Showing 57001 words to 60000 words out of 294767 words

Chapter 20 - Gudun Kaddara Book 2 Hausa Novel Complete

ita sam sam baiyi mata ba,duk sanda ta kalli goumar din ba wanda ke dawo mata a rai sai MAINA. Kafin bacewarsa kusan duk inda zashi goumar na hannun damansa ne tare zaku gansu,shi yasa duk sanda taga gilmawarsa ko taji muryarsa sai ta dinga ganin kamar mainan ta gani.

Shi kansa ya karanci yadda take kauce ma al'amuransa da dama,duk kuwa da cewa a baya abokiyar fadansa ne,kuma abokiyar wasanshi ne,kaf gidan ita tafi kowa zaqewa wajen kiransa da BAQIN BUZU,musamman da tafi kowa kyau da hasken fata a gidan. Muddin za'a yi zancan baqaqe sunansa take fara jefowa koda zaikai mata bugu,amma a yanzun duka babu wannan,tsakaninta dashi gaisuwa ce,sai kuma magana idan ta kama.

"Maza ku hau bayan aunty mimi tayi muku doki" goumar ya fada yana sauke mata yaran bisa wuyanta batoul kuma a cinyarta.

Bata kulasun ba kamar yadda ta saba saici gaba da tayi da zura charge na game dinta. Benazeer tafi batoul rawai kai, hannayenta dukka biyun ta sanya ta kama gashin sultana din da kyau ya riqe tana fadin

"Doci....doci" da gwarancinta. Zafi taji sosai,ta miqa hannu cikin zafin nama ta buge mata hannun tana bata fuska,sai kuwa ta saki kuka sosai,daidai sanda ama ke shigowa da ummin aneesa. Maqociyarsu ce wadda tun ama na zuwa tana komawa nijer suke zumunci sosai. Tasu tazo daya ne saboda kamanceceniyar dabi'u da kuma halaye,hakanan macace itama me matuqar kirki da sanin ya kamata. Kusan duk wani da ya shafi ama yake hulda da ita ya santa da ummin aneesa,saidai ita din shekarunta basu qarasa na ama ba da kadan.

Zaresu daga jikinta dukansu goumar yayi yana fadin

"A'ah baki da gaskiya Benazeer,ya za'a yi ki jawa anty mimi gashi,da zafi fa" a shagwabe yarinyar ke sake bare bakin kuka,musamman data hangi ama na shigowa,sai ta fara dagawa aman hannu.

Sanda ta iso zata dauketa suka hada ido da sultana,wani nauyinta sultanan taji,sai ta miqe a nutse tana kwashe tarkacenta hadi da cewa ummin aneesa

"Barka da yamma,ina yini?"

"Lafiya lau sultana,ya gida,su aneesa har sun gaji da tambayarki,nace ni kaina baki shigomin bare a saka ran ranar visiting ki rakani din muje tare da suketa naci" qaramin murmushin gefan baki ta saki kamar yadda yanzun ya zame mata al'ada,bata fiya maida magana ba,hakanan tafi ganewa ta amsa maka da murmushi kawai. Bata kuwa sake cewa komai din ba har takai bakin qofa,tana jiyo ama na fadin

"Ina take zuwa?,nan nan shopping nace tazo aje sai tace bata zuwa,idan tana da sautu zata bayar" guri maman aneesa ta samu ta zauna,ita daya ce mutum bare wadda bata shafi rayuwar iyalin mayak'i ba da tasan ainihin meke faruwa cikin rayuwar mutanen gidan

"Zaman shurun baya damunta hakanan?" Maman aneesa ta fada tana zama saman kujera

"Shine abinda yaketa damuna aisha(asalin sunan maman aneesa),zaman hakanan bashi yiwuwa,inaso naga rayuwarta ta matsa zuwa wani mataki kuma,bai kamata ta zauna haka ba,ba karatu ba mijin,yaran ma kana kallonsu gasunan gasunan kawai tamkar ba naka ba,makaranta nakeson sanyata,koda bataso dole yanzu taso karatu,inason canzata daga ainihin sultana zuwa wata sultanar,kuma nasan babu abinda zaiyi wannan aikin da wurwuri irin ilimi,nigerian turkish zan kaita" ama ta qarasa fadi alamun damuwa suna bayyana qarara saman fuskarta.

