Showing 213001 words to 216000 words out of 294767 words
Chapter 72 - Gudun Kaddara Book 2 Hausa Novel Complete
a daren data tashi donyin alwala tayi sallah kaman jiya,kawai saita samu kanta da fashewa da kuka,kukan da ita kanta ba zatace ga dalilin zuwansa ba,kawai tana jinta cikin wani matsanancin kadaici da batasan dalilin samuwarsa ba,tana jinta a matsayin wata gajiyayya da bata da sauran qarfin jiki dana zuciyarta,jikinta da zuciyarta dukka ba dadi,tana jin kamar an toshe dukka wasu qofofinta na walwala.
Washegari saita tashi a sukurkuce gaba daya,nutsuwarta qalilan ce,damuwa tana neman yi mata yawa,tana jin wani mugun kadaici baya ga kasalar data zanyataya gaba,sai ta dinga jin kamar ita daya ke rayuwa cikin duniyar ma gaba daya ba cikin gidan ba. Abinda tayi noticing shine,tamkar rashin zuwansa gidan cikin kwanaki ukun yana damunta,kamar tana ankare da kowanne motsi nasa kenan indai rashin zuwansa gidan ya dameta?,bataji wani ko wata kuma koda sau daya ya ambaceshi cikin kwanaki ukun ba,suna sane da dalilin rashin xuwan nasa kenan?,ko kuma suma basu sani ba?,sun watsar da lamarinsa ne kamar yadda ya watsar da nasu?. Wani lokaci sai tayita kallon benazeer da batoul,kamar tanason yin wata magana data shafi daddynsu da su,sai kuma wata zuciyar ta gargadeta
"Koma ina yaje ya daina xuwa gidan yana sane.....akwai mahaifiyarsa akwai yaransa a ciki kin manta?" Abinda yakan xo mata akai kenan,sai ta share maganar tayita qoqarin dora walwala saman fuskarta.
A satin da ake fuskanta program dinta zaiyi magana ne kan wani yare dake qasan Ethiopia,dukka sai abubuwan suketa zuwa mata a slow,tana kadaice kanta don ta samu damar yin aikin,amma kuma sai hakan ya zame mata kamar wani sabon tashin hankali,don duk sanda ta kadaice da zummar tayi aikin sai tunaninsa tare da wani mutuwar jiki ta saukar mata,saidai ta tattare komai ta bawa tunanin lokacinsa,sannan ta samu da qarfi da yaji tadan taba aikin kadan.
*********Kwanaki biyu suka rage ranar program ya zagayo,gashi kuma bata tsinana wani abun azo a gani ba. Tana kyautata zaton muddin satin yazo ya sameta a haka sam ba zata iya bada abinda ake buqata cikin program din ba,don haka ranar wani alhamis,qarfe takwas na safe ta shirya da zummar tafiya office,qila acan din idan tana ganin gilmawar mutane ta samu karsashin hada aikinta. Uwa uba kuma ga dioura da take da tabbacin zata taimaka mata.
Qarfe tara saura ta yiwa ama sallama,tayi kyau cikin wata wata doguwar rigar Indonesia me launin baqi da adon sea green,ta fita sosai a muslim girl dinta,amma idan ka ganta zakayi tsammani daya daga cikin musulman wata qasar da bata shafi Africa bane. Ayana na zaune take ficewa daga falon,taja numfashi tana dauke idanu daga kan sultana din. Tana bala'in kishin kyau da ajin da Allah ya zubawa yarinyar,ta rasa da wacce hanya zata doke tauraruwarta gaba daya?,tana ji inama ace itace sultanar,wai mema sultana ta rasa a rayuwa?,wannan itace tambayar da ayana kullum ke yiwa kanta,sai kuma qwaqwafin son jin tsakaninta da yaa maina din akwai aure ko babu?. Ama nada tsare gida idan taso, mutum ce kuma mara son tsurku ko mutum ya dinga shiga lamuran da basu shafeshi ba,wannan ya sanya take shakkar sako mata maganar.
