Showing 81001 words to 84000 words out of 294767 words
Chapter 28 - Gudun Kaddara Book 2 Hausa Novel Complete
bata amsa tana gyara zamanta
"Kada ki dauka naji haushi ne ko nayi fushi ko kuma zanyi fushin,ko kadan,shekarun da muka dauka abinda nake gani cikin idanunki na saba ganin irinsun......amma yanzun rayuwa tana sauyawa ne,yaranki yaran aliyyu ne,bai kamata kina bari suna karantar wannan harshness din dake cikin idanuwa da kalamanki ba,wani abun bau cancanci 'ya'ya suna sani akan iyayensu ba,wata kakkaifa kuma qaqqarfar dangantaka ne da tafi qarfin kowa yayi shishshigi a cikinta.........zamu je umra cikin satinnan in sha Allah,daga can zamu wuce nijer sai bayan bikin aminata da yasmine zamu dawo,amma immediately saboda maganar gidan tv dincan" kai ta gyada hawaye suna son sauko mata,amma batason tayi kukan,kada ama ta zaci don ta mata fada ne
"Kiyi haquri" tace da ama bayan aman ta miqe,a sanyaye ta waiwayo tana dubanta
"Ke ya cancanci ayita bawa haquri sultana,ba za'a daki mutum a hanashi kuka ba,kawai dai kukan saffa saffa ya dace kayi,tunda kayi imanin ko meye ya sameka ko zai sameka daga Allah ne" kai ta sake kadawa a sanyaye.
Hannuwanta dukka biyun ta sanya ta lullube fuskarta dasu tana sakin wani asirtaccen kuka. Ita kanta ciwon da qirjinta ke mata a kullum ta tuna da ita din wacece ya soma isarta,bataso,tanaso ta rayu da zuciya sakakkiya kamar kowa,ta rasa me yasa ta kasa watsar da komai,ta manta da komai?,ta manta da wanzuwarsa a duniya kamar yadda yayi nesa da rayuwarsu itama ta nesanta kanta da komai da yashafeshi
"In sha Allah wannan zai zama jigon addu'a ta a wannan tafiyar......in sha Allah zan gayawa ubangiji na......zan roqeshi da dukkan sunan da yake amsa addu'a idan an kirashi da su,zan masa magiya ya sake nesantaka daga cikin tunani......daga cikin rayuwata ni da 'ya'yana......zan roqi ubangiji ya kawo silar tsinkewar igiyarka data daureni" ta yiwa kanta wadannan alqawuran.
Tana takawa zuwa dakinta amma tunani ne fal zuciyarta. Duk da rakinta da ake gani.....duk da qin yarda da daukan qaddarar da wasu ke gani kaman ta gaza JARUMA ce sultanar,zama da igiyar wani da bakaso tsahon shekaru babban nauyi ne,ya kamata susan abunyi akai......amma wai ina maina?,INA MAINA YA SHIGA?,YANA RAYE KUWA ANYA?. Da wannan tunanin kadai saida zuciyarta ta buga,idan har ya mutu a ina?,a hannun wa?,waye ya sururta d'anta?.
*_M A I N A_*
Wani irin matsakaicin falo ne dake da wani irin atmosphere mai matuqar daukan hankali da tafiya da tunani. Komai dake wajen tun daga color da yanayin da aka tsarashi da kuma unguwar da ainihin ginin ma yake zakasan ya banbanta ya kuma yi nisa qwarai da kalar tamu rayuwar.
Cikin daya daga cikin luxury sofas dake zagaye da falon yake zaune sosai,irin zaman da zakasan lallai yayi relaxing yadda ya kamata,bashi kuma da nufin tashi yanxu,hakanan da alama ba wani schedule dake a gabansa.
Zabgegen farin ba'abzine,jazur tamkar ka sanya yatsa jini ya fito,dogo me murjajjen jiki,ma'abocin baqar sassalkar suma,tun daga saman kanshi,girarshi,gashin idanunsa har zuwa kumatunsa da aka yiwa sumar wani irin gyara dake zamewa fuskar mazaje ado na musamman me kama da gold a inda akasan daraja da kimarsa.
