Showing 255001 words to 258000 words out of 294767 words

Chapter 86 - Gudun Kaddara Book 2 Hausa Novel Complete

Taso rakasu Dr Camille har bakin mota amma dr din tace tayi zamanta,ita dinma hakan ya mata,don yunwa gaba daya ta kashe mata jiki,batasan kuma zuwa yanzun me zataci ba,shu daya ke iya sarrafa mata abu ya bata ya zauna mata lafiya lau. Ama ce tazo ranta,tabbas a wajenta kawai zata samu yadda takeso,sai kawai ta fidda waya ta turawa aman saqon neman abincin gargajiya daga wajenta,don tana kunyar kiranta kai tsaye.

Motarsu Dr Camille na tashi taji sautin shigowar wata motar, ba'a yi minti biyu ba muryoyinsu ya karade farfajiyar gidan. Suhail da sardauna,dukkansu ta dauki muryoyinsu

"A nan ya kamata mu zauna don tattaunawar nada muhimmanci sosai"

"Shiga ka fito,kazo kuma ka gayamin ma'anar zaka sake angwancewa muji mu muna nan zaune gardawan banza kakeson maidamu ko?"

"Ku kuka so shegen banza" ya maidawa suhail amsa yana dawowa ciki don ya dauka musu drinks.

Tunda suhail yayi maganar taji kunnuwanta kaman sun dan toshe na wucin gadi,tayi shuru tana sauraren muryarsu sanda sardauna ke sake tambayar suhail din. Waje daya idanunta ke kalla,don haka har ya shigo ya dauki wayar ya fice bata ma lura dashi ba,tadai jiyoshi yana musu jagoranci zuwa saman kujerun concrete dake filin 'yar farfajiyar tasu.

*_masu siyan anko da masu zuwa dannar qirji duk ku shirya_*🧐🧐

*_ni nayi nan saikun taho_*

*_sauka on the way in sha Allah_*


_KWANKWASON JIMINA_*

*_TSUTSAR NAMA_*

*_AMEENATOU_*

*_GUDUN KADDARA_*

_DUKKA AYARIN LITATTAFAN KUDINSU YA KAMA KAMAR HAKA_*

LITTAFI DAYA_400
BIYU_800
UKU_900
HUDU_1200

_IDAN TA BANKI NE ZAKI SANYA KUDINKI A WANNAN ASUSUN_

6019473875
Musaa Abdullahi safiya
Keystone bank

_ANTAYA SHAIDAR BIYANKI ZUWA GA WANNAN NUMBER_

09166221261


*Masu tura katin waya ko vtu kuma kai tsaye wannan number zaku tuntuba*

09134848107

*Maqotanmu kuma al'ummar qasar nijer zaku tuntubi wannan number dinne kai tsaye don biyan naku kudin*

09033181070


*ZAFAFA FAMILY na maraba daku*🫂🫂🫂🫂🫂*_GUDUN ƘADDARA_*

*H U G U M A*

BOOK 02 PAGE 136


Abinda ta sake shiryawa saman tray ta ajjiye jikinta a sanyaye saman stool. Gaba daya hankalinta taji ya koma wajen inda suke zaune. Duk da bata iya jiyo komai amma sai ta kasa zama waje daya. Ta bude abincin da zummar taci duk sai taji gaba daya ta qoshi. Mayarwa tayi ta rufe,ta jawo wayarta ta bude,zuciyarta na bata shawara ta kira bibi ko su batoul su debe mata kewa,nan ma taji koda ta kirasu din kamar ba zara iya magana ba,don haka ta ajjiye wayar,ta maida idanunta ta aza saman tv wadda keta aikinta ba tare da volume ba.

Sosai kunnuwanta sukayi nisa da son jin abinda suke magana akai,amma kuma bata iya jiyo komai din sai dan guna guninsu wanda bata iya tantance ko meye suke cewa. Baya ta zame ta kwanta tana dora kanta saman pillow. Wata irin kasala na sake rufeta,tana jin batason daga koda yatsanta ne

"Me suke tattaunawa?,da gaske zai barta tayi rayuwarta kamar yadda taketa nanata masa?,da gaske bata da buqatarsa?,da gaske zata iya rayuwa babu shi?" Har tsakiyar ranta takejin amsar da tafi dacewa da ita kamar NO ce fiye da YES,ta soma wassafa rayuwarta ita daya ba tare dashi ba,sai kawai taji kanta ya kasa dauka,ta dauke kanta gefe tana girgiza kai,batasan me takeji ba,bata kuma san me zata fuskanta ba.