Bismillah tayi tana xura muqulli don bude qofar motar,sai idanunta suka fada kan gidan. Daidai lokacin laila daketa knocking gami da danna bell ta gaji,ta juyo a hankali tana saukowa daga saman 3step din dake qofar gidan. Idanu suka hada da sultana,har cikin ran laila sai data ji wani abu. Tana da wani irin aji da kyau dake qara mata kwarjini,tana kishin halittar sosai,duk da har yau batasan meye ainihin alqarta da haidar ba,to amma a yanzun da takeson ganin yaa haidar din da yayi mata batan dabo kusan kwanaki shida kenan,tana jin ita kadai zata tambaya inda yake din.
Tun a kallon farko sultana din ta janye kallonta daga kanta,batasan me yasa take mugun qin jinin yarinyar ba,a qalla batajin haka akan ayana,nata abun baikai har can ba,bata sani ba ko don ayana din tana da nasaba da jinin ama dake da kima a idanunta.
Taji takun takalmanta masu tsaho,kuma jikinta ya bata tana nufo direction dinta ne,don haka adan gaggauce ta qarasa bude motar ta shiga ta maida murfin ta rufe. Dab da laila din zata qaraso wajen ta dage dukka glass din windows dinta,ta tayar da motar. Tana tsaye daga gaban motar tayi reverse ta bata wuta tana barin wajen.
Ta madubin gaban motar take hangenta,tana tsaye tana bin sawun motar da idanu kafin ta maida dubanta ga motar gaba daya. Idanunta ta janye tana jan wani mugun tsaki kamar zata tsinke harshenta. Karon farko taji wani mugun haushin maina ya kamata. Na meye zai dinga bari wai mata suna bibiyarsa?,inda ya kame kansa hakan zata faru?.
"Kinfi kowa saninsa ai.....ayana jininsa ne ba yadda zaiyi da ita,wannan kuma itama akwai tabbacin ba banza ba ya rangwanta mata har take samun daman biyar sawunshi" wata zuciyar ta karanta mata hakan cikin nutsuwa
"To meye alaqarsu?" Ta yiwa kanta da kanta tambayar
"Allah masani" zuciyarta ta sake bata masa. Tambayar data rasa amsar tata tafi tsaye mata a rai,ta sake jan tsaki wani tsumammen bacin rai da batasan na meye ba ya taso yana shirin rufeta. Bacin ran ganin laila?,ko bacin ran ganin laila din tazo nemansa?,ko baqincikin rashin ganinsa na tsahon kwanaki ba tare da tasan ina ya tafi ba?,duk batasan wannan amsar ba,tambayoyin da wasu daga cikinsu ma bata yarda da wanzuwarsu cikin dalilan sauyawar mode dinta ba.
Iska laila ta furzar tana jin zafin kanta da kanta data dosheta ma,dama tun ganinta na farko da ita ya kamata ace ta fahimci zatayi girman kai,irin kyau da take dashi da tasirin ilimin daya bayyana a jikinta kawai ya isheka ka fahimci zatayi ji da kai. Ta kalli kanta daga saman har qasa. Yau ita laila bello wata mace ta disga?,laila bellon da kaf fadin abuja duk diyar da take jin kanta ta isa mace neman qulla alaqa takeyi da ita?.
"Laifi nane" ta bawa kanta amsa.
Maida kallonta tayi tana nazarin gidan data fahimci kamar daga nan ta fito. Suhail yace mamanshi a nan gidanta yake,saidai kuma shi maina din bai taba zancan da ita ba bare ya bata fuskar zuwa,haka kawai taji hankalinta yana bata a wannan gidan take,don haka sai kawai ta fara takawa tana nufar gidan.
