Showing 69001 words to 72000 words out of 294767 words
Chapter 24 - Gudun Kaddara Book 2 Hausa Novel Complete
Murmushin ta kan fita ne a duk sanda ta tuna da quruciyarta,ta tuna da rayuwarta a niamy,ta tuna irin tabara da rashin hankali da zallar wauta data tafka,yadda ta qaunaci rawa,xuwa party zuwa birthday kamar hauka,a yanzun idan dukka ta tuna wannan sai kunya ta kamata. Ta sake tabbatarwa da lallai komai lokaci gareshi,komai kuma yana zuwa ya shude ne cikin rayuwa tamkar a allon majigi.
Abu guda daya ke zuwa ya tsinke kyakkyawan zaren wannan tuna baya nata,idan ta tuna da MAINA. Komai yana shafewa a zuciya da ruhinta,komai yana shafewa daga tunaninta amma banda abu daya,banda MAINA banda yadda ya yiwa rayuwarta da mutuncinta dirar mikiya,banda yadda ya wargaza mata kyakkyawar rayuwa yabar mata wata rubutacciyar qaddara a rayuwarta,ya kuma shura qafafunsa ya bace battt daga sararin duniya tamkar zuwan walqiya da daukewarta. Komai ya sauya cikin rayuwarta amma wannan tabon yana nan a zane radam......wannan tsumammiyar qiyayyar tana nan a rubuce dara dara bata kauce ba,daga qarshe takan buge da xubda hawaye me tarin yawa.
Takan jaye jikinta daga cikinsu fateema Ahmad duk lokuttan da suke hirar samarinsu,soyayya ko hirar data shafi 'yammatanci,saboda a sannan kowacce ta soma cika mace,takai kuma ganiyar 'yammatancinta. Cikin jiki da ruhinta takejin kwata kwata bata cikin sahunsu,to meye zai zaunar da ita a cikinsu ana hirar da ba layinta ba?.
Su kuma dukkan wannan sun azashi ne cikin zallar miskilanci irin na sultana,son zaman kadaici da zaman shuru,kamewa da rashin son hayaniya. Takan saki siririn murmushi da jerarrun fararen haqoranta a duk sanda suke mata tsiya
"Kin fiya shuru shuru wallahi,ke ba dama ki zauna ayi hirar arziqi dake."
"Baku riski sultana a sanda take sultanan ta ba,kun samu sultanar nijeria ne,sultanar hassan Ibrahim gwarzo,sultanan ama,auntyn benazeer da batoul.......ba sultanan nijer ba,sultanan bibi da aba,da hirar tsiya ma duka sai anyi,saikun nema wajen fakewa daga gareta" takan raya haka ne cikin zuciyarta.
Ta riqi sallah sosai,ta kuma koyi azumin litinin da alhamis a gida ko a makaranta,tun daga sanda suka karanta hadisin dake bayanin falalar azumin litinin ko alhamis basu taba ruskarta tana da cikakkiyar lafiya ba tare da tayi azumin nan ba. Saidai har yanzu jikin nan yana nan ba wata qiba,amma kai tsaye ba zakace a rame take ba,sai tsaho data qara,duk wata halitta tata ta qara cika,kyawun nan na cikakkiyar buzuwar asali,jinin NADEEYA MUHAMMAD MAYAK'I ya hudata sosai,ya zamana har hirarta akeyi sashi sashi cikin makarantar,domin kaf cikar makarantar da batsewarta babu wata diya mace data isa ta tsaya a tudun mizanin kyau tare da ita,wannan ya sanya take sake kame kanta da kuma fita a dukkan shirgin da ba nata ba. Sai kuma Allah ya zuba mata farinjini da kwarjini wajen juniors,bata da mugunta ko kadan,hasalima cikin sabbin shigowar nan duk yarinyar da ta gani ne rawar kai iyayi da surutu sai taji tana tausaya mata,wani lokaci kuma ta saki murmushi don suna tuna mata da shekarun baya da suka shude mata.
