Showing 294001 words to 294767 words out of 294767 words
Chapter 99 - Gudun Kaddara Book 2 Hausa Novel Complete
"Hajiya na'ima kenan?" Ya jefa mata tambayar,don kusan yasan matar saboda tsananin kirkinta da yadda take masifar son yaranshi,hakanan khumrarta da turarenta na dabanne,hatta da su benazeer turarenta ya fara kama jikinsu, ba'a zancan bedrooms dinsu dama zuwa parlor
(Nima dashi nake using,kabbasa ko khumra duka,karkiyi missing sister,wanda ya sanni a zahiri yasan hakan,me buqatar tuntubarta ga number dinta nan +234 803 212 7953,it's not paid advertisement,na kawo muku ne kawai don qaruwarku,zan saka muku sample a status dina ku gani).
"Ita,me kawo sabbin design na laces tare da ama?" Murmushi ya saki
"Taya zan manta wadda ta qawata gidana da jikin matata da sasanayan qamshin dake bani nutsuwa?,anya ba mallaka a qamshin nan?" Sosai ya bata dariya yadda taga yana wani narke mata hadi da lullumshe ido,ta saki sassanyan dariyarta ta kama hancinsa taja
"Kaiko?"
"Keko?" Shima ya rama suka saki dariya gaba daya.
"Me muka samu?,zakkar ce za'a fitar mu kawowa hajjaju account numbers dinmu?" Dariya ya sake bata,ta dago takardun tana kalla
"Daddy ina zakakai kudi haka?,lissafin shagunan BB ne,sai kuma kudaden dana ware inason a ginawa bibi masallatai da makarantu da rijiyoyi a nijer da Nigeria,sadaqatul jariya"
"Ma sha Allah,kin rigani a fili na rigaki a zuci" sai ya gyara zamansa
"Za'a yi da naki kudin,nima zanyi nawa in sha Allah,Allah ya sanya kabarinta dausayi daga dausayin aljanna"
"Ameen ya hayyu ya qayyumu" ta amsa masa har yanzu tana jin kewa da rashin bibi a ranta.
"BB kuma ai kin cika mana gidan da masu B,so dole za'a fadada shagunan dama.kamfanin,inason sakawa Birra Da little Bibi nasu share din,amma bansan ya za'a maida sunan ba,B din ya zama uku" murmushi tayi
"Wannan aikin ama ne,na tabbatar zata fitar" kai ya gyada
"Gaskiya ne,inajin jibi tasneem din sardauna da muzaffar din suhail zasuyi party na gama primary section,zamuje duka da yaran,saimu barsu a can mu qarasa wajen ama,auren atta da almu da saddi duka takeso a hada Next month in sha Allah" yayi maganar yana kallon agogon Rolex dake hannunshi
"Ma sha Allah,abun ba wuya,Allah ya nuna mana ya rayasu su kuma,lallai akwai babbar hidima kenan"
"Ameen ya hayyu ya qayyumu,ama zata qarasa cika burinta.....amma fa ina da complain" ya fadi sanda take miqewa don su wuce cikin gida ta bashi kulawa yadda ta saba. Barin abinda takeyi tayi ta waiwayo tana dubansa cikin kulawa
"Na me fa bloodline?" Murya qasa qasa yace
"An yiwa kowa takwara...... yaushe ni za'a yiwa aliyyu haidar takwara?" Dariya ke cinta tana dannewa,kusan sati guda kenan tayi PT ya nuna mata positive,amma taqi gaya masa,kaman kuma yasan da hakan ya dameta da zancan samun wani cikin,shi ko dan qin haihuwar nan ma ta matasan zamani baya cikinta.
Sai data gama tattara komai tana murmushi idanunshi shi kuma suna kanta ya kasa gajiya da kallonta,ya kuma kasa dauke idanunsa,sannan ta daga fararen idanunta nan da bibi ce tayo irinsu sak tace
"Biyoni ciki na gaya maka" tana fadi ta juya da dan sauri sauri tana dariya tayi cikin. Qaramin ihu ya saki na farinciki,ya tabbatar dole akwai abinda ta tanadar masa,sai ya dauki wayarsa yabi bayanta da 'yar sassarfa yanason cimmata fuskarsa fes da farincikin da yanzun baya rabo dashi,kuma itace silar wanzuwarsa a ciki yana fatan kuma har qiyama.
*_Tammat bihamdillah_*
*_Dukkan yabo godiya da jinjina sun tabbata ga Allah me kowa me komai daya bani ikon kammala wannan littafi 17/08/2024_*
*_tsira da aminci su qara tabbata ga fiyayyen halitta annabi Muhammad S W A_*
*_haqiqa na yaba muku fans,masoyana bisa haquri da juriyar bibiyata,duba da yadda wannan karom rubutun yazo min da matsaloli da yawa wadanda ban san zasu kunno kai ba,ban kuma shriyawa zuwansu ba,amma duk da haka ubangiji yayi riqo da hannayena,da taimakonsa da qarfafawar gwiwar masoya har muka kawo qarshen littafin nan a yau,haqiqa na gode muku qwarai da gaske,masoya masu bani qwarin gwiwa,masu qoqarin bani uzuri da fahimtata,ina fatan Allah ya baku uzuri a ranar da kowa yake da buqatar hakan daga wajensa_*
*_Da yawa sun jure,sun danne qorafinsu sai supporting da encouraging,Allah ya qara zumunci ya hadaku da dukkan alkhairi_*
*_masoya mabiyana na kafar AREWABOOKS na yaba qwarai da juriya da haqurinku,ubangiji ya cika muku hannuwanku da rayuwarku da alkhairi maras yankewa, MASU FIDDA MANA Allah ya ganar daku,ya wanke muku zakatanku daga cutar da suka samu zukatanku na daqile ci gaban wani_*
*_ina roqon duk wanda na batawa kona masa ba daidai ba ya yafemin,ina fatan Allah ya sadamu da alkhairinsa a gaba_*
*Zafafabiyar na matuqar godiya a gareku,duk da tarin kusakuransu da ajizancinsu amma kun musu uzuri irin wanda masoyi kan yiwa masoyinsa, ubangiji ya dafawa lamuranku damu gaba daya*
*_subhanakallahumma wabi hamdika,ashhadu an la'ilaha illa anta,astgafiruka wa'atubu ilaika_*