"Wanne irin Nigerian Turkish kuma?,kin manta da school din su aneesa ne?" Maman aneesa ta fadi tana duban ama. Kai ama ke jinjinawa sosai

"Oh yes,yes,yes,anyi haka,tabbas kamar makarantar ita zata dace da irin sultanar"

"Qwarai ma kuwa,kin manta taurin kan humeir da yadda ta dauko fara bani wahala,yanzu humeir zakice ita ce?"

"Gaskiya,gaskiya,nayi mamaki wai humeir ce harda azumin tadawwu'i" dukkansu sai suka sanya dariya,saboda sauyawar humeir din ta musu dadi qwarai,don abune da basu taba tunanin faruwarsa ba,amma sai gashi daga fara zuwan yarinyar makarantar tearm guda kacal ta sauya.

Sosai suka tattauna akan makarantar da yadda take matuqar tasiri wajen canzawar halaye da kuma dabi'un yaro

"Duka duka sati biyu ya rage suyi hutu,idan sun dawo kuma hutun na wata daya ne za'a debi sabbin dalibai"

"Shikenan,faduwa yazo dai dai da zama" ama ta fadi tana jin dadin shawarar. Ayadda taga makarantar tayi tasirima rayuwar yaran ummin aneesa din,sai taji tana da imani da yaqinin dari bisa dari sultanarta zata sauya,zata koma kalar sultanar da take da buqatar gani,zama koma uwa abar alfahari wa 'ya'yanta.

Sati biyun yaran ummin aneesa suka dawo,suka kuma fara gudanar da hutunsu,a wannan zuwan ama ta sake saka idanu kan dabi'u da halayensu,sai ta sake samun gamsuwa dari bisa dari sultanan ta samu wajen karatu. Kai tsaye ta shaidawa aba,da farko cewa yayi

"Amma kina ganin me yiwuwa ne mu dauketa mu kaita har kano makaranta bayan bata da kowa can?"


*_KWANKWASON JIMINA_*

*_TSUTSAR NAMA_*

*_AMEENATOU_*

*_GUDUN KADDARA_*

_DUKKA AYARIN LITATTAFAN KUDINSU YA KAMA KAMAR HAKA_*

LITTAFI DAYA_400
BIYU_800
UKU_900
HUDU_1200

_IDAN TA BANKI NE ZAKI SANYA KUDINKI A WANNAN ASUSUN_

6019473875
Musaa Abdullahi safiya
Keystone bank

_ANTAYA SHAIDAR BIYANKI ZUWA GA WANNAN NUMBER_

09166221261


*Masu tura katin waya ko vtu kuma kai tsaye wannan number zaku tuntuba*

09134848107

*Maqotanmu kuma al'ummar qasar nijer zaku tuntubi wannan number dinne kai tsaye don biyan naku kudin*

09033181070


*ZAFAFA FAMILY na maraba daku*🫂🫂🫂🫂🫂


*_GUDUN ƘADDARA_*

*H U G U M A*

BOOK 02 PAGE 30


"Yaran ummin aneesan fa?,suma ba kano din suke tafiya ba?,don Allah aba kada ka hana,kada kuma ka bari ta gane zucoyarka tayi rawa akan al'amarin,muna da buqatar mu.maida sultana ainihin mutum,aikin da maina ya gagara yi inaso na aiwatar masa,koda baya raye na tabbatar hakan zai bashi sukuni cikin kushewarsa" ta qarasa fada zuciyarta na yin wani irin nauyi. Shuru yayi tun daga lokacin bai sake cewa komai ko ya nuna baiso din ba,hasalima da dukka kudinsa ya bayar akayi komai daya dace,itakam sultanan ma batasan meke faruwa ba,don rayuwar kebe kai tafi komai yi mata dadi a yanzun,sai ayi abu cikin gidan sau babu adadi amma bata sani ba.

K'arfe tara na dare ta tura qofar dakin sultana din ta shigo. A lokacin benazeer na rungume a kafadarta tana taba rigima,batoul na cinyar aba tana bacci,don ita din ba kasafai ta fiya rigima ba.

