Showing 36001 words to 39000 words out of 294767 words

Chapter 13 - Gudun Kaddara Book 2 Hausa Novel Complete

tunda tazo duniya bata taba jin digo ko kwatankwacinta cikin ranta game da wata halitta ba.

A hankali sai kuma takai hannunta saman shafaffen cikinta. Itakam har yanzu bata yarda da zancan wai ciki gareta ba,bataji cikinta ya dago ba,bataga ya qara girman komai ba,hakanan batajin komai banda qinson cin abinci da dan banzan fitsari da take yawaita tashi cikin dare,sai kuma rashin lafiyar da ai ita dai tasan normal ne kowa yana iya cuta.

Kamar kuwa jira akeyi takai qarshen tunanin nata taji wani abu ya harba sau biyu a marartata kwatankwacin bugun zuciya. Ta miqa hannu da sauri dai dai gurin ta danne tana zare ido tare da saka ran sake jin wani abu. Saidai kuma tsayin sakanni shuru bataji komai ba,wannan ya sanya ta saki hannun nata hawaye na cika mata idanuwa.

Indai da gaske ne cikinne ita wallahi babu abinda zatayi dashi,d'an maina ne fa kenan ko?,ita zata haifawa baqin mugu azzalumi yaro?,sun hada jini kenan kamar yadda taji ana fada?,Allah ya kiyaye ya kuma sawwaqe ta hada jini da maina,la shakka shawarar bibi itace dai dai,bibi din masoyiya ce ta gaske,wadd bata qaunar kukanta ko damuwarta,batason dukkan wani abu da zai zamewa rayuwarta barazana,tsahon shekaru tana akan haka. Towel din ta maida cikin zafi tana jin cewa gari yana wayewa zata buqaci bibi ta kaita a cire d'an aliyyu daga jikinta,ta tako da kuzarinta daga bandakin tana fitowa.

Tsaiwa tayi daga bakin qofar cikin mamaki tana kallon ama wadda ke zaune sosai cikin dakin,ta kuma qarawa dakin haske da qwayaye biyu dake manne a bango gudun kada sultana din ta tsorata. Idanu ta daga daga inda take zaunen tana duban sultanar,sai ta gyara zamanta tana cewa

"Qaraso ciki,nazo dubaki ne na tarar bakya ciki" sakin qofar tayi tana takowa cikin dakin,har cikin ranta tana jinjina tsantsar kulawar da ama ke bata,ta yadda da wannan dari bisa dari, kowanne motsinta ama na dame dashi,ko yaya kuma ta sauya tana riga kowa fahimta ta kuma bi ba'asin matsalar ta maganta mata.

Wayar hannun nata ta ajjiye bayan sultana din ta zauna tana dubanta

"Sultana,magana nazo muyi dake,ki nutsu sosai ki fahimceni kinji?" Kai ta gyada a hankali tana kallon qwayoyin idanun ama

"Me yasa kikeso ki MUTU?" Ama ta jefa mata tambayar kai tsaye,tambayar data saka sultana zaro fararen idanunta tana duban ama a rude

"Ni kuma ama?,ni nakeso na mutu?,banaso na mutu ama......"

"A'ah,qarya kikeyi,keda bibi duka so kukeyi ki mutu" sake rudewa tayi ainun,saboda kalmar mutuwar girma take mata

"Allah a'ah ama,banaso"

"Amma kikeso a zubda miki ciki?,bakisan duk wadda aka zubarwa da ciki mutuwa takeyi ba?" Tsam tayi tana duban ama hawayen nan nata da basu da wuyar fita tana zartowa daga idanunta. Tsaf ama ta karanceta,da alama abu ya fara tabata,saita dora da cewa

"Ungo wannan ki gani,ki kuma karanta,adadin mata nawa ne suka mutu duk akan silar zubda ciki" hannu tasa ta karba din,ta shiga folder din da ama ta shirya komai ta soma kalla wani kuma ta karanta bayanan da suke da harshen France.

Bata iya qarasawa ba cikin matuqar tsoro da razani ta miqawa ama wayar hannunta yana rawa,ama tasa hannu ta karba tana dorawa da cewa

"Dukansu KARUWAI ne sultana, ba'a daura musu aure da ubannin masu cikin ba,me zai kaiki layin karuwai?,don kawai kin tsani MAINA......"

