Showing 270001 words to 273000 words out of 294767 words

Chapter 91 - Gudun Kaddara Book 2 Hausa Novel Complete

suke riritawa......na taba halittar da sukewa masifaffen so......muddin na zauna a lokacin fushin aba zai iya lalata rayuwata,don bansan da wanne furuci zai jefeni ba......motsa zuciyar ama da nayi a sannan sannan kuma tana ci gaba da kallona zai iya saukar da fushinta a kaina......na tafi ne da zummar sai kowa ya huce sannan na dawo,ashe wata QADDARAR tana biye da dukanmu.....ashe ke din nabar mikia ajiyar bayin Allah cikinki......ni kuma qaddarar mutanen da zasu kamaji su nemi shigar dani kalar aikinsu yana bibiyata.....da qyar na kubuta daga hannunsu,sunmin daurin talala,sun barni inje dui inda zani,amma duk takuna qwaya daya tak suna biye dashi.....ashe bazanga girman daddyn sardauna ba?,me yasa bazan girmama musu laila ba?,shine silar kubutata daga hannunsu,ya daukeni ya bani kalar rayuwar da nake buri,duk kuwa da cewa......daga ranar dana aikata miki abinda ya farun duk wani buri na na zama soja ya zagwanye ya fita a kaina......na kalli kaina a madubi yafi sau shurin masaki ina gayawa kaina tabbas bani da imani......aikin soja bai dace dani ba.....tunda har na iya haikewa wannan 'yar qaramar babyn ta bibi......na iya sauke mata huqatuna masu girma da nauyi na shekara da shekaru ba tare dana duba qanqantarta ba......ashe dai wannan babyn itace rayuwata.....mabudin farinciki na...... wannan babyn ita zata zama mummy..... Mummyn twins da upcoming triples in sha Allah......." Ya qarasa fadi murmushin farinciki da nasara yana kubce masa.

Duka idanunta ta zaro waje tana kallonsa,sai kuma ta shagwabe masa kwatankwacin yadda take masa a baya

"Do you know how i survived yaa maina.....na kusa mutuwa fa kafin na haif......." Yatsansa ya dora mata saman lips dinta yana fadin

"Shshshsh......." A tausashe

"Nasan komai sulthana..... kowanne motsi na rayuwarki ina da information akai har zuwa rana ta qarshe a hassan gwarzo.....kina cikin depression da anxiety a lokacin...... yanzu kuma ga beloved person a gefanki.....Likitanki,duk da ba bangarena bane amma na miki alqawarin baki kalar kulawar data banbanta data kowa.......ke kika dasamin son twins sulthana......daga ranar dana fara ganin hotunansu benazeer suka zama jarrabawar rayuwata.....Allah ya jarabceni da soyayyarsu irin wadda bayan ke ban taba jin irinta akan kowa ba idan kika cire ama........ashe su din nawa ne......daga randa kuma nasan cewa nawa ne......a ranar burikana suka ninninku....Wallahi,Allah sulthana burina a duniya kiyita haifa min uku uku bibbiyu" hannunsa ta kama tana dariya ta aza saman goshinta,ta buda baki zatayi magana sautin wayarsa ya katsesu.*_GUDUN ƘADDARA_*

*H U G U M A*

BOOK 02 144



Sunan ama ke yawo saman screen din wayar,ya saki sultana yana daga wayar.

"Me kakeyi haka ne aliyyu?,ban gaya maka ga Dr Noor nan ba?"

"Afwan ama....." Ya fada. A tausashe,bata sake cewa komai ba ta katse wayar,shima sai ya kashe yana ajjiyeta a gefen sa.

Ido ya zubawa sultana kaman bazai dauke idanun nasa ba sai kuma yace

"Get ready......yau ko gobe zamu bar gidan nan......zamu tare a namu gidan sulthana bazan iya zama a nan kusa ba" dubansa tayi,tana mamakin hakan da yace,don tayi tsammanin zai rayu cikin gidanne kamar sauran kawunnansu. Kai ya jinjina mata yana miqewa ya nufi toilet.

Tsarki yayi yayi alwala sannan ya fito itama yace taje tayi,ya zare shaddar jikinsa data gama yamutsewa ya sauyasu da wani tattausan yadin vicuna me asalin tsada da aka yiwa aikin kufta na zamani. Ita kanta data fito sai daya dauki hankalinta,ta fahimci gayunshi ya ninka sosai,idan batayi da gaske ba da alama zai nuna mata feleqe da iya ado.

Jawota yayi ya karata da jikinsa yana murmushi

"Idan baki gaji da kallona ba mu zauna,sai na bawa Dr Noor haquri,mu shanye fadan ama tare dake" rau rau tayi da idonta. Duk sanda taga Dr noor sai ta tuna wahalan da tasha cikinsu benazeer,bata tunanin akwai wani guri dake daukan allura a jikinta da ba'a bulashi ba

"Don Allah yaa maina......kace mata kada tayimin allura,ko magunguna kadan don Allah"ta fadi tana narke fuska.

