Showing 177001 words to 180000 words out of 294767 words

Chapter 60 - Gudun Kaddara Book 2 Hausa Novel Complete

sukeyi sosai,idan ka gansu zakayi tsammanin sun girmi shekarunsu. Da kadan da kadan wasu abubuwan nasu suke juyewa zuwa na babansu. Shape din idanunsun sak irin nasa lion eyes din data sakawa suna,data kalli qafafunsu kuma yanzun sai ta sake gani tamkar nashi

"Ya akayi har kika haddace qafarsa?" Wata zuciyar ta tuhumeta,sai taja tsaki tana jin haushin kanta da kanta,don itama bata san ya akayi hakan ya faru ba,ta maida qofar ta kulle ta taka tana komawa ciki,sannan tazarce direct zuwa toilet.

Ruwa ta hada me yawa ta hada me yawa tayi wanka,ta gasa jikinta da kyau da ruwa me dumi sosai,sai taji dama dama,gabbanta suka saki ciwon da take danji ya ragu.

A nutse ta zauna ta soma shiryawa gaban madubi,haka kawai yau din taji tana sha'awar shiga party din yaran wanda tsahon shekarun da aka dauka ana celebrating birthday din nasu bata taba wani daukan abun da muhimmanci ba. Kafin ta kammala sun mata knocking ya kusa sau uku.

Atamfa taji tana sha'awar sanyawa,wanda ta jima sosai rabonta da ita. Ta bude Wardrobe dinta ta tsaya tsaf tana qarewa kayan kallo kafin daga bisani ta jawo wata straight gown ta atamfa da aka yiwa adon shawbrosky tun daga samanta har qasa. Dinkin ya zauna mata das a jikinta,hakanan kalar atamfar ta haskata ainun,don data gama ta dora dankwalin saman kanta zakayi tsammanin daga maqwafciyar qasar take. Sosai qirar jikinta ta fita,shape dinta dukka ya gama fita,ita kanta data kalli kanta a mudubi saida shigar ta qayatar da ita. Duk wani salon ado da sanya atamfa zamanta da ama ya sanya ta iyashi,ba zata iya qididdige yawan adadin abubuwan data koya wajen ama ba.

Har zata sanya qaramin mayafinta saita fasa,haka kawai taji idan ta saka mayafin kamar ta bata adonta,yau daya tanason ta sake sosai cikin yaran,tana jin cewa idan batayi da gaske ba tsaf aliyyu zai iya janye mata yara,yanayin yadda taga suna maqale masa da yadda suke yawaita zancansa har basa maganarta kamar haka.

Baqanqe plate shoe da suka haskaka fatar qafarta ta saka,ta shafe jikinta da tsadajjen perfume dinta sannan ta dauki wayarta tana fita zuwa falon da take jiyo 'yan qananun hayaniya da tashin kida maras qarfi da yawa.

"Wow,ma sha Allah" ta fadi cikin ranta,irin yadda akayi decorating parlor din dole ya burgeka,ba zaka taba tsammanin cikin parlor din bane. Idanunta akansu benazeer,wani irin ado akayi musu irin na larabawa,takanas ama ta dauko matar ita ta shiryasu.

Uwa me dadi,duk jama'ar gurin amma haka suka tattare gown din suka nufota,ta durqusa tana murmushi gami da bude hannayenta tana jiran isowarsu,daidai lokacin stella maqociyarsu 'yar asalin qasar england ta bude qofar falon da akayi qaraurawa,ya sanyo qafarsa cikin falon sanye da trouser din da baqar shirt wadda ta fidda ainihin hasken fatarsa me cakude da sirkin jaja jaja.

Ita ya fara hangowa kaman yadda itama nata idanun a kanshi suka fara sauka. Ita ta fara dauke kai sai shima ya dauke nashi kan tamkar ma a wunin ranar ba qani abu saya sake hadasu baya ga gaisuwar da sukayi da safiya.

