Showing 174001 words to 177000 words out of 294767 words
Chapter 59 - Gudun Kaddara Book 2 Hausa Novel Complete
don biyan naku kudin*
09033181070
*ZAFAFA FAMILY na maraba daku*🫂🫂🫂🫂🫂
*_GUDUN ƘADDARA_*
*H U G U M A*
Book 2 page 91
Hawaye kawai take fiddawa ta gaza aiwatar da komai,itakam me ya maidata ne?,tun daga sanda suka hadu a France bashi ds aiki sai luguguitata,ya maidata kamar wani babyn wasa?,meye ya rage ne a jikinta bai taba ba?,meye ya rage a jikinta hannunsa da bakinsa baikai wajen ba.
Bata da qarfin qwatar kanta don haka hawaye da idanu sune kawai nata,har sai da yayi me isarsa ya gama,ya saketa yana maida numfashi amma kukan da yaga tanayi ya sanyashi sake kamota har zuwa saman sofa din dake dakin. Qafafunsa ya raba ya sanyata a tsakiya,bayanta ya jingina da qirjinsa yana sauke numfashi a hankali idanunsa a lumshe,har sai daya daidaita numfashin nasa ta yadda zai iya magana.
"Inata tabaki bakiso ko?, I can't control my heart.......if you know what double means to soyayyarki ce.....na soki tun kina zallar jini a jikin nafessa.......na soki lokacin da kika wanzu a mahaifarta,na soki sanda kika shaqi iskar duniya,na kuma dora da sonki tun daga wannan ranar kawo yau........abinda ya faru tsakaninmu na tabbatar ubangiji ya hukunta hakan saboda ya mallakamin ke......banda hakan ya faru da bazan taba ganewa cewa ina sonki so na soyayya ba......bazan taba gane ina sonki so na auratayya ba,zanta dauka cewa so nake miki na 'yan uwantaka,so irin na uba da 'yarsa ne kawai,zan yita fafutukar mallaka miki miji na gari ne ba tare da nasan cewa ni din nine nafi cancanta dake ba.....ke jinina ce sultana kuma ruhina,ko baki sona,koki yarda ko kada ki yarda ke din BUGUN ZUCIYATA CE......I can't stop loving you till my last breath........Tu es mon bonheur, tu es ma vie(kece farincikina kece rayuwata" ya furta yana sakin gauron numfashi da ya motsa zuciyarsa.
Wani irin takejin kalamansa cikin zuciya da jikinta,gaba daya yanzun bata fahimtar kusan komai,siririn kukanta kawai ke fita yana ratsa kunnuwa da zuciyarsa,duk sanda take kuka irin wannan wannan kukan nata na quruciya yake tunawa,wanann kukan data dinga yi masa sanda ya karbe jaririn budurcinta da bai gama cika ba
"Me kikeso?" Ya tambayeta calmly don bai qaunar kukan
"Ka maidani....."
"Ya isa.....muje" ya fadi a taqaice yana miqewa. Tsam ta miqe itama,cikin jin nauyi da kuma jin tur da abinda ya faru ta tsinci kayanta da suke d'ai d'ai cikin dakin. Jikinta ba qwari ta maida scarf dinta saman kai,ta lalubo hand bag dinta da sauran tarkacen agogo da dankunnenta da ya ciresu daya bayan daya ba tare ma da yasan yayi ba. Dukka bata da lokacin maidasu jikinta,don haka ta tattarasu ta watsa cikin jakar,ta xura takalminta tayi tsaye a bakin qofa tana jiransa,kamar wadda za'a ce ket ta zura da gudu
A nutse ya isa wajen saqale suit,suit dinnasa ya dauka ya maidasu jikinsa,ya gyara musu zama sosai a jikinsa,ya tsaya gaban mirror din dake saqale a kusurwar office din saman dressing table ya dauki comb yana gyara hair style dinsa. Cikin second goma ya koma tsaf abinsa,tana tsaye tana satar kallonsa,cikin ranta tana gulmarsa sanda yake daura agogon hannunsa saman lafiyayyar fatarsa me wadatar gargasa
"Har yanzun wanann shegen iyayin da gwallin kamar mace yana nan" ta fadi a ranta tana tuna sanda yana maina dinsa,dan jami'a cikin jami'ar niamy,yama akayi ne ya zama likitan zuciya?,bayan ya taso a matsayin soja kuma likita?.