Ta kusa mintuna ashirin a haka kafin taji muryoyinsu sun fara tashi,kamar musu sukeyi,kamar kuma rigima sukeyi,abu guda kunnenta ya iya jiyowa, muryar maina sanda yake fadin

"Da laila da ayana dukansu......." Sai ta gaza jin abinda yake fadi daga qarshen.

Iya jin sunyensu kadai a bakinsa sai daga sanya gabanta tsananta faduwa,ta runtse idanunta tana qoqarin daidaita bugun zuciyarta. Fargabarta tana sake qaruwa,kada dai ace ya aminta da zancanta,ya kuma yarda da abinda ta fada din?.

Idanunta ta sake lumshewa da suke mata yaji yaji kaman hawaye na shirin fita. Har yanzu tana jin tashin muryoyinsu,tsahon lokaci tana jinsu kafin daga bisani taji hayaniyar ta lafa,sai kuma maganganunsu qasa qasa da dariyar suhail da sardauna.

"Hasbunallahu wani'imal wakil" ta fada tana gyara kwanciyarta. Komai qwace mata yayi,sai hawaye kadan kadan da suke fita mata daga qasan idanunta tana sharewa,daga qarshe ta dinga furta

"La'ilaha illa anta subhanaka inni kuntu minazzalimin" kadan kadan tana neman daukin ubangiji.

Mintuna kusan talatin taji an buda qofar dakin,ta ware idanunta da suka sauya launi. Akan fuskarsa suka sauka sanda yake takowa cikin dakin,shima ita yake kalla,ranshi ba dadi da yadda yaga fuskarta alamun ta danyi kuka don har fuskar tadan kada tayi ja,dole sai an tauna madaci wasu lokutan ake samun maslaha,don haka ya kauda kanshi kaman bai gani ba qasan zuciyarsa tana masa ba dadi,ya wuce zuwa inda ta ajiye kayan abincin.

Zama yayi ya bude komai ya qare musu kallo sannan ya ja qaramin bowl din data ajjiye ya zuba ya sanya cokali ya sauka qasa ya ajjiye a gabansa.

Lion eyes dinsa da suka rusuna saboda zafin zazzabi ya daga ya zube mata su,yadan lumshesu kadan sannan ta motsa bakinsa a nutse yana miqa mata hannu

"Taso nan" jiqaqqun idanunta ta daga ta kalleshi,sai ta saukesu qasa a hankali,ta yunqura da karyayyiyar zuciya jikinta a mace,ta fara takawa a hankali. Idanu ya bita dashi yana kallon takunta,tausayinta yana ratsashi a hankali a hankali,sai ya miqa mata hannu kafin ta qaraso yana gyara mata inda zata zauna.

Sosai ra zauna a gabansa ya gyara mata skirt din jikinta,ya dago bowl din ya ciro cokalin ciki ya debo abincin yakai bakinta

"Bismillah" ya furta,saita maimaita itama ta bude bakinsa ya saka mata. Ta runtse idonta tana tauna abincin a hankali.

Da gaske komai da zai fito daga hannunsa dabanne a wajenta da bakinta,me hakan yake nunawa?. Duk yadda take ganin zata iya,zata iya ci ita kadai zata iya gamsar da kanta da buqatunta a hankali a hankali sai komai yake neman qaryatata. Me yasa take gazawa akan komai?,me yasa kasawarta ke fito akan komai da komai?

"Ba zaki iya ba sai dashi" wani sashe na zuciyarta ya bata amsa kai tsaye cikin sallamawa daga lamarin gaba daya. Maganar ta tsaye mata a rai,da gaske hakanne ko kuwa?.

Tana tsaka da wannan tunanin ta daga idanunta,sai taga ashe ita yake kallo shima,ya ritsata da idanunsan nan da a yau kallon cikinsu ya haifar mata da wani irin abu da bata taba jinsa ba,a take kuma idanunta suka hada hawaye fal har hakan ya nuna cikin qwayar idanunta masu sheqi.

