Showing 264001 words to 267000 words out of 294767 words
Chapter 89 - Gudun Kaddara Book 2 Hausa Novel Complete
fuska da idanunsa sun sauya,da alama wani abu yana ci masa rai
"Inaso na huta sosai kafin mu sauka a maradi......i need your assistance" ya kuma fadi da muryarsa me laushi. Rasa me zatace masa tayi,dukka maganganunshi guda biyun kamar ya sanyata ne a duhu a kansu,sai ta zabi kawai tayi shuru akan ta furta komai,amma kuma maganarsa nacan qasan ranta tana kai kawo.
Tun daga zuciyarta har gangar jikinta ita daya tasan abinda takeji,tanaso ya fahimceta a hakan da take,ya kamata kuma ace yayi hakan a matsayinsa na wanda ya raineta,rainonsa ce ita.
Wani babban maison d'hôtes(guest house) sukayi masauki. Daga yadda aka karbesu ya tabbatar mata yana da matuqar kima da daraja a wajen. Daki na musamman aka basu,wanda suka taras da komai an shirya cikan dakin.
Ba alatun cikin dakin bane ya dameta,abincin data gani kawai shine a gabanta. Tayita qoqarin mazewa har zuwa sanda ya wuce toilet,ta tabbatar wanka zaiyi zai kuma jima kafin ya fito,tunda tun ba yau ba ta sanshi da jimawa gurin wanka.
Bata jira ya wani fito ya bata abinci yadda ya saba ba ta zagw ta hau qaramin table da aka shirya komai akai. An jima ba'a hadu ba, abincin qasarsu ta gado,yau ko tashin amai da tashin zuciyar ma bataji,ta dinga diban abincin tana aunawa cikinta,wanda batasan ma ta jima zaune tana aikin ciki ba sai da taji cikinta ya dauka,ta ajjiye robar madarar tana hamdala.
Waiwayar da zatayi ta ganshi tsaye bakin qofar toilet,yana sanye da bathrobe data bayyana ni'imtacciyar sumar qirjinsa. Wani irin nauyi taji ya kamata,da alama ya jima yana qare mata kallo,sai kace wata kwancen yunwa?. Yadda tayi tsuru tsuru ya bashi dariya sosai,amma ya danne,yaci gaba da takowa,yanason yaga yau qarshen basarwarta.
Daidai kanta ya tsaya yana duban yadda ta yiwa table din kaca kaca,sai ya miqa hannu yana daukan kwalin madarar data shanye har guda uku yana juyata a hannunsa.
Madararta ta asali,madarar da akayi rainonta da ita,madarar data zame mata tamkar uwa......madarar da jama'a da dama suke jin haushinta saboda ita.
"Inajin nan gaba ni zaki fara cinyewa idan kina jin yunwa......bari na rufawa kaina asiri" ya furta yan jawo wayarsa. Mutum biyu ya kira,duka kiran bai wuce na minti biyar ba,sai ya kashe wayar,yaja kujera ya zauna yana kafeta da idanunshi.
Kai ta dauke,kallon da yake binta dashi yayi mata nauyi da yawa,amma da alama shi sam bayajin haka.
Sau uku tana waiwayowa suna hada idanu,ana hudun taga ya miqe yana ja baya,ya wuce wajen qaramar luggage dinsu ya bude yana fidda kaya.
Kafin yakai ga fara saka kayan tayi wuf ta fada bandaki,gaban mudubi ta tsaya tana fidda idanu kunya tana kamata,ta ware hannayenta tana kallonsu,ita kanta batasan haka taci abincin ba,madarar kuwa a baya kwali daya kawai take iya sha,amma yau gata da shanye kwali uku,ta lumshe ido tana tande baki,sosai madarar tayi mata dadi a harshenta,ta manta rabonta da shan madarar kwata kwata,a yanzun sai takeji ta koma mata sabuwa.
Kafin ta fito ya gama shiryawa yaci abinda zaici ya kuma gyara wajen. Tana fitowa idanunta akan kwalayen dake jibge tsakiyar dakin,mamaki ya kamata,madarartace da take mutuwar so kwali kwali masu yawan data tabbatar zata iya gama rainon cikinta da ita. Ta fara takowa a hankali yana kwance saman sofa bed,bedside lamp ya haske idanunsa don duhun magariba daya fara shigowa.
"Nayi rigakafi?" Ya tambayeta yana kallon kwalayen da idanu. Kunya ta sanyata juyawa baya da sauri tana komawa can bakin window din dakin.
*********Tun daga gate din gidan ta dinga sakin ajiyar zuciya. MAYAK'I mansion house....... gidan da yake da dimbin tarihi cikin rayuwarta,tarihin da bazai taba goguwa ba a rayuwarta. Komai yana nan yadda yake,sai kyau da gidan yake dadawa ko yaushe saboda tsantsar kulawa da yake samu daga mamallakan gidan.
