Showing 192001 words to 195000 words out of 294767 words

Chapter 65 - Gudun Kaddara Book 2 Hausa Novel Complete

Dukka hankalinsa yana kan yarinyar,wadda itama tana ganinsa ta sake narkewa jikin ama. Cikin nutsuwa da kuma girmamawa ya qaraso gaban kujerar da ama din ke zaune akai ya zauna sosai a qasa yana miqawa benazeer din hannu. Nata hannun ta miqa masa sai ya jata cikin jikinsa yana jin yadda nata jikin yayi dumi sosai

"Barka da warhaka ama" ya gaidata cikin girmamawa. Ajiyar Zuciya ta saki tana gyara zamanta,ita daya tasan me take tunawa

"Barka kadai"

"Ya gida yame jikin?"

"Alhamdulillah da sauqi,ta karba magunguna ai,amma da yammar nan za'a maidata su sake gwada jininta" shuru yayi hannunsa saman sumar yarinyar yana shafawa,tausayinta sosai yakeji haka kawai yana ratsashi

"Akwai inda yake miki ciwo yanzun?" Ya tambayeta cikin nuna kulawa,kai ta gyada masa tana nuna masa kanta,kan ya kama a nutse ya karanta mata addu'o'i,sannan ya zare idanunsa ya maida ga ama

"Wanne asibiti ne?,yanzun lokacin zuwa ganin likitan yayi?" Ya tambayi ama din

"Mamarsu ta sani.….." ta furta tana dan duban sultana,wadda tunda ta bude qofan ta zauna a hannun kujerar dake daura da qofar. Haka kawai takejin jikinta dukka a mace,batason kuma wucewa daki don kada ama taji ba dadi game da hakan da zatayin

"Alright" ya amsawa ama a taqaice. Miqewa yayi yana daukanta saman kafadarsa yace da ama

"Tanja tana kusa?,ta fiddo mata takalminta" ya amsa yana yin hanyar waje.

"Ki dauki takalminta cikin shoe rack,kisa mayafinki kuje" ama ta bata dukka umarnin lokaci guda tana miqewa daga zaman da tayi don dauke batoul da bacci ya dauketa a wajen.

Kawai take dari dari dashi da kuma tsoro tsoro,kaman ta dojewa ama din amma kuma sam ba zata iya ba,ala dole tayi yadda ama dij tace,ta fito sanye da wani mini hijab data dora saman doguwar rigar jikinta.

A seat din kusa dashi ya zaunar da benazeer din,tanata zuba tabararta,yau aiki ya samu shi kuma yana biye mata,tasa hannu ta bude seat din baya ta shige ba tare da tace komai ba,shima din bai tanka ba ya kunna motar ya soma motsata suna barin layin.

Dukka dakiyarta da dauriyarta ta tattaro sannan ta hada kalaman

"Ina yini" lion eyes dinsan nan ya daga,ya kalleta ta cikin glass din gaban motar. Kamar idanuwanta sunsan ita yake kalla itama takai nata duban ga mirror din,take idanunsu suka hadu waje guda. Shi ya fara janye kallonsa daga kanta yana amsa mata murya ciki ciki

"Lafiya" yadda ya amsa mata din sai ya tsaye mata a rai,yayi mata kama da lokuttan baya ko tace shekarun baya s nijer,sanda yake mata ire iren wadannan abubuwan a duk sanda sarautar tashi ta motsa. Daga haka bai sake cewa da ita komai ba,itama bata sake fada din ba,to me zatace bayan ma tasan bata da abun fada din.

Yana driving yana hira da yarinyarshi,sam kaman ma bata cikin motar,duk da benazeer na zazzabi amma baki bai mutu ba,surutu kuma ba'a daina ba,a haka suka isa asibitin. Kaman dazu yanzun ma daukarta yayi sukayi gaba,tana biye dasu a baya har suka isa reception. Shi ya gabatar da abinda zasuyi da tattacen faransancinsa,suka bashi number ya tafi daga gaban office din yana jiran number su ya nuna.

Sanda number ya fito wayarsa tayi ringing,ya katse kiran suka shiga office din likitan. Yar asalin qasar faransa,me yawan fara'a da kirki da kuma son yara,tana ta jan benazeer da wasa,saita daga kai tana murmushi ta dubesu

"beau couple,vous êtes parfaits l'un pour l'autre(kyakkyawan ahali,kun dace da juna)" ta qarasa fada tana kallon fuskar sultana. Dan qaramin murmushi ta saki tana satar kallonshi ta gefan idanunsa,sai taga shi duka hankalinsa ma yana kan wayarshi. Haka kawai taji ranta ya quntatar mata,wataqila wannan yarinyar fa yake magana da ita?. Bata qarasa wannan tunanin ba taji yana cewa

"Je suis désolé, quand ils auront fini, ils me trouveront dehors, je lancerai un appel d'urgence au téléphone(Yi hakuri, idan sun gama za su same ni a waje, zan yi kiran gaggawa a waya)" murmushi tayi

"aucun problème monsieur(babu matsala yallabai)". Matsawa yayi ya shafa sumar benazeer yana cewa

"Il n'y a pas de contestation(banda taurin kai),ba zasuyi miki allura ba kinji my angel?,see you soon" ya qarasa fada yana dan jan kumatunta. Murmushi tayi tana bashi peck a bayan hannunsa.

