Showing 18001 words to 21000 words out of 294767 words

Chapter 7 - Gudun Kaddara Book 2 Hausa Novel Complete

qasar nijer zaku tuntubi wannan number dinne kai tsaye don biyan naku kudin*

09033181070


*ZAFAFA FAMILY na maraba daku*🫂🫂🫂🫂🫂*_GUDUN ƘADDARA_*

*H U G U M A*

BOOK 02 PAGE 09


Numfashi me nauyi ama ta aje tana sake murza tafin hannun sulatana dake tsakiyar hannunta wanda ya sake yayi laushi sosai

"Ya hayyu ya qayyumu birahmtika astageesu" ta furta qasa qasa tana lumshe idanuwanta. Batasan me qaddara ta tanadarwa gobensu ba gaba daya,saidai ko meye tana fatan yazo ya wuce sa gaggawa,ko meye kuma tana fatan yazo ya wuce musu cikin sauqi.

Hannunta ta saje miqawa ta jawo wayarta tana sake lalubar number wayar maina,har yanzu akwai dacinsa da ciwonsa qasan zuciyarta,tana sake jaddadawa kanta da gayawa kanta ba zata masa ta sauqi ba,ba zata kuma sassauta masa ba dole tayi masa mafi munin hukunci,saboda ba haka takeso ya rayu da nashi iyalin ba,ba haka takeso ya soma gina rayuwarsa data zuri'arsa ba,tana da buqatar tsatso me kyau wankakke daga wajensa tamkar yadda ahali da salsalar mahaifinsa suka kasance.

Babu wani abu da ya canza,har yanzu dai gaya mata akeyi wayar na a kashe ne. Furzar da iska tayi daga bakinta tana sake gayawa kanta duk nisan kiwon da yayi zaije ya dawo ya sameta.

Sai data duba lokaci taga yadda dare yaketa sake nisa sannan ta fidda hannunta daga na sultana,ta miqe ta zare yalwataccen mayafinta da kowanne motsi yake fidda qasaitaccen qamshi. Toilet ta shiga ta dauro alwala don batajin zata iya samun bacci,ta shimfida darduma ta tada salla.

Raka'a shida tayi ta sallame,ta bude ipad dinta tana buda app na qur'ani cikin nutsuwa ta soma karantawa ko zuciyarta zatayi sanyi daga abinda takeji.

Duk bayan kowannw minti sai ta aza idanunta akan sultana da har yanzu jiya iyau. Tayi nisa takai gwargwadon izifi biyu ta sake dora idanunta akan sultana,sai taga hannunta da qafafunta suna wani irin motsi kamar ana jijjigasu.

Da hanzari ta aje qur'anin ta kuma miqe tana nufarta da sassarfa,dab da zata isa inda take sultana din ta soma fusge fusge kamar wadda aljanu suka yiwa mummunan kamu,kafin daga bisani ihu ya biyo baya da dakusashiyar muryarta data fara budewa. Gaba daya gigicewa ama tayi da irin abinda taga sultana din tanayi,sosai take jijjiga tana kuma ihu tare da kiran sunan maina kaika dauka wasu gaggan mayu ne suka kamata. Rungumeta tayi sosai a jikinta gudun kada ta farke dinkin jikinta ko ta jiwa kanta rauni,tana rungume da ita din tana kiran sunanta,saidai bisa dukkan alamu bata fahimtar ma abinda takeyi bare wanda ke kusa da ita,abinda ya sanya hawayen tsananin tausayinta ya sauka a idanun ama. Tanason ta matsa gaban abun kira ta kirayi nurses amma tana tsoron sakin sultana din,cikin taimakon Allah kamar Dr chafa'atou tasan halin da ake ciki sai gata ta turo qofar dakin ita da Dr cha'aibou.

Hannuwanta dake cikin aljihun labcoat dinta ta zare tana nufosu da gaggawa

"Ta farka ne?" Ta tambayi ama tana tayata riqe sultana

"Ta farka Dr amma a mafi munin yanayi" ta bata amsa tana qoqarin dauke qwallar data sauka saman idanunta. Dr cha'aibou ta yiwa magana ya qaraso ta sanyashi ya duba allura cikin drawer din da suka ajjiye dukka tarkacen allura ruwa da magungunan da sukasan ciwonta yana da buqata.