Akwai alamun baqi jifa jifa tun daga farfajiyar gidan,abinda ya sake bata tabbacin da gaske kawai hidima cikin gidan,abinda kuma ya ninka fargabarta,tunani iri iri ya dinga darsuwa a ranta.
Sanda ta shiga falon bibi tsohuwa me ran qarfe,ta sameta zaune ana duba sabbin dinkunan da aka kawo mata ita da masu aikin sassanta. Tana nan yadda take,sai tsufa data qara yi kadan,don a haka tana samun kulawa ta musamman daga 'ya'yanta,kowanne ba baya bane wajen bata kulawa.
Baki bibi din ta kama tana kallon sultana da maina dake biye a bayanta wanda ita sam sultana dinma batasan yana bayanta ba
"Idonku kenan?,tsabar salo ku iso qasar nan ku wani yada zango a niamy,nan din ta muku kadan kenan?" Tayi tambayar tana jifan maina da harara. Itadai sultana Allah Allah take ta qarasa gab da bibi ta samu waje ta qunshe kanta,don gani takeyi kamar bibin na ganin abinda ke tattare da ita,rashin sani batasan tuni bibi ta dade da sani ba,hasalima da abun take kwana take kuma tashi cikin ranta,kullum addu'arta ubangiji wannan karon ka baiwa wannan 'yar marainiyar taka da sauqi,ya ubangiji ka zama gantanta,ka fanshe mata wahalarta ta wancan karon.
Hardewa tayi garin sauri,ta tafi tayi taga taga zata fadi,kafin hakan ya faru tuni maina ya cimmata da wani irin zafin nama ya kuma riqeta tsam,yayin da bibi ma duk da ciwon da qafafunta keyi ta miqe tana zabga salati kamar ba ita ke lanqwashe tana ciwon qafafu ba. Kafeta yayi da idanu qwayar idanunsa na nuna yadda yayi matuqar tsorata da yadda ta tafi zata fadin, muryarsa a maqoshi ya furta
"Sannu......ki dinga kula.....don Allah.... Please" maganar data tabbatar daga tsakiyar zuciyarsa ya furtata,da alama ya kadu sosai da faduwar tata.
Zame jikinta tayi a dabarance saboda idanu na kansu,kowa kuma sannu yakeyi mata,ta gyara lullubin kanta tana mamakin yadda bibi keta sababin batasan ciwon kanta ba har yanzu?,me yasa ba zata dinga abu a hankali ba?.
"Don Allah bibi daga isowata?,ku duminki baki bari naji ba?" Ta furta a shagwabe tana narke murya,irin shagwabar nan data saba yi mata sanda tana sultana baby dinta.
"Yo ba dole ayi miki fada ba,irin wannan gaggawar ai bata masu juna biyu bace"
"Shikenan na shiga uku" ta fada tana jin kamar bibin ta dora mata dala da gauron dutse,ta tona mata asiri gaba jama'a,harda wanda baisan ma me yake faruwa ba yau ya sani,sauta juya da hanzari tana wucewa hanyar bedroom din bibin tana mita cikin ranta.
Zamewa yayi ya zauna sosai yana gaida bibi din,shima bai tsira daga rigimarta ba,don meye bazai dinga saitata ba bayan yanzu ba ita daya bace?. Zukudi yayi yana kallonta,yau din da alama bibin da rigima ta tashi. Abun mamaki,mainan da ake hanashi ladabtar da sultana......yau shi ake bawa wuqa da naman hukunta sultana?,wato kowa dai yana son abinda ya fito daga tsatsonsa,kowa yana son abinda ya shafeshi,da gaske kuma bibin tanason ganin zuri'arsa masu yawa?.
_KWANKWASON JIMINA_*
*_TSUTSAR NAMA_*
*_AMEENATOU_*
*_GUDUN KADDARA_*
_DUKKA AYARIN LITATTAFAN KUDINSU YA KAMA KAMAR HAKA_*
LITTAFI DAYA_400
BIYU_800
UKU_900
HUDU_1200
_IDAN TA BANKI NE ZAKI SANYA KUDINKI A WANNAN ASUSUN_
6019473875
Musaa Abdullahi safiya
Keystone bank
_ANTAYA SHAIDAR BIYANKI ZUWA GA WANNAN NUMBER_
09166221261
*Masu tura katin waya ko vtu kuma kai tsaye wannan number zaku tuntuba*
09134848107
*Maqotanmu kuma al'ummar qasar nijer zaku tuntubi wannan number dinne kai tsaye don biyan naku kudin*
09033181070
*ZAFAFA FAMILY na maraba daku*🫂🫂🫂🫂🫂*_GUDUN ƘADDARA_*
*H U G U M A*
BOOK 02 PAGE 142
"dakin bibi me dadi" ta fada tana sakin murmushi sanda ta shiga dakin. Ta furta haka ne saboda tuna mata abubuwa masu yawan gaske da dakin yayi. Gudun makaranta,boko da islamiyya gaba daya,gudun dukan yaa maina......neman wajen buya duka cikin dakinne. Murmushi ta sake saki tana hayewa gadon bibin,har cikin ruhinta da jikinta ta dinga jin wani dadi yana ratsata,tabbas kowa yabar gida gida ya barshi,quruciya kuma abune me dadi da tunashi yakan bawa zuciya farinciki da walwala.