Murmushi me sanyi ya saki ta gefen bakinsa yana daura agogon,ya kamata sosai tana satar kallonshi amma ita din bata sani ba,sai ya kauda kai har sai daya gama daura agogon nasa sannan yadan yardar da hannunsa yana cewa
"Idan baki qoshi da kallona din ba...... ni ba sauri nakeyi ba,mu zauna ki qarasa saimu wuce", mugun firgita tayi dataji ya fadi hakan,ta wani basar tana juya masa baya,ko zata yarda da kowanne sharri nasa amma banda wannan,bakinta ta murguda cikin jin haushin me zata kalla?.
"Allah ya sawwaqe,me zan kalla?"
"To ni na sani ne?,kinsan ance tsakanin miji da mata ai sai Allah ko?,na sani ko kewar......." Kaman tasan me zaya fada tayi hanzarin tararsa da fadin
"Pleeeeassseee......." Tana dora hannunta saman kunnenta gami da runtse idonta da kyau. Tilas siririyar dariya ta kubce masa,ya dauki wayarta data manta ya fara takowa har ya iso bakin qofar,sai yasa dukka hannunsa saman kafadarta yadan matsar da ita gefe,ya zura hannunsa cikin Jakarta ya ajjiye mata wayar sannan ya zura key din daya lalubo yana bude qofar,dukka idanunsa bisa fuskarta yana hango yan qananun kamanni tsakaninta da su batoul can qasa qasa,yayin da idanun nata suke a rufe,amma kuma tana iya feeling idanun nasa cikin jikinta.
Nishadi yakeji sosai cikin ransa tare da wani energy cikin jikinsa,don haka ya saka slow music dake tashi da wani sassanyan sarewa,wannan ya taimaka qwarai wajen kashe mata jiki,tayi relaxing sosai jikin kujerar tana aje numfashi,qamshinsa da takeji duka ya buwayi hancinta,ko ina na jikinta idan ta motsa qamshinsa yake bata.
Idanunta a rufe saidai batasan inda suka nufa ba,tadai dauka zaya kaita ne TV station din. Duk bayan wasu mintuna sai ya juya yadan kalleta,hira yakeso suyi koda fada ne,koda tsonakarta yayi amma kuma yadda ta tsume din yasan ba zatayi magana ba,don haka yana sane ya dauke kan motar zuwa babban titin dake da yawaitar shops a wajen.
Daya daga cikin shop din da yafi siyayya a ciki ya tsaida motar,sai a sanann ta bude fararen idanunta a hankali,ta zauna sosai tana duban wajen,sai taji zuciyarta na narkewa. Da gasken yake bazai kaita ba,kalaman bakinta dukka ya qarar dasu,batasan ta yadda ma zata fara roqarsa ba.
Dubansa tayi sanda ya zagayo ya miqa mata hannunshi.
"Koda sau daya ya kamata mu siya gift na birthday din su benazeer tare......ko don farincikinsu......na tabbatar zasuji dadi" kanta ta kawar gefe,kaman ba zata ce komai ba,kaman kuma ba zata motsa ba,sai kuma ta juya a hankali ta zura qafafunta waje yasa hannunsa ya riqe hannun data hanashin
"Kada ki zama marowaciya mana......i need these soft hands" ya furta yana laluban hannayenta ya matsesu gam cikin nashi.
Babban shop ne da suke saida kowanne irin nau'inkan kaya da suka shafi yara. Kaya masu kyau da daukan hankali. Sukayi tsaye a bangaren chocolates yana goye da hannayensa bayan ya zame hannunsa daga nata a nutse
"For the first time daddy da mommy zasuyiwa yaransu siyayya" ya fadi yana kashe mata ido gami da dage mata gira guda daya. Kanta ta kawar gefe tana jin wani iri,kalmar daddy da mommy din tana mata girma da yawa. A tausashe yaja hannunta
"Oya.....choisissez la bonne chose pour eux(zabar musu abinda ya dace)" ya fadi yana daukan cart. Dole ta fara takawa tana duba kayan.