Shi ya hada allurar ya kuma yi mata. A hankali sai yanayinta ya fara daidaita,saidai kuma dukka jikinta ya fara sakewa,kafin daga bisani ta sake komawa wani baccin.

Shuru dakin ya dauka idanunsu dukka a kanta,kafin daga bisani Dr chafa'atou ta furzar da iska tana maida dubanta ga ama

"Dole zata hadu da attack dama irin wanda aka yiwa rape suke haduwa dashi,saboda wannan abun da akayi matan kusan daidai yake da rape a tunani da kuma qwaqwalwarta,tunda anyi shine bisa qarfi da tilastawa,kwanyarta sam batasan meye sahihin ma'anar aure ba bare ta banbance,amma in sha Allah ina saka ran idan ta sake farkawa zata farka babu dukka wadannan abubuwan,ki kula da kyau don ba dogon bacci zatayi kamar irin wannan data fark daga shi ba,ko na turo miki nurse hajja ta tayaki zama?" Kai ama ta girgiza a sanyaye,bata buqatar kowa ya tayata tunkarar wannan,bata da buqatar wani ya aboceta cikin wannan lamarin,tanason ta tunkari komai ita daya da zuciya da gangar jiki irin ta UWA.

Tunda Dr chafa'atou ta fadi haka ta tattara ta dawo gaban gadon ta tare,qarfe biyu qarfe uku qarfe hudu dukka saman idanunta suka wuce,bacci ko gezau baibi ta kusa da ita ba bare ya gwada daukarta,har zuwa sanda sanyin dake bayyana gabatowar asuba ya soma busawa,a sannan sultana din ta fara bude idanunta a karo na biyu,wannan lokacin cikin nutsuwa,saidai kuma tana jin dukka jikinta wani iri babu dadi,sannan daya idon nata kuma yaqi bude mata da kyau yadda takeso. Jin hakan ya sanyata daga hannu da niyyar shafa fuskar taji me ya hanawa idon nata budewa da ganin abu da kyau. Riqe hannun nata ama tayi da sauri tana fadin

"Bari karki goce qarin ruwan" a nutse ta waiwayo gefanta,idanunta suka sauka kan fuskar ama din,a hankali kwanyarta ta fara tuna mata abinda ya faru da ita na qarshe. Tunanin da ya sake hargitsata karon farko cikin hayyacinta,sai wani irin nannauyan kuka me sauti ya kufce mata.

Tana iya tuna sanda maina ya tsiraitata ya yage kowanne tufafi dake jikinta,tana iya tuna sanda hannuwansa ke kaiwa guraren da ita kanta tana kyautata zaton ma qilan bata taba tabawa ba,tana iya tuna sanda lokacin da ya sadar da kansa da wajen da ko kallonsa bata yi duk da a jikinta yake......wani kukan ya sake qwace mata me matuqar sauti fiye dana baya,sai dukka wani qarfin hali da qwarin gwiwar ama ya kwaranye,ta rungume sultana din sosai a jikinta tana lallashinta.

Sun jima a haka kafin kukan nata ya ragu,sai ta koma sauke ajiyar zuciya kafin ta bude bakinta cikin hardewar harshe tace

"Ruwa" sakinta ama tayi ta bude carton din ruwan dake aje gefe ta ciro guda daya ta hado da glass cup din da aka shirya a wata qaramar cabinet a dakin. Ajjiuesu tayi a gefe sannan ta fara qoqarin tadata zaune don taji dadin shan ruwa. Siririyar qara sultana ta saki tana runtse ido saboda azabar da taji na ratsata,kowacce gaba ta jikinta ciwo takeyi mata

"Sannu,daure kisha ruwan sai na saka ruwan dumi na gasa miki jikinki ko?" Ama ta fadi a tausashe tana kallon qwayar idanun sultana cikin matuqar tausayin ta shigo stage din da bai kamata ce ta shigo shi ba.