Murmushi ya qwace masa,ya saka tafukan hannayensa biyun duka ya kamo fuskarta tsakiyarsu yana matso da fuskarta dai dai tasa

"Ki yarda dani....duk cikin da za'a raineshi cikin soyyaya da kwanciyar hankali daban yake da wanda ba'a raineshi ta haka ba,zakiyi lafiyayyen ciki fiye dana baya......ba allura ba tarin magunguna ba kwanciya asibiti........in sha Allah" da iya kalaman bakinsa kadai sun saukar mata da nutsuwa,ya sanya mata hijab ya kama hannunta suna wucewa falon.

Bata tashi jin kunya ba sai da suka hada ido da Dr Noor. Ta tuna abubuwa da dama da suka wuce lokacin cikinsu benazeer,wai yau sai gata zaune gaban dr noor din da wani cikin.

Ta dubata sosai ta kuma tabbatar da komai lafiya,amma tace

"A kula da ita sosai,don cikin kamar wancan ne nake tunani" sai ya tuna maganar Dr Camille,satin da tace su koma tahowarsu nijer ya tashi basu koma ba,ya barshi ne da zummar zasu je din idan sun koma paris.

"Wannan karon kamar kinfi jarumta ma.....kamar 'yan uku nake hasashe......" Dr Noor ta fadi cikin salon tsokanar nan nata

"Amma sir maina yaci gari......don ba haka mukayi dake ba......"

"Please don Allah Dr Noor" sultana ta fada tana qunshe bakinta cikin matsananciyar kunya,ta tabbatar tsiya Dr noor zatayi mata,zata tuna mata maganganun data dinga fada ne cikin quruciya da kuma damuwar da ta ninkawa kanta saboda cikinsu batoul.

"Wani abu ne Dr?" Maina dake son ya samu abun tsonakarta ya tambayi Dr noor

"A'ah sir.....abar kaza cikin gashinta" Dr noor ta fadi tana dariya dariya

"Zan iya siyan labarin?" Ya tambayi Dr noor yana duban sultana data marairaice masa dariya nason zuwa masa,ya tabbatar ta sheqa quruciya me yawa shi yasa bataso aji.

"Idan farashin yayi mani sai na siyar" Dr noor ta kuma fadi bayan ta gama hade komai nata

"Dollar dari uku yayi?"

"Ma sha Allah labari yayi tsada......tace ba zata sake ma aure ba bare ta haihu,ta gama haihuwa har abada.....su wadannan ma ita ba ita tayi cikinsu ba su sukazo suka shiga cikinta bata sani ba......kana zaman zamanka abu ya shige maka ciki yayita hura maka ciki cikinka yana zama qato don mugunta bayan kai ko abinci baka iya ci?.......at last kuma ta fashe da kuka......na shiga tausayinta a ranar irin tausayin da ban taba yiwa wani patient nawa ba".

Da farko dariya tazo masa,amma maganar Dr noor ta qarshe ta narkar masa da zuciya har ya kasa dauriya ya sanya hannunshi ya lalubi hannun sultana ya riqe sosai cikin nasa. Bashi ba har dr noor din ma data tuna da labarin kana kallon fuskarta zakaga ta sauya. Ita kuwa murmushi kawai takeyi qasa qasa kanta a qasa, quruciya da wautar data tafka ke dawo mata.

Koda ya bawa Dr Noor Dollar din qin karba tayi,amma ya sanya almu yabita da ita har motarta ya saka mata a seat din baya.

Shuru ya ratsa bayan fitar Dr Noor,ya kasa cewa komai sai murza tafin hannunta kawai da yakeyi,yana hango irin jarumtar da tayi duk da quruciyarta,har yanzu ya kasa hasashen abinda zaiyi mata ya biyata

"Am really sorry sulthana.....har yanzu sai naji kamar idan nace miki kiyi haquri bai wadatar ba"

"Sorry for what ya maina?.....qaddararmu ce.....akwai wanda ya isa YA GUJEWA QADDARARSA,gudun qaddara fa guzurin tarar da ita". Kai ya jinjina yana mamakin yadda taji hausa haka,koda yake Nigeria ta zame musu kamar gida kuma uwa.

Yaso zamansu ya dore a falon amma hakan bai yuwu ba,a hankali a hankali sai ga masu dubiya cikin gidan da baqi sunata shigowa. Dole badon yaso ba ya tattare falon yayi qaura yabar musu nan.

