Showing 183001 words to 186000 words out of 294767 words
Chapter 62 - Gudun Kaddara Book 2 Hausa Novel Complete
na tv station din.
A nutse ta ajjiye motarta,ta zagayo tana daukan jakanta. Harabar maaikatar tasu babu wadatar zirga zirgar jama'a sosai saboda zuwan wurin da tayi,ita kanta yau tasan tayi sammako,ta kalli agogonta sanda take tafiya cikin nutsatstsen takunta dinnan ga hanyar da zata sadata da floor din da office dinta yake. Kafin ta qarasa ta hadu da ma'aikatan da sukayi shigowar wuri irinta,dole ta dorawa fuskarta murmushi kaman yadda ama tayi mata
Elevator ne ya ajjiyeta,ta fito tana takawa a nutse hadi da qoqarin fidda wayarta. Yasmine ce,ta saki siririn murmushi,itakam ko kudin da ake janye mata na kira sam bata ji,koda yake yanzun ta zama 'yar kasuwa sosai yanzun. Sanda ta daga da muryar bibi taci karo,murmushinta ya sake qaruwa,har yanzu tana son bibinta,tana ji da ita,bata kuma taba manta gatan data gwada mata,duk da ya zame mata matsala,ya kuma so ya zama silar samun tasgaro ga rayuwarta,amma da yake tayi komai ne da kyakkyawan nufi bawai don rayuwartata ta samu damuwa ba sai gashi komai yazo cikin sauqi.
Tana tafiya a lobby din zuwa office din nata tana waya da bibi,jifa jifa suna gaisawa sa staff's din da suke cin karo dasu,har takai bakin office din,ta fidda card na bude qofan ya karashi jikin qofar,ya bada sauti na alamun tsaro ya bude kansa,ta murza handle din tana tura qofar gami da fadin
"Karki bata bibi,sai na zauna sosai cikin office na zama comfortable sannan zan kirata"
"To ya rage ya naku,ungo ni" bibi ta fadi tana miqawa Yasmine wayar,jin hakan ya sanya sultana qit ta kashe kiran tana dariya,don ta san qarshen zancan,qorafi ne kawai yasmine din zata cikata da shi.
Tsaf murmushin dake saman fuskarta ya dauke saboda abinda idanunta suka gani. Maina ne,aliyyu haidar,yana zaune tsaf abinsa saman kujerarta ta office,yayi relax sosai abinsa,ya zare eye glasses dinsa key da wayarsa duka suna saman table din,daga gefe kuma madaidaicin tray ne dauke da wasu qananun bowls da butar shayi.
Yayi wani masifaffen kyau cikin tsadaddar suit din jikinsa da aka saqata da zare da auduga me daraja. A nutse kuma tsaf ya watsa mata lion eyes dinnan nasa da ayau ta gansu sun rusuna qwarai fiye da kullum
"Come in" ya furta calmly yana tsareta da idanunshi da suke shigar mata da wani magnet me qarfi cikin jikinta. Tayi tsaye ne kawai cike da mamaki,ita bata shiga ba kuma ita bata fita ba. Wai ta yaya yake samun access da komai nata?,bayan tayi imanin bashi da wani mabudi nata?,yaushe ya shigo?,yaushe ma ya taho gaba daya?,ya akayi yasan da wannan plan din nata bayan duk duniya daga ita sai zuciyarta suka yanke wannan shawarar?.
Bataga tahowarsa ba sai isowarsa bakin qofar,dav da ita ya tsaya idanunsa cikin nata,hancinta ya shaqi qamshinsa da kyau daya ratsa ta qwaqwalwarta ya sauka a zuciyarta. Tamkar zai gogo jikinta ya fidda hannunsa guda daya daga aljihun wandonsa ya maida qofar ya rufe still dai bai zare idanunsa daga nata ba.