Zamewa sukayi daga jikinta sanda suka hangoshi yana takowa zuwa cikin falon da tsahon nan nasa dake cakude da murjajjen jiki da ya zamewa tsahon nasa ado sosai. Idan ka kirashi dogon namiji kai tsaye bakayi kuskure ba,sumarshi ta zauna sosai a kanshi tana ta qyalli. Kai tsaye ya wuce wajen ama dake zaune guri dayayayin da benazeer da batoul ke rige rigen isowa wajensa don sun ganshi ne a bazata,basu taba tunanin da gasken zaizo ba kamar yadda uncle goumar ya gaya musu.


_KWANKWASON JIMINA_*

*_TSUTSAR NAMA_*

*_AMEENATOU_*

*_GUDUN KADDARA_*

_DUKKA AYARIN LITATTAFAN KUDINSU YA KAMA KAMAR HAKA_*

LITTAFI DAYA_400
BIYU_800
UKU_900
HUDU_1200

_IDAN TA BANKI NE ZAKI SANYA KUDINKI A WANNAN ASUSUN_

6019473875
Musaa Abdullahi safiya
Keystone bank

_ANTAYA SHAIDAR BIYANKI ZUWA GA WANNAN NUMBER_

09166221261


*Masu tura katin waya ko vtu kuma kai tsaye wannan number zaku tuntuba*

09134848107

*Maqotanmu kuma al'ummar qasar nijer zaku tuntubi wannan number dinne kai tsaye don biyan naku kudin*

09033181070


*ZAFAFA FAMILY na maraba daku*🫂🫂🫂🫂🫂*_GUDUN ƘADDARA_*

*H U G U M A*

BOOK 02 PAGE 94


Sosai ya zauna daidai qafafun ama kamar zai shige cikinta ko kuma qanqanin yaro,irin wannan zaman a baya yakeyi a gaban ama din,yana kuma matuqar jin kewar yin hakan duk sanda ya tuna.

"Barka da warhaka ama" ya fadi sanda ya zauna daidai, batoul da benazeer kuma suka haye jikinsa suna masa hayaniya.

"Barka kade,mun yini lafiya?" Ta amsa masa da dan sakewa har abun ya sake sanya zuciyarsa yin fari.

"Alhamdulillah,ya fama da yara?" Ya furta yana kallonsu benazeer daketa cusa masa alawa a hannu da baki

"Alhamdulillah" ta fada a nutse tana duban fuskarsa,sam sai yaqi yarda ya kalli aman saboda tambayar tata da yayi shi kansa yasan tana da nauyi,to amma ya quduri aniyar gyaran komai ne shi yasa ya shirya fara tunkarar gyaran.

Cikin yaran ta shige abinta tana fama dasu,ta fidda wayarta tana musu hotuna da qananun videos gaban manyan cakes dake dauke da hotunan su benazeer da batoul din. Kallo daya tak zakasan cake din ya lashi kudi,duk daya hawa shida gareshi.

A zahiri yana fama ne da qiriniyarsu batoul,wanda tunda suka ganshi sukaqi komawa wajen baqinsu,sun cikashi da tambaye tambaye

"Daddy ashe zakazo...... Daddy mummy ce tayi inviting dinka?,daddy munyi missing dinka......har uncle goumar ma muka gayawa,yace mana dama zakazo" ya biye musu sosai,duk gift din da suka karbo shi suke kawowa yana ajjiye musu,saidai kuma fiye da rabin hankalinsa yana kanta.

Duk wani motsi nata idanunsa yana kai,wani shauqi ke fusgar zuciyarsa,duk sanda ta gilmashi sai yaji kaman ya jawota zuwa jikinsa yayi mata kyakkyawar runguma. Bugun zuciyarsa yana qaruwa haka idanunsa ke sake qanqancewa......baisan me yakeji me zafi haka tattare da ita ba,baisan wanne irin maganadisu ne yake janshi a kanta ba,kamar ba dazu dazu suka kasance tare da juna ba,har sai daya fara tilastawa kanshi qoqarin controlling abinda yakeji game da ita.