Dab da dab yake da ita,kusan ko cikakken taku daya babu na tazara a tsakaninsu,yana bibiye da ita. Duk sanda jikinsa ya gogi nata sai taji wani iri,shikam kamar ma ko a jikinsa ko kuma da gayya yakeyi ne bata sani ba. Duk sai ya nemi sukurkuta nutsuwarta,har ta dinga zaben wasu abubuwan ba dai dai ba
"Huta kawai,suis-moi(biyo ni)" komawa baya tayi tana biye dashi,tana noticing nasa komai zai dauka me tsada ne,komai nasa me kyau yake zaba hakanan wanda yake bada kala da nutsatstsen nau'i,hakanan komai ya dauka din sai taji yayi mata dari bisa dari,batasan dalili ba,ko har yanzu wannan chemistry din dake tsakaninsu yana nan?,don ko a baya kusan zabinsu akan komai daya ne.
A karan kanta taga siyayyar ta fara yawa,amma kuma batason masa magana kan hakan. Sanda ya fara jidar musu turare saita koma baya kawai ta zubawa sarautar Allah Ido
"Ba abinda yaran suka rasa,wannan abun kamar almubazzaranci ne ai" cart na uku daya cika ya saki ya waiwayo,sai suka hada idanu
"Bance kice komai ba,m'as-tu entendu?(kinji ni?" Ya furta da sigar seriousness cikin maganarsa
"Nima shishshigi na" ta fadi can qasan zuciyarta tana dauke kanta. Murmushi kawai ya saki,yasan taji haushi ne da tsaidatan da yayi,baya jin ko meye zai kashewa yaran zai biya zai kuma sauke haqqinsu dake kanshi,a dukka tsahon shekarun yana jin kamar ya dawo dasu yayita hidima musu ita dasu din gaba daya.
Kusan awa guda suka kashe cikin shop din,suka kuma cika bot din motar da siyayya me yawan gaske.
Sake zubawa sarautar Allah ido ta sakeyi sanda suka dauki hanya,saidai ga mamakinta TV station Street ya hau. Batace masa uffan ba tana jira taga me zayayi,sannu a hankali sai gasu cikin harabar gidan,ya samu parking lot ya tsaida motar,ya kasheta ya waiwayo yana dubanta
"Kije ki dauki excuse" maganar yadan bata mamaki. Yadda take kallonsa ya tabbatar masa tana da buqatar qarin bayani,sai ya dage mata dukka girarsa
"Wannan shine adalcin kawai da zan iyayi miki,kada ki wuce mintuna sha biyar......." Ya fadi yana duba agogon hannunsa kana ya dauke dubansa daga kanta kaman baiga kallon zallar mamakinsa da take jifansa dashi ba
"vous perdez votre temps(kina bata lokacinki)" ya fadi still ba tare daya dubeta ba.
Ba sanin jiya ko yau tayi masa ba,hakanan a sanin yau dinma wasu sabbin halaye da kuma dabi'u yake fitarwa,kulashi din tamkar baiwa kanta horo ne kaman yadda ya alqawarta mata,dole ta bude murfin motar tana fushi tana kumburi ta fice,saidai kuma itama zata d'ana masa,wannan mulkin mallakar da yakeyi mata ba zata bari ba.
_KWANKWASON JIMINA_*
*_TSUTSAR NAMA_*
*_AMEENATOU_*
*_GUDUN KADDARA_*
_DUKKA AYARIN LITATTAFAN KUDINSU YA KAMA KAMAR HAKA_*
LITTAFI DAYA_400
BIYU_800
UKU_900
HUDU_1200
_IDAN TA BANKI NE ZAKI SANYA KUDINKI A WANNAN ASUSUN_
6019473875
Musaa Abdullahi safiya
Keystone bank
_ANTAYA SHAIDAR BIYANKI ZUWA GA WANNAN NUMBER_
09166221261
*Masu tura katin waya ko vtu kuma kai tsaye wannan number zaku tuntuba*
09134848107
*Maqotanmu kuma al'ummar qasar nijer zaku tuntubi wannan number dinne kai tsaye don biyan naku kudin*
09033181070
*ZAFAFA FAMILY na maraba daku*🫂🫂🫂🫂🫂*_GUDUN ƘADDARA_*
*H U G U M A*
BOOK 02 PAGE 92
Minti goma kacal ta dawo,fuskarta a dan daure,don gaba daya abinda aka tsara zasuyi a yau din yayi silar rushewarsa,sai uzurin tana da maras lafiya ta basu.