".......ama don Allah,daina kiran sunansa" ta fadi da sautin kuka sosai,tana jin mafitar da take hango qofarta a bude qofar ta ida rufewa ruf,gaba kura baya sayaki,ashe sauqin da take hasashen samu babu shi,ta tsorata da irin bayanan data gani,itakam ya za'a yi taso ta mutu haka?,da irin wadannan shekarun qanana?.

"Na daina kiran sunansa sultana,kiyi haquri......amma.......ki share hawayenki,ki kuma bani aron hankalinki nan" shuru ya ratsa dakin na wasu mintuna sultana na qoqarin saisaita kanta sannan tadan samu 'yar qaramar nutsuwa

"Kin yarda bakison ki mutu?" Ama ta tambayi sultana. Da sauri ta daga mata kai

"Amma tunda bibi tayi zancan bansan ta yadda zance mata kada a zubar ba"

"Ni nasan yadda zan hana haka faruwa don banason ki mutu,abinda nakeso kawai shine,kibar cikin ki haihu,zan karbi ko meye kika haifa ke kuma kiyi tafiyarki kiyi rayuwarki babu me takuraki,kinga shikenan babu ke ba mutuwa"

"Amma wajen haihuwar ai ake mutuwa ama" ta fada da sautin quruciya fal muryarta

"Inji wa?,inda haka ne suk da bamu haifeku ba ai ko?,waye a cikin gidannan kika taba gani ya mutu don zai haihu?" Shuru tayi tana son tunawa. Babu,babu wadda ta gani ko ta sani iya wayonta da akace ta mutu wajen haihuwa,amma wajen zubda ciki kuwa gasunan yanzun ta gansu da idonta bila adadin.

"Kin yarda zakibi dukka tsarina ni kuma na tsallakar dake daga fadawa mutuwa?" Duk wanda zai kauda maka mutuwa aiba abun gudu bane,bare ama din da zuwa yanzu take jinta kamar mahaifiyar data haifeta,don haka ta gyada mata kai

"Da kyau,amma abinda nakeso fa dake shine,kada ki gayawa kowa wannan maganar da mukayi dake kinji ko?,idan ba haka ba zasu daukeki sukaiki gun cirewa da wurwuri kafin na gama nawa tsarin"

"To ama"

"Yayi kyau,maza kwanta sai da safe,kada kuma kiqiyin bacci kinji ko?komai zai wuce in sha Allah" Kai ta jinjina mata. Ama bata bar dakin ba sai data tabbatar ta kwanta,ta kuma lullubeta ruf sannan ta kunna mata karatun qur'ani da madaidaiciyar qira'a ta kashe hasken dakin sannan ta fice.

A daren bata kwanta ba sai data ci rabin plan dinta,don tana ganin tana kwanciya kamar lokaci zai qure mata,don bata da isashen lokacin gama komai da komai da takeso.


*_KWANKWASON JIMINA_*

*_TSUTSAR NAMA_*

*_AMEENATOU_*

*_GUDUN KADDARA_*

_DUKKA AYARIN LITATTAFAN KUDINSU YA KAMA KAMAR HAKA_*

LITTAFI DAYA_400
BIYU_800
UKU_900
HUDU_1200

_IDAN TA BANKI NE ZAKI SANYA KUDINKI A WANNAN ASUSUN_

6019473875
Musaa Abdullahi safiya
Keystone bank

_ANTAYA SHAIDAR BIYANKI ZUWA GA WANNAN NUMBER_

09166221261


*Masu tura katin waya ko vtu kuma kai tsaye wannan number zaku tuntuba*

09134848107

*Maqotanmu kuma al'ummar qasar nijer zaku tuntubi wannan number dinne kai tsaye don biyan naku kudin*

09033181070


*ZAFAFA FAMILY na maraba daku*🫂🫂🫂🫂🫂*_GUDUN ƘADDARA_*

*H U G U M A*

BOOK 02 PAGE 19


A daya daren kuma ta kammala shirinta gaba daya,cikin daren da kowanne ya kwanta a cikin gidan,daren da suke sanya ran washegarin safiyar ranar za'a fita da sultana a zare tayin cikin......a daren ta shammaci kowa a cikinsu,harda 'ya'yan cikinta saddi da almu,a daren dai ta fice daga gidan,ITA TANJA DA SULTANA ba tare da sani ko ankarewar kowa ba.

