Showing 189001 words to 192000 words out of 294767 words
Chapter 64 - Gudun Kaddara Book 2 Hausa Novel Complete
Tunda suka shiga gidan ya wuce bedroom dinsa ya barta da suhail a falo suna hira,wadda kusan indai suhail ne sun saba da irin wannan doguwar hirar shida laila din,don ba baqin juna bane. Har kafin ma a fahimcesu ana zaton soyayya sukeyi,saidai daga bisani sai aka fahimci haduwar jini ne kawai ba wai soyayya ba.
A dakin ya kashe dukka awannin saman system,sanda magariba tayi ya leqo yayi musu magana,suhail ya wuce daura alwala don su hada jam'i,ita kuma ta gyara zamanta tana fadin
"Ina fashin salla ne yaa maina" kanshi ya dauke kaman baiji ba,baisan me yasa takeson bayyana masa komai ba,akwai abubuwan da yasha jin basu dace ta gaya masa ba amma haka kai tsaye take gaya masa.
Tana nan zaune har suka kammala sallar,yayi zaman azkar dinsa har isha'i tayi suka sake jam'i suka idar. Tun yana sallar yake zuba idanu yaji ta jira aunty din tata,amma sai baiji ba,don haka bayan ya kammala azkar dinsa a nutse ya shafa,ya miqe yana nade carpet din da sukayi sallar.
"Dare yanayi......call them mana kiji idan sun iso,ya kamata ki wuce tun yanzun" ya fadi da sarautar nan tasa da takan motsa masa time to time,wadda me masifar qara masa kwarjini ainun da haiba.
Dan kame kame ta farayi,abinda ya sanyashi zama saman one sitter sofa din dake falon ya hade qafafunsa daya saman daya yana kallon idanunta
"Banjin fa sun iso......amma dai, lemme call" ta furta da sauri sauri tana zuge jakarta ta fiddo wayarta.
Cikin motsinta da idanunta ya gano qaryarta,taso tahowa ne kawai taqi jiran lokacin da zasu dawo saboda ta matsu ta ganshi shi yasa tayi qaryar yau din zasu dawo
"Sakata a handsfree" ya bata umarni nakai tsaye yana ajjiye carbin hannunsa a side table.
"Okay" ta amsa qasa qasa,wayar ta fara ringing,
muryar aunty din ta fito tarwai.
Tun daga yanayin yadda suka gaisa ya tabbatar masa basu da masaniyar tahowarta ma
"Yaushe xaku iso aunty?" Tayi qarfin halin tambaya,don ko ba'a gaya mata ba koda bata kalleshi ba ta sani jifanta yakeyi da kallo da wannan fitinannun idanun nasa
"Next week by now in sha Allah muna gida"
"Alright.....saikun iso"
"Yauwa.....byee,ki gaida nenne(mamarta)" sauke wayar tayi daga kunnuwanta amma sam taqi yarda ta kalleshi,shi dinma yasan ba zata iya hada idanu dashi ba,don ba abinda yafi qin jini irin qarya.
"Ina da alqawarin fita dasu BB suhail,can u please help me?,ka dauketa ka sama mata daki for one week?" Da sauri ta dago idanunta ba tare data shirya ba, muryarta a raunane tace
"Amma yaa haidar..... nan din fa akwai spare din daki,meye laifi don an barni cikin guda daya?tunda dai daddy da nenne dukkansu sun yarda dakai?" Kafeta yayi da wani irin kallo,ya yadda duk iya zamansa dasu yarinyar bata gama sanin halinsa ba tabbas
"es-tu dans ton sens ?(kina da hankali?)" Ya tambayeta da harshen faransanci saboda ranshi da ya fara baci. Qasa tayi da kanta,ya jima yana dubanta kafin ya janye idanunsa daga kanta
"Wannan ba tarbiyyarki bace kema kuma kin sani,ba zaki kuma fara yanzu ba,pack your stuff za'a kama miki masauki......" Ya fadi mata yana daukan counter dinsa. Daidai nan wayarsa ta dauki tsuwwa. Daddy ne yake kira sai ya koma ya zauna yana daga kiran
_KWANKWASON JIMINA_*
*_TSUTSAR NAMA_*
*_AMEENATOU_*
*_GUDUN KADDARA_*
_DUKKA AYARIN LITATTAFAN KUDINSU YA KAMA KAMAR HAKA_*
LITTAFI DAYA_400
BIYU_800
UKU_900
HUDU_1200
_IDAN TA BANKI NE ZAKI SANYA KUDINKI A WANNAN ASUSUN_
6019473875
Musaa Abdullahi safiya
Keystone bank
_ANTAYA SHAIDAR BIYANKI ZUWA GA WANNAN NUMBER_
09166221261
*Masu tura katin waya ko vtu kuma kai tsaye wannan number zaku tuntuba*
09134848107
*Maqotanmu kuma al'ummar qasar nijer zaku tuntubi wannan number dinne kai tsaye don biyan naku kudin*
09033181070
*ZAFAFA FAMILY na maraba daku*🫂🫂🫂🫂🫂*_GUDUN ƘADDARA_*
*H U G U M A*
BOOK 02 PAGE 101
Cikin girmamawa da mutuntawa ya gaidashi,bawan Allahn yana daya daga cikin mutanen da yake ganin girmansu qwarai.