*_GRADUATION DAY_*
Rana ce me matuqar tarihi cikin rayuwarta,ranar data sanyata xubda hawaye me yawa,ranar data sakata dana sanin zaman da tayi ba karatu a wadancan shekarun,ranar kuma data sakata a godiyar Allah me tarin yawa daya fiddata daga duhu zuwa haske.
Taro ne akayi gagarumi na saukar dalibai tare da yayesu,tana cikin dalibar farko da aka kira aka karramata har hawa uku gaban dubban al'umma,gaban familynta,gaban mutanen da suke tamkar iyaye a wajenta,gaban mutanen da suka debe tsammanin zamantowarta a yadda take a yanzun.
Duk inda ta motsa kyaututtuka ne na yabawa da karramawa. Da yawa mutanen dake wajen da sukasan family din MAYAK'I sun mata kyaututtuka na alfarma,har sai da goumar ya taso ya dinga tayata karba.
Data dawo mazauninta ta zauna kasa jurewa tayi,taja hijab dinta ciki ta boye fuskarta tana kuka. Abun mamakin sai batoul ta kalli benazeer cikin kwabe fuska kaman zata saki kuka
"Benz(haka take kiranta don bata iya kiran full name din ya mata tsaho da nauyi),waye yasa aunty kuka?" Waiwayowa benazeer din tayi ta zubawa sultana idanu,itama sai ta kebe baki kamar zata sanya kukan tana duban goumar
"Oncle.......ko itama aunty ta tuna da daddynmu da kace yayi tafiya?" Sosai maganar ta doki qirjin sultana,har batasan sanda ta fidda rabin fuskarta ba tana duban goumar. Kamar dama ya shiryawa hakan,shima ita yake kalla,suka zubawa juna idanu na wasu lokutta suna kallon kallo. Tanata hadiye bacin ranta da maganganun da takeson gaggaya masa saboda cikin bainar jama'a suke. Wato kebewar da yake da yaranta har gaya musu yakeyi suna da wani daddy da yayi tafiya?,waye ya sashi?,shi awa?,meye hadinsu da daddyn da yake musu maganarsa?, tabbas ba zata qyaleshi ba,sai tayi warning nasa,kada ya sake bari wannan maganar ta shiga kwanyar yaranta,bata buqatar hakan.
Wannan maganar kawai ta dauke hawayen fuskarta,sai suya da zuciyarta keyi mata tana fakon goumar tana jira su samu matsawa daga wajen ta amayar masa da abinda ke cikin ranta.
Bata samu wannan damar ba sai da suka tashi komawa gida,bayan taro ya watse,makaranta ta sallamesu sai kuma zuwa karbar result na exam dinsu. Ta gama koke koken rabuwa ita dasu fateema Ahmad da ameena aleeyu,aminan qwarai da ba zata taba mancewa dasu ba,sunyi exchanging phone numbers da full address nasu,har Adress dinta na nijer dukka ta basu saboda batasan me rayuwa ta tanadarwa gobenta ba, al'amuranta bata fiya basu amana ba,ta fahimci caccanjawa sukeyi a duk sanda sukazo hakan,koda yake umarni ne daga rabbussamawati.
Ita da aminata,najma da yasmine su ya dauka a motarsa wadda bai jima da siyenta ba bayan kama aikinsa baya bayan nan da kammala karatunsa. Kusan duk wani hali da dabi'a na maina yana dasu. Har rabon motoci aba ya yiwa samarin cikin dangi yace bazai amsa ba,yafison ya fara hawa wadda ya siya da guminsa. Kusan aqidar maina ne,neman nakai,ya tsani a masa alfarma,ya tsani ya rabu da wani ya dinga cin albarkacinsa,wannan dalili ya sanya har yabar gida baida motan hawa na kanshi,duk da cewa akai akai yana bisa hanya duk kusan sati ko sati bibbiyu tsakanin niamy da marad'i.
Ta fahimci akwai wata kyakkyawar alaqa tsakaninsa da najma,saidai a yanzun ba komai take magana akai ba shi yasa batace komai ba,amma tunda su aminata sukazo ta karanci akwai gulma fal bakinsu,bata dai tsaya ta basu lokaci bane,amma ta tabbatar sai sun fesa mata koda ba zata saurara ba.