Tana driving din amma gaba daya hankalinta yana wani wajen,wannan ya sanya kafin takai gidan tv din sai da akaci tararta a hanya saboda sabawa doka da tayi. Koda ta isa ma kulle kanta tayi a office,aqalla saida ta dauki awa guda tana sauraren qur'ani cikin wayarta,tayi wasu daga cikin addu'o'i sannan ta samu confidence. Ta daga waya ta kira dioura ta gaya mata ta shigo,tana kuma buqatar taimakonta
"Gani nan madam" ta gaya mata da rababbiyar hausarta.
Ama da tanja suna kitchen ama din tana duba kayan cefanen da yayi qasa da wanda ya qare,don yau goumar zai shigo Paris,shi daya ne kuma ke iya mata siyayya yadda takeso,don ita kanta bata jurewa zuwa supermarket,kasancewar ta saba,a nijer da Nigeria gaba daya komai ana kawo musu ne daga manyan supermarket n can,saidai ayi bill ta biya.
Ayana ce taji qaraurawar,ta sauke wayarta wadda take turawa maina saqo ta manhajar watsapp duk da bata da tabbacin samun amsa,don bai fiya bashi muhimmanci ba,ta miqe da saurin taje ta dawo ta qarasa ta tura masa.
Kallon kallo sukayi a tsakaninsu na wasu sakanni,dukkansu hakanan suka ji basu yarda da juna ba,sai laila tayi qoqarin sake fuskarta tana kallon ayana don taga alamun akwai alamun jinin haidar a jikinta
"Ama tana nan?" Kaman ba zata amsata ba,sai kuma tace
"Tana ciki" ta saki qofar tana juyawa ciki ba tare data sake kallon laila ba. Itama bata damu ba ta sako kai tana biye da ayana din.*_GUDUN ƘADDARA_*
*H U G U M A*
BOOK 02 PAGE 114
Batayi mata tayin zama ba,hakanan bata kuma cewa da ita komai ba ta koma ta zauna tana ci gaba da danne dannen wayarta.
Dan kallonta kadan laila tayi tana mamakin wacce 'yar wulaqancin still ta sake haduwa da ita?,kodai dukka jininsa haka suke da miskilanci irin nasa?,a haka zata rayu a cikinsu?,ta yiwa kanta tamabayar.
Sanda ama ta fito idanun akan laila dake tsaye ya fara sauka
"Baquwa garemu?" Ama tayi tambayar saboda kallo da laila kebin ama din dashi. Da sauri laila ta saki tunanin da takeyi tana sakin fara'a,koda ba'a gaya mata ba wannan din tabbas itace uwa ga abun sonta,itace ta haifa yaa haidar,kamanninsu sun nuna haka,saidai kuma abinda ya bata mamaki,kwata kwata shekarun ama basuyi kama da na matar da zata aje d'a kaman maina ba
"Baquwa ce ama" sai kuma tadan sunkui da kanta.
"Ayana ya zaki bar baqo a tsaye?,ga guri zauna" ama ta fadi tana nunawa laila waje. Kame kame ayanan ta soma yi,tasan halin ama din sarai akan hakan zata iya saba mata
"Na dauka ta zauna ai" harara ama ta jefa mata,saita samu waje ta zauna tana fuskantar laila.
Tana dan sussunne kai wanda ya sake haskawa ayana lallai da wani abu,abinda ya sake tunxurata ta gyara zamanta taji da wacce uwar tazo,saidai kuma waya take dannawa kaman batasan me akeyi cikin falon ba. Bayan gaisuwar shuru yadan biyo baya
"Ban gane fuskar ki ba yammata" ama ta fadi sanda tanja ta gama ajjiyewa laila ruwa da lemo
"Laila ce ama......qanwar sardauna" murmushi aman tadan saki,suka sake gaisawa sai kuma wani shurun ya sake shigowa.
