Showing 252001 words to 255000 words out of 294767 words
Chapter 85 - Gudun Kaddara Book 2 Hausa Novel Complete
amsa masa a ladabce. Wayar ya katse yana shirin maidata mazauninta,saidai kuma yaci karo da tarin miscals harda na Dr Camille a ciki. Bayason hayaniya ko doguwar magana don haka ba kiran wanda yabi din,ya maida wayar silent ya ajjiyeta yana maida kanshi saman pillow yana jin yadda kanshi yake sarawa.
Dai dai sanda abdulhamid yake tsaka da share sharensa a falon bayan ya kammala da harabar gidan. Yadan ja baya kadan kamar yadda itama adan tsorace ta dakata da nufar kitchen din da takeyi,ta tsorata saboda tayi tsammanin shine a falon sai kuma taga akasin hakan.
Kafin tayi yunqurin komai ya rusuna yana gaidata cikin harshen turanci da yake kyautata zaton shi takeji. Amsa masa tayi tana masa kallon rashin sani,sai kuma ta dauke kai tana wucewa kitchen.
Raba idanu ta shiga yi tana tunanin meye ma zata dafa da zai zauna mata a cikinta?,ta manta rabonta da shiga kitchen ko girki,tadan kwana biyu.
Tukunya ta dauraye ta dora saman gas,sai taji takunshi da sallamarsa. Waiwayowa tayi,yadan russuna yana cewa
"Madam na gama, abincin dama zan dora miki,ban dauka zaki tashi da wuri ba" da idanu ta bishi,sai kuma ta motsa labbanta tana cewa
"Waye kai?" Baiyi mamakin tambayar ba saboda yasan bata sanshi din bane
"Nine nake kula da gidan gaba daya,mu biyu ne akwai abdulgaffar......amma yaje gida,zai dawo soon in sha Allah" kai ta jinjina,daga yanayinsa tasan dan Nigeria ne
"Ba damuwa kaje zan dafa"
"Okay maa" ya amsa mata sannan ya juya yana fita daga kitchen din.
Sai data kwashe wasu mintuna tana kame kame kafin ta tsaida abinda zata dafa din. Kafin ta kammala duk sai taji kaman ta jigata,iska na neman kayar da ita. Ta samu ta gama da qyar,ta shirya a tray kaman yadda yakeyi mata,taja stool ta zauna,ta dauki spoon ta fara diba.
Daga taste har abincin duka sai taji baiyi mata,tsaki taja,ta sake diba karo na biyu tana zaton zata iya daurewa,nan ma still taji abincin ya tsaya mata a wuya,tilas ta tureshi ta soma tunanin meye abunyi?.
Wata tukunyar ta sake azawa tana canza wani abincin,saidai shima koda ta kammala din kaman wancan haka taji yayi mata. Tayi rau rau da idanu,hala tana cikin matan da idan suna da juna biyu ba kasafai suke iya cin abincin hannunsu ba?. Dukka dauriyarta ta tattaro ta sake aza wani girkin,saidai shima still tana fara ci ma taji amai ya taso mata,da qyar ta samu ya kwanta mata,sai kawai ta soma hawaye. Tafin hannunta ta saka tana gogewa,gidan shuru, kitchen din ba dadi,dakin ma ba dadi,haka duk girkin ba dadi,yaya zatayi ne?..
Fahimtar cewa indai ba shine ya bata abincin ko daga hannunsa ya fito ba to lallai ba shakka bazai zauna mata a cikinta ba,don haka ta haqura gaba daya,ta dafa Madara tasha sosai ta koma daki tana ci gaba da kwanciya.
Da azahar tana kwance taji an kira wayarta,baquwar number ce amma ta qasar Paris din. Kaman ba zata daga ba ta danne zuciyarta ta daga din. Daya daga cikin gidajen abinci ne dake daura dasu suke tambayarta meye da meye take buqata na lunch dinta?. Ido ta lumshe tana budewa,sosai taji zuciyarta ta tabu
"Qui a ordonné qu’on apporte de la nourriture ?(wanene ya bada umarnin a kawo abinci?)" Ta jefa musu tambayar. Dan dauke wuta tayi saboda tana duba sunan wanda ya bada order din,sai daga bisani ta furta
"Monsieur aliyyu maina(yallabai)" ta kira sunan nasa da rashin iya furta sunan da kyau
"Ku barshi ba buqata" ta fadi tana jin ciwo a ranta. Bazai iya tsaiwa ya bata kulawa ba?
"Je suis désolé monsieur, il a déjà payé la nourriture, donnez-nous une chance de vous l'apporter.(kiyi haquri madam,ya riga ya biya kudin abincin,ki bamu dama mu kawo miki)" ta fada cikin girmamawa.