Sosai ya tsaya a gabanta,irin tsaiwar da idan yayi kyakkyawan motsi zai iya hade tazarar dake tsakaninsu. Tsaiwarsa a gabanta ya qara masa mugun kwarjini cikin idanunta,irin kwarjinin data jima bataji irinsa ba,ya tokare mata ko ina da tsahonnan nasa, hakanan ya hana qwayar idanunta sukuni ko motsin kirki kwata kwata
"Kina mamaki ne?" Ya jefa mata tambayar kai tsaye da muryarsan nan me ratsa kunnuwa
"Kin manta wannan din uncle maina ne?,wanda ya raineki da wadannan hannayen....." Yayi furucin yana daga mata hannunsa qwaya daya bayan ya zaroshi daga aljihunsa.
"........yadda maina ya sanki yasan halinki bana tunanin kin san kanki haka,yasan me zaki aikata da abinda ha zaki aikata ba..... fuskanki kawai tana iya bani labarin abinda yake cikin qirjinki da zuciyarki......" Ya furta yana hade gap din dake tsakaninsu.
"Kada ki tsorata.......ba wani abu zaki bani ba......bacci kawai nazo ki tayani......jiya ban samu isashen bacci ba" ya furta yana sabule jakar kafadarta ya ajeta a gefe. Sake miqa hannu yayi ya zare pin din data maqale rolling din kanta dashi,a hankali mayafin ya soma ware kanshi da kanshi,ya riqe hannayenta cikin nasa wannan ya sanya bata da damar tsaidashi har ya gama ware kansa ya zame ya fadi qasa.
Baqar lallausar sumarta da tasha mayuka da gyara ta bayyana,kyakkyawar fuskarta ta fito tarwai,sai ya sakar mata hannu daya ya miqa hannun masa guda dayan ya soma zuge zip din gaban abayar tata.
Hannu dayan da ya sakar mata ta saka ta riqe hannunsa tsam adan razane,muddin yaci gaba da zuge zip din to ba makawa komai nata zai bayyana ne, don bata sanya vest ba ganin rigar me kauri ce, underwear ne kawai a jikinta.
Da idanunta da suka qara laushi ya kalleta, muryarsa a dan sarqe yace
"No" yana girgiza mata kai,sai ya shammaceta ya zuge zip din gar zuwa gwiwarta.
Dukka numfashinsa yaso yayi qaura,farar bra din jikinta zuwa farin underwear dinta sun sauka sun xauna kuma dai dai saman farar lallausar fatarta da a kullum take cikin gyara da kulawa. Albarkatun qirjinta dukka suka tsone masa idanu,ya kasa janye dubansa daga kansu,cikin wani irin zafin nama ya jawota zuwa jikin nasa numfashinsa yana kai komo.
Kyakkyawar runguma yayi mata,ya miqa hannu yana ware band din kanta,hakan ya bawa sumar kanta damar bajewa saman kansu shi da ita gaba daya. Cusa kansa yayi tsakanin wuyanta,da muryar rada yace mata
"Karkiyimin gardama please,i want a peace please,am sleepy" daga haka bai barta ta qara sukuni ba ya dauketa cak ya nufi sofa da ita rigar da mayafin da takalminta dukka suka zame a wajen.
Sosai ya kwanta saman cinyarta hankalinsa kwance bayan ya cire suit din jikinsa sai fara qal din vest dake jikinsa dake fidda lallausan qamshi,gaba daya yayi mata kane kane saman cinya tamkar yaro yaso rigima saman cinyar mamansa.
Hankalinta gaba daya a rarrabe yake,yanzun idan akayi mata knocking fa?,wanne amsa zata basu?. Idan kuma tsautsayi yasa akayi tsammanin shurun da za'a ji bana lafiya bane akayi attempting shigowa fa?.