Juyawa yayi ya fice a nutse yana sanya wayar a kunnensa.

Idanunta ta lumshe tana jan numfashi da kyau saboda wani motsuwa da ranta yayi,ta zaci uzurin lalurar benazeer din tafi dukkan wayar da zai daga din muhimmanci?. Kiran sunanta da likitar tayi shi ya dawo da hankalinta,ta sauka daga kujerar da take kai ta koma saman wadda ta tashi tunda tafi kusa da likitan,tayi qoqarin tattara hankalinta don suyi abinda ya kawosu su gama.

Cikin minti ashirin da biyar suka gama komai,ta karba dukkan sauran magungunan da zataci gaba da amfani dasu.

Sun fara fitowa zuwa haraban asibitin benazeer taja tunga ta tsaya. Ta juya tana kallonta,sai babbata fuska takeyi

"Lafiya kuma?"

"Mummy ni ki daukeni" idanu sultana ta fiddo waje tana kallonta

"Dauka benazeer?,bakiga kinyi nauyi ba?, infact ma kin girma fa" narke mata tayi tana shirin sakar mata kuka

"Mummy amma bani da lafiya fa,bakiga daddy dauka yakeyi ba?" Sak ta tsaya tana dubanta,wayo ya fara sangartasu kenan?,to ita din ba zata lamunta ba,don haka ta hade rai tsam tana dubanta

"Ba zan daukeki ba don kin fara wayau ai,ki wuce mu tafi ko kuma ki jira daddy din naki yazo ya daukeki" qafa ta soma bugawa zata tabare mata,wannan din ya fusatatata ta daka mata tsawa sosai.

Har inda yake tsawan ya taddashi,sai ya leqo da kanshi daga seat din driver da yake zaune qafafunsa a waje yana amsa waya ta handsfree. A kansu idanunsa ya sauka,sai ya dauke kallonsa ya maida kan diyarshi.

Hawaye takeyi sosai tana share fuskanta da bayan hannunta,suna hada ido ta tako da gudu ta qaraso wajensa ta fada jikinsa.

"Daddy mummy ce...... " Benazeer din ta fada cikin shesheqar kuka. Cikin jikinsa ya sanyata sosai yana fadin

"Am sorry,cool down B" ta samu abinda takeso saita lafe tana goge hawayen.

Fuska a hade tana sake kama kanta ta bude back seat kaman yadda sukazo ta shiga,tana shirin maida murfin ta rufe muryar data dade da haddace ta waye taji ta cika motar,da alama waya yakeyi,ya kuma jona wayar da speaker din motar

"Halan waye ya taba B?" Laila ta fada tana fidda murmushi me sauti. Ware idanu benazeer tayi wadda itama batasan waya akeyi ba,ta kalli maina sannan ta kalli speaker din

"Mummy ce"

"Rabu da mummy,sai an zaneta ko?" Laila da batasan alaqarsa da benazeer ba ta fadi. Murmushi benazeer ta saki tana leqen sultana dake baya. Ba benazeer ba,ko maina bai isheta kallo ba. Saidai wani abu da yazo ya tsaye mata a wuyanta me matuqar tauri da zafi.

Dama da yace zai amsa kiran gaggawa wayo zaizo yi cikin motar da wannan yarinyar?,ashe su ya rainawa.hankali,kenan ciwon bai dadashi da qasa ba?,kawai sai taji idanunta sun fara mata yaji yaji,alamun suna neman dalilin da zasu fidda qwalla,saidai kuma cikin tsananin dakiya sa jarumtarta ta girgiza kai alamun a'ah,akan meye zatayi qwalla?,shi din waye da zatayi masa qwalla

"Am on my way"

"Saika qaraso dear........" Ta fadi tana katse kiran da sauri kaman wadda tasan tayi laifi.

Sallamarta ta qarshe sai ta dinga mata amsa kuwwa cikin kunne,tana ji ya tayar da motar suka fara fita daga asibitin,batace komai ba,bata motsa ba kuma bata bude idanunta ba.

Tana jin hirarsu daya bayan daya,wanda duk kalamansa a nan zallar qauna kulawa da soyayyar da yakema yaran suke nuna kansu. Batasan me yasa shariyarsa take mata ciwo a zuciya ba,bayan irin wannan abun ta jima tana buqatar ya dinga yi mata,a yanzun data samu kuma batasan me yasa ta kasa jin hakan dai dai bane.

