Showing 165001 words to 168000 words out of 294767 words
Chapter 56 - Gudun Kaddara Book 2 Hausa Novel Complete
ba saboda bataga ama ba,tana a tsayen tana replying massages din wayarta aka danna qararrawa.
Ta daga kai tana duban qofar da zummar tambayar waye taga an turo qofar da alama ba'a rufeta ba gaba daya.
Itace abu na farko da idanunsa ya fara kaiwa kanta,kamar yadda itama dashi ta fara tozali, zagayayyun lion eyes nashin nan da taga sunyi wani irin haske a safiyar,kamar kuma an qara musu girma. Sassanyan kyansa dake kwance saman ba'abzinar fuskar nan tasa dake wannan kwarjinin na tun asali,tun duniya na kwance,gayun nan dai da duk wanda yasan aliyyu maina na kwance a yanxunma a jikinsa,irin gayun dake nuna zallar wayewa kwanciyar hankali da kuma tarin ilimin da ya mallaka,ilimin da ya qarawa fuskarsa kwarjini,ya kuma haifar da zallar nutsuwa cikin kowanne taku da kuma motsi nashi. Suit din jikin nashi tamkar kamfanin sun qirqireta ne kawai saboda shi,idan ka kalleshi babu abinda zaya hanaka rantsewa wani balarabe ne.
Sai da yaji kamar an harbi zuciyarsa da ganinta a tsaye,kyanta ya bugeshi sosai,ya kuma motsa masa ainihin kishinsa da yaketa qoqarin dannewa a kanta. TAURIN KANTA da sauransa kenan har yanxu?,bazai gaya mata taji ba?,sai ya gyada kai,shi daya yasan me ya shirya mata.
Sake maimaita sallamarsa yayi yana tsugunnawa a nutse yana sabule tsadajjen sau cikinsa daya sakaya qafafunsa a ciki. Kafin ya dago yaji muryar ama tana amsawa,wanda sai data iso cikin falon sosai sannan ta fahimci waye?.
Dagowa yayi suka hada idanu da ama, murmushi zai kubce mata ta danne,saita buge da fadin
"Kaine?" Nasa murmushin ya sake mata,wai ala dole sai tayi fushi itama da fushin wani?,banda abun ama meye alaqar dake tsakanin dangantakarsa da ita da kuma dangantakar sultana dashi?. Duk da haka sai ya dake shima,yana sake dauke idanunsa sosai daga sultana kaman baisan da tsaiwarta a wajen ba
"Nine ama......ko na koma?". Baki tadan tabe
"Banason sanabe,idan zaka qaraso ka qaraso,kaga abanka?" Kai ya girgiza duk kuwa da cewa yaga wucewarsa,to amma yanzun bai shirya haduwa dashi ba,so yakeyi su hadu ranar da zai kasheshi da mamaki
"No,bamu hadu ba"
"Yanzun nan ya fita" ta fada tana nufar dining. Qasan ranta sai takejin wani sanyi da dadi suna ratsata,amma kuma bata bari hakan ya nuna a kan fuskarta ba.
Kanshi tsaye shima dining din ya nufa,don bazai bari yayi Missing abincin ama dinsa ba. Tana qame a wajen har ya qaraso,ya jawo kujerar dake kusa da tata ya zauna yana fadin
"Barka da safiya ama,fatan kun tashi lafiya,ashe nan ne location naku"
"Lafiya alhamdulillah"
"Ya hanya?,bansan zaku taho ba ama......har yanzun baki dawo dani bane cikin 'ya'yanki?" Yayi maganar cikin karyewar murya da nuna rauni. Batajin yanzunne right time da zasuyi irin wannan maganar dashi,don haka ta bashi amsa a dunqule da cewa
"Kai kaso....in ka shirya cin abinci ne bismillah,tunda ka iskemu magana ya qare ai" murmushi ya saki,ya fahimci inda tasa gaba,don haka baice komai ba ya miqa hannu yaja butar shayi
"Amma zan wuce" ta fadi tana jinta duk a takure. Mamakin qarfin halinsa takeyi,kaman ba shine ya hauro musu gida daren jiya ba yazo ya muqurqusheta,amma yanzun don qarfin hali da qwarewa a rainin wayo wai shine yake tambayar ashe nan ne location nasu?. Ita kanta yadda ya dubeta a gaban ama din ba zaka dauka cewa ya taba ganinta ba,ya basar yayi zamansa
"Ban gane zaki wuce ba?, c'mon zauna kici abinci,haka akace miki ana zuwa aiki da empty stomach?" A hankali ta matso tana jan next chair,ta haqura da wadda ta fara ja din saboda tayi kusa dashi sosai
"Ina kwana" ta furta a hankali kaman wadda batason yin magana sanda take shirin zama.