K'arfe sha biyu na daren ranar amma tamkar rana ce cikin zuciyar ama. Mace mai kamar maza wanda ko sau daya tun daga quruciya zuwa girma zuciyarta batasan karaya ko tsoro ba. Ita ke tuqa motar da hannuwanta ba tare data dorawa kowa nauyin tuqata ba bare a buqaci sanin ina ya kaisu?.

Gudu kawai take shimfidawa cikin lafiyayyar motar tata,sultana na bacci abinta lakadan a baya,tanja na zaune daga gefan ama din tana rarraba idanu. Har yanzu cikin fargaba ita take,ga tsoron daren da suke ketawa saman shimfidaddiyar kwaltar da zata sadaka har cikin qasar nigeria.

"Ki saki jikinki tanja,ba abinda zai biyo baya sai alkhairi,ba kuma abinda zaya faru" ama ta fadi idanunta nakan kwalta data cika da full light na fitilun motar masu tsananin haske. Ajiyar zuciya ta saki tana gyara zamanta

"Amma hajiya,bakya tunanin dole zasu bibiyi inda muke?"

"Ta yaya?,na cire duka layukan wayata,sannan koda yayyena da muke uwa daya uba daya basusan inda na nufa ba,tanja......zan iya sadaukar da komai nawa saboda na kubutar da cikin maina......zan iya sadaukar da numfashina dama rayuwarta,JINI NA NE......jinin maina ne" ta fada zuciyarta na tsinkewa,rauni yana son saukar mata don batasan a nahiyar da mainan yake ba,bata kuma san a wacce duniya yake ba a yanzun.

Dai dai sanda saqonta ke sauka ga wayoyin dukkan mutanen dake da muhimmanci a gareta,suka kuma cancanci tayi musu bankwana dai dai lokacin tayoyin motocinta ke shiga qasar KANO. ta zabi kano dinne saboda tasan zaiyi wuya hankali yakai can,asalima ta zabi kano ta zama hanyar fitarta daga nijer da nigeria din gaba daya, saboda batasan kowa ba acan,basu da kowa ballantana a samu fargabar wani da suka sani ya gansu.

Ba bata lokaci tabi cikakken kwatancen da dillalin data kama hayar gidan na sati biyu a hannunsa ya turo mata. Cikin kwanciyar hankali ba tare da kuskure ko batan kai ba sai gasu sun isa qofar gidan dake jerin rukunin gidajen SHARADA NNDC QUATERS.

"Alhamdulillah,alhamdulillah,allahumma inni as'alukal birru wattaqwa" ama ta furta tana zare belt din jikinta sannan ta buda murfin motar tana fita.

Seat din baya ta bude,sultana dake zaune kawai ba tare da sanin ainihin meke faruwa da ita ba ta daga kai suka hada ido da ama. Murmushi ama ta sakar mata

"Sannu daughter,fito mu shiga ciki ki huta" tayi maganar da sakakken murmushi akan fuskarta hadi da miqa mata hannunta. Ba musu ta kama hannun aman ta fito da ita,sai ta miqawa tanja key tana cewa

"Ki bude ku shiga ciki,zan daidaita parking motar sai na biyoku". A ladabce tanja ta karba,tana gaba sultana dake takawa da qyar tana biye da ita,don bata tana kusan doguwar tafiya irin haka a mota ba. Duk inda zasu muddin yanabda airport to tabbas jirgi zasubi suje su dawo,zata iya cewa wannan shine karon farko data taba shigowa nigeria ta mota.