Kyawawan 'yammatan buzayen da suketa daukan hankulan jama'a suka jera reras su hudu bayan tashin motarsu aba suka wuce zuwa inda goumar ya ajjiye motar tasa. Hirar suke amma sultana bata fiya sanya musu baki ba,don burinta kawai ta fesarwa goumar abinda yake cikinta.
Akwai takadda guda daya ta sultana da ya tafi karbowa don haka suka dan tsaya suna tattaunawa daga bakin motar tasa kafin ya iso ya bude musu.
Yaro ne da duka duka bazai wuce shekara sha hudu ba ya iso gurin. Fari ne siriri,yana da dan tsaho kadan,yanayin zubin fuskarsa kadai zai shaida maka bafulatanine usul. Sanye yake da wata dakakkiyar shadda sai maiqo takeyi fara qal,kanshi sanye da jar dara sosai irin ta ainihin bare bari. Kana dubansa kasan daga gidan gata ya fito,kuma alamun jikinsa da fatarsa na nuna ainihin jin dadi da yake ciki.
A gabansu ya tsaya yana sallama fuskarsa a sake. Dukkansu suka daga kai suna dubansa,aminata ta amsa masa,sai sultana ta maida kanta tana daidaita qananun litattafan azkar dinta data qarasa debowa daga drawer dinta ta jikin gadonta don bawa 'yan ss2 da zasu maye gurbinsu damar cin gadonsu da kyau. Gaishesu yayi sannan yace musu
"Wai anason yin magana da wannan" ya fadi yana dan murmushi hadi da nuna sultana da yatsa. Kusan dukkaninsu sai da wuta ta dauke musu na wucin gadi,ba sultana kadai ba,su kansu saida tsoro da fargaba ya cika zukatansu. Suka zuba mata idanu dukkansu,yayin da ita kuma ta zubawa yaron nata idanun ba tare da sanin takamaimai amsar da zata bashi ba.*_GUDUN ƘADDARA_*
*H U G U M A*
BOOK 02 PAGE 37
______________________________
https://chat.whatsapp.com/CKY0xZDtpby6MTkGrPkXLr
____________________________
"wai inji wa?" Najma tayi qarfin halin tambaya da alamun sanyi qwarai cikin muryarta
"My broz....gashican,yace idan ba damuwa zai qaraso.....don Allah aunty ya qaraso din,mun gaji so muke mu aurar dashi mu huta" ya fada yana qyalqyala dariya,da alama akwai sakewa sosai tsakaninsa da wanda ya aikoshi din.
Dukkansu suka maida dubansu inda yaron ya nuna musu. Baiyi qarya ba,matashin saurayine fari tas da yayi zubin buzaye yarensu,saidai su da yake suna shaida duk wani da sukejin harshe daya dashi take suka shaida bafulatanine shima tamkar qaninsa. Yana sanye da shadda da hula sak irin ta qanin nasa,komai nasu irin daya kamar yadda suke kama da juna
"Kaje kace masa matar wani ce" muryar goumar ta ratsa kokwanto da walagigin da zukatansu suka shiga na yadda zasu kaucema wannan kiran.
A birkice ta daga kai tana kallon goumar
"Matar wani?" Ta furta a fili amma a hankali. Juyowa goumar yayi wanda yaji fitar lafazin nata yana duban qwayoyin idanunta kamar yadda ta kafeshi da nata
"Eh..... qarya nayi?" Ya fadi kanshi tsaye yana sake kafeta da kallonsa. Mummunan faduwa gabanta taji yayi. Tsahon kwanakin watannin da kuma shekarun bata taba tuna cewa wai har yanzun itadin matar aliyyu bace,bata sake tuna har yanzun a sunan matar aure take ba,bata sake tuna akwai igiyoyin aurensa guda uku qwarara a kanta ba.....to wai zaman meye takeyi da igiyoyin auren maqiyinta kuma makashinta?,me ta zauna tana yi dasu tsahon shekara hudu?. Kai ta jinjina tana zare kallonta daga kan goumar,taji daci qwarai har saman harshenta,saidai kuma taji dadi da yayi mata tuni da wani muhimmin al'amari da ya kamata ta tuna dashi ta kuma kawo qarshensa cikin rayuwarta gaba daya.