Ama din bata yau bace ba kuma ta jiya ba,sannan ita din uwace data taso gidan dake da yara mabanbantan halaye,yara irin maina da sultana,kuma kowanne take iya fahimtar yaren da yake magana dashi,bawai iya maganar baki kawai ba
"Kina lafiya ko?" Ama ta sake tambayarta
"Lafiya qalau,nazo inata knocking ne sai kuma naji gidan shuru,kwana wajen takwas bamuyi waya da yaa haidar ba,ban kuma ganshi ba" a fusace ayana ta daga kanta,abinda ama ta riga ya ganta don kusan tana bangaren da dole aman zata gani,amma saita kawar da kanta ta tattara hankalinta akan laila.
"Ayyah,tafiyace ta taso masa"
"Okay,ban sani ba wallahi" ta fada tana dan jan mayafinta kadan,daidai nan ayana ta miqe tana wucewa zuwa daki da wani irin saurin da ya sanya dukkansu suka bita da kallo. Sai data bacewa ganinsu sannan ama ta maida dubanta ga laila
"A wacce makaranta kike karatu cikin Paris din?" Dan daga kai tayi ta kalli ama
"Ba karatu nakeyi ba" sai ama ta dage girarta
"Ayyah,me kike a Paris to ke kadai?" Dan daburcewa laila din tayi,gabanta ya dinga faduwa,kada dai ta fassarata da wata ma'ana ta daban,ita dake buqatar yabo da soyayyarta
"Hutu nazo.....sai na samu aunty na bata dawo ba ita da mijinta......amma jibi nake kyautata zaton zasu dawo,ina can masauki ina jiransu......ya haidar ne ya kamamin safe place" boyayyen numfashi ama din ta saki,bata tantama akan tarbiyyarsa da kamewarsa,amma dan adam ne shi kaman kowa,shaidan kuma game da mace bashi da amana sam
"Yayi qoqari......amma a yadda yake da kishin nan ko 'ya'yansa bazai kamawa masauki ba bare sultana matarsa,aikin gidan Tv din ma da takeyi na tabbatar temporary ne kafin ya hutsance mana" ama din ta fadi babu damuwa sam saman fuskarta
"Mata?,yaya?" Laila ta samu kanta da fadi tana duban ama kai tsaye. Murmushi ama din ta saki,don ta samo amsar abinda takeson sani,ta kuma isar da saqon da takeson isarwa din duka lokaci guda
"Eh,yana da tsananin kishi tun yana qanqaninsa" wuta ce ta daukewa laila tsaf.......duk wani gaba da zata sadar da fitar furuci daga bakinta ya dauke,shurun yaci gaba da wanzuwa a falon,yadda bata sake cewa komai ba haka ama bata sake magana ba,saita maida kanta ga wayarta tana amsa kira.
Dole.laila ta miqe tana mata sallama,sai ama ta tsaidata ta sanya tanja ta dauko mata wata leda a daki. Lace ne me matuqar tsada cikin irin wanda take yin order,tarkacen turaruka da hijabai masu kyau ta hada mata,kayan ba masu yawa bane amma kudinsu suna da nauyi,ita kanta lailan ta sani.
"Na gode" laila ta fadi a sanyaye
"Ki gaida gida" ama ta furta cikin fara'a ta taka mata har qofar falon.
Maida qofar tayi ta rufe tana furzar da iska,saita dawo saman kujera ta zauna hankalinta ta lulawa ga tunani. Dole ta girmama laila don sun riqe mata danta bai fada wata hanya ba,sun kuma bashi kulawa da gata cikin mutuntawa bakin gwargwado. Da laila da ayana dukkansu ta karanci kowaccensu,manufarsu guda daya ce. Maina mijin mace hudu ne,kuma yana da damar ya auri dukkan macen da musulunci ya halasta masa,amma yanzun lokaci ne daya kamata ya shiga rububi da rigimar 'ya'ya mata da kowaccensu take a shirye don mallakarsa?. Ita kuma sultana fa?,me yasa hankalin sultana yayi nisan kiwon data kasa hango abinda ita taketa hango mata?. Tambayar data yiwa ama tsaiwar mashi kenan cikin kwanyarta wunin ranar gaba daya,duk inda ta juya taga gilmawar benazeer da batoul sai taji abun ya fado mata. Su din 'ya'ya mata ne da zasufi kowa jin dadi idan suka tashi sukaga mahaifinsu da mahaifiyarsu a tare suna rayuwa qarqashin inuwar aure.