Komai tana yine bisa dakiya da dauriya,don batason barin wajen kota sauya abinda tayi niyya don kada ya dauka saboda shi ne,wannan ya sanya yadda ya bagarar da ita itama sai ta bagarar dashi kamar bata ganshi ba ko batasan da wanzuwarsa a wajen ba,saidai kuma can qasan ranta batasan me yasa takejin haushin yadda ya wani basar ba,kamar bai ganta ba,kamar kuma baisan da ita a wajen ba,kamar ba dazunnan ya gama jagwalgwalata kaman tsohon maye ba?. Amsar da zuciyarta ta bata raina mata wayon da yayi yana pretending ma duniya kaman ba komai tsakaninsu shine abinda yafi bata haushin.

"Meye naki don ya nuna haka?,dama haka kikeso ai yaci gaba dayin walau a zahiri ko a badini ko?" Wani sashe na zuciyarta ya bata amsa,sai taja qaramin tsaki,tana jin ba wannan tunanin ya kamata tayi ba,tunanin yadda zata fita aikinta gobe hankali kwance ba tare data hadu dashi ba shi ya kamata ya dameta,ta sake jan wani tsakin still dai sanda take gyara ma wata yarinya 'yar qasan Bangladesh gashinta da ya kwance daga jikin ribbon saboda santsi.

"Lokaci yayi" maman yarinyar ta furta da yaren France tana kallon ama tana murmushi

"To bismillah,ni 'yar kallo ce ai,na gama nawa aikin" ama ta maidawa matar amsa. Duka duka ayeesha ba zata haura shekarun haidar ba,amma jininsu ya hadu sosai da ama,kaf neighbor's dinsu su sukafi mu'amala da juna

"Ku taso birthday girls" ayeesha ta fada tana murmushi gami da kallon su benazeer da suketa dabdalarsu akan maina.

Gyara daurin igiyar straight gown dinta takeyi tana tsaye daga tsakiyar yaran,eye glasses din data mannawa idanunta ya qara fidda sirrin kyanta. A hankali ta waiwaya wai taga ko su benazeer din sun taso,sai idanunsu suka shiga cikin na juna. Cikin wani irin salon ya kafe idanun nata a cikin nasa yana aike mata da saqo ta nan inda yake zaunen,duk yadda taso ta janye idanun nata ta kasa,har sai daya tabbatar bugun zuciyarta ya qaru yadda yakeso,sannan ya sake mata wani shu'umin murmushi yana dauke kallonsa daga kanta.

Dole ta koma baya ta zauna a hankali saboda wata kasala daya sake mata,kanta ta dan dafe kadan tana ayyana

"Mugu" cikin ranta. Da shigen kallon yake punishing dinsu a gida tun yana yaa maina,dan makaranta,yaa maina me shekarun da basu rufa talatin ba. Dauke hannun tayi da sauri sanda ta tuna yana dai falon,batason ya karanci lagonta,saidai still ta sake kamashi yana mata wannan mayen kallon nasa. Wanann karon bata bari ya riqeta ba ta janye dubanta da sauri, murmushi ya kubce masa wanda iyakarsa saman labbansa

"Inda kin isa ki tsaya mana kici gaba da kallon nawa ki gani idan ban saki kin magantu a gaban kowa ba" ya fadi daga can qasar zuciyarsa. Yasan dukkan wani salo ko lago da zai iya kamata red handed ta kowanne fanni da yake da buqata,to amma kuma yana daga mata qafa ne saboda yanason ya dafata yadda ya kamata.

A sace take kallon kowa dake falon,ba wanda ya lura da abinda yakeyi din,wannan ya sanya taja numfashi da kyau ta furta sannan ta miqe tana zare glass din idanunta. Idan ma yazo ne don ya hanata sakewa itakam ba zata lamunci haka ba,don itama bata shiga rayuwarsa ba na meye xai shiga tata.

Cikin mintuna gurin ya dauki saiti yadda ya kamata,'yan abubuwan da ayeesha ta tsara saboda yara a wajen qananun games dukka akayi aka gama,sai aka fara karban gift,sai a sannan ya fidda wayarsa yayi kira duka duka da baikai na second biyar ba.