Baisan bayanin da Dr noor ta yiwa ama ba,amma wani sabon salon jinya yaga an fiddo dashi. Ama din ta shigo da kanta sunyi maganganu da sultana,baisan me suka tattauna ba,amma ya damu mutane su janye yaji meye ama ta fadi?. Tanja ta aiko sashen ta soma gyaran wani bedroom din daban,da alama kuma umarni tanja ta samu,duk wani motsi na sultana tana kula dashi,sun hanata komai,komai tana daga zaune akeyi mata shi wunin ranar.

Baya falon amma yana bibiye da komai shima ta CCTV camera din dake cikin falon. Yadda sultana din ta sake cikin mutane ya masa dadi,amma kuma yana jin su nesantashi da ita. Yana jin lokacin cin amarcinsa ne amma sunason kawo masa cikas. Wani abu da yayi masa dadi yadda ya fahimci time to time tana duban sashen dakinsa. Hakan ya masa dadi sosai,mutum ne shi me matuqar son a nuna soyyaya a gareshi,musamman ga abinda shima zuciyarsa ke matuqar so din.

Sanda ya idar da sallar la'asar cikin masallacin layinsu sai yayi zamanshi daga gurin da shekarun baya yafi zama cikin gidan. Iskar wajen tana masa dadi qwarai tana kuma saka masa nutsuwa sosai. Kira ya shigo wayarsa,koda ya duba sai yaga sardauna ne.

Sau biyu yana kira bai sameshi ba,don dama bai kira suhail ba,yasan idan ya kira xasu taba rigima yadda suka saba.

"Boss.....sir.....surukina" duka sardauna ya fada lokaci guda. Murmushin nan nasa me sanyi ya qwace masa

"Kaima yau?"

"Ai dole,ba sake tabbatarwa da nayi dacen dan uwa ba irin wannan lokacin,familyn ama akwai karamci da mutunci,na dace da samun ayana......an bani ayana halak malak"

"Alhamdulillah" maina ya furta a fili. Har cikin zuciyarsa yana jin farinciki yana ratsashi. Duk da sun soshi basu sameshi ba,amma kuma ya musu silar samun mazaje tamkarsa,yayi silar danganasu da inda yake tabbacin za'a riqesu kaman yadda zaiyi nasa qoqarin.

"Saika qara masa da bayanin kawu ya karbeni hannu bibbiyu,laila ta zama tawa" ya jiyo muryar suhail daga gefe. Maganar tasa ta saka dole murmushin ya sake kubcewa maina,ya girgiza kai kawai yana fadin

"Zamuyi waya anjima,amma wannan surukin naka ka samu majanyi da kyau ka daure masa wannan kan nashi dake fama rawa" dariya sardauna ya saki shima suka katse wayar a tare.

Wayar ya mayar gefe yana dora idanunsa ga bangaren sashensa. Yana kallon yadda masu dubiya ke shiga suna fita,ya sake ajiyar zuciya. Bazai iya jurewa ba gaskiya,tunaninsa ya karkata yadda zai dauketa subar gidan.*_GUDUN ƘADDARA_*

*H U G U M A*

BOOK 02 PAGE 145


Koda ya koma sashen bayan sallar magariba still ba ita kadai bace. Daki ya wuce yana kumburi shi kadai,shi ya rasa wannan zaman na meye?,ko haihuwa akace tayi iyaka kenan ko?. Wannan abun ya sanya ya fara yanke shawarwarin bazai ma barta ta haihu a nijer ba,ya tabbatar idan ya barta haihuwa a nan shikam ya kade,tashi ta qare.

Kafin ya fita sallan isha'i ya gwada kiran wayarta,tanata ringing amma bata daga ba,daya duba CCTV din daki sai ya samu wayar saman madubi,da alama a nan ta barta. Yaja gajeran tsaki,ya maida akalar kiran nasa zuwa ga yaronsa.

"A gyara gidan da kyau,duk abinda babu ko ake da buqata a cikin gidan ka yiwa cha'aibou magana a zuba"

"Okay sir" ya amsa masa da girmamawa. Bazai iya jurewa ba,sunzo gida hutu kuma ace an buge dayi masa haka?,haqurinsa a yanzu gajere ainun,gwara komai ta fanjama fanjam.

Daya dawo sallar isha'i ma sai ya samu bata a sassan. Ranshi yaso baci amma daya tuna babu me aikata haka sai ama saiya hadiye abinsa. Ko ina fes an gyara,amma kuma bata ciki,duka sai yaji sashen ya masa zafi,don haka ya wuce toilet kai tsaye.

Wanka yayi ya fito ya shirya cikin wani material cotton transparent na India da aka yiwa dinkin zamani me kyau. Sosai kayan suka karbeshi,turaren nan nasa me sanyin qamshi ya wadata jikinsa dashi,ya dauki wayoyinsa yana duba lokaci. Shi wato kota tashi ba'a yi ma bare a nemeshi a baci abinci?,rabonsa da abinci tun azahar,ya gyada kai,har yanzu fadar sultana kenan bata gama mutuwa ba.