Hannu takai qasan gadon bibi,ta taba wata Locker nata da take ajjiye ajjiye. Kaman wasa ta saka hannu ta jawo locker din
"Bibi da alqawari" ta furta tana murmushi. Komai nata da take ajjiyewa yana cikin locker din tun wancan shekarun,ba kasafai bibi take bari ake sauya mata furniture ba saboda duk sanda za'a canza din sai an siya me matuqar tsada,takan ce
"A barsu basu tsufa ba,jikin da zashi cikin kabari qarqashin qasan qasa ya kwanta meye na buri kuma?"
A nutse ta dinga fidda kayan ciki, murmushi na qwace mata,komai kuma tana tuna sanda ta ajjiyeshi a wajen,har zuwa sanda hannunta yakai kan wani kwalban turare.
Ba komai a ciki,turaren ciki ya qare ya kuma bushe dai kwalbar kawai. Riqe kwalbar tayi da kyau cikin tsakiyar hannunta tana sakin murmushi,kwanyarta kuma tana dawo mata da sanda ta kawo turaren nan ta boye.
Turaren ya maina ne,sanda yana ainihin zakinsa cikin gidan,sanda yana maina dan makarantar sojoji a niamy.......sanda ya kwashe mata teddies dinta karo na biyu,ta rasa meye itama zata dauke masa da zai bata masa rai,sai ta tuna da cewa mayen turare ne,kuma duk cikin turarukansa ba turaren da yafi so irin wannan. A sannan ta maqale ta window din dakinsa sanda yake neman turaren,ya dinga hargitse kayansa,yayi nema yayi nema cikin dakin har ya gaji,tana maqale a window tana masa dariya,tsautsayi ya sanyashi yaji dariyarta,ya kuma zagaya ya damqota. Koda yayi nufi hukuntata a sannan bibi tsohuwa me ran qarfe ta dire tace bata yarda ba,shi ya faye zafin zuciya,don kawai ya ganta a window din dakinsa sai yace ita ta dauka?. Bata mantawa haka ta taqarqare ta dinga sheqa rantsuwa harda qananun hawaye akan itafa ba itace ta dauka ba.
Sanda tunaninta yakai qarshe dariyar dole ta qwace mata
"Astgafirullah" ta furta a fili,ita kanta a yanzun idan tana tuna kalar quruciyarta abun dariya yake bata,komai nada lokacinsa a rayuwa.
"Irin wannan murmushi haka?,ko bayan an rabu da oga kuma taninsa aka kebe anayi?" Muryar aminta ta ratsa kunnenta.
Da sauri ta dago,suka hada idanu da aminata,dukkansu sai suka sanya dariya,aminata da tayi nauyi sosai ta qaraso tana hayewa gefan gadon bibi itama.
"Boss yau ya iso gidan nan,tun baiyi magana ba naga kowa yana shiga hayyacinsa...." Aminata ta fada tana tuna waye maina din da yadda ya saita rayuwarsu.
"Baki manta ba kenan?" Sultana ta fada tana duban aminata cikin dariya,tanason mata tsiyar nauyin da tayi tana tsoron kada taje ta tonowa kanta tata tsohuwar ajiyar
"Inaaaa......waye zai manta da yaa maina?,ko su djamilla da suke tasowa yanzun baya zaune a gidan ai sun sani bare mu da muka rayu dashi" tana shirin tambayar yasmine sai gata tare da amarya najma.
Bacci taso yi amma suka kashe dukka awannin a dakin bibi suna hirar yaushe gamo,basu suka bar dakin ba sai yamma liqis sannan balkissa me aikin bibi ta shigo ta gyara dakin,daidai sanda bibi din ke gyaran fallen alqur'aninta tana mitar jikokinta na gidan da suka ara suka lalata mata.