⚜️⚜️Ya sani har ya kwanta bacci bata shigo dakin ba,to amma yayi tsammanin taras da ita bayan ya farka sallar asuba amma sai yaga lokacinma wayam. Yayi tsammani dukka fushi takeyi dashi akan maganar da Bibi tun ta shekaran jiya,to amma shi ya dauka zata yi masa uzuri,ta dauki bibi a mizanin mahaifiya wadda bazai iya musanta mata ba,saidai yayi mata gyaran kusakuranta cikin hikima idan buqatar hakan ta taso. To a lokaci irin wannan,matsalar sultana da maina matsala ce me matuqar sarqaqiya,dukkaninsu daga maina har sultana babu wani wanda zaiqi a cikinsu,babu kuma wanda bayaso,saidai dole yayi kaffa kaffa game da duk lamarin da ya shafi maina,saboda gudun son zuciya ya shigo ciki,ko kuma duniya tayi masa kallon maras adalci meson kansa da d'ansa,dole ya sanya buqatun sultana da maslaharta a gaba data maina,kodon maraicinta.

Bayan ya gama addu'o'insa ya jawo wayarsa da zummar kiran ama din ya nuna mata kulawa ko yaya ne,ko ba komai ita din uwa ce,itama tana jin yadda kowa yakeji a ransa game da d'ansa,saidai kuma saukar saqon da sunanta saman screen din wayarsa ya katse masa dukka wani hanzari nasa.

_amincin Allah ya tabbata a gareka,nayi imani a sanda saqonnan zai riskeka tuni na jima da yi muku nisa ni da d'iyata kuma surukata,inason shaida maka cewa munyi nisa ni da ita domin tseratar da abun farautarku,nisan da banajin nemanku zai iya cimmana,ina rubuta maka wannan saqonne don baka zabi guda biyu......ko ka jirani har na dawo daga balaguron tseratar da rai nayi.....ko ka sawwaqe igiyar aurenka dake kaina idan kaji ba zaka iya zaman jiran hamdiyya ba,ga yarana nan zasu iya kulawa da kansu na sani haqiqa.......ina muku fatan alkhairi......ina kuma fatan saduwarmu ta gaba ta zama da alkhairi,bissalam_.

Hannunsa ya sanya ya sharce gumin dake goshinsa yana jin wani tashin hankali yana sauko masa. Babu MAINA babu HAMDIYYA sannan kuma babu SULTANA gaba daya,duka cikin wat uku kacal?,wannan wacce irin jarabawa ce haka ke tunkararsu?,wacce irin musiba ce haka?. Kaman an mintsini aba sai ya miqe cikin hanzari,ko slippers din qafarsa bai maida ba cikin sassarfa ya nufi sashen ama.

Loko da saqo na cikin sassan ya fara bincikewa kamar wani zautacce,kaf ya karade sannan ya koma kewayen gidan ba ama ba dalilinta,sai ya sake komawa bedroom dinta a nan yaga shaida. Ta kwashe duk wani abu nata me muhimmanci kamar yadda maina yayi. Haka dakin sultana an kwashe kusan komai nata me muhimmanci,a farfajiyar gidan kuma da ya duba yaga babu motarta guda daya,a nan ya saddaqar da cewa lallai abinda ta fada din da gaske ne.

Bai tsaya duba qarfe nawa ba a sannan ya soma dokawa abdulhakeem kira. Da alama yana kusa da wayar,don bugu daya ya dauka. Abirkice aba ke tambayarsa hamdiyya ta iso?.

"Ta iso ina?" Ya tambayeshi cikin daurewar kai

"Don Allah idan ta iso kada ku bata dama ta sake fita ko ina"

"Akan me kake magana ne hamidou?,ina hamdiyya din tace zata je?,ina cewa ko jiya munyi waya tana nan nijer,bata kuma cemin zata zo Nigeria ba" komawa da baya aba yayi ya zauna,sannan ya warwarewa abdulhakeem komai.

Shi dinma ya rude,don har yanzu ana ju da auta,wanann gatan da soyayyar ba inda suka je,musamman mutuwar iyayensu ya sanya sun sake dora mata gata

"Kada ka damu aba,muddin tana cikin Nigeria dinnan ba zata fita ko ina ba,zamu dubata kuma zamu tabbatar ta dawo dakinta" abdulhakeem ya fadi cikin fargaba xa kaduwa,duk da yana boye hakan a zahiri gudun sake jefa aba cikin wata damuwar.

Ya jima zaune a wajen,baisan ta yaya zai tunkari bibi yace mata ama ta dauke sultana ba, ba'a san kuma ina suke ba,ina suka dosa?,sanda kuma zasu dawo din kwanaki ne da suka tasamma watanni sha biyu qila harda doriya.