"Don Allah...... nan din fa ba gida bane wajen aiki ne"
"Ban gaya miki stay at home ba?,na baki izinin fitowa?......duk wanda ya miki knocking ki gaya masa kina tare da mijinki" yayi lafazin yana yin wani irin juyi,ya koma rub da ciki yana gyara kwanciyar kansa saman cinyarta tare da miqa hannunsa ya zagaye qugunta ta baya. Idanu ta sake fiddawa tana mamakin qarfin hali irin nasa,saidai kuma tana tsoron cewa wani abu,don gwara wanann punishment din nasa akan me gaba dayan. Bata gama wanann tunanin ba taji ya kamo hannunta ya dora tafin hannun nata saman tattausar sumarsa yana cewa
"Bacci......bacci nakeyi mummyn twins" ya qarashe fada yana lumshe idanunsa yana jin yayi comfortable yadda ya kamata.
_KWANKWASON JIMINA_*
*_TSUTSAR NAMA_*
*_AMEENATOU_*
*_GUDUN KADDARA_*
_DUKKA AYARIN LITATTAFAN KUDINSU YA KAMA KAMAR HAKA_*
LITTAFI DAYA_400
BIYU_800
UKU_900
HUDU_1200
_IDAN TA BANKI NE ZAKI SANYA KUDINKI A WANNAN ASUSUN_
6019473875
Musaa Abdullahi safiya
Keystone bank
_ANTAYA SHAIDAR BIYANKI ZUWA GA WANNAN NUMBER_
09166221261
*Masu tura katin waya ko vtu kuma kai tsaye wannan number zaku tuntuba*
09134848107
*Maqotanmu kuma al'ummar qasar nijer zaku tuntubi wannan number dinne kai tsaye don biyan naku kudin*
09033181070
*ZAFAFA FAMILY na maraba daku*🫂🫂🫂🫂🫂*_GUDUN ƘADDARA_*
*H U G U M A*
BOOK 02 PAGE 98
Yadda yayi ruf da ciki saman cinyarta ya sanya take iya jin bugun zuciyarsa sosai. Bugawa takeyi fiye da kima,sai hakan ya zama tamkar wani Aiken saqo ne zuwa ga gangar jikikta gaba daya.
Sannu a hankali taji bugun zuciyar tasa yana dai daita zuwa matakin da kowacce zuciya ke bugawa,a hankali taji numfashinsa yana fita a hankali,ya soma sauke numfashi da wani irin nutsuwa,saidai lokaci lokaci yana sauke ajiyar zuciya tamkar wanda yayi tsaren gudu,ga kuma qanqame qugunta da yayi sosai kamar zata bace masa.
Nauyi da nutsuwar daya qara yi saman cinyoyinta ya tabbatar mata bacci ya daukeshi,hannuwanta dake saman tattausar sumarsa ta kalla,ta kasa janyesu,sai kallon yatsunta da suka nutse cikin sumar tasa takeyi. A hankali ta soma motsa yatsun nata suna sake nutsewa cikin sumar tasa,wani irin taushi da santsi take dashi. Sannu sannu yadda hannunta ke shigewa cikin sumar sai ya tuna mata da wasu shekaru can baya da suka shude,lokacin da yake daukanta saman wuyansa,ta riqe gashinsa da kyau tana dariya,duk da tasan akwai zafi amma baya nuna mata hakan,lokacin da yake kwanciya saman pillow tayita jagwalgwalata da sunan kitso zatayi masa,wani lokaci ta hanashi bacci har sai ya tashi,wani lokaci kuma yayi baccin dole da bai shirya ba.
Wata ajiyar zuciya ce ta kufce mata,sai ta dauke hannuwan nata a hankali tana maida kanta saman makarin kujerar,duk jikinta ya mutu murus,babu wani sauran laka a jikinta itama,ya gama saukar mata da kasala me yawan gaske,gefe guda ga sammakon da tayi itama bayan kuma bata samu yin isashen bacci ba a daren jiya.
Idanunta a lumshe taji vibration na wayarsa dake ajjiye dab da cinyarta kusa da kanshi. Bude idanun nata tayi a nutse tana kallon wayar.......sunan laila ne ya fito radau saman wayar. Batasan me yasa ba sai taji an motsa zuciyarta,ta zubawa sunan ido yanata yawo saman wayar,tanason ta dauke kai da idanunta amma ta kasa,wai wacece wannan laila din?,tanason sanin wacece,haka kawai takeso ta sani din,tanason taji muryarta koma wacece ita.