Ba jimawa akayi knocking,da kanshi ya miqe ya bude. Ma'aikata ne na wani kamfanin sarrafa kayan qarau da kayan yara sanye da rigunan wajen aikinsun suka fara shigowa da kwalaye suna jerawa,a sannu a sannu saiga kwalaye sun kusa guda ashirin suka kammala suka juya suka fice. Ama na daga zaune tana kallo komai amma batace komai din ba,kuma bata motsa ba,ya juyo suka hada idanu da ita saita kau da kai,batason yaci gaba da karya mata da kuma tsinka mata zuciya,soyayyar yaran da take gani cikin idanunsu har kamar ma taso tafi qarfin kalar soyayyar da su suka gwada masa sanda yana yaro.

"voici un cadeau de papa(ga kyauta daga baba)" ya fadi yana duban yaran. Sai da suka kalli ama sanna suka kalleshi,kaman hadin baki suka rungumeshi dukka su biyun suna fadin

"Merci papa" tattaresu yayi cikin jikinsa yana sauke boyayyara ajiyar zuciya,bayajin duk duniya akwai me iya fahimtar yadda yake son yaran.

Tsbaar zumudi sai suka kasa jira,dukka aka tattaru wajen bude kwalayen. Sutturu ne kala kala daga manyan kamfanin kaya na duniya dake samar da kayan yara designers masu quality da tsada. Kamfanin da ama din kawai ta gani ya sanya ta jinijina abun,ita din uwace me fahimtar yaren d'a koda bada harshen dake furta kalma yayi maganar ba. Ita din 'yar kasuwa ce da kusan kowanne kaya ta gani tasan a wanne aji yake,ko ba tare sukayi siyayyan ba amma ta sani kudade ya kashewa yaran masu ciwo.

Kowanne kwali da abinda ya qunsa,na sutturu takalma kayan kitso agoguna da sauransu kowanne kwali goma goma benazeer din da batoul.

A nutse ta dan juya idanunta tana satar kallon sultana,a guri daya take zaune sam bata cikin sahun masu kallon gift din.

"Sultana" ama ta kira sunanta,ta dauke idanunta daga wayarta da take latsawa tana duban ama din

"Na'am ama" gauraya idanunsu sukayi waje daya,haka kawai sultana din taji nauyi yadan kamata

"Ki duba kitchen an kawo order na abinda za'a ci,ki dinga shirya komai yadda za'a iya dauka ayeesha ta tayaki fitowa dasu,kallon gift dinnan bazaiyiwu a gamashi a lokaci qanqani haka ba"

"Okay" ta amsawa ama din tana qoqarin ajjiye wayarta.

Duk da dukka kalamanta cikin gajerun furuci ne amma hakan bai hanashi hango kyawun labbanta ba,kwadayinsu ya kamashi har sai daya hadiye yawu a bakinsa a hankali. Ta fara wucewa zuwa kitchen,yadda tayin yasan hali,zai wuya ta basu gift din daya cika mata bayan mota dashi. Murmushi ya saki a boye,idan tasan wata batasan wata ba ai.

Duqawa yayi a nutse daidai saitin kunnen benazeer ya gaya mata wani abu,ta daga kai da sauri tana fidda idanu waje

"Good daddy....." Bata qara minti daya bama ta daga murya duk da slow music din dake falon amma saida sautinta ya fito saboda zazzaqar murya gareta

"Mummy...... Ina gift namu?" Cak ta tsaya sannan ta waiwayo tana bakin qoqarin hana idanunta kallon fuskarsa,don tasan saitin bigiren da yake tsaye,ta fidda fararen idanunta waje da kyau tana duban benazeer yayin da takejin idanunsa na yawo saman fuskarta amma ta share

"wanne gift?" Ta tambayi yarinyar tana kallonsu duka ita da batoul da suka zuba mata idanu,kai ta karyar

"Ki tuna dai mummy.....na dazu fa.....daddy yace kin saya mana da yawa" dole a sanann ta kalleshin ba don taso ba. Kwata kwata kaman baya wajen ma,don ya maida dukka hankalinsa akan wayarsa ne kaman baiji me benazeer ma ta fada ba. Kafeshi tayi da kallo waiko zayaji a jikinsa ya daga kanshi,amma sai taga ma ya sake gyara zamansa yana bawa wayar hankalinsa.