Yana wannan tunanin sai ga Omar kamar an jefoshi,wayarsa a hannu,ya tsaya gaban aba yana miqa masa Wayar. Hannu ya sanya ya karba yana dubawa. Saqo ne dai daga hamdiyya tana dora ma Omar din alhakin yiwa bibi bayani

_"Ka gaya mata Omar ta kwantar da hankalinta,nayi alqawarin dawo mata da sultana cikin aminci"_ wannan shine statement dinta na qarshe.........

⚜️Komai akwai cikin gidan,kusan ba abinda suka shiga dashi sai kayan sawarsu da ba wani masu yawa ba,sai kuma kayan abincin gida da tayi order ta wani app suka iso gidan babu dadewa suka dire mata komai.

Sai bayan magariba ta nutsu,wunin ranar suna dan gyare gyare cikin gidan ita da tanja,sultana na baccin gajiya,zuwa magariba din har abincin dare tanja tayi,bayan sallar isha'i dukkansu suka hadu cikin madaidaicin falon da duka duka baifi girman toilet din ama ba nacan nijer da kuma gidanta na nan dake abuja ma.

Zuwa magariba tanja da ama sun kintsa gidan tsaf,duk kuwa da cewa bawai zama zasuyi ba gaba zasu qara nan da wasu 'yan kwanaki amma ama ta tanadi komai da zasu buqata a kwanakin,ciki harda abincin ci ruwan sha da drinks.

Zuwa magariba har girkin dare tanja ta gama. Ama na gama sallar magariba din ta fito falon tana cewa tanja

"Shiga ki duba sultana,tun yamma data kwanta banji motsinta ba" ta fadi tana zama saman kujerar falon hadi da kunna tv plasma din dake zaune saman TV stand.

Bata da wata sanayya da gidajen tv sosai,don ba ma'abociyar kallo bace,don haka tabar tv din saman channel din dake haska labarai a dai dai lokacin.

Bata gama maida numfashinta ba tanja ta fito a dan rude

"Hajiya zazzabi ne ya saukarwa sultana fa,kuma irin me zafinnan da likita yayi magana akai" ajjiye wayar hannunta da zuwa yanzu ta sauya layi zuwa na Nigeria,shima temporary ne,don dole tana da buqatarsa wajen neman visa dinsu da kammala komai na tafiyarsu,uwa uba kuma ita din ma'abociyar hawa social media ne duba labaran kasuwanci da sauran al'amuran da suka shafi rayuwa

"Subhanallah,ya salam,muje na gani" ama din ta fada hankalinta yana dan daguwa.


*_KWANKWASON JIMINA_*

*_TSUTSAR NAMA_*

*_AMEENATOU_*

*_GUDUN KADDARA_*

_DUKKA AYARIN LITATTAFAN KUDINSU YA KAMA KAMAR HAKA_*

LITTAFI DAYA_400
BIYU_800
UKU_900
HUDU_1200

_IDAN TA BANKI NE ZAKI SANYA KUDINKI A WANNAN ASUSUN_

6019473875
Musaa Abdullahi safiya
Keystone bank

_ANTAYA SHAIDAR BIYANKI ZUWA GA WANNAN NUMBER_

09166221261


*Masu tura katin waya ko vtu kuma kai tsaye wannan number zaku tuntuba*

09134848107

*Maqotanmu kuma al'ummar qasar nijer zaku tuntubi wannan number dinne kai tsaye don biyan naku kudin*

09033181070


*ZAFAFA FAMILY na maraba daku*

*_GUDUN ƘADDARA_*

*H U G U M A*

BOOK 02 PAGE 20


Riris ta sami jikin nata,dole ta soma laluben asibiti dake kusa da GRA din ta hanyar taimakon MAP. Allah ya taimaketa ta samu wani private hospital nan kusa dasu wanda ko a qafa ma kana iya takawa.

Ta sani dama babu makawa,qarin ruwa ne dole shi za'a mata,saboda irin wannan zazzabin gaba daya sanyawa yake lokaci daya ruwan jikinta yayi qasa. Nan gabanta suka kwana, tausayin sultanan yana ratsa ama. Ta hadu da azababben laulayi me zafi,bata sani ba ko harda quruciya a ciki?.

Cikin


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login