++Don aiki a ranar tayi aiki sosai,ta kuma kammala duk abinda ya dace ace ta gama din da taimakon dioura. Amma irin gajiyar da takeji a gabbanta ta wuce qa'idar aikin da tayi,don daga qarshe tare suka fito daga gidan da dioura,ita tayi driving nasu,basu rabu ba sai da sukazo traffic jam,ta bata motar ita kuma ta tsaida taxi ta wuce.
Hannunta dukka ta bude tana tarbar benazeer da batoul da suka taho da gudunsu,ta zauna tana yiwa ama barka da gida,sai aman ta bita da kallo. Komai na sultana kaman yana sauyawa,kuzarinta ta fahimci kamar tana loosing dinsa,sannan kaman akwai boyayyar damuwa qasan zuciyarta da take qoqarin dannewa. A yanzun sultana ta riga ta zamewa ama wani sashe na rayuwarta,ko babu auren maina bisa kanta,ko babu benazeer da batoul shekarun da sukayi da sultana tana jinta kamar su saddi da almu.
"Lafiya kike?" Ta yiwa sultana tambayar wadda ta shiga nazarin falon ko zataga wani abu da zai gaya mata anyi wani baqo a gidan bayan fitarta. Da sauri tayi qoqarin tattara hankalinta,tadan saki murmushi tana cewa
"Alhamdulillah ama,aiki nayi yau sosai me yawa"
"Allah yayi jagora"
"Ameen,bari na shiga na huta" har ta kusa isa dakinta ta waiwayo
"Benazeer.....maza gayawa tanja,don Allah idan akwai fulawa,zata iya soyamin waina?,da manja da albasa da yawa" cak ama dake qoqarin gyara sabbin kayansu benazeer data yi musu order ta daga kai ta kalleta. Suna hada idanu haka kawai sai sultana din taji wani iri
"Na gaji da abinciccikanmu ama,na dade banci waina ba"
"Akwai kayan a kitchen,indai tanja ce akan aikinki bata nawa" ama ta fadi tana maida kanta ga abinda takeyi, juyawa tayi tana wucewa dakinta,yayin da benazeer ta fella da gudu don Isar da saqon sultana din.
A daren dukka juriyarta ta qare,ba shiri ta sauka daga saman gadon,ta xura hijabinta ta fito.
Dakin ama kai tsaye ta wuce inda yaran suke kwana tun xuwan ayana. Ta samesu tanja na shiryasu xasu kwanta,don benazeer ma harta kwanta din,ama na qoqarin daidaita musu sanyin ac din dakin.
Dukkansu suka juya suna kallonta,tun tun dazu data gama cin wainar fulawa tace bacci takeji ta wuce daki.
"Ama aronsu benazeer zaki bani,zasu tayani kwana" duk sai suka zuba mata idanu,saboda abune da bai taba faruwa ba tunda ta haifi yaran.
Idanunsu harda na yaran taji ya mata nauyi,kallon da suke binta dashi ya sanyata komawa gefan gadonsu ta zauna. Cikin kawaicin nan na ama da takejin yana dab da qurewa,cikin halin ko in kula tace
"Gasunan ai,tafaddal" dukkansu murna suke yaran,tuni banazeer ta diro daga gadon tana rarumar blanket dinsu
"Ajjiye wannan mana hajjaju" sultana din ta fada tana murmushi,cikin zuciyarta tana jin tana samun sassauci.