Tana qananun qwalla tana komai ama ta tada ta,ta zuba mata ruwan ta shanye ta kuma sake buqatar wani,haka ta dinga zuba mata tana shanyewa har sai da tasha rabin gorar sannan tace ta qoshi.

Da kanta ama ta tara ruwa me dumi qwarai ta dawo cikin dakin

"Muje ki wanke jikinki ko zakiji dadi" a hankali sultana ta kauda kanta gefe kadan tana jin zuciyarta kamar zata fashe,ganin ama kawai tuna mata yake da maina da abinda ya aikata mata,wai shin ta yaya zata iya ci gaba da kallon ama?,ta yaya zata iya tubewa ama jikinta tayi mata wanka?. Mutum biyu rak a rayuwarta suke mata hakan,daga bibi sai tanja,batajin akwai sakewa tsakaninta da ama da har hakan zata kasance

"Ina bibi ta?" Ta tambaya cikin rauni ba tare data Kali ama ba

"Suna gida,dare yayi yanzunma asuba ce,amma goben nasan da sassafe zaki ganta"

"Zata yimin idan tazo" tace da ama tana jin kamar harshenta take yanka a duk sanda ta buda baki tayi magana,saboda sam sam a yanzun furta kowacce kalma ta daina bata sha'awa,tafi sha'awar kurumtaka da bebantaka akan komai,batason jin duk wani sauti ko kuma kalma bare ta tuna mata da ALIYYU MAINA.

Tsaiwa ama tayi kawai tana nazarinta,har yanzu taqi waiwayowa bare ta dubeta,sai ta taka a hankali ta isa sashen data maida kanta ta zauna,ta jawo hannunta ta saka cikin nata

"Sultana?" Ta kirata kiran da ya ratsa mata jiki,ta kuma daga kumburarrun idanunta da dayan bai iya gani da kyau ta kalli ama sannan ta maida dubanta qasa

"Inason ki daukeni daga yau a matsayin bintou mahaifiyarki da baki santa ba,inaso daga yau ki sanya a ranki ni ba babar maina bace,ban haifi d'a aliyyu ba,ke kadai na haifa,zaki iya daukata a matsayin mamarki da zaki iya gayawa dukka damuwarki?" Kiran sunan maina din ya saukar mata da wani zafi daga zuciyarta,amma kuma data dubi ama saita tuna cewar.......matar bata taba takura mata ba,bata taba shiga huruminta ba bare ta dameta ko ta hantareta cikin gidan yadda sauran matan kawunnanta suke mata,bata taba mata wata mummunar magana ba,hasalima ko meye zatayi ba ita cikin masu yi mata caaa. Abinda kuma ta gani idanun ama din a sannan yayi kama da abinda d'a yake gani cikin idanun mahaifiya,haka kawai taji wata nutsuwa ta saukar mata tattare da ama din,bata daice mata komai ba,amma kuma bata sake musawa ba,ta kamata ta kaita bandakin ta kuma fara yi mata dukkan wani abu da tasan zai sanya taji dadi cikin jikinta,cikin hikima kuma tana shaida mata ciwukan dake jikinta don kada tayi wani abu me qarfi da zai kawo matsala a wajen.

Abun yayi mugun yi mata banbarakwai tare da daure mata kai,dinki a wajen hanyar fitsarinta?, tabbas kasheta kawai maina yaso yi,bata taba gani ko jin an dinke wajen ba,sai qwalla ta cika mata idanu ta kuma ga gangaro tabi ta saman kuncinta ta hade da ruwan wankan dake a jikinta,dama koda ama bata gaya mata ba tasan wajen ba lafiya yake ba,don ita kadai tasan yadda taji gurin yayi mata,tanajin kamar ba'a jikinta yake ba,zallar radadi da zugin da yake mata ne kadai yake tabbatar mata a jikinta har yanzu yake.

