tsarinsa yake,saidai abu ya kubce masa ba tare da saninsa ba.
Komai da yake da buqata ta shirya masa,sunayi suna hirarrakinsu da suka shafesu,wanda kusan fiye da rabi akan business nasu ne,nata da na yara su batoul boutique boutique dinsu,yadda kullum suke sake fadada suna buda rassa a garuruwa da qasashe na kurkusa da nijer din
"To ni sai yaushe za'a bani manager a BB boutique din?" Qaramar dariya ama ta saki sanda take cire masa maballan gaban rigarsa
"Haba aba.....da wanne zakaji fisabilillahi?,ga shekaru suna sake hawanka,kada bibi tace nice na sukurkuta mata d'a...Kai kanka sabgoginka neman matallafi kake fa ka manta?" Sai datakai qarshen maganar sai taji kaman bai dace tayi ta ba,bataso yaji ko kusa a ranshi tana nemawa maina sassauci ne daga bangarensa,tanaso sai ranar daya gama dukka cije cijensa akan d'ansa ya fito yayi duk hukuncin da zai sanya fushinsa ya gama fashewa gaba daya a wuce wajen, fushin nasa da ta tabbatar dai dai yake da fadan gwaggo a kofa,duk wani dagiyarsa da cijewarsa ta gama ganin lagonsa. Baice komai ba kuwa,saidai ta fahimci fuskarsa tadan bada wani reaction,don yanayinsa ya sauya kadan,sai ta bagarar da wancan zancan ta dauko masa wani zancan na daban.
Yunwa ita ta fara tashinta kamar mahaukaciya,a gigice ta kuskure bakinta tana mamakin yadda ta jiqe haka da gumi,wanka take buqatar tayi amma yunwar cikinta tafi damunta,ta kalli agogo saura kadan hudu ta cika,sai kawai ta fice kitchen a gaggauce.
Tanja tanata tambayarta me takeso amma ta kasa mata cikakken bayani,sai kawai tanja din ta matsa ta bude wani mazubi ta zuba kunun gyada me kyau daya cup din madara me dumi ta ajjiye mata a gefanta
"Na gode tanja" ta fadi tana fara daukan cup din kunun gyadar ta soma kurba a hankali. Tsaiwa tanja tayi tana kallonta yadda take lumshe idanu tana enjoying kunun kamar batasha ba dazu. Qamshi qamshin lemon tsamin yake sake bata nishadi sosai,ta gama tas dashi ta dauki cup din madarar
"Allah tanja ulcer ke neman yimin illa,qarfi da yaji tanason maidani wata acici ga shegen lalaci me yayi zafi?,wannan ai aikina sai ya samu damuwa" ta fada a shagwabe tamkar sultanar data sani can shekarun baya
"Haqqun" kawai tanja tace da ita tana duban fuskarta, cikin zuciyarta tana sake haqiqancewa tabbas lallai dai yaro a koda yaushe yaro ne,kowacce mace da irin lokacin da quruciya take barinta koda kuwa yara nawa ta haifa,kallon sultana din kawai takeyi,tanata aika madara cikinta. A*_GUDUN ƘADDARA_*
*H U G U M A*
BOOK 02 PAGE 121
Itama sai data gama tas da ita sannan ta dire cup din tana fadin
"Alhamdulillah" ta miqe tana cewa
"Bari nayi wanka nayi sallah,in sha Allah yau bazanyi baccin wuri ba saina kammala research dina" ta furta tana maida dubanta kan tanja
"Lafiya tanja?" Sultanar ta tambayeta tana kallonta. Murmushi ta saki tana girgiza kai,tana kuma qoqarin danne dariyar dake cin ranta
"Aah ba komai,a fito lafiya"
"Allah yasa,kin samu ladana ai" ta fada tana fita a kitchen din tana duba miscals din data gani cikin wayarta data bari kunne sanda take bacci.
Har zata wuce dakinta taji ana danna bell,ta daga kai daga duban wayan tana sauya akalar tafiyarta zuwa bakin qofa,ta bude tana ja da baya.
Likitar jiya ce,maqociyarsu da tayi alqawarin tahowa da result din gwajin sultanan. Matar nada fara'a da kuma kirki sosai,da murmushi take tambayar sultana ama
"Tana ciki,shigo nayi miki magana da ita" ta amsa mata tana qoqarin mayarwa matar murmushin da take faman doka mata. Haka kawai ganinta ya sanya gabanta yankewa ya fadi,ita ta manta ma jiya sunje asibiti,tunda dai taji dadin jikinta na meye sai an damesu da duba result?.
Wajen zama ta bata sannan ta nufi hanyar dakin ama,sai kuma ta tuna bata ciki,don taji tanja na fadin aba ya shigo gida,don haka ta dawo ta zauna tana kiran layin ama.
Bugu biyu ta dauka,saita fara isar mata da saqon zuwan matar
"Ba damuwa,a bata drinks da snacks,tadan jirani kadan aba yana toilet idan ya fito zan sameta a falon.....ku debe mata kewa"
"Toh ama" ta amsa mata tana sauke wayar. Hada idanu sukayi da matar,ta sakar mata murmushi sai itama tayi saurin gayyato murmushin ta jefeta dashi,haka kawai takejin zuwan matar cikin gidan bai kwanta mata ba,ta daure cikin harshen faransanci tayi mata bayani
"Ba komai,ta kammala a nutse". Miqewa sultana tayi,ba zata iya zama tare da ita ba,hasalima wanka takeson yi zafi kuma takeji,don haka ta wuce kitchen kawai ta yiwa tanja bayanin anyi baquwa ama tace akai snacks. Tasan tanja din ta iya yaren France daidai gwargwado da zata iya hira da likitar,wannan ya sanya kawai ta wuce daki kai tsaye,ta fidda kayanta ta fada wanka.