Shuru tayi kuka yanason zuwar mata,batasan kuma me dame zatace su kawo ba,don haka tace musu abincin africa,yankin Sahel ta datse kiran.
Ba jimawa suka iso,ta bude qofar ta karba idanunta akan qofar dakin. Tanajin kamar ta zauna a falon,sai kuma ta wuce zuwa cikin dakin. Ko takan abincin bata biba,sai data tabbatar yunwa na gab dayi mata illa.
Wunin gaba daya a kwance yayishi,salla kawai ke tayar dashi,don ko abinci baibi ta kansa ba banda ruwan fresh milk da yake dirkawa kansa saboda yiwa kansa garkuwa daga yunwa. Saidai duk da haka hankalinshi yana kanta,baya son kuma kai kawon abdulhamid a cikin gidan a matsayinsa na baligi ga kuma matar aure a ciki,don haka yayi mata order din abincin da kansa.
Bai samu sassauci daga zazzabin ba sai kusan qarfe goma na dare. Ya sake jawo Madara yasha sosai ya wuce toilet don yin wanka jikinsa ka fidda gumin saukar da zazzabin yayi.
Sai a sannan ya samu yayi sallar isha'i,ya cire bathrobe ya sanya doguwar riga mara nauyi wine color saqar qasar morocco. Sai a sannan ya samu ya duba tarin kiraye kirayen da suka cika masa waya. Daya bayan ya dinga bin mutanen dake da muhimmanci yana kiransu. Ciki harda Dr Camille wadda ta zama itace ya qarshe,tace ta kira ne tahi ya jikin madam komai lafiya ko?.
"Alhamdulillah" yace da ita yana jin hankalinsa yana karkata wajenta
"Muryarka tayi qasa da yawa Dr lafiya kake?"
"Ciwon nan dai Dr" ya gaya mata. Kusan Dr Camille na daya daga cikin mutane biyun da yake gani lokaci bayan lokaci kan ciwon cikinsa.
"Ya salam,amma baka kirani ko ka kira Dr Muhammad ba?"
"je vais bien maintenant(na lafiya yanzu),kada ki damu"
"Allah ya qara lafiya,but idan ta yiwu goben sai a dubaka" akan haka suka rabu da Dr Camille.
Wayar yake juyawa a hannunsa,har cikin zuciyarsa yaji yana da buqatar ganin suhail da sardauna kan batun ayana dama lailan duka idan hakan ta yiwu,don haka ya maida akalar kiran nasa zuwa garesu.
Sardauna ya fara kira,kuma nan da nan suka gama waya dashi da yake he is serious ba kaman suhail ba,ya kuma bashi tabbacin goben zai shigo,sai ya danna kiran suhail
"Baka da kirki mutumina.....angonci ne ya sanya ka daina koda daga kiran mutane?"
"Ban sani ba,idan na sake angoncewa soon zaki fahimci komai"
"Ban gane ba?" Suhail ya masa tambayar cikin mamaki
"Zaka gane, gobe inason magana dakai kai da sardauna,ina da damuwa da zamu tattauna,zaka shigo kamar qarfe nawa?"
"Ina fatan lafiya?" Suhail ya tambaya cikin kulawa
"Khair in sha Allah" ya bashi amsa
"Ameen.....duk sanda sardauna ya taso kayimin magana sai nayi qoqari dukka mu shigo lokaci daya" ya amsashi
"Fine..... hakan yayi..... goodnight" ya katse wayar,sai ya ajeta saman pillow ya miqe yana son zuwa ya leqa lafiyarta.
_KWANKWASON JIMINA_*
*_TSUTSAR NAMA_*
*_AMEENATOU_*
*_GUDUN KADDARA_*
_DUKKA AYARIN LITATTAFAN KUDINSU YA KAMA KAMAR HAKA_*
LITTAFI DAYA_400
BIYU_800
UKU_900
HUDU_1200
_IDAN TA BANKI NE ZAKI SANYA KUDINKI A WANNAN ASUSUN_
6019473875
Musaa Abdullahi safiya
Keystone bank
_ANTAYA SHAIDAR BIYANKI ZUWA GA WANNAN NUMBER_
09166221261
*Masu tura katin waya ko vtu kuma kai tsaye wannan number zaku tuntuba*
09134848107
*Maqotanmu kuma al'ummar qasar nijer zaku tuntubi wannan number dinne kai tsaye don biyan naku kudin*
09033181070
*ZAFAFA FAMILY na maraba daku*🫂🫂🫂🫂🫂*_GUDUN ƘADDARA_*
*H U G U M A*
BOOK 02 PAGE 135
Ji tayi gaba daya kanta yana neman kasa daukar yanayin da take ciki. Ba shiri ta kunna data ta kuma kirayi goumar ta waya.