Zuciyarta na gargadarta akan ta dauke kanta daga wayarsa amma ta kasa,haka ta miqa hannu ta dauki wayar daketa fidda qamshin tsumammen turarensa daya kama jikin komai da yake tu'ammali dashi. Tayi shipping ta daga kiran sannan ta sanya wayar a kunne, zuciyarta haka kurum na wani irin luguden duka
"Helloooo dear...... good morning,ina hanya in sha Allah,bazan wuce awa daya ko biyu ba zan iso paris......amma champs elysees din ko zaka sa azo a daukeni please ko ka qaraso da kanka?" Ta qarasa maganar a shagwabe da kuma karyar da murya da alama tanason karya taurin kansa ne
"Bacci yakeyi saman cinyata" ta samu kanta da fadi zuciyarta na mata zafi,ranta kuma yana raya mata abubuwa da dama. Dif laila tayi daga daya bangaren,dukka wutarta ta dauke daga bayyanar sautin muryar sultana dake bayyana zallar kamun kai da ajin dame muryar ta mallaka. Qarfin hali tayi ta tattara dukka dauriyarta gabanta yana faduwa tare da mamakin wacece wannan da zatace yaa haidar yana bacci saman cinyarta?,ba zata tana mummunan tunani a kansa ba,don ita kadai shaida ce akan tsarkin zuciyarsa,tsahon zamansu da shekarun da sukayi tare dashi ko kallon banza bai taba yi mata ba bare akai ga batun wani maganar banza
"Ke din wacece?" Laila ta jefawa sultana tambayar. Tambayar saita zowa sultana da salon rainin hankali,ita din zata kalla tace wacece?
"Idan ya tashi kina iya tambayarsa" ta amsa mata a taqaice,sannan ta saki siririn tsaki tana katse wayar?. Kasa aje wayar tayi ta dinga kallon number din,sai taji tana da sha'awar duba cikin wayar,to amma kuma ta riga ta shiga security wayan. To wacace wannan laila din?,zata iso paris nan da awa daya ko biyu?,it means kenan akwai wani boyayyar alaqa a tsakaninsu?,me zatazo tayi masa tana baligar mace yana baligin namiji tun daga wani waje?,a gidansa zai sauketa?. Tambayoyin dukka taji sun mata girma da yawa,ranta yana sake baci,ta motsa kadan tana leqa fuskarsa.
Fayau take dauke da wani irin kwantaccen kyau,komai na fuskarshi na aje cikin tsari da baiwar iya halitta ta ubangiji. Mix take gani na kamannin batoul da benazeer saman fuskarsa,abinda duk tsahon shekarun bata taba gani ba sai yanzun. Kamar jira suke ya dawo rayuwansu dama,suna ta juyewa zuwa kamanninsa.
"Ki rage fada please" taji ya fada qasa qasa kaman me mayen bacci
"Ki maida wayan silent,ki kuma daina picking mini call" ya sake fada yana gyara kwanciyarsa sosai hankali kwance.
Mamaki yadan kamata,kada dai ace yana sauraren abinda duk take fadi?,bai bata dama ta biyu ba ya saka hannu ya jawo hannunta sai gata gaba daya ta kifo saman kansa tayi masa rumfa
"Sleep please......na sani kema baki samu cikakken bacci ba" ya hanata motsawa ya hanata sakat,haka taci gaba da yi masa rumfar,tun tana qananun tunanuka har idanunta suka soma mata nauyi,sannu a hankali bacci yayi awan gaba da ita.