"No...... don't cry" ya fadi a tausashe,sai ya zaro tissue daga gefansu yana miqa mata. Bata musa ba ta saka hannu ta karba ta fara tsane idanunta

"Kin qoshi?" Ya tambayeta yana dubanta. Kanta ta gyada a hankali

"Good" ya fadi yana maida ragowar tissue din cikin kwalin. Ruwa ya tsiyaya ya miqa mata,ta miqa hannunta zata karba hannunsu ya hadu waje daya. Dukansu shida ita babu wanda baiji wani abu a jikinsa ba,yayi saurin sakar mata ruwan wanda saura kadan itama ya subuce daga hannunta. Kamar kullum ya hada kan kayan guri guda,ta bishi da satar kallo ta gefan ido. Tana jin kamar tace masa kada ya fita daga dakin,amma kuna tana jin nauyin fadan haka.

Bayanta ta mayar jikin kujera tana lumshe idanunta gami da fidda numfashi a hankali.tanason tuna daidanta da kuma kuskurenta,a cikin wannan tunanin nannauyan bacci yayi awon gaba da ita,dukka jikinta ya sake saboda qoshin da tayi,wanda tun ranar qarshe daya bata abincin rabonta data qoshi haka.

Lokacin da ta farka tayi mamaki sosai ganinta kwance saman gado kuma lullube cikin duvet,ta dudduba jikinta a hankali mamakin dai bar barta ba haka ta sauka tana duba lokacin sallar azahar. Lokacin bai qure ba amma dab yake da fita,wannan ya sanya ta qara azamar shiga toilet.

Tana idar da sallah wayarta ta dauki tsuwwa,ta miqa hannu a nutse tana jawo wayar. Number goumar ne,don haka ta daga kiran.

Muryar batoul ta fara ji,cike da karsashi take magana

"Mummy assalamualaikum" murmushi ya subuce mata,muryarsu na daya daga cikin abubuwan da suke sanya mata nutsuwa a wannan lokacin

"Wa'alaikummussalam B" murmushi ya qwacewa yarinyar,har tana jin sautinsa ta wayar

"Mummy ina kwana?" Karyar da kai sultanar tayi tana jin dadin jin muryarta

"Lafiya lau B.....amma yanzun ba safiya bace,ko bacci ama ta barku kuka dinga yi?" Dariya ta qyalqyale dashi

"A'ah,yanzun nan mamy tanja ta gama gasa mana cake.... uncle goumar yaje ga siyo mana whipping cream strawberry flavor ta saka a ciki" murmushi ya qwace mata,yaran badai son cin dadi ba,bakinsu yasan kwadayi qwarai,ko don sun saba tun suna qananu?,saidai kuma duk da hakan bai sanya an barsu sun sangarce ko kuma sun miqe da samun duk abinda sukeso ba

"Ma sha Allah,a yiwa mamy tanja godiya sosai"

"Mummy.....we missed you.....don Allah ama tace mu tambayeki muzo mu ganki?" Maganar ta sanya sultana jin nauyi da kunya,me ama ke nufi?,ya zata hana yaran zuwa?,ita kanta marmarin ganinsu takeyi,inda da hali ma kuma da zaiyiwu aman ta bata dasu zatafi kowa farinciki da hakan,amma ta sani wannan magana bame yiwuwa bane,koda wasa kuma ko a mafarki ba zata ce a bata su batoul ba,don sun zama halak malak din ama da aba,mallakinsu ne ko duniya ta shaida

"You are welcome BB" ta fada a gajarce don batasan ko ama tana wajen ba.

Ihunsu taji daga cikin wayar da muryar mutumin nasu goumar,sai kawai ta ajjiye wayar tana murmushi. Batasan wanne qarfin qauna goumar din yakewa yaran ba,ba wani abu da yake barinsu su nema su rasa,real definition of uncle ne shi din.

Samun kanta tayi da tunanin me zata samawa yaran suci a matsayin barka da zuwansu?. Ta dinga tunani daga qarshe ta yanke abinda zata basun,tasan ba abinda suke so irin kayan maqulashe,don haka ta qarfafa jikinta ta miqe tana zare hijab dinta ta lullube kanta da madaidaicin mayafin daya dace da rigar jikinta.

Har cikin ranta takejin walwala sosai,ta dinga takawa cikin lobby din don ta wuce zuwa kitchen din,daidai sanda taga qofar dakin dake daura da nata a bude. Idanunta saman qofar dakin tana qiyasta a nan ya koma kwana kenan.