A yanzun ita din wata sultana ce ta daban data fara sanin dadin rayuwa,kyawun rayuwa da kuma cikakken 'yanci da rayuwa ke dashi,tanaso tayi rayuwa kamar kowa,tana so tasan me duniya da rayuwa suka qunsa?,tanason ta fita tayi gwagwarmayar da al'umma zasu amfaneta,dole ta kawo qarshen wannan maqalallun igiyoyi da ko daya bataga amfanin barinsu a sarqafe ba.
Najman ce a gaba dukkansu suna baya su uku,tana iya hango yadda fuskar saurayin ta canza sanda qaninsa ya iskeshi a sanyaye yana labarta masa,batasan ya suka qarke ba,tadai ga yabi bayan motarsu da kallo har suka fice daga makekiyar harabar makarantar.
Cikin motar kanzil bata ce ba,aminata da yasmine sunta hirarsu,goumar da najma da batasan me suke fadi ba suma tasu hirar suke,sai ita daya da suka fari da hannu dafe da gefan kanta tanata zane saman bangon littafin dake cinyarta,wanda ita kanta batasan me take zanawa ba saboda tsabar tunani.
Iska ta shaqa sosai da suka shiga tangamemiyar harabar gidan aba dake garin abuja bayan jirgi ya saukesu a airport. Tadan bi harabar gidan da kallo yadda ya qawatu matuqa da gaske. Sabon gida ne da basu jima da tarewa ba,duka duka sati biyu. Cikin shekarun nan wani irin tumbatsa arziqin aba dama na hamdiyya ABDU ME KANO wato ama keyi,kaman an sake yiwa dukiyarsu yayyafin albarka,mahaukatan kudi kowannensu yake samu. Yanzu haka sun budewa benazeer da batoul manyan manyan boutique cikin garin abuja har guda uku,wanda kowanne kudade ya lasa ba qananu ba,saboda girman boutique din ya kusa wani mini supermarket din B&B BABY DREAM. Komai nasu na dabanne saboda ana sarrafashi ne daga wani kebantaccen kamfani dake sanya tambarin B&B a kowanne kaya,shi yasa kayansu ya fara zama na daban,ya kuma samu karbuwa qwarai da gaske,karbuwar kuma tana da nasaba da yaran da Allah ya hore musu wani irin farinjinin mutane.
Randa sultana tazo wani hutu ta amshi wayar yaran da ama ke musu amfani da ita tana duba account nasu na insta abun ya bata matuqar mamaki. Followers suke dasu masu yawan gaske. Account ne na musamman da ama ta bude kawai saboda yaran,ba abinda take dorawa sai hotunansu. Tun sultana tana kallon pics din har ta gaji saboda yawansu,ta aje wayar kawai tana murmushi
"Kakar zamani" tayi gulmar ama a ranta tana dan dariya qasa qasa.
Motar goumar ya tsayar a farfajiyar ajiyar motoci dake gidan wadda gari ne kusan guda,ya kalli najma
"Samomin wani abu me dan sanyi,ki tahomin da BB(benazeer da batoul)zamu fita dasu wani guri"
"Okay sir" ta fadi tana murmushi sannan ta bude motar ta fice.
"Akwai abinda na riqe miki ne madam?" Goumar ya fadi yana gyara qaramin pillow din dake gefan kujerarsa. Sai data sanya qafafunta waje sannan ta waiwayo
"Goumar" ta kirashi kai tsaye wani irin tsauri na fita daga cikin qwayar idanunta
"Na'am madamme" ya amsa fuskarsa a sake ba komai
"Karka bari ka barar da sauran mutuncin dake tsakaninmu"
"Tofa!,ikon Allah,me kuma nayi?"