Da shanyayyun fararen idanunta ta waiwayo tana duban ama,kafin ta janye idanun nata ta dorasu akan benazeer da aman ta kwantar mata saman gadon,sai kuma ta dauke duban nata daga kan benazeer din ta sake maidawa fuskar ama

"Hala shirin kwanciya kikeyi?" Ama ta tambaya tana sake qarema sultanan kallo. Ta sauya sosai,har yanzun dai batayi qiba ba,amma jikinta yayi kyau kai sai ka rantse bata taba sanin d'a namiji ba bare ayi zancan haihuwar 'yan biyu,wannan kyawun nata ya sake fita da wani irin sirri na cikar cikakkiyar mace,idanunta sun sake girma da haske,hatta da idonta dayan da ya samu dan matsalar da sai ta sanya masa glass babu lallai kai ka fahimci hakan saboda yadda suma suka bude fes dasu kaman dayan. Gashinta ya wani sake cika kamar kowacce gaba ta jikinta ke fara nuna girma na asali bawai girman da samuwar ciki ya tilasta zuwansa ba.

"Eh ama" ta amsa mata tana bude man shafawarta sannan ta koma ta zauna saboda ta fahimci da magana ama din ta shigo.

"Ya kamata,sultana"

"Na'am ama" ta amsa mata a sanyaye tana fatan ba wani sabon abu bane kuma ya taso

"Kinsan rayuwa babu abinda yakai ilimi dadi da daraja,babu kuma abinda yakai ilimi maidaka cikakken mutum haka ne?" Kai ta gyada a sanyaye karo na biyu

"Mun yanke shawara,in sha Allah nan da sati biyu masu zuwa tare zaku wuce kano tare da yaran ummin aneesa,zaki fara makarantarsu,saidai mun roqi alfarmar koda daga j.s3 ne idan hakan ta samu" ama ta qarashe fadi tana zubawa sultana idanu. Kai ta jinjina,ita a yanzun batajin akwai wani abun da zai taba mata zuciya,ko ya sosa mata rai,batajin akwai wata tsana ta wani abu cikin zuciyarta da zatayi girman tasirin wutar tsana da qiyayyar dake ruruwa yanzu haka a zuciyarta

"Allah ya kaimu" sultanan ta fadi a sauqaqe kai tsaye kuma ba tare da taji komai cikin zuciyarta game da batun ba. Sake kiran sunanta ama tayi a karo na biyu,sai ta kuma amsawa tana duban ama

"Ki daure kiyi karatu sultana,banason wadanda suka sanki a shekarun baya su sake ganinki dai still yadda kike,ba wani ci gaba,babu kuma abinda ya canza daga gareki" murmushin qasan zuciya ne ya subuce mata,tadan murmusa ta yadda ita kanta ama din ba zata gani ba,ita wai meye ya ragewa rayuwarta?,bata da MANUFA burika da fata na rayuwarta dukka sun jima da bizne kansu cikin qarqashin duk wani buqatu na rayuwarta gaba daya.

*********K'arfe takwas na safiya suna qofar gidan ama,yaran ummin aneesa da suka kasance 'yammata kamarta a shekaru ne. Anata zuba kayansu cikin mota,sunata kuma kai da kawowa cikin 'yar hargowa da rigingimu nasu irin na sako da sako.

Daga gefe daya sultana na tsaye kawai,jingine jikin motar. Sanye take da uniform da yayi matuqar karbarta ainun,idanunta saye cikin farar kwalbar glass wanda ya zame mata tamkar ado,ba zaka taba tunanin lalurar idanu bane suka sanyata sakasu,sun amsheta ainun,sun kuma qarawa zagayayyun idanunta wani irin kyau da kuma kwarjini matuqa.

Sai da aka gama komai tas sannan ta buda motar ta shiga,ama ta shiga gaba dauke da BATOUL, goumar ya buda gidan baya dauke da BENAZEER yanata cakularta da wasa tana qyaqyacewa da dariya. Shigowarsa gefanta ya sanyata daga shanyyun kewayayyun idanunta ta kalleshi dasu. Kusan tare suka kalli juna,wannan yayi sanadiyyar haduwar idanunsu guri guda.

Hasken fararen idanunta ya dakeshi sosai,yayi saurin zare idanunsa shima yana ci gaba da tsokanar benazeer suna sake cikawa sultana kunne. Basu kuma bar kunnuwannata sun huta ba har suka isa airport. Wannan karon su aneesa nata murna,sun huta dogon zaman mota daga abuja zuwa kano,tafiyar jirgi ce cikin mintuna qalilan zasu isa.