"Don Allah balkissa idan kin gama gyaran dakin a maida canopéé din gadon nan yadda zanji dadin yin bacci" idanu bibi ta wurga mata
"A ina?,ba dakina ba ehe.......ban iya diban zunubi ba kwana da matar wani a dakina" idanu Sultana tabi bibi dashi tana mamaki,yau ita bibi ke hanawa kwanan dakinta?. Ba ruwan bibi,don bata ma tsaya taji ta bakinta ba tayi gaba abinta.
Wanka tayi ta sauya kaya,tana idar da sallar magariba taci abinci sosai irin abincinsu na gargajiya wanda a baya bata damu dashi ba. Madararta takeson sha matuqa,to amma batasan inda zataga maina ba bare ta karba,don tunda suka iso gidan bata sake ganin gilmawarsa ba.
Dole ta haqura,ta yafa mayafinta ta wuce cikin gidan da bata samu shiga ba. Sassan oncle bashar uncle umar uncle issofou dukka tabi daya bayan daya suka gaisa. Sassan uncle umar da yake sassansu goumar tasan samu mutane don haka tafi jimawa a can. Tana can din taji ama ta dawo,tunda suka shigo gidan basu sameta ba,tasan kuma duk tana can wajen hidimar auren dan gaban goshinta ne.
Ta iske sashen surukar tata kuma uwa a gareta fes cikin tsari fiye da kowanne sashe na gidan kamar dai yadda aka saba. Masu aikinta keta zirga zirgar shirya mata abinci,ita kuma tana nata dakin tana wanka. Tana zama batoul da benazeer suka fito wadanda tanja ta sanyasu sukayi wanka suka sauya kayan bacci,don ama tace kada su haura tara na dare yau basu kwanta mata ba. Yawon wunin yau kaf dasu tayi gaban mota. Su suka zauna suna rage mata lokaci da shirmen hirarsu. Duk idanunta sun daddaure don ita kanta a mugun gajiye take jinta,ga abincin da taci ya qarasa kashe mata jiki gaba daya.
A shirye tsaf ama ta fito,idanunta da kulawarta dukka suna kan familynta sultana da yaranta. Tana yiwa ama din sannu itama tana yi mata sannu,duk kunya saita kama sultanan.
A nan qasa ama ta sanya aka sauke mata abincin, sultana ta dinga zuba musu don cikinta babu space,madara kawai take da buqata kuma bataga me batan ba. Ama nacin abincin suna tattauna tafiyar tasu,har zuwa sanda zuwaira me aikinta ta qaraso tana mata sallama zata wuce sassan 'yan aiki.
"Kafin ki wuce,ki tabbatar kin nemo almu ko saddi,su bude tsohon sassan yayansu su gyarashi don inajin yau dai a gidan zasu kwana,naga kuma jikin sultana ya fara nauyi zaiyi wuya bata kwanta da wuri ba"
"To ama in sha Allah" ta amsa mata
"Yayi da jiki don Allah" ta sake jaddadawa zuwaira
"Yanzun kuwa in sha Allah". Nauyi da kunya suka sake kama sultana,tayi qasa da kanta tana wasa da serving spoon din hannunta. Ko a jikin ama taci gaba da sabgar gabanta,har zuwa sanda su batoul suka gama cin nasu abincin suka musu sallama suka wuce dakinsu dake manne dana ama.
Kamar jira yakeyi su fita ya sako qafafunsa cikin falon. Yana sanye da wata kaftan abaya na maza kalar Navy blue. Kalar tayi matuqar haska farar fatarshi,yau din harda wata qaramar hula saman kanshi sample din tashi ka fiya naci,sai fuskarsa ta fita sak kamar wani baqin balarabe.
Tare suka amsa sallamarshi da ama,amma ita saita dauke dubanta daga wajensa gabanta yana faduwa da wani irin kishinsa da taji yana taso mata. Shikam bai iya janye nasa idanun ba daga kanta,yayita qoqarin kiranta yaji ta samu abinci yadda ya kamata?,amma bai sameta ba,ya kira su almu atta da saddi dukkansu sunce basu ganta ba,haka yayita musu fada kaman su suka boyeta.
Sai da yayi da gaske yayi controlling idanunshi, already ama ta ganshi,saita kame kanta da kyau itama tana basarwa.
A gaban ama ya zauna yana tanqwashe qafafunsa ya soma gaidata. Ta amsa masa tana tura masa kwanukan abinci gabansa. Bai musa ba bai kuma ja ba saboda a mugun yunwace yake,ga tarin gajiya a jikinsa,tunda suka shigo garin bai zauna ba,ya jawo ya buda ya fara zubawa. Kadan ya zuba saboda dare ya riga ya fara yi, bayason cika cikinsa da yawa da abinci,ya fara ci suna ci gaba da magana da ama,duk sai sultana ta jita a wajen kamar a takure.
Atta ne yayi sallama da maqullai a hannunsa
"Kaine kayi