Yanayin kayan dake jikinsa pajamas ne masu gajeran wando da kuma gajeran hannu,farare tassss tasu masu tsananin taushi da aka saqasu daga audiga mafi tsada da daraja. Dogoyan fararen qafafuwansa da hannayensa dukka lullube suke da gargasa baqa sidik saidai duk yawan gargasar bata hana bayyanuwar murdewa damtse da qafafunsa ba da kuma tsananin da fatarsa ke dashi wanda ke cakude da sirkin ja......duk da a zaune yake structure na jikinsa ya fita sosai a matsayin mutum ma'abicin shiga gym da daga qarafuna.
Babu gilmawar annuri ko kadan saman fuskarsa,hannunsa na dauke da tab dinsa,a nutse kuma yana bin hotunan daya bayan daya yana kalla.
A duniya bai taba jarabtuwa da soyayyar wani abu da baisan asalinsa ko tushensa ba irin yadda ya jarabtu da soyayyar wadannan twins din ba,a duk sanda yake kallon hotunan yaran yakanji tamkar ya cirosu daga jikin hotunan ya gansu a zahiri,yakanji har a ransa soyayyar d'ansa da goumar ya gaya masa sultana ta haifa tana hauhawa a ransa,yaron da ya tabbatar da gangan goumar yaqi bari ya gansa tsahon shekarun,duk wata jafa ko hanya da zaiga yaron goumar din ya tosheta,ya gaya masa.muddin yanasin ganinsa ya dawo gida,ya dawo cikin ahalinsa ya fuskanci ko ma meye. Abinda ya tabbatar goumar bazai fahimta ba a sannan,duk bayanin da zaiwa goumar bazai fahimceshi ba,shi daya yasan meke faruwa dashi,shi daya zai iya fahimtar damuwar da matsalar. Ya zuwa yanzun yana jin haqurinsa ya gaza...... tafiyarsan nan ta qarshe da ta zama cikamakin burikansa tazo masa da abubuwan ban mamaki masu tarin yawa,mafarkinsa yakai ga gaci,ya cimma nasarar rayuwar da a mafarki bai taba tunanin zata isar masa ba......yanajin yakai qarshe,ya kuma tuqe......yana da buqatar yayi gaba da gaba da ahalinsa......ya shirya karbar kowanne hukunci,ya kuma shirya fuskantar su dukka gaba daya. Yanason ganin d'ansa.....yana da buqatar ya bayyanawa d'ansa shi waye a wajensa,amma kuma dukka wadannan abubuwan me ya tanada?.
"Ina da rabb" ya bawa kansa amsa,saboda yayi imani shi daya yasan me yake cikin zuciyarsa,shi daya yasan gwagwarmayar da ya fada shi daya yasan yadd ya rayu ya kawo wadannan shekarun har ya qarasa zama CIKAKKEN MUTUM ya fita a cikakken DR MAINA.
Shawara guda daya tak zuciyarsa ta bashi yaji farinciki da gamsuwa. Yaji a ransa tabbas mafitarsa kenan,ya dangane da dakin Allah yakai masa kukansa kamar yadda ya saba,a wannan karon ya nemi qwarin gwiwar tunkarar ahalinsa,ya nemi jarumtar iya karbar kowanne hukunci da mahaifansa zasu yanke masa
"Harda hukuncin rabuwa da sultana?" Mummunan tunanin da yaso birkitashi ya darsu a zuciyarsa lokaci guda.
Kai ya dinga girgiza da sauri da sauri yana jin kowanne sashe na jikinsa na qaryata yiwuwar karbar hakan. Ya aza dukka qarfinsa ya tankwabe tunanin gefe,ya tattara hankalinsa akan sabon hotunan yaran.
Murmushi ya dinga saki yana binsu da kallo gami da saukesu daya bayan daya akan tab din kamar yadda ya saba. Yana da hotunansu bila adadin dashi kansa baisan yawansu ba,abinda ya sani dai ba'a taba dora wani hoto nasu a personal Instagram account din yaran bai saukeshi ba. Yayi bincike yayi bincike amma ya kasa fahimtar 'yan wanne qasa ne?,ina ne asalinsu?, ba'a taba dora hoton wani abu ko hoton wani ba sai nasu,ba wani abu da aka tana dorawa da zai sanyaka fahimtar su din su waye.