"Goumar kana gida?"
"Ikon Allah,yau kuma babu baqin buzun?" Bata cikin mode na tsokana wasa ko zolayarsa,don haka taqi bi takai
"If kana gida don Allah zan kira ka bani su batoul mu gaisa"
"So soon haka?" Ya fadi yana mata dariyar shaqiyanci,bai damu data amsa ko kada ta amsa ba ya dora da cewa
"Har kin fara missing nasu matar oga?,na zaci you don't care fa gaba daya" ido ta lumshe,karon farko yau dai tayi Allah wadai da zallar tsokana irin ta goumar
"Goumar...... goumar"
"Yes ma" ya amsa mata
"Zaka bani su ko na haqura?"
"Na isa?,inje ki hadani da oga ya janyemin subsides?,biki yana matsowa shi nakeso yamin walicci kada yace ya fasa"
"Kai ka jiyo" ta amsa masa tana zaquwa ya daga video call din data fara.
Wata nannauyan ajiyar zuciya ta saki sanda fuskokinsu ya bayyana cikin screen din. Suka fara murnar ganinta suma,da alama sun fara kewarta kamar yadda ta fara nasu. Yadda suke murnar ganinta ya sake sanyayar mata da jiki,takai hannu a hankali tana shafa qasan mararta da wata halittar ubangiji ke kwance a ciki. Lallai d'a da uwa sai Allah,ta yarda babu wani yanayi ko rintsin daya isa ya tsinke wannan kakkaifar soyayyar dake tsakaninsu.
Tunda take dasu bata bata dadewa dasu haka suna hira irin wannan lokacin ba. A yau din gaba daya fuskarsa take gani cikin nasu,wani motsinsu da wasu dabi'un nasu a yau take ganin zallar kamanceceniya da mahaifinsu.
Sun debe mata kewa matuqa kaso hamsin cikin dari,sun kuma sanyata farinciki. A hankali ta dinga tuna wasu daga cikin hadisai da suka karanta a makaranta na 'ya'ya mata rahama ne. Sunyi treating nata kamar sunsan damuwar dake zuciyarta duk da qarancin shekarunsu,wanda ta tabbatar inda namiji ne ba lallai ya iya hakan.
Wannan nutsuwar ya bata damar samun bacci,wando yazo ya dauketa ba tare data shirya ba da wayar a hannunta.
Yayi mamaki daya tura qofan dakin ya jita a bude,mamakinsa ya sake qaruwa da ya ganta a kwance amma kuma dukka fitilun dakin a kunne.
A hankali ya isa gaban gadon,ya tsugunna idanunsa saman fuskarta yana jin wani abu yana fusgarsa game da ita. Wunin yau duka da bai ganta ba yanajin tamkar ya shekara bai ganta ba,amma dole yayi hakan,don ya sake tabbatarwa kansa zuma ce saida wuta da kuma dabaru kafin komai ya gama daidaita. Ya gaji shima so yake komai yazo qarshe.
Wayar hannunta ya fara zarewa,sai ya bude yana duba waye ta kira?. Murmushi ya saki bayan yaga da waye ta gama wayar,ya maida idanunsa kanta yana sake sakin murmushi.
Yaran da ake kawarwa da kai,yaran da akaqi shayar dasu.....yaran da akaso turewa tun suna kwanan farko a duniya,yaran da akace ba'a so an barwa duniya yau su ake bege har haka?.. qaramar dariya ya saki,al'amuran sultanan akwai ban dariya wani lokaci.
A nutse ya tashi ya dagata cikin hikima ya gyara mata kwanciya da kyau,yaja mata duvet ya rufeta sannan ya sanya mata pillow daga gabanta. Yana zare hannu ta miqa hannun nata ta yiwa pillow din kyakkyawar runguma tana cusa kanta a qasansa. Dariya ta bashi da kuma tausayi,ya saki murmushi yana ci gaba da kallonta har sai data nutsu ta daina mutsu mutsu gaba daya,ya sani tana buqatar dumin wani ne a kusa da ita,amma tsabar fitina ya hanata tsaiwa ta fahimci inda zuciyarta ta dosa. A nutse ya busa mata addu'a yadda bazai tasheta ba ya kashe mata fitilar dakin gaba daya yaja mata qofar ya rufe yana ficewa.