Cikin kyakkyawar shigar farar long sleeve shirt da farin trouser masu matsakaicin kauri da wani irin sulbi mallakin kamfanin Calvin yake. Komai nashi fari ne qal,tun daga kan undies dinsa na ciki har zuwa kayan jikin nasa,takalmi agogon fata luggage da kuma wani zagayyen farin eye glasses da ya fidda kyawun qwayar idanuwansa data sanyawa suna da lion eyes.
Wani irin sassanyan kyau yake fitarwa,wanda hasken rana maras zafi da yake tsaye a cikinta yake sake tona asirin kyan nashi ta hanyar fidda kyawun baqar nannadaddiyar sumarsa ta asalin ba'abzine dake karban gyara da kuma zallar kulawa. Sumar ta qawatashi matuqa da gaske,ta fidda sirrin kyakkyawar fuskar nan da shekarun da ya samu da kuma hutu ke sake bayyana cikar kamalarshi. A 'yar tafiyar ta sati uku kacal ya sakeyin fresh,ya kuma sake cika,cikar data dace da tsahon nan tasa dake nunawa a dukka gabbansa koda a zaune yake.
Yana tsaye yayi crossing qafafunsa,idanunsa nakan wayarshi,amma kuma tsaiwarsa a wajen ta fusgi hankali da zukatan mata da yawa dake wajen ba tare da yakai hankalinsa kai bama.
"Daddy......daddy" ya fara jiyo muryoyinsu benazeer sama sama,duk kuwa da nisan da hankalinsa yayi hakan bai hanashi jiyosu din ba.
Cira kansa yayi a hankali yana duban direction din da yake jiyo muryoyinsu daga wajen. Dole sassanyan murmushin nan nasa ya subuce masa ba tare daya shirya ba,ya miqe ya tsaya sosai kaman me bayyanawa wadanda ke satar kallonshi ainihin tsahonsa,ya maida wayarsa aljihu,ya soma tattare hannuwan rigarsa zuwa gwiwar hannunsa,don yasan dole yasha cafa yau,sai ya goye hannun nasa a qirji yana sakin murmushi idanunshi a kansu yana dakon isowarsu
"Oh god.....damn it" wata baturiya da tun dazun ta mace a kansa ta furta tana rufe idanunta,ya gama tafiya da ita ainun,ta kuma yarda itama da kanta wajen kyan sura da kuma iya sace zukatan 'yan maza,to amma a yau din ta hadu da mutumin da takejin wani mugun kwarjini da shakkar tunkararsa,tayita attempting ta taddashi inda yake tsaye tun dazu amma ta kasa.
Batoul yau ita ta riga benazeer isowa,ita ya fara dagawa sama sannan ya sauke ya dauki benazeer,duk kallo sai ya koma kansu, saboda yadda sukayi bala'in daukan hankalin mutane. Suna da kyakkyawar surar da idan ka kalla dole ka sake kalla,tsafta da kuma iya sanya sutura data zamewa yaran ado tun suna jarirai.
Da surutu suka barke masa,yaji a jikinsa ido.yayi yawa a wajen,don haka ya dakatar dasu,ya waiwaya yana kallon goumar
"Samin luggage a mota mu wuce" ya kama hannuwansu yana yin gaba,goumar ya jawo luggage din suna barin wajen.
Sai data ajjiyewa aba baqin coffee dinsa sannan ta dubeshi
"Dr ta kawo result na sultana,barin je na karba"
"Ba laifi,gwara da aka kawo da wuri,ya kamata asan wanne ciwo ne ayi masa rigakafi da wuri"
"Gaskiya kam....." Ama ta amsa masa tana zura dan madaidacin hajib ta dauki wayarta ta fice.
Da fara'a ama ta bawa doctor hannu suka gaisa,sai tanja ta matsa gefe ta basu waje,itama bakinta ya huta da gwagwarmayar France din da taketa hadawa don suyi hira da matar. Yar gajeruwar gaisuwa ta baki suka sakeyi,ama na tambayarta aiki ta amsa mata da
"Alhamdulillah" tunda musulma ce,shuru nadan sakanni ya biyo baya tana qoqarin fidda takardar gwajin daga cikin takardunta data taho dasu.
"Ina tayaku murna madam......" Ta fadi da fara'a tana miqawa ama takardun. Daurewa kan ama yayi,amma sai tayi tunanin kamar bataji abinda ta fadi bane da kyau,ta miqa hannu tana karbar takardun sanda take sake cewa
"Dole tayi haquri da wasu canje canje da zata dinga ji,daga wadannan satittikan har zuwa sati sha biyu sha biyar har sati na ashirin ga wasu matan" idanu kawai ama ta zuba mata,mamakinta yana sake ninkuwa,ita sam bata fahimci inda zanca dr ya dosa ba,saboda bayanan dr kaman tana bayani ne ga mutumin dake kiwon kaji?.
"Kaman yaya