"Lafiya alhamdulillah aliyyu,kaga baquwa ko?,sardauna nata fadan me yasa aka barta ta taho,mamana rigimammiya ce,kuma na yarda dakai,na tabbatar she's safe a wajenka" dan murmushi kadan ya fidda yana cewa
"In sha Allah daddy"
"To ma sha Allah,kada ta wuce ona week,tacemin gidan aunty surayya zata sauka ko?" Kallonta yayi,sai ta marairaice masa alamun kada ya fada ya rufa mata asiri
"Eh haka tace" ya bawa daddyn amsa,don bazai taba iya mara mata baya tayi qarya ba,don qaryar tana cikin dabi'un da bai iya ba,hasalima abune da idan kanason ganin tsananin bacin ransa kayi mata ita,idan ya gane shikenan,idan bai gane ba Allah ya taimaketa
"Tow yayi,kada ka barta ta wuce one week kaji haidar?"
"In sha Allah daddy"
"Allah yayi muku albarka......ya aikin?" Ya sauka daga kan wancan maganar ya koma masa hirar wajen aiki. Sun dan tattauna da daddy din a taqaice sannan sukayi sallama,ya ajjiye wayar yana dubanta ransa na sake baci da kalar qaryarta
"Kina so ki xama maqaryaciya ko?" Kai ta girgiza da sauri,don ta sanshi farin sani akan yin qarya,duk yadda kake dashi yanzu yanzu zaku bata,yanzu za'a ji kanku akan qarya
(Don Allah,don Allah iyaye mu kula,mu tsaya tsayin daka game da tarbiyyar yaranmu,wallahi wallahi qarya masifa ce,itace silar rugujewar komai da kuma dukkan wahalhalun rayuwa da mukesha,wasu qarairayin kuma daga wajenmu yayanmu suke koya,kiyi qaramar qarya kina ganin batakai ta kawo ba wallahi tana affecting tunanin yaro sosai,misali ungo nan,zo ka ka karba,jeka dauko takalminka mu tafi sai ya dawo ya tarar kin gudu kin barshi,duk da irin haka suke farawa,zasuga au ashe idan na fadi magana kaza ba daidai yadda abu kaza yake ba ashe akwai wani abu da ake cimmawa,ko babansu ya dawo ki karkace ki shirga masa qarya don ki Kare kanki bayan duk suna kallo,da haka saimu wayi gari muga mun cika al'umma da maqaryata,muyita mamaki ina suka samo wannan dabi'a,bayan ba daga ko ina bane daga wajejenmu ne,Allah ya bamu ikon gyarawa ameen).
Siririn tsaki yaja yana kauda kanshi gefe,sai kuma yayi wami gajeran tunani,daddyn ya riga ya damqa amanarta a hannunsa,dole ya kula ma dashi kansa hotel din da zaya sauketa,kafin gobe ya laluba mata inda zata zauna cikin gidajen abokan aiki,don bayason xaman hotel ga mace baliga babu muharrami,don haka ya miqe tsaye yana kallonta,yama fasa suhail din ya kaita,gwara ya kaita da kanshi,fatansa su rabu 'yar mutane ta koma gidansu lafiya
"Wuce muje" ya fadi a dake. Dakewarsa bata dameta ba saboda kaita din da zaiyi da kansa ya mata dadi,hakanma daraja ce,sai yayi gaba yana barwa suhail din sallahun ya jirashi yanzun zai dawo.