*W A S H E G A R I*
Tun sha biyu na rana taji gaba daya cikinta an yasheshi tas,kamar bata san wani abu waishi abinci ba a duniya. Ta jima tsaye gaban madubi tana duban kanta cikin jin tausayin kanta da kanta. A jiya da yau tana jin kamar ita daya ke rayuwa cikin gidan. Jiya duka bataga koda gilmawarsa ba,a yau tayi tunanin zai leqo amma shuru,saidai ta samu breakfast daga wajen abdulhamid kuma yau din da yake ba ita tayi girkin ba ta samu ta danci wani abun.
Ba zata iya maimaita cin abincin dazu ba,don haka yanayin nata kuma yazo mata dashi,dole ta yafa mayafin baqar abayar jikinta 'yar qasae Egypt dake fidda wani qyallin tsadajjen yadin da aka saqa rigar dashi da kuma adon duwatsun da akayi mata.
Fuskarta tayi fayau ta kuma yi haske ainun,saidai kuma tadan fada kadan saboda yanayin laulayi da take fama dashi.
Isarta falon kawai hancinta ya tabbatar mata yana a wajen. Ta shaqi iskar falon da kyau idanunta nason lalubo daga inda yake a zaune.
Cikin qawatattun sofas da suka yiwa falon qawanya,gabansa dauke da madaidaicin tray,saman cinyarsa kuma system ce da hasken screen din ke haske gilashin idanun daya sakaya qwayar idanunsa a ciki.
Cikin jikinsa yaji ana kallonsa,a hankali ya shammaceta yayi caraf ya kamata,tayi wani wawan dauke kai gabanta yana faduwa,sai ta maida kanta hanyar kitchen cikin ranta tana tambayar kanta da kanta meye ya sameshi haka ya fada?.
Kaman zata zagaye sai kuma ta biyo ta hanyar da yake zaune.
"bon après-midi(barka da rana)"
"Comment vas-tu?(ya kike?)" Shima ya tambayeta a taqaice,duk kuwa da cewa kwanciyarta da tashinta dukka yana monitoring,ya saita komai ta cikin laptop dinsa da CCTV din da dakin yake dashi
"Lafiya qalau" ya fadi tana wucewa kitchen. Cikin ranta kamar ta tamabyeshi,amma sai taga na meye?,ita dake dauke da cikinsa ma ya ajjiyeta a gefe?.
Abinda take tunanin zata iya ci ta hado,ta dauko a tray tana jin kamar ta juye duka cikin cikinta duk da tayi imani zaiyi wuya ta iya ci.
Muryar Dr Camille ce ta daki kunnenta sanda take fitowa,dole ta aro fara'a ta aza saman fuskarta tana nufar Dr din dauke da tray din hannunta
"Lallai maman baby lafiya kike" Dr Camille ta tsokaneta. Tsokanar data sanyata sakin murmushi,ta qarasa gabansu kawai ta dire dukka abinda ta fito dashi tana samun waje ta zauna tana gaidata cikin girmamawa ita da baqon likitan da suke tare.
Da idanu yaketa monitoring dinta,yadda taketa qoqarin karramasu dr Camille tamkar ta sansu,tanata qoqarin musu fara'a da basu tarba ta girmamawa. Duk da taurin kanta da kuma kafiyarta tun a shekarun baya tana da wasu dabi'u da da yawa ba'a sanya mata rai dasu. Na farko mutum ce me mugun tausayin da nan da nan ta yiwa mutum kuka saboda tausayi ba komai bane. Na biyu tana da son taimako,a lokacin komai yawan kudi ko tsadar suttura ko wani abu na amfani da za'a bata muddin taga mutum nada buqatar wannan abun zata sadaukar masa. Har wani lokaci 'yan gidan kanyi mata shaguben batasan ciwon dukiya ba.
Duk da abinda ta kawowa su Dr Camille din ba cimarsu bane amma sunci sun kuma yana sosai da abincin africa. Bayan sun gama dinne Dr Muhammad ya fara dubashi,ya gama masa tambayoyi da qananun gwaje gwaje
"Kafi kowa sanin history na ciwonka......ya kamata ka kiyaye Dr aliyyu" Dr Muhammad ya fada yana komawa mazauninsa. Sultana dake wasa da yatsunta ta daga kanta kadan ta saci kallonsa,wanne irin ciwo ne wannan?. A hankali kuma sai tunaninta ya dawo kan darensu na rannan,yadda ya dinga wani abu daya firgitata ainun
"Dama yana da ciwo har haka amma bai taba gayamin ba?" Ta tambayi kanta da kanta,sai kuma ta tuna yanayin da suke ciki,don haka ta kauda wannan tunanin.
Tana zaune Dr Muhammad ya bashi shawarwari, shawarwarin da ta dinga jin sun mata nauyi, kunya ta kamata sosai,da yake bature ne shi din, kuma akan aikinsa yake don haka bai damu ba,kanshi tsaye yake masa bayani.