Qofar motar na bude don haka yayi tsammanin shigowarta,maimakon haka sai yaga ta cake daga bakin qofa. Tana da yaqinin yanzun haka gida zaice zai kaita,ita kuma ba zata taba lamunta a gansu tare ba kaman yadda aka gansu a nijer,idan aka gansun tare wanne sauran dalili gareta?,me zata cewa ama ko aba?, infact ma ita batason kowa cikinsu ya ganta dashi.
"Excuse me.......baki gaji da zaman Tv station din bane?" Ya tambayeta cikin zolaya ta window din motar
"Let's go......lokaci yana qurewa.....na tabbatar batoul zasuyi kewanki if kika je musu late"
"A motata zan koma gida tunda a ita na fito" ta fadi tana basarwa. Dan nazarinta yayi na wasu daqiqu,sai ya amsa da
"Is okay,yayi" yana buda murfin motar ya fito. Wayarsa ya ciro daga aljihu bayan ya haye bayan motar,yakuma yi magana da bata wuce ta minti daya ba kacal sannan ya kashe ya maida wayar aljihunsa. Baice mata komai ba ya fidda daya wayar tashi yana latsawa,ba'a cika mintuna ba babban qofar station din ya bude motarta ta shigo.
Motar tabi da kallo tana mamaki,sam ita ta manta ma da batun motar tunda tsoro ya kamata a lokacin. A nutse ya sauka daga motar ya doshi farin bafaransen da ya fito daga motar. Key ya karba daga hannunsa ya miqa masa wani key din,sannan ya juya a nutse ya dubeta
"Bismillah" ya fadi yana bude mata front seat. Idanunsu suka hadu waje daya,ya zuba mata ido yana sauke mata nannauyan kallo da idanunsa. Zare idanunta tayi daga kansa,lallai sai qafarta qafarsa?,ta yaya zata musa masa?,bata sani ba,don haka dole ta sauke hannuwanta ta soma takawa a nutse tana nufar motar.
Da wani sassanyan kallo yake qarewa takunta kallo,komai nata a nutse kamar ba baby sultanarshi gwanar rawar kai ba,komai nata ya canza,yana hangen tasirin fushi kadan kadan daga can tsakiyar idanunta,withtime zai wanke komai daga cikin zuciyarta kamar komai bai faru ba,yana sanya ran hakan in sha Allah.
Maida murfin yayi ya rufe,sannan ya zagaya seat din driver ya shiga,ya kunna motar amma bai tasheta ba,ta mirror tana iya hangen yadda suke debo kayan suna maidawa boot din tata motar.
Sai da suka kammala sannan yayi bismillah,ya tayar da motar a nutse suka fice daga gurin.
Daga can farkon street din nasu ya gangara gefe a hankali ya ajiye motar,ya juya barin da take zaune din yana jifanta da wani sassanyan kallo. Cikin jikinta take jin dukka idanun nasa,amma qemene taqi dubansa,har sai da wayarsa dake ajiye a tsakiyarsu ta kada.
Kaman an fusgi hankalinta ta juyo da dan hanzari,sunan AYANA shi yake yawo kan screen din. Sai daya gama qarewa sunan kallo sannan ya miqa hannu ya kashe sound din ya maida wayar silent,sannan a hankali ya maida idanunsa kanta. Sabanin daxun yanxun waje take kalla ta window din motar. Sai kuma ta sanya hannu ta bude motar tana ficewa daga ciki ba tare data bari yaga fuskarta ba.