Sai daya shiga sashen bibi ya bata kusan awa daya,suyi hirar arziqi idan abun ya motsa ayi tsiya,har ya gama zamanshi ya miqe yana wucewa sashen ama,don dukka hankalinsa yana can.

Kusan dukkan wata kulawa data bata lokacin haihuwar benazeer da batoul ita ama keson dawowa da ita a yanzun,itama tanata mamaki can qasan ranta, meye Dr noor ta gaya mata daya sanyata takatsantsan da ita irin haka?. Tunda ama tayi kiranta sashen nata ta kuma sanyata ta fadi da meye da meye takeso aje a dauko mata daga sashenta ta dinga tunanin to meye zatayi?.

Daga sanda ta fahimci ama na nufin a sassanta zata zauna sai dukka jikinta yayi sanyi,ta lafe cikin kujerun ama kamar mejin bacci,saidai idonta biyu tana jin yadda aka tashi hankalin tsohon dakinta da gyara.

Wannan karon ko daya bataji farinciki ba,bawai don batason zama da ama ba,ko kuma bata shaida kirki ko jin dadin da ama ke bata ba da dukkan wani nau'in kulawa da riritawa ba..... a'ah,zuciyarce kawai a wanann karon taqi yarda ta karbi nesantata da akeson yi da halitta mafi soyuwa a cikinta.........mutum guda daya tak.....amma daya tamkar da dubu a gareta wato ALIYYU MAINA.

idanunta suna hango yanayin da zai shiga,a yadda ta hangi abubuwa bila'adadin cikin idanunsa akanta.....tasan hakan ba qaramin tabashi zaiyi ba. Bama maina ba,ita kanta bata da tabbas din zata iya jurewa?,zata iya karbar yanayin?. Wani tsohon tsumammen abu ke taso.mata a zuciyarta game dashi,wanda zata iya cewa bata taba jin wani abu irinsa ba a zuciyarta game dashi a wannan lokacin ba.

Zuciyarta ta saba da sassanyan qamshin nan nasa data tsana,a yanzu tana jin kamar ta dawwama tana shaqarsa,dumin faffadan yawaltaccen qirjinsa,laushin da taushin gargasar dake kwance a ciki,dumin jikinsa da kuma dumin numfashinsa dukkansu wani abu ne da idan ta tuna takejin kowacce tsiga a jikinta ta tashi.

Sanda take kaiwa qarshen duka wannan tunanin ta zuqi numfashi kafin ta aje nutsatstsiyar muryarsa dinnan tayi sallama cikin falon.

Dukka jikinta taji kaman an zuba mata wani abu,zuciyarta ta soma sanyi,ta ware fararen manyan idanunta a kanshi. Cikin jikinsa yaji tana a wajen,ya wurga idanunshi kadan take suka fada kanta.

Kamar yau suka fara ganin juna,wani shauqi yana fusgar kowannensu,ta cikin idanuwansu kowanne yake aikewa dan uwansa zazzafan saqo,ya dan qanqance idanunsa kadan kamar me tambayarta wani abu,sai ya sauya akalar tafiyarsa zuwa direction din da take.

Duk taku idan yayi jikinta marabtarta yakeyi,duk motsinsa zuwa gareta sai bugun zuciyarta ya qaru da wani irin dokin zuwanshi gareta. Saidai kafin yakai ga isowar sautin muryar ama ya sanyashi tsaiwa cak sanda take magana ita da tanja suna fitowa daga kitchen din tanja tana biye da ita.

Cikin hikima ya juya tamkar ba wajen yayo ba,saidai akace uwa uwace,kallo daya tak tayi masa ta fahimci ina ya dosa,amma ita dinma sai ta bishi a haka.

Ta wuce zuwa saman kujera ta zauna tana tambayarsa yaushe ya shigo?,tanja kuma ta wuce wajen sultana tana miqa mata bowl cike da kankana da madara.

"Na gode" ta fadi tana karba,ta sauke qafafunta qasa ta aza bowl din saman cinyarta ta fara kaiwa bakinta a hankali. Tun batayi nisa ba batoul da benazeer suka shigo,kai tsaye kowacce ta nema cokalinta zata sanya ciki. Maza maza ama ta korasu tana cewa

"Wanann na mummy ne ita kadai,kuje tanja ta hada muku wani" tanja ta dinga musu dariya tana dan jan kumatunsu

"Tun yanzu yayinku ya fara wucewa,ama ta fara daina yayinku yara" batoul dariya ta dinga yi, benazeer ce ta dan bata rai,don batason ace


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login