Basu kuwa dauki lokaci ba,duka duka mintuna qalilan suka sauka a filin sauka da tashin jiragen sama na malam aminu kano,daga can din kuma suka samu daya daga cikin motocin dake zirga zirga cikin airport din ta daukesu zuwa HASSAN IBRAHIM GWARZO.

****Motoci da dalibai fal qofan makarantar. A irin wannan lokacin akan samu cikowar mutane irin haka da ababen hawa.

Cikin lokaci qalilan suka isa office na shugaban makarantar,ama tayi dukkan abinda ya dace goumar yana tsaye yana rungume da twins. Daga goumar din sai ama,su biyun kacal sukafi sakewa dasu fiye da kowa,sun gane goumar sosai kamar yadda suka gane ama din.

Tattaki suka yima sultana har zuwa hanyar da zata sadata da bangaren mata. Iya ama da su benazeer,don goumar tun daga can mararrabar section din maza da na mata suka dakatar dashi. Haka tsarinsu yake,kome alaqarka da mutum ba zasu tabi bare ya tsallake wannan shingen ba muddin ba section din jinsinka bane.

"Allah ya bada sa'ar karatu sultana,shikenan sai munzo visiting?" Ama ta fadi tana duban fuskarta. A sanyaye ta daga kai ba tare data dubi ama ba,hankalinta yana rarrabuwa akan yadda rayuwa zatazo mata cikin makarantar. Ta gani komai da ama ta shigar ta shigar dashi ne dai dai da na kowacce yarinya matashiya budurwa.

"Shikenan,Allah ya bamu alkhairi" ama ta sake fadi,sai sultana din ta kuma jinjina kai kana ta fara taku daya biyu zata wuce ciki,saidai kuma batasan dalili ba,can qasan zuciyarta takejin wani irin nauyi yana mamayarta,kamar akwai abinda takeson aiwatarwa,kamar akwai abinda zuciyartata keso wanda ta gaza yi mata shi*_GUDUN ƘADDARA_*

*H U G U M A*

BOOK 02 PAGE 31



"sultana" taji sautin muryar ama na kiranta. Waiwayowa tayi suka hada idanu,a hankali sai ta sauke idanunta akan batoul da benazeer. Sauko da batoul din ama tayi ta miqa mata ita,takowa tayi a hankali ta qaraso gaban ama din,hannayenta ta sanya duka biyun ta karbeta. A hankali ta dora idanunta saman fuskarta, fuskokinsu suka gauraya waje daya,sai yarinyar ta sakar mata dariya tana qoqarin kamo eye glasses dinta. Batasan ya akayi ba saita tsinci kanta da sakin wani siririn murmushi,ta saka nata hannun ta riqe dan qaramin hannunta. Daidai lokacin benazeer ta fara gwaranci.

Sake daga kai tayi ta kalli benazeer din,hannu take miqa mata tana zillo kamar zata fado,maida BATOUL tayi daya side din ta amshi benazeer,sai ta hadasu dukka su biyun ta rungumesu a qirjinta ba tare data shiryawa hakan ba. Luf sukayi daga ita har su,yaran sunyi shuru cikin qirjinta kamar wadanda sukasan meke shirin faruwa,kamar wadanda sukasan tana shirin yin nesa dasu ne har na tsahon watanni uku. Cikin qirjinta taji zuciyarta tana bugawa da kyau,sai ta maida idanunta kawai ta lumshe.

Idanun itama ama ta lumshe tana jin wani yanayi yana sauka a zuciyarta,tsakanin uwa da d'a sai rabbussamawati,koda kuwa dan na shege ne muddin akwai zuciya a qirjin uwar. Ta bude idanunta sanda sultana ke miqa mata su,sai dukkansu suka riqe gaban hijabin sultana din suna qyuyar sauka. Murmushi hade da hawaye ne suka subuce ma ama din,hakanan sultanar itama hawayen ne maqale a kuncinta. Cikin dabara da waqar da ama keyi musu ta samu ta amsosu,saidai har suka bar wajen idanuwansu da hankulansu yana kan mamarsu.