A haka suka shafe awa guda da rabi,gaba dayansu jikkunansu da numfashinsu sun gama gauraya da juna. Shine ya fara farkawa,ya bude idanunsa a hankali yana dubanta. Kyakkyawar fuskar rigimammiyar qanwarsan nan baby sultana,yau din ta zama madam sultana,duk wani sirrin kyau nata ya bayyana,irin kyawun da bai taba gani ba tsahon zamansa da ita. Hannu ya miqa saman lips dinta,yana da muradin taba bakin tsiwa.
Cikin jikinta taji yanayin da take ciki ya sauya sosai,ta bude idanunta a hankali,sai kuma ta qarasa budesu da sauri,a lokaci guda kuma tayi wani irin hantsilawa a tsorace sai gata ta zauna sosai sama sofa din. Idanu take bubbudewa cike da mamaki,ita dake a zaune kanshi a saman cinyarta ya akayi ta koma a kwance,ta matse sosai cikin jikinsa saman doguwar sofa guda daya,wanda koda da yaro ka kwanta sai jikkunanku sun matsi na juna?.
Yadda ya zauna calmly yana qarewa santala santalan hannayenta da dogon wuyanta kallo,yadda baqar sumarta me tsaho da santsi ta baje a sassan jikinta ta sake zama ado a tattare da ita ya tuna mata jikinta ba kaya,ba komai sai bra da underwear.
Da azama ta cure waje daya tana kifa kanta saman cinyarta,itakam wannan wanne irin abun zub da mutunci yake jawo mata?. Siririn murmushi ya saki yana kada kai,duk da bai gaji da kallonta ba bazai kuma gaji din ba,amma dazun kafin ta farka daga bacci ya morewa idanunsa kallonta yadda ya kamata,ta kuma tayar masa da feelings dinsa qwarai,to amma bayason ya cika zaqe mata ko matsarta da yawa dashen da yake da niyyar yi cikin zuciyarta ya rasa kyakkyawan gurbi da muhallin da yake fata.
Tsam ya miqe yana fadin
"Tashi ki bani abinci......am starving" yayi maganar yana dosar toilet dinta. Ta tsakanin gashin kanta da ya lullubeta take satar kallonsa har ya shige toilet din,ta miqe da mugun hanzarin ta doshi bakin qofa ta rarumi abayanta ta maida,saita soma laluben key din office din bayan ta dauki handbag dinta.
Sama da qasa ta rasa maqullin,sai a sannan zuciyarta ta soma raya mata ya boye ne,cak ta tsaya,tabbas xai aikata,tunda har yana iya gane komai saman fuskarta data shirya,kaman yadda yasan tsaf meye zata aikata da wanda ba zata iya yi ba.
Dole ta koma saman kujerar ta zauna tana furzar da iska,saita daga kanta a nutse tana duban agogo
_nan da awa daya ko biyu zan iso paris.....ko zaka qaraso da kanka ka daukeni please_ muryar laila ta fado mata a rai. Agogon ta jefawa harara ta janye idanunta tana jan tsaki.
"Rashin kamun kan yayi yawa" ta fadi qasan ranta tana kuma jan qwafa,ta maida dubanta ga wayarsa kamar me jiran shigowar wani kiran. Can qasan zuciyarta kuma sai takejin babu me laifi sai shi,don meye?,don meye ya fito daga family na mutunci zai dinga jaye jaye?. Lumshe ido tayi abun yana tsaye mata a rai,yanason bata musu sunan family kenan?
"Sunan family ko sunan 'ya'yanku?" Ta jiyo sautin tambayar data sanyata bude idanunta gaba daya tana neman amsarta.
Sosai ya hakimce mata saman sofa din,ta dinga zirga zirgan debo abincin dake shirye cikin tray wanda batasan ma ya akayi ya samu shigowa office din ba,harda kuma wai abincin da ta tabbatar daga kitchen na station dinnasu aka kawo mishi. Ta qasan idanu yake qare mata kallo,bata da abun cewa sam bakinta ya kullu,to meye ma zata ce masa?,ya riga ya gama kulle mata baki,itakam zuwa yanzun ma tsoro yake bata,ta yadda duk