*_KWANKWASON JIMINA_*

*_TSUTSAR NAMA_*

*_AMEENATOU_*

*_GUDUN KADDARA_*

_DUKKA AYARIN LITATTAFAN KUDINSU YA KAMA KAMAR HAKA_*

LITTAFI DAYA_400
BIYU_800
UKU_900
HUDU_1200

_IDAN TA BANKI NE ZAKI SANYA KUDINKI A WANNAN ASUSUN_

6019473875
Musaa Abdullahi safiya
Keystone bank

_ANTAYA SHAIDAR BIYANKI ZUWA GA WANNAN NUMBER_

09166221261


*Masu tura katin waya ko vtu kuma kai tsaye wannan number zaku tuntuba*

09134848107

*Maqotanmu kuma al'ummar qasar nijer zaku tuntubi wannan number dinne kai tsaye don biyan naku kudin*

09033181070


*ZAFAFA FAMILY na maraba daku*🫂🫂🫂🫂🫂*_GUDUN ƘADDARA_*

*H U G U M A*

BOOK 02 PAGE 10


Kuka sosai ta sakarwa ama saboda kalar azabar da takeji sanda ama din ke gasa mata jikinta. Tausayinta ya cika zuciyar ama din fal,kamar ta zauna itama tayita mata kuka ko ta barta kawai taji da ciwukan jikinta,saidai kuma hakan ba zaya yiwu ba,gatan da zata mata kenan hakan kuma shine zai sanyata ta warware da wuri. Itama ama din bata hanata kukan ba,tana ganin idan tace tayi shuru ko kada tayi kuka bata yi mata adalci ba,aika aikar da maina din yayi mata ko uwar mata ce ita sai taji jiki,bare yarinyar da har yanzu rainonta akeyi.

Tsaf ta wanketa ta lullubeta da towel,ta kuma riqeta cikin takatsantsan suka dawo cikin dakin ta tayata ta shirya,ta fidda simple gown cikin kayanta ta bata tace ta saka,sannan ama din ta matsa gaban kayan tea dake jere ta fara hadawa sultanar wadda tunda ta gama shiryawa ta maida idanunta ta kulle. Gaba daya ji takeyi ko duniyar batason kalla,yanzun waye da waye yasan abinda maina yayi mata?,me zata cewa mutane?,da wanne ido zata kalli 'yan gidansu?,qawayenta dama 'yan unguwarsu?,me ta yiwa maina haka daya gwammaci ya kasheta ya huta?,bata taba zato ko tsammanin zata farka ta ganta cikin gidan duniya ba.

"Tashi kisha sultana" ama data gama hadawa ta dawo ta zauna gefanta ta fadi cikin salon lallashi. Bata iya bude qullallun danunta da hawaye ke ratsasu yana fitowa ba ta girgizawa ama din kai. Batajin akwai wani abu me sunan abinci da zaya isha shiga cikinta,sam ita bata sha'awar komai ma koda kuwa ruwa don ya zame mata dole ne ta karba a dazun ta sha.

Duk yadda ama ke tunanin zata lallabeta ta karba tea din amma ta qiya,daga bisani ma daina amsawa ama din tayi,sai ta koma kamar wadda bacci ya dauka,dole ama ta mayar ta aje,saita koma kujerar dake fuskantar sultana din tana nazarinta lokaci lokaci,yayin da wani kaso na hankalinta ya tafi ga ci gaba da karatun qur'aninta ko zata samu sassauci cikin zuciyarta,ta wani bangaren kuma bata gaji ba hakanan bata sare ba da gwada kiran wayar maina,amma dai duka sammakal,ba abinda ya sauya,wayarsa a kashe take.

Kafin a kirayi sallar asuba baccin gaske ya sake daukar sultana,wani irin wahalallen bacci da babu armashi ko karsashi ko kadan a cikinsa. Gyara mata kwanciya kawai tayi ba tare data tasheta ba,ta wuce bandaki tayi wanka ta hado da alwala sannan ta dawo ta tada salla.

Sallamarta daga sallah yayi dai dai da shigowar aba,ta bishi da kallon mamaki,tamkar wanda baiyi sallar asuba ba?,ko kuma a nan cikin asibitin yayi?,tafi zaton hakan,don fuskarsa batayi kama da fuskar wanda ya tashi daga bacci yanzu ba,tafi kama da fuskar mutumin da bai samu cikakken bacci ba.