"Bari naga wata" maina din ya fada yana rage gudun motar tashi,sannan kuma a hankali ya soma gangarawa gefen titi kusa da wasu shops yana neman area din da ake parking

"Alhamdulillah" ya fadi bayan ya tsaida motar,ya kasheta yana bude side dinsa ya zura qafafunsa waje.

Kamar a mafarki cikin rufaffun idanunta taji muryar yarinyar dab dasu,gabanta yayi wani mummunar faduwa,hakanan ba tare data shirya ba ta soma ware idanun nata sanda muryarta me karadi ke tashi

"Na gode sosai da ka bani damar ganin B......B.....how far?,ya jikin?" Ta fadi da murmushi sosai saman fuskarta tana yunqurin xagayawa side din kujerar benazeer.

Sisiririyar bafulatana sanye da gown na chiffon da bata sauka idanun sawunta ba,ta sanya qaramin scarf ta manne idanunta da baqin sun glasses,qafafunta saye da takalmi sneakers daya dace da material din.

A shekaru zata iya bata shekara uku,a kyawun sura kuwa tabbas koda wasa ba zatayi gigin shiga sahun da sultana take ciki ba, ba'a maganar diri da structure na jiki,amma a idanun sultana sai taga gaba daya ta kowanne fanni ma kamar ta kere mata.

Sanda ta bude side din benazeer din ta sako kanta tana bawa benazeer hannu tare da tambayarta jikinta duk dai taji kaman iskan wajen yana neman yi mata kadan.

A nutse ta dauki wayarta da qaramar jakarta,ta sanya hannu ta bude murfin motar ta sanyo santala santalan fararen qafafunta waje tana fita a motar,wannan motsin ya sanya laila ta ankara da zaman mutum a seat din bayan.

_KWANKWASON JIMINA_*

*_TSUTSAR NAMA_*

*_AMEENATOU_*

*_GUDUN KADDARA_*

_DUKKA AYARIN LITATTAFAN KUDINSU YA KAMA KAMAR HAKA_*

LITTAFI DAYA_400
BIYU_800
UKU_900
HUDU_1200

_IDAN TA BANKI NE ZAKI SANYA KUDINKI A WANNAN ASUSUN_

6019473875
Musaa Abdullahi safiya
Keystone bank

_ANTAYA SHAIDAR BIYANKI ZUWA GA WANNAN NUMBER_

09166221261


*Masu tura katin waya ko vtu kuma kai tsaye wannan number zaku tuntuba*

09134848107

*Maqotanmu kuma al'ummar qasar nijer zaku tuntubi wannan number dinne kai tsaye don biyan naku kudin*

09033181070


*ZAFAFA FAMILY na maraba daku*🫂🫂🫂🫂🫂*_GUDUN ƘADDARA_*

*H U G U M A*

BOOK 02 PAGE 103



Qamshinta da motsinta yaja hankalin laila,ta daga kanta tana bin bayanta da kallo. Bataga fuskarta ba amma gabanta yayi wani mugun faduwa

"Mummy karki tafi ki barni" benazeer da taga fitan sultana ta fadi. Sosai tayi qoqarin daidaita mode na fuskarta sannan ta waiwayo,sai a lokacin laila da take binta da kallo ta samu daman ganin fuskarta da kyau.

New TV show presenter Sultana mohmoud,ta shaida fuskarta,tun a ranar data fara program din,a ranar aka fara ganinsa da ita,a ranar kuma taji tayi matuqar burgeta,har ta dinga jin tamkar itama ta sauya hannu ta koma aikin jarida. Qwarewarta kawai zai sanya kayi tunanin ta dade a harkar,kyanta ya burge laila qwarai ya kuma bugar da ita,to amma kuma me takeyi a mota tare da maina?. Saurin kauda tunanin daya darsu a zuciyarta tayi,muddin ya kasance wata alaqa ce data danganci soyayya tsakaninsu to tayi imanin kashinta ya bushe,don ita kanta da take mace tahi imanin wanda yake da sultana babu abinda zaiyi da ita.

"Zan shiga in sha coffee" ta bawa benazeer amsa tana shiga shagon coffee dake daura dasu.

Jakarta kawai ta daura saman table din,ta kuma order din coffee din,yanata zuba tururi da qamshi a gabanta amma batasan meye zatayi dashi ba,haka kawai zuciyarta dukka taqe a quntace, idanunta nakan qofan Glass din da ta yiwa wajen qawanya,wadda bata hana wanda ke ciki hango kai kawon jama'ar waje.