Sai daya gama saukesu tsaf sannan ya sauya wallpaper na iPhone da tab dinsa da sabon hoton nasu kaman yadda ya saba. Tsaiwa yayi yana kallon yadda hoton yayi kyau saman screen din wayar tasa,wani miskilin murmushi ya kubce masa.
Mutanen da suke mu'amala dashi wansunsu da yawa suna tsammanin yaran 'yan uwansa ne,banda sunsan single yake da yawa zasu zaci nasa ne yaran saboda yawan hotunansu da yake dasu,da kuma yawan dorasun da yakeyi zaman dukka screen nasa da yake using dashi. Wasu lokutan shi kansa yakan gayawa kansa ya zaqe da yawa,to amma shi kansa baisan me yasa yake jinsu har cikin jininsa ba.
Knocking da akayi a qofar falon dake waje hade da kada bell ya sanyashi daga kansa,ko ba'a yi magana ko ya duba camera ba yasan waye,ba wanda ke hada masa irin wannan rubdugun knocking da bell din idan ba suhail ba,sai ya aje tab din ya miqe zuwa bakin qofar.
*_KWANKWASON JIMINA_*
*_TSUTSAR NAMA_*
*_AMEENATOU_*
*_GUDUN KADDARA_*
_DUKKA AYARIN LITATTAFAN KUDINSU YA KAMA KAMAR HAKA_*
LITTAFI DAYA_400
BIYU_800
UKU_900
HUDU_1200
_IDAN TA BANKI NE ZAKI SANYA KUDINKI A WANNAN ASUSUN_
6019473875
Musaa Abdullahi safiya
Keystone bank
_ANTAYA SHAIDAR BIYANKI ZUWA GA WANNAN NUMBER_
09166221261
*Masu tura katin waya ko vtu kuma kai tsaye wannan number zaku tuntuba*
09134848107
*Maqotanmu kuma al'ummar qasar nijer zaku tuntubi wannan number dinne kai tsaye don biyan naku kudin*
09033181070
*ZAFAFA FAMILY na maraba daku*🫂🫂🫂🫂🫂*_GUDUN ƘADDARA_*
*H U G U M A*
BOOK 02 PAGE 44
Yana bude masa qofar ya dawo ciki abinsa ya koma inda ya tashi ya zauna. Suhail din ya shigo kunnensa manne da waya yana amsawa. Hannun kujera ya samu ya zauna yana ci gaba da amsa wayar,yayin da maina ke sake ci gaba da kallon fuskokin yaran.
"Haka Allah yake jarabtar bayinsa da qaunar wasu bayin nasa na daban da basusan da zamanka ba" suhail ya fada yana danna wayarsa. A nutse maina ya daga kai yana duban fuskar suhail cike da mamakin furucinsa. Yaune karon farko da yayi magana akan yaran cikin kwantar da harshe da kuma murya. Kusan ko yaushe yafi zabar tsokanarsa da yi masa iya shegen
"Mutumina gwara kayi aure ka haife mana twins dinnan ko fuskokin yaran nan zasu huta" sau tari saidai yayi murmushi kawai ya shafi sumarsa. Har yanzu cikin suhail da ahmad bello da sukewa laqabi da sardauna.....mutanen da suka zame masa shaqiqai kuma makusanta bayan barinsa gida basu taba sanin ya taba aure harda yaro ba.
Wani irin mutum ne shi tun asali me tsananin zurfin ciki,zaiyi wahala kaji qorafi ko wani zance daban a bakinsa. Tun a halittarshi yana da qaranta magana da surutu......a yanzun kuma sai abun ya zame masa ninki.
Akwai yawa yawan mutane da sukayi tsammanin kurma ne shi din,rana ta farko kuma da yayi magana a gabansu a mamakance suke waiwayowa suna dubanshi saboda ranar ne suka fara jin lafazin bakinshi.