Yana fitowa idanunsa suna kan gidan,daidai saitin window din nata, hankalinsa yana kan yaran,bayason ya musu alqawari ya gaza cikawa,don yanason su tashi da dabi'ar cika alqawari.
Seat din driver ya shiga ya tayar da motar. Full light din da ya yiwa motar yana kunnawa sau biyu yana kashewa sai taji tamkar da ita ake sanda take tsakiyar yaran tana qoqarin su qara assignment dinsu. A nutse ta daga kanta ta kalli window din gabanta yana dan tsinkewa, zuciyarta ta bata ko shine zaya dauki yaran?,amma kuma zai kunna mota tun yanzun bayan da qafa zai shigo?. Wannan tunanin ya sanyata kauda kai ta sadda kanta qasa. Duk yadda akayi zai fita ne da wancan yarinyar, that's why bazai iya zuwa ya kwashi yaran ba,iya wannan tunanin ya saukar mata da qunci a zuciyarta.
Kaman goumar yasan tambayar da taketa yiwa kanta kenan saiga muryarsa yana baiwa ama saqo
"Yanzun naga ya maina zasu fita da laila......yacemin zai zo ya dauki su benazeer"
"Sai ya iso" ama ta amsa,don bai boye mata wacece laila ba ta riga ta Santa.
Sosai ranta ya qara baci,ta dinga jin koda yazo ma ba zata bari yaran suje ba,tunda laila gaba take da 'ya'yansa,saita sake karkata hankalinta akan yaran,daidai sanda akayi knocking qofar dakin nata.
"Goumar ne" ya fadi tun bata tambaya ba,daya daga cikin dabi'unsa masu kyau baya taba shiga waje ko inane ba tare daya nema izini ba
"Baqin buzu?" Ta tambaya yau daya tana jin sha'awar tsokanarsa
"Ban sani ba mummyn twins" qaramin murmushi ya qwacewa kyakkyawan fuskarta,inda yasan yanzun sunan baya bata haushi,dadi ma yakeyi mata da bai dinga fadi da zummar ya tsokaneta ba
"Indai ka yarda da baqin buzu sunanka ka shigo,idan baka yarda da sunan ba ka koma"
"Indai kin yarda da matar babban yaaya,matar maina MAYAK'I kike to tabbas zan shigo" dif wuta ta dauke mata,ta xubawa qofan idanu kafin kuma ta sauke idanun nata akan yaran. Kamar suma suna fahimtar abinda yake fada din dalla dalla,dukkansu sun gwalalo mata fararen idanun nan nasu masu wani irin kala irin na ubansu
"Kallon kuma na meye?" Ta jefa musu tambayar tana kallonsu,dariya duka suka saki sai suka maida kansu ga rubutun nasu, daidai nan goumar ya tura qofar ya shigo.
Kamar ko yaushe suka miqe suka maqaleshi ya daukesu sannan suka koma suka zauna. Yawancin lokuta idan ya musu hakan saita tuna sanda maina yake yaya kuma uba a wajenta,fiye da wannan kusancin ne a tsakaninsu.
Daga qarshe dai komawa tayi 'yar kallo,suka gama assignment suka shiga shirmensu su da goumar din,wanda dukansu basa gajiya dashi,sannan tanja ta shigo musu da abinci sukaci,a hankali kuma bacci ya kwashesu suka zube a wajen.
Da murmushi yake dubansu sannan yace
"Yara kun looser......yau ba fita da daddy kenan". Maganar goumar saita zame mata tamkar fami cikin zuciyarta,ta daga idanunta ta kallesu,saita maida kanta ga tattara karikicen karatunsu.