"Da batoul da benazeer basu da wani abu a duniya yanzun,kayi qoqari ka daina yi musu tilawar abinda babu wanzuwarsa a duniya......haka nima......ni ba matar kowa bace,ba matar wani bace ni" wata siririyar dariya ya sake mata,ba abinda yake ganowa a idanu da fuskarta sai zallar quruciya da har yanzun shi baiga ta fita kwata kwata a jikinta ba
"Basu da uba a duniya.....ke ba matar kowa bace to kece kika kashe musu uban?" A kaikaice ya waiwaya tana dubansa,maganar tasa ta sake tsaya mata a wuya kamar mulmulallen dutse. Gaba daya abinda ta fahimta goumar kallon shashasha kuma yarinya yakeyi mata,baima dauki maganarta da muhimmanci ba.
"ko ya mutu koma ya rayu wannan duka ba abinda ya shafi sultana bane,abu daya sultana ta sani,bata da wani hadi ko alaqa ta kusa kota nesa dama ko waye" ta fadi da salon tsiwar nan tata data jima bata taba ba
"Ashe dai da sauran bakin har yanzu" goumar ya fada qasa qasa yana dariya sanda take fita a motar. Ta jishi sarai,bata kuma gama fahimtar abinda yake nufi ba,saidai duk da haka ta juyo ta zabga masa harara,ta murguda qaramin bakinta tace
"Baqin ba'abzine,Allah ya qara gwara da Allah ya barka a baqinka" ta buga murfin motar ranta yana suya da ambatar mata sunan maina tana qarawa gaba zuwa cikin gidan cikin sassarfa.
Dariya sosai ya kwashe da ita yana duban hanyar da tabi
"Baki gama laushi ba kenan,hali zanen dutse" ya fada a ransa yana gyada kai gami da ci gaba da dariyarsa sannan ya sanya hannu yana daga glass din motar zuwa sama tare da duban hanyar dawowar najma.*_GUDUN ƘADDARA_*
*H U G U M A*
Book 02 page 38
Tunda sukayi maganar nan da goumar walwalarta ta sake daukewa tsaf,duk yadda ta motsa sai zancan goumar ya fado mata a rai
"Matar wani" kalmar data dinga jin nauyinta qwarai,take kuma dugunxuma mata rai. Abun ya tsaye mata qwarai a rai,ashe duk duniya kallon da ake mata kenan?,ita din matar maina Aliyyu ce?. Cikin jikinta ta dinga jin qyamar danganta kanta da matar maina,ta dinga jin ranta da zuciyarta sunqi su yarda da wannan batun.
******K'arfe takwas ne da mintuna na dare, cikin kebantacciyar wajen da aka killace aka kuma zuba masa dining table na alfarma da daukan hankali. Ama ce keta qoqarin serving aba da bibi,wadda tunda tazo bata koma nijer din ba saboda wani likitan gargajiya da take gani cikin kano. Ciwon qafarta ne ya soma matsantawa ama tace ta zauna ayi masa magana,ta fara zuwa kuma alhamdulillah sauqi ya samu,a hakan rigimar komawa nijer takeyi nan da kwanaki masu zuwa.
Magana suke tsakanin aba da bibi, benazeer da batoul nata hawa cinyar bibi su sauka su dane bayan ama. Ba wanda ya damu da zirga zirgar wasansu da sukeyi,sai ama dake qoqarin hanasu wani lokaci gudun kada daya daga cikinsu ya fadi.
"Wadannan 'yan qaqur din.....wai ina tsohuwarku ne?" Bibi ta fada tana danqo benazeer da kirinkinta ya ninka na batoul,komai nata sak irin na sultana sanda tana qarama,har goumar ya saka mata wani suna wai little sultana
"Tana daki bibi"
"Ni me yarinyar nan keson xama?,anya kuwa kanta qalau?,ace kaine zaman daki ko gajiya bakayi?,ba zaka fito cikin al'ummar muhammadu rasulullahi fa ka zauna ayi tadi dakai?" Bibi ta fada cikin jajjabi.
"Jeki kira uwarku" bibi tace