Agogonta ta duba,a qalla mintuna goma da shigowarta wajen kenan,sanda zata daga kai daga agogon benazeer ta shigo

"Mummy kizo wai mu tafi, za'a ajjiye aunty laila a hanya"

"Aunty laila?" Ta yiwa kanta da kanta tambayar tana duban idanun benazeer. Kai ta gyada tana kallon sultana din. Numfashi ta ajiye tana qoqarin controlling kanta

"Ku wuce zan biyo ku a baya" ta bata amsa tana jawo cup din takai bakinta wai ko hakan zai rage mata abinda takeji.

Kaman ba zata motsa ba yarinyar sai kuma ta juya tana fita a wajen a sanyaye.

Yana jingine da jikin motar yayi crossing qafafunsa ya kuma goye hannayensa a qirji yaga fitowarta ita kadai,idanunshi a kanta har ta qaraso

"Daddy tace wai mu wuce zata taho".idonsa ya lumshe gami da budesu duka lokaci daya

"Me kikace mata?" Ya tambayeta

"Da waye kikace mata zamu tafi?" Ya sake gyara tambayar yadda zata fahimta

"Da aunty laila....."idanu yadan zaro sai kuma ya saki murmushi. Ya samarwa laila taxi kuma har ta wuce,don shima bawai yanason yadda take rabarsa bane,kawaidai yana tuna karamcin daddy da mutuncin sardauna,tanacin darajar mutum biyu.

Mota ya budewa benazeer ya kwnatar mata da kujera sannan yace

"Zauna,karki fito har sai na dawo,ki zauna kiyi game ko ki kwanta" ya fadi yana fiddo mata wata mini game wadda dama ya ajeta cikin motar ne sabodasu. Baki ta washe tana karba da sauri,ta kwanta abinta kuwa tana maida hankalinta ga game din.

Hannun rigarsa ya gyara sannan ya fara takawa zuwa cikin coffee bar din.

Tunda ta kurba sau daya bata qara ba,ta ajjiyeshi a gabanta tana juya tea din da spoon,tayi nisa a duniyar tunanin da batasan ina ta tafi bama,sai inuwarsa ta gani saman kanta.

Yayi qyam a gabanta da wanna tsahon nasa da dakiyarsa,fuskar nan ta fito a asalin sunansa na aliyyu haidar,ya motsa bakinsa cikin wata ginshira da izza data jima rabon data ganta tattare dashi

"Kin shiya tafiya da qafafunki ko kuma ni kike jira na daukeki?" Ya mata kwarjini sosai ta yadda ba zata iya kallon cikin idanunsa ba,amma duk da haka tayi namijin qoqarin kauda fuskarta gefe

"Idan kika qara minti daya zaune a wajen nan da hannayena xan daukeki,kuma kinsan hukuncinki basai na gaya miki ba......and benazeer ba zata hana aiwatar da komai ba" yayi maganar yana gyara hannun rigarsa. Ba shiri ta suri handbag dinta tana miqewa tsaye. Hannu ya miqa mata yana tsareta da idanu,ta fahimci abinda yake nufi,don haka ba musu ta miqa masa hand bag din,ya sakata a gaba suka fice daga wajen bayan yaje ya biya kudin abinda ta karba din.

Da kansa ya bude mata gidan gaba yana basarwa,tadan dubi benazeer da tayi kwanciyarta a baya,ta shiga a hankali ta rufe,ya daidaita zamansa ya tayar da motar.

Bai ajesu gida ba sai daya gama yawon yima yaransa siyayya kaf,kaman ta sanya hannu aka ta saki ihu,don sam zaman cikin motar ya gama gallabarta,shi da benazeer kawai suke sabgarsu,yaqi sakata ma a cikin hirarsu gaba daya.

Koda ya ajesun ma bai shiga gidan ba ya juya abinsa bayan ya raka benazeer da sayayyarsu har bakin qofa,ya tsugunna yayi kissing nata ya wuce.

Itama dauke kai tayi ta wuce ciki,saidai kuma can qasan ranta tana jin wani qunci yana saukar mata. Ba abinda idanunta ke nuna mata sai yadda yake hira sosai da wancan yarinyar tashi,wai wacece ita?,meye ne alqarsa da ita?.

"To ke menene sha'aninki da ita?,suje su qarata mana" wani sashe na zuciyarta ya gaya mata,saita ja tsaki tana qoqarin fincike komai daga ranta, tsakin da ya sanya ama waiwayowa ta kalleta,tayi sauri ta dake ta dauki jakarta tana wucewa ciki.

Duk yadda taso fidda abun daga ranta tayi amma a banxa,don sanda ta kwanta saman gadonta,sanda garin ya sake daukan shuru,dare ya fara nisa sai komai yake neman kwance mata,ta dinga laluba murmushi guda daya tak da yayi mata a yau din ta rasa,magana tsakaninta dashi bata iya tuna guda daya ba,hirarsa kaf da yarinyarsa


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login