Yadan saci kallonta sai ya fahimci maganar da zaiyi ma kamar ba zata samu gurbin zama a wajenta ba,don haka ya miqe,ya dauki yaran da daya da daya ya fita dasu zuwa dakinsu. Sanda ya dawo tana bakin qofa yana shirin kulle dakin,ya dubeta yasan saki murmushi. Tunda taga yayi murmushin ta tabbatar tsokana ce ta dawo dashi,sai ta dan tsuke gira tana cewa
"Sai kuma me?"
"A'ah,gulman mijinki nazo gaya miki,sai kuma na ganshi da wata bafulatana mazauniyar France zasu fita yawon shaqatawa ke kina cikin gida a zaune" harara ta balla masa, goumar din duk yadda zai bata takaici ya iya
"To sai me?,su wuce the great wall ma,sukai qarshenta su dawwama a can" saita ja qofarta tana rufewa. Tana jiyo dariyarsa daga bakin qofar harda durqusawa,sai ta kasa barin qofa,lokacin yadan daga murya yana cewa
"Kinci bashi wallahi......amma dai ina gaya miki,tabbas mijinki rububinsa ake,abu daya da Allah ya rufa miki asiri shine bame fuskar da za'a tareshi bane,nima kuma ki godemin,don na tsare miki kishiyoyi da yawa" tanason yaba masa baqar magana amma kuma batason yasan ma taji abinda yake fada,saita juya zuwa ciki taja jan tsaki kamar zata tsinke harshenta.
Haka kawai taji komai ya quntace mata,daga bisani ta dinga masifa ita daya da ranta kaman an mata wani abu. Ta gama shirin kwanciyarta kaf,ta matsa bakin qofar dakin ta murza key ta barshi a jiki,don haka kawai jikinta yake bata zaya shigo.
**Daure da towel a qugunsa ya fito daga wanka,faffadan qirjin nan nasa me cike da gargasa sun kwanta luf sunbi jikinsa sosai,sai suka sake fidda qirarsa ta qaqqarfan namiji ma'abocin motsa jiki da daga qarfe.
Agogo ya kalla,sai yaja siririn tsaki,sosai yarinyar ta bata masa lokaci yau,kwata kwata yayi niyyar kama mata wajen kwana ne kawai,amma ta dinga amfani da damarta don tasan matsayin daddy da sardauna a wajensa har sai data tsaya taci abinci,ta saka order din wasu kayan amfanin,wannan ya bata masa lokaci har sukayi dare haka.
Cikin lallausan pyjamas ya shirya kansa,ya wuce kitchen riqe da wayarsa,ya kunna coffee Maker ya hada coffee me zafi sosai saboda iska da take dan kadawa me dadi a daren,iskar data haifar masa da kasala da kewarta me yawa.
Koda ya juye a cup sai ya fita zuwa balcony dinsa,inda zai samu daman kallon gidan sosai. Yana kurba jifa jifa yana duba wayarsa,rabin hankalinsa kuma yana kan gidan dake dauke da halittu mafi soyuwa a wajensa a duk fadin duniya.
Ya kusa minti goma sha biyar kafin ya shanye din,ya ajjiye mug din yana jin kewarta tana qaruwa cikin ransa,gaba daya zuciyarsa da ruhinsa yafi karkata ga yaje yaji duminta,koda na awa daya ko biyu ne,ya tabbatar muddin baije din ba,babu shi babu bacci me dadi,bama lallai ya samu baccin,don haka ya miqe ya ajjiye wayoyinsa gaba daya,ya zura slippers dinsa dake ajjiye a gefe ya fito cikin nutsuwa yana saka hannayensa cikin aljihun pyjamas dinsa.
Batasan adadin sau nawa taji juyi ba daga kwanciyarta zuwa wannan lokacin,wani irin qunci takeji cikin qirjinta sosai wanda ita kanta batasan meye dalilin hakan ba.
Jin da gaske baccin yaqi zuwa saita miqe tana maida cap dinta ta bacci,ta zuro qafafunta qasan gadon tana shirin yunqurawa sai taji ana taba qofar dakin. Da farko ta tsorata sosai,amma daga bisani hancinta ya fara dauko mata qamshinsa yana aiko mata dashi. Zuqar qamshin tayi da kyau,sai taji wani kaso na qullewar da qirjinta yayi yana sassautawa,sai kuma murmushi ya subuce mata,tadan cije lips dinta,hasashenta yayi daidai kenan,dama tasan zaiyi wahala baizo ba,kawai sai ta koma saman gadon abinta ta nannade cikin duvet tana fidda murmushi tana kuma jiyo motsinsa sama sama.