Duk qiftawar idanunta a kanshi yana ji a jikinsa,saidai ya basar din kaman baisan me yake faruwa ba,saima ya fara sakin qaramin murmushi still fuskarsa nakan wayar.

Haka kawai taji ranta yadan sosu,tayi imani ba yadda za'a yi ta kalleshi jar hakan baiji a jikinsa ba,yana daya daga cikun abinda ta haddace sanda suna 'ya'yan bibi,tana tashen jin takai matsayin sultana,yana jin hakai aliyyu haidar dinsa. Yasha cewa saiya tsone mata idanu,don a sannan tana da dabi'ar tsureshi da kallo a duk sanda tayi laifi

"Dauken wadannan idanun magen naki a gun!" Saboda tsaban yadda yake damunta da fadin hakan sai da takai duk magen data gani saita tsaya ta qarema idanunta kallo,tanason taga wanne irin idanu ne da ita haka da yake goranta mata dasu,wannan ya sanya itama ya baida qaimi wajen kiransa da

"Me idanun zakuna" tun baisan tana fadi ba har sunan yazo kunnenshi,a ranar tasha horo sosai,amma maimakon ta daina saima ta sake maida kai wajen kiranshi da hakan,sunan da duk gidan ita daya ke fadinsa.

"Laila" sunan ya fado mata a rai,taja qaramin tsaki zuciyarta na raya mata qilan dasu yake chart

"Sai me?" Ta tambayi kanta,shi yaga zaya iya

"Amma yana cikin yaranshi suna hidima me muhimmanci a wajensu?" Wani sashe na zuciyarta ya furta. Ranta ta sakejin ya quntata da taga yana gyara Bluetooth din kunnensa da alama kiran waya ne ya shigo masa

"Ta yiwu ayana ko laila ce" can wani bangare na zuciyarta ya sake fadi

"Sai meye ne?" Ta sake gayawa kanta a tsawacen da sai da taja numfashi ta daidaita kanta.

"Bansan suna ciki ba.....idan na gama abinda nakeyi na baku key kuje ku dauka" ta fada tana juyawa ranta na mata wani zafin da batasan dalili ba tana wucewa hanyar kitchen din.


_KWANKWASON JIMINA_*

*_TSUTSAR NAMA_*

*_AMEENATOU_*

*_GUDUN KADDARA_*

_DUKKA AYARIN LITATTAFAN KUDINSU YA KAMA KAMAR HAKA_*

LITTAFI DAYA_400
BIYU_800
UKU_900
HUDU_1200

_IDAN TA BANKI NE ZAKI SANYA KUDINKI A WANNAN ASUSUN_

6019473875
Musaa Abdullahi safiya
Keystone bank

_ANTAYA SHAIDAR BIYANKI ZUWA GA WANNAN NUMBER_

09166221261


*Masu tura katin waya ko vtu kuma kai tsaye wannan number zaku tuntuba*

09134848107

*Maqotanmu kuma al'ummar qasar nijer zaku tuntubi wannan number dinne kai tsaye don biyan naku kudin*

09033181070


*ZAFAFA FAMILY na maraba daku*🫂🫂🫂🫂🫂


*_GUDUN ƘADDARA_*

*H U G U M A*

BOOK 02 PAGE 95


Boyayyan murmushi ya saki yana satan kallonta ta qasan idanunsa,salon kallon da duk qwqwarka ba zaka taba zaton ita din yake kalla ba,yadan cije lips dinsa na qasa sannan ya buda muryarsa cikin qasaitar nan tasa data jima bata jita ba ya kira sunanta

"Sulthana" har inda take sautin ya isketa,ya riski kunnenta da wani irin amo daya sanya tsigar jikinta tashi,duk yadda taso ta qaryata kunnuwanta dake jin zaqin sunan a bakinsa amma hakan ya kasa gamsar da zuciyarta.

Kamar kada ta tsaya ko kuma kada ta juyo,to amma cikin jikinta tana ji ama tana ankare da komai,don haka ya tsaya sannan ta juyo tana dauke fararen idanunta daga kanshi

"take the keys and bring them the gifts" ya fadi da muryar bada umarni nakai tsaye muryarsa a dake da wani irin deepness


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login