_KWANKWASON JIMINA_*
*_TSUTSAR NAMA_*
*_AMEENATOU_*
*_GUDUN KADDARA_*
_DUKKA AYARIN LITATTAFAN KUDINSU YA KAMA KAMAR HAKA_*
LITTAFI DAYA_400
BIYU_800
UKU_900
HUDU_1200
_IDAN TA BANKI NE ZAKI SANYA KUDINKI A WANNAN ASUSUN_
6019473875
Musaa Abdullahi safiya
Keystone bank
_ANTAYA SHAIDAR BIYANKI ZUWA GA WANNAN NUMBER_
09166221261
*Masu tura katin waya ko vtu kuma kai tsaye wannan number zaku tuntuba*
09134848107
*Maqotanmu kuma al'ummar qasar nijer zaku tuntubi wannan number dinne kai tsaye don biyan naku kudin*
09033181070
*ZAFAFA FAMILY na maraba daku*🫂🫂🫂🫂🫂*_GUDUN ƘADDARA_*
*H U G U M A*
BOOK 02 PAGE 93
Ayana ce,ya saki qaramin murmushi saboda kiran yazo masa a dai dai.
Da muryar nan tasa dake matuqar tafiya da ita yayi mata sallama,ta amsa cikin zumudi da kuma karadin nan nata
"Yaa maina......ba call ba tex,why na?"
"Munyi wannan dake?" Ya tambayeta a dake,don ya fahimci rawan kanta yayi mugun yawa. Yayi imani bata sanshi bane a baya da duka batayi irin wannan abun da takeyi yanzu ba
"Nooo...." Ta fada murya a karye tana karyar da wuya
"I think zan samu kulawa tun yanzu,coz next week in sha Allah Ina tahowa nan,zakuyi magana da daddy,naji kaman yace ba cikin school zan zauna ba"
"Alright..... yayi,karbi nan" yace da suhail yana kallonsa.
"Karbi mana,maza ka tayata hira,she's my sister also" ya fada yana cin serious kaman wani abbansa. Dariya tasi kama suhail din,sai kawai yasa hannu ya karba wayar,maina din kuma ya juya zai shige ciki.
"Kunyi magana ne da laila?,tacemin cikin satinnan zata shigo Paris,tanason zuwa ta gaidaka......tayi missing naka,I was surprised da kalamanta,ina ji a jikina anya ba wani abu a boye?" Tsaiwa yayi cak sannan ya juyo yana duban sardauna,kalaman zuwan ayana da zuwan laila suna masa yawo saman kai
"Did she tell you something?" Ya tambayi sardauna,kai ya girgiza yana tabe baki
"No.....kawai yadda take bawa komai naka muhimmanci ne yasa na saka ayar tambaya" murmushi maina yayi, sardauna yana da kara da alkunya,amma rashin maganatuwar laila ga kowa tsakanin daddy da sardauna hakan ya masa,don fadi musun da zatayi tamkar ta masa wani dabaibayi ne
"Kada kayi mata shishshigi to malam ka turata ga abinda ba shine zabinta ba.....wataqila akwai wani a boye cikin rayuwarta" kai sardauna ya girgiza sai maina yaci gaba da wucewa ciki
"Kada ka jima a wankan nan naka,don akwai gurin da zamuje" sardauna ya fadi
"In sha Allah" ya amsa musu a gajarce.
Sama sama ta dinga jin hayaniya da kuma knocking duka lokaci guda,nauyin baccin da tayi ya bata mamaki,taja lokaci sosai,amma kuma ba abun mamaki bane saboda ita kanta tasan gajiya ce sosai a jikinta. Dankwalinta ta dauka ta daura sannan ta sauko daga saman gadon,tasa hannu ta murza key din ta bude qofar ta jawota baya.
Benazeer ce da batoul sanye da fararen singlet da gajeran pant,da alama shiri ake musu na birthday din,don gyaran gashin dake kansu kadai ya gaya mata hakan.
Dukkansu ita suke kallo ba wanda yayi magana a cikinsu,tadan fiddo idanu waje tana dubansu
"What's happening?" Tayi maganar da muryar bacci,cikin idanunsu take kalla,sai take ganin idanun nasu tamkar na maina
"Mommy an kusa a fara fa.....mummy baki shirya ba" benazeer ta fadi a shagwabe
"Bacci nayi yanzun zan fito,shikenan?" Kai suka gyada a tare
"Yes mummy" kasa maida qofar tayi ta rufe har suka wuce,girma yaran