Kallon da maina din yakewa suhail ya tabbatar tambaya ce cikin idanun nasa,amma yasan zaiyi wahala ya tambayeshin kai tsaye,don haka ya aza wayar saman qawataccen glass table din gabansa ya goye hannayensa a qirji yana duban idanun mainan
"Na fada soyayya da kallo daya tak aliyyu......I don't know how to explain it....abun kamar shirin film,ganina daya tak da ita ta ban kuma ganinta ba,har yanzu ban mance fuskarta da kuma kamanninta ba.....ina jinta kusa da zuciyata qwarai,bazan kuma fasa nemanta ba a duk inda nake tunanin zan ganta".
Kamar maina ya samu statue haka ya zuba masa idanunshi har ya kammala,suhail din ya fuskanci hakan,yasan halin mutumin qwarai da gaske,ba lallai ya fahimci dukka dogon bayanin nan nasa ba,don haka yaja dan qaramin tsaki yana daukar wayarsa
"Bansan me yasa na zauna naketa maka bayani ba bayan zuciyarka ba'a halicceta don taso diya mace har tayi sha'awar aure ba.......abu daya naga kana yiwa mahaukacin so wadannan yaran da bakasan nahiyar ma da suke ba" ya qarashe maganar yana zuba idanunsa kan wayarsa. Maganar tasa ta sanya maina maida dubansa saman fuskar tab dinsa,sannan ya zame tab din ya ajjiye yana hade hannayensa guri guda
"Me yasa ka yiwa zuciyata wannan fassarar?" Ya jefawa suhail tambayar da wani irin sound me taushi saidai kuma cikin tsakiyar taushin muryar tasa akwai wani irin deep amo me saurin isar da saqo kunnen me saurarensa koda baka shirya hakan ba.
Sai da suhail ya waiwayo ya kalleshi sannan yace
"Ah..... Mr man,nayi qarya ne?,ko iya yadda LAILAH keyi maka tsahon shekaru inajin ya kamata zuciyarka ta narke ka saurareta......amma fa banga alama ba,ba alamun zakayi giving up,ko kunyar sardauna baka ji?" Kai kawai ya kada yana kallon gefansa
"Akwai abubuwa da yawa da baki bazai iya bayaninsu ba suhail......."
"I see" ya maida masa cikin gatse,sai kuma ya tsaya cak yana sake duban maina
"Kai.......if i can remember kamar naga face din yaran nan zuwa na umra last fa?" A nutse maina ya sake kallonsa ba tare da ya motsa ko yace komai ba,saidai cikin qasa da second biyu ya fahimci ba wasa bane irin na suhail,da gaske yake
"Really?" Ya tambayeshi yana dage dukka girarshi biyun
"Yes.....da gaske nake.....kaman a hannun rival dinnan da kaji ina bawa sardauna labari.....a harami ne tabbas" haka kawai ajiyar zuciyar da maina baisan dalilinta ba ta kufce masa,muryarsa so cool yace
"Zuciyata gaba daya ta karkata zuwa umra,ka dubamin yadda zan samu ticket da wuri mana please"
"Kai da ka fini xuwa akai akai ai kaman ka fini sanin masu siyan ticket da wuri ko?"
"Baya nan man din.....baya kusa" ya amsa mishi da alamun zaquwa sosai cikin muryarsa,sannan shigowar Moses wanda ya fito daga kitchen dauke da breakfast tray na ogan nashi yaja hanakalinsu.
Rusunawa yayi ya gaida suhail,suhail din ya amsa masa yana dan janshi da tsokana kadan sannan moses din ya wuce yana shirya dining
"Amma zuwa nayi muji yaushe sardauna zai dawo,mu kammala lissafi saboda nasan kowa yana da nashi plan din ko?"