Ta shiga dakinsu,ta kuma sameshi cikin tsafta da tsari. Yanayin dakunan da yadda ta samu daliban ciki kawai ya soma gaya mata inda tazo din waje ne na tarbiyya,waje ne na cikakken karatu,waje ne kuma bana wasa ba. Kintsattsun matasa kamarta,kowacce ta karbeta hannu bibbiyu,hakanan itama tayi iyakar bakin qoqarinta a ranar tata ta farko ta sake musu an gaisa da kyau,daga nan kuma ta kama kanta ta soma sabgogin gabanta da qoqarin fahimtar komai.

*_3:45 am_*

Tsakiyar baccin da bai jima da daukarta ba saboda tsananin tunanin da har yau batasan meye qarshe da mafitarsa ba taji ana tashinta cikin nutsuwa. A hankali ta buda idanunta tana qarewa dakin kallo, tunaninta ya dawo fes yana tuna mata a inda take din a yanzun. MAKARANTA kwanyarta ta tuna mata.

Gefan da ake tabata din ta waiwaya. Tana zaune riqe da uniform dinta a hannu tana kallonta,fuskarta qunshe da murmushi. Fatima ahmad yusuf idan bata manta ba shine kiran data kirayi kanta dashi sanda suke gabatar da junansu. Kusan tafi kowa kusa da ita ita da ameena aleeyu dake maqwafataka da ita ta hannun hagunta.

"Ki tashi,lokacin sallar asuba ya kusa,mu samu mu gama komai a nutse kafin captain ta fara counting" ta fadi mata tana ci gaba da harhada abubuwan da zata dauka. Idanu da baki sultana ta saki tana kallonta,saita maida dubanta ga qaramin agogon dake dakin. Sallar asubahin tun yanzu?, counting na meye za'a fara?. Bata ida wannan tunanin ba taga shigowar ameena aleeyu tsaf cikin uniform. Binta tayi da kallon mamaki,ko hudu na dare bai cika ba? ,A wannan daren me kuma sukeyi su din haka?.

"Qarasa muje muyi alwala da wuri kada mu samu cinkoso muyi shigen ta jiya" ameena ta fada tana zama sanya hijabinta sannan tace

"Kin tashi lafiya sultana?,mamaki nasan kikeyi ko?,dukkanmu haka mukayi kaman naki dinnan farkon zuwanmu makaranta,dole kowanne daliba ya tashi da wuri yaje yayi alwala ya wuce masallaci sallar asuba,muddin ka makara kuma.....hmmm akwai qura,ni da fatima ba zamu iya tuna randa muka makara din ba,saboda muna cikin dalibai masu kiyayewa" kai ta jinjina tana sake binsu da kallo kamar baqin halitta,kawai saita juya a hankali ta maida kanta ta kwanta tana lumshe idanuwanta hadi da cewa

"Kuje zan taho" tare suka juyo gareta

"Karkiyi haka,da zaki taso mu wuce zaifi fa" kanta ciwo yake sosai,don ko baccin awa biyu cikakke batayi ba,runtse idanun ta sakeyi tana jin kamar damunta kawai sukeson yi

"Kuje kawai karku damu" shuru sukayi na wani lokaci suna duban juna,saboda sunsan horon da takeson jefa kanta din ba mai dadi bane,abune da kowanne dalibi cikin makarantar ke qoqarin kaucewa. To amma ba yadda suka iya kasancewar dukkansu ba masu son shishshigi ko hayaniya bane sai suka qyaleta.

Duk da baccin bai dawo ya dauketa ba gaba daya amma ya soma fusgarta ta soma jin hayaniya sama sama,kowacce daliba tana tashi gami da kwasar uniform dinta a gurguje tana sanyawa. Idanunta ta qarasa budewa tsaf sanda wata kakkaifar murya ta soma fadin

"One......two...... Three......" Jin kamar ana guje guje ya sanyata bude idanun nata. Dakin duka ya hargitse,kowa takai takai yakeyi wajen qoqarin saka uniform sannan kuma ya fice da gaggawa kafin a kammala qirgen. Haka kawai tsoro ya dirar mata,ta sauko da sauri cikin firgicin wanne abune me muni zai iya samunta idan suka fice suka barta a nan,sai ta lalubi hijabinta ta zura tabi bayansu ba tare data tsaya sanya uniform ba.

Da gudu gudu wasu ke nufar gate dinsu na farko,tun kafin su isa ta jiyo shigen wancan muryar tana counting itama,saidai dab da zasu isa me lissafawan taja qofar ta bame,sai gani sultana tayi dalibai suna zubewa bisa


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login