Dab da zata gifta dakin ta soma jin sautin muryarsa,cikin calmness dinnan nashi

"In sha Allah next week ko upper week zamu shigo Niger din......"

"Lafiya ko?" Daga cikin wayar ta jiyo sautin muryar uncle umar yana tambayarsa

"Neman aure oncle......nigeria da kuma niamy in sha Allah"

"Hasbunallah" ta fadi tana gifta dakin da sassarfa tana jin qafafunta kaman ba'a jikinta suke ba.......tana qoqarin sarrafa tashin hankalin da takeji cikin zuciyarta tana kuma tuhumar kanta me ya kaita tsaiwa jin maganarshi cikin waya.

Da qyar ta qarasa kitchen,ta samu stool ta zauna saiga hawaye kamar ana tunkudosu.......auren zaiyi da gaske?,meye makomarta kenan?, meye matsayinta a gurinshi?,a ina ya ajjiyeta?.

"Sultana......ki fitar da kanki daga sabgar nan......kiyi ta kanki kiyi ta rayuwarki......taki qaddarar ce qila kiyita haifa masa yara babu cikakken zaman aure.....ki sauke wannan daga nan ki samawa kanki mafita...... zaiyi aure saboda baki da wani matsayin komai a wajensa....baki kuma isa komai ba.......ki zama jaruma....ki zama jajirtacciya......ya hado laila ayana da dukka danginsa ya aura mana" zuciyarta ke gaya mata hakan cikin tsawatarwa.

Kokawa sosai ta dinga yi da zuciyarta tana wassafa yadda zata iya handling maganar. Maganar tafiya neman aure kenan ya kira suhail da sardauna yayi musu?,zasuyi masa rakiya kenan?,su zasu zame masa abokan ango?. Kifa kanta tayi a tafukan hannayenta tana wassafa girman tashin hankalin da takeji cikin zuciyarta,yayin da tsoro ya mamayi zuciyarta,anya zata iya jurewa wadannan abubuwa?,tana tsoron kada wani abu ya samu dan tayin halittar dake kwance qasan mararta......halittar da takejin wani matsanancin soyayyarsa banbanci da abinda taji a cikinsu benazeer,ko don su din bata gama sanin me ake nufi da gundarin abinda kalmar d'a ke nufi ba?,ko don a sannan batasan ciwon kanta ba?.

Ta sake shafa mararta a karo na biyu tana sake addu'ar ubangiji ya tsare duk abinda take dauke dashi. Mamakinta kuma yana sake linkuwa,me zata haifa haka da duk irin tashin hankalin da takeji daga zuciyarta zuwa gangar jikimta bata taba jin wani alama na akwai wani mummunan abu da yake faruwa dashi ba?,bata taba jin alamun girgiza daga zamansa qasan mararta ba?,tabbacin wata ajiya ce ta ubangiji dashi kadai ya barwa kansa sani.

_KWANKWASON JIMINA_*

*_TSUTSAR NAMA_*

*_AMEENATOU_*

*_GUDUN KADDARA_*

_DUKKA AYARIN LITATTAFAN KUDINSU YA KAMA KAMAR HAKA_*

LITTAFI DAYA_400
BIYU_800
UKU_900
HUDU_1200

_IDAN TA BANKI NE ZAKI SANYA KUDINKI A WANNAN ASUSUN_

6019473875
Musaa Abdullahi safiya
Keystone bank

_ANTAYA SHAIDAR BIYANKI ZUWA GA WANNAN NUMBER_

09166221261


*Masu tura katin waya ko vtu kuma kai tsaye wannan number zaku tuntuba*

09134848107

*Maqotanmu kuma al'ummar qasar nijer zaku tuntubi wannan number dinne kai tsaye don biyan naku kudin*

09033181070


*ZAFAFA FAMILY na maraba daku*🫂🫂🫂🫂🫂GUDUN KADDARA
Chapter: B00K O2 PAGE 137
*_GUDUN KADDARA_*
*HUGUMA*