"Bazan zauna jiran sardauna ba.......kuyi komai koda bananan ba matsala bane,tunda idan na dawo dinma duka duka bazan haura sati daya ba zan wuce paris......next month asibitin zai fara aiki in sha Allah"
"Alright......ba matsala" suhail ya fadi yana lalubar wata number
"Kwana nawa zakayi?" Idanunsa na a rufe,yatsansa guda daya ya dagawa suhail sannan labbansa suka motsa da
"Month". Sai ya maida kansa ga dannar wayar,ya sani duk sanda maina ya shiga irin wannan mode din bai fiyason takura ko yawan magana ba,wannan ya sanya suke dauke masa qafa da kuma yi masa uzuri,duk da basusan taqamaimen damuwarsa ba har kwanan yau.
********Benazeer da batoul ke akan gaba janye da wasu kyawawan qananun qawatattun luggage dai dai su wanda ama ta bada order yinsu musamman saboda benazeer da batoul din tun daga dubai. Kowanne luggage na dauke da sunayensu a jiki da wani ruwan gold din rubutu. Abayar jikinsu ma haka ta kasance,gray color ce da tayi masifar dacewa da yanayin yaran. Kubul kubul dasu babu rama babu mummunar qiba,hutu jin dadi da zallar nutsuwa ta bayyana tattare dasu. Komai dake a jikin dayar akwai jikin dayar,abinda zai matuqar rudar dame kallonsu yayi tsammanin mutum daya ne aka tsagashi gida biyu,don hatta da rufaffen takalmin dake qafarsu na kamfanin D&G ba abinda ya banbantasu dana juna,haka siririn agogon gold dake hannuwansu.
Suna gaba ama da sultana na biye dasu,su dinma abayar ce a jikinsu me matuqar tsada da daukan hankula.
Batasan me ya sanya ba wannan karon tunda suka diro madeena gabbanta suke a sanyaye,tayita neman tsari daga sharrin shaidan koda shike da niyyar hanata ibada wannan karon tuquru kaman yadda ta saba,tunda shi din maqiyin duk wani dan adam ne,ta sanya hannunta ta gyara zaman glass dinta dake taimakawa ganinta,wanda akayi mata tun a wancan lokacin da idanunta suka samu raunin gani. Tun zuwansu Austria ama ta sanya aka sabunta mata shi,aka maidashi na ado sosai,a wancan lokacin qin yin amfani tayi dashi,sai a sannu data fara fahimtar inda rayuwarta ta sanya gaba ta nemeshi,ya zuwa yanzun kuwa tana nan dasu kala kala,dukkansu zaka dauka tana sakasu ne saboda ado.
Ba yadda aba baiyi da ita ya fiddata a duba idanun ayi mata aiki me kyau ba amma ta qiya,tsoro takeji qwarai,tana ganin idan aka tabata ana iya rasa idanun duka ma.
Kamar ko yaushe suna isa masauki tayi wanka taci abinci ta wuce masallaci,tayita zuba idanun ganinsu benazeer da batoul amma bata gansu ba,har ta kammala ta dawo bata gansu ba.
Samunsu tayi cikin dakin sun baje kayan ciye ciye sunata fama,benazeer tafi batoul bawa abun muhimmanci,ita batoul da alama ta gama ta koma kan waya.
Harara ta watsa musu dukkansu sai suka nutsu,bata ce musu komai ba har tashiga ta sake wanka ta fito,sai ta samu dakin wayam da alama sun gudu wajen ama,ta gyada kai tana jan qwafa ta koma saman gado ta nade ta fidda wayarta tana dan duba wasu abubuwa da suka shafi channel din da take sanya ran farawa aiki tare da dakon jiran shigowarsu. A qalla yanzun sun fara girma,shekara hudu cikin ta biyar ai sun san gabas sunsan yamma,ba zata barsu haka siddan su dinga zuwa waje me alfarma irin wannan ba tare da sunsan muhimmancinsa ba. Har ta gama jiran bacci ya saceta basu dawo ba,basu hadu ba sai data tashi sallar asuba,sai data kammala tata sallar sannan ta tashesu sukayi tasu,ta ritsasu tana tambayarsu me ya zaunar dasu jiya?.
Inda inda suka fara mata,daga qarshe batoul ta sanya kuka, benazeer ce me bada haquri,ta