Da sallamarsa ya shigo,fuskarnan sam babu walwala ko ta gamun gafara sai tarin damuwa da firgici. Kujera yaja gefan gadon sultanan dake bacci,ama tayi qoqarin shafa addu'arta cikin rashin qwarin gwiwa ta soma gaidashi. Gaisuwa daya rak ya amsa mata yabiyo bayanta da tambayar

"Yaya ta kwana?"

"Gata nan alhamdulillah"

"Da sauqi jikin nata?" Ya sake jefawa ama tambayar kai tsaye

"Eh,da sauqi,don har nayi mata wanka"

"Yaushe likita zai shigo?" Ya kuma tambaya yatsunsa harda cikin na juna

"Basa wuce shida na safe" sai ya jinjina kai kawai,bai sake cewa komai ba ya zaro wayarsa ya soma gwada kiran wata number. Bugu biyu ta shiga ya soma magana da wanda ya daga kiran

"Inason ayi cancel tafiyar nan,a maidata sati na sama.....eh yau din gobe dama jibi duka ina da wani uzuri..... okay yayi Allah ya kaimu" ya fadi qasa qasa.

Maganar da taji aba din yanayi shi ya tuna mata da shirin tafiyarta Nigeria wanda da a yau zata yishi,sam wannan abun ya sanya ta manta da komai,sai ta ciro wayarta tana dubawa.

Tarin miscal ta gani na masu aikin gidanta na nigeria,musamman bilki miscals dinta yafi na kowa yawa,sai kuma miscal din yayanta. Dukkansu tasan kowa yanason yaji qarfe nawa ne zata sauka,ta duba lokaci har yanzu a biyar da rabi suke,idan ta kira yaaya din a daidai lokacin yayi safiya da yawa,tunda ko banza me iyali ne shi,don haka saita soma kiran bilki.

Dab da zata katse ta daga tana fadi cikin girmamawa

"Afuwa hajiya,bacci ne ya daukeni bayan na idar da sallah,ina kwana?"

"Lafiya lau bilki"ta amsa mata cikin rashin karsashi

"Yauwa dama inata son naji qarfe nawa zaki sauka don nasan me za'a tanadar miki,don tun jiya an gama kintsa gidan,me gyaran batiran inverter dinnan ne kawai bai iso ba,amma shima yace qarfe bakwai na safiya zai shigo" Boyayyen numfashi ta saki

"Ya taho a nutse,kada kuma ku dora komai saboda ni,tafiyar nan ba yau ba"

"Toh hajiya,sai gobe kenan?"

"Ba gobe ba kuma jibi ba,kawai duk sanda na shirya sake zuwan zai sanar muku"

"To hajiya,Allah yasa lafiya,Allah ya bamu aron rai"

"Ameen" kawai ama ta amsa mata tana gimtse kiran.

Yadda dakin yayi shuru da yawa saita kasa sakewa,haka kawai takejin wani iri,daga ita har aba kalma daya game da ciwon nata hadasu ba wai da zummar tattauna,batasan inda ya dosa ba ko kuma me yake saqawa a ransa ba,sai kawai ta buge da danna wayarta,wanda ita kanta batasan me takeyi ba,kafin daga qarshe ta shiga sms ta soma rubutawa maina gajeran saqo ta number wayarsa

_"Duk inda kake kada ka kuskura kakai dare baka dawo gida ba,wannan din umarnina ne"_ . Abinda ta rubuta masa kenan a gajarce ta tura masa.

Qofar aka taba sannan kuma aka murdata aka bude. Dr chafa'atou ce sanye da kayan gida,kai bazaka taba cewa likita bace ita din. Da alamu sammako itama tayi,kuma duk yadda akayi ta kwana da abunne itama cikin ranta.

Cikin girmama juna suka gaisa,ta gaida aba cikin matuqar girmamawa shima,sannan ta fara duba sultana din tana yiwa ama tambayoyin yadda


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login