Bayan wasu mintuna taga wayarta tana haske,koda ta duba sai sunan da yayi mata saving dashi ya bayyana,maida wayar tayi ta ajjiye tana murmushin,har tayi iya yinta ta katse.
Iska me dumi ya furzar daga hunhunsa yana maida wayarsa da dole ta sanyashi fita ya daukota cikin aljihunsa,bayason ya matsanta kan sai ya shiga,duk da idan yaso zai shiga din,to amma bayason tada kowa cikin gidan. Kwata kwata issue din laila ya sanyashi baiyi wani dogon nazari akanta ba,inda a nutse yake tabbas zai gano zata aikata hakan,ya watsa hannayensa yana daga kafadarsa,lallai bazai qyaleta ba,wannan abun da ta ciwa kanta bashi ne.
Murmushi me dan qaramin sauti ta saki sanda taji shuru,ta tabbatar ya gaji ya wuce,ko iya yau kadai ta dan rama kadan daga cusa matan da yakeyi ya kuma hanata katabus,da wannan murmushin saman fuskarta bacci ya dauketa.
********Cikin kwanaki biyar din data dauki hutu ko qofar gida bata fita,tana daki zuwa parlor tana hada ayyukanta. Da zarar anyi knocking Bell zata tattara komai ta wuce daki kafin a shigo,wannan ya sanya tsahon kwana uku basu hadu ba,har sai rana ta hudu,ranar da benazeer ta tashi da zazzabi.
Da yammaci ne dukkansu suna zaune a falon, benazeer din an rakwarkwabe jikin ama anata zuba shagwaba,dama yaya lafiyar kura bare tayi hauka,sultana na zaune da system saman cinyarta,gefe kuma kayan sawa na asalin qabilar KANURI,ta gama shirinta tsaf, gobe kawai idan Allah ya kaimu take jira.
Door bell aka kada,sai ta daga kanta daga aikin da takeyi ta maida ga qofar,yau din bata da sauran option dole itace me budewa, benazeer na cinyar ama, batoul tsahonta baya kaiwa,dom haka ta tattare tarkacen dake saman cinyarta ta miqe tana gyara top din jikinta hadi da gyara daurin scarf dinta da santsinsa yasa ya kusa faduwa ta nufi qofar.
Adan darare ta bude,don jikinta yana bata shine. Kaman yadda ta zata din kuwa shine,yana tsaye qyam daga bakin qofar,sanye da baqin trouser da baqar shirt short sleeve data fidda qirar damtsensa sosai. Ya sakaye idanunsa cikin baqin glasses daya fitar da tsananin kyawun fuskarsa,hannayensa dukka cikin aljihun trouser dinsa,wannan ya sanya ya sake cika qofar gaba daya.
Wani mugun kwarjini taji yayi mata,gabanta ya yanke y fadi. Ga mamakinta sai taga tamkar bai ganta ba,ya dauke kansa yana shigowa cikin falon kamar bata wanzu a wajen ba.
_KWANKWASON JIMINA_*
*_TSUTSAR NAMA_*
*_AMEENATOU_*
*_GUDUN KADDARA_*
_DUKKA AYARIN LITATTAFAN KUDINSU YA KAMA KAMAR HAKA_*
LITTAFI DAYA_400
BIYU_800
UKU_900
HUDU_1200
_IDAN TA BANKI NE ZAKI SANYA KUDINKI A WANNAN ASUSUN_
6019473875
Musaa Abdullahi safiya
Keystone bank
_ANTAYA SHAIDAR BIYANKI ZUWA GA WANNAN NUMBER_
09166221261
*Masu tura katin waya ko vtu kuma kai tsaye wannan number zaku tuntuba*
09134848107
*Maqotanmu kuma al'ummar qasar nijer zaku tuntubi wannan number dinne kai tsaye don biyan naku kudin*
09033181070
*ZAFAFA FAMILY na maraba daku*🫂🫂🫂🫂🫂*_GUDUN ƘADDARA_*
*H U G U M A*
BOOK 02 PAGE 102