'ya'yanta data tuna ya
bata wani irin qwarin gwiwar cilli da kuma tunkude kowacce kalar damuwa. Ta mige tana garfafawa kanta gwiwa ta soma duba duk wani abu da takeso tana hadawa waje guda.
Girki tayi sosal irin wanda
ta jima batayi irinsa ba, duk da yadda gamshin wasu abubuwan ke neman galabaltar da ita amma tuna benazeer din da batoul kadal yana saka mata qwarin gwiwa.
Koda ta gama bata fidda komai ba ta barshi cikin kitchen din, ta gyara komal yayi mata yadda takeso, sannan cikin kasala ta juya zata fice a kitchen din.
Yana tsaye ya harde
hannayensa yana kallonta, kuma dukkan alamu sun nuna yadan jima tsaye a wajen don har ya jingina sosal da bakin gofa. Suna hada ido ta kauda kai, batason taci gaba da kallonsa bare gazawa ko rauni ya mamayeta.
Ci gaba tayi da takowa, yayin da yaci gaba da kallonta yakuma d'ana mata tarko har zuwa lokacin data iso dab dashi.
Sosai yaso dauke kanshi daga gareta, ya ja numfashi har zuwa cikin hunhunsa amma zuciyar. tagi daidaita daidal da matakin da yakeso. Ba tare daya shiryawa hakan ba, ba kuma tare da yaso hakanta kasance ba ya sanya hannunsa ya fusgota cikin jikinsa.
Sanda ta isa ga
faffadan girjinsa sai taji kamar an yaye mata wani abu dake lullube a girjinta. Sassanyan gamshin nan nasa da a yanzu a duk duniya babu abinda takeso take kuma gaunar shaga... gamshin ainihin fatarsa laushinta da duminta ya mamayeta.
"Kin gama kuka dazun......yanzun kuma kinzo kina girki..... banason dukka wadannan dabi'un
please.... ko meye kikeyi abinda yake cikinki yana sane dashi" kaman jira takeyi dama yace wani abun ko kuma yayi wani motsi sai kawai ta cusa kanta cikin gir jinsa ta fashe da wani irin kuka. Kuka me wani irin sauti daya rudashi ya kuma daki zuciyarsa lokaci guda. Ya dagata daga jikinsa yana rige kafadunta da dukka hannayensa biyu
"What's happening?....mene kuma?" Ba zata iya cewa komal ba don tana ganin ta katse kukan bame yiwuwa bane...... yaga alamun hakan shima, don haka bai sake tambayarta ba ya rigeta da kyau ya fita da ita falon. Saman kujera ya azata
ya koma yasa a gabanta ya zauna dirshan yana kallonta. Bai rogeta ta tsaida kukan ba, saboda yadda take kukan kadal ya tabbatar masa daga zuciya ne.
Bai ce da ita komal ba
sai daya tabbatar dai dai lokacin zuciyarta tayi sanyi
"Me ne kuma ya faru?, ko har yanzun dal na matsa miki?, ina takuraki?, ko kina bugatar wani space dinne sama da haka?" Dukka tambayoyinsa sai suka bata masifan haushi, tama rasa gane masa gaba daya?, me yasa bazai fahimceta ba?, baya ganewa ne?, baya gane yanayinta ne?, anya ba da gangan yakeyi ba?, bayan kuma ya tabbata yafi kowanne mutum iya karantar badininta daga tsakiyar idanunta?.
"Kina da wata matsalar dani ne?, idan akwai ki gayamin zanyi gogarin kauce ma hanyarki...... na miki algawari ne kuma ina gogarin cikawa.... please let me know
idan akwai wani matsala". Dukka maganganunsa suna nuna bai
fahimta komai ba, da gangan ne ko kuma iya gaskiyarsa kenan ita bata sani ba, abu daya ta sani, dukka wadannan maganganun ba su take burin ji daga bakinsa
"Kaine matsala!" Shine abinda taketa son gaya masa amma kuma batasan da wacce siga zata fasa mishi maganar ba.
Bayan hannunta ta saka tana sake goge fuskarta,sai ya sanya dukka hannunsa biyu ya zuba tagumi yana kallonta. Can gasan ransa kaman ya saki mata dariya amma yana cijewa. Ka nema abu da kanka amma kuma kazo ka buge da bawa kanka punishment?, shi kam bai taba ganin wannan abu irin na sultana ba.
Gajeruwar hanya me saugi amma ta maidata doguwar tafiya. Shi din mutum ne daya ci burin samun ingantacciyar soyayya zazzafa
daga wajen matarsa...
....ba
kowacce kalar soyayya ba wadda bata amsa sunanta


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login