Sai daya daga kanshi suka hada idanu,ya faki idanun ama ta yadda ba zata ganshi ba ya sake mata wani irin narkakken kallo yana lumshe idanunsa sannan yace
"Alhamdulillah" labbansa na wani irin motsawa. Ta fahimci ma'anar gaisuwar tasa,saita kau da kai taja itama butar coffee din ta soma zubawa.
Sam kaman baisan da ita a wajen ba,dukka hankalinsa ya tattara yana jan ama da hira,tadan soma dojewa daga baya tadan sake masa kadan. Yayi kaman ya manta da ita ne,amma duk wani spoon ko mug da zatakai bakinta yana lissafe da adadin. Har yanzun tana nan da wannan halin na yiwa abinci riqon sakainar kashi. Sanda ya fahimci dab take da qoshi sai ya fiddo wayarsa daga side pocket din jikin rigarsa.
Saqo ya tura mata cikin hikima ta yadda ama ba zata fahimta ba,ya maida wayar ya ajjiye yana ci gaba da duban ama cikin tsananin kulawa yadda ya saba mata.
Tayi zaton wani Tex ne me muhimmanci,wannan ya sanya ta jawo wayar ta buda
*_zanyi warning naki a karo na qarshe,muddin kikayi kuskuren fita aiki.......bazan gaya miki what's going to happen ba.......but zaki gani a aikace_*. Maimaita saqon ta sakeyi tana satar kallonshi,abu nashi taga alama yama wuce gona da iri,wai ana dole ne?,lallai sai ya maidota cikin rayuwarsa?,lallai sai ta maidashi itama cikin rayuwarta?.
Tsaf ya karanci meke reading saman fuskarta,sai ya miqe a nutse
"Nayi mantuwa ina zuwa" yadan sauka daga wajen yana fita da 'yar sassarfa. Ajjiye pork din hannunta tayi ama ta bita da kallo tana furta
"Ma sha Allah" qasan ranta,sai yanzun sultana ke zama cikakkiyar mace,shekarunta suke kaiwa dai dai shekarun cikar 'ya mace,ita kanta tayi mata kyau sosai
"Na qoshi ama,zan tafi yau na makara sosai,akwai abubuwan da zan duba na program dinmu na next week"
"Allah ya taimaka,saikin dawo" har ta fara barin wajen idanun aman yana kanta
"Ki kula da kanki sultana" ama din ta fadi. Sai taji maganan ya ratsata sosai,har sai daya waiwayo ta kalli ama sannan a sanyaye tace
"In sha Allah" juyawan da zatayi ya shigo,bata yarda ta kalleshi ba ta sanya kai zuwa ba.
Lips dinsa ya cije yana sakin wani boyayyen siririn murmushi,yaro man kaza ya fadi a ransa,hankalinsa kuma kwance yake dawowa wajen amansa,don sosai yakejin dadin hira da ita a wannan safiyar,ta dan sake masa ba kaman yadda take masa a baya ba.
_KWANKWASON JIMINA_*
*_TSUTSAR NAMA_*
*_AMEENATOU_*
*_GUDUN KADDARA_*
_DUKKA AYARIN LITATTAFAN KUDINSU YA KAMA KAMAR HAKA_*
LITTAFI DAYA_400
BIYU_800
UKU_900
HUDU_1200
_IDAN TA BANKI NE ZAKI SANYA KUDINKI A WANNAN ASUSUN_
6019473875
Musaa Abdullahi safiya
Keystone bank
_ANTAYA SHAIDAR BIYANKI ZUWA GA WANNAN NUMBER_
09166221261
*Masu tura katin waya ko vtu kuma kai tsaye wannan number zaku tuntuba*
09134848107
*Maqotanmu kuma al'ummar qasar nijer zaku tuntubi wannan number dinne kai tsaye don biyan naku kudin*
09033181070
*ZAFAFA FAMILY na maraba daku*🫂🫂🫂🫂🫂*_GUDUN ƘADDARA_*
*H U G U M A*
BOOK 02 PAGE 87
A nutse ta bude motar ta ta shiga tana ajjiye hand bag dinta daga gefe,ta tattara hankalinta ta sanya muqulli ta kunnata sannan ta tayar da ita ta soma barin unguwar a nutse.
Radio ta kunna don ta rage mata kewa,zantukan ama ke dawo mata da wasu tunanuka da suka shafeshi keson kutso mata kai wanda bata da buqatarsu. Tana mamakin qarfin halinsa da yadda yake abubuwan kanshi tsaye,duk da halinsa da dabi'unsa ba ta jima da saninsu,amma a yanzun yana shirin zame mata sabon mutum. Yadda ya sake girma ya sake zama cikakken mutum haka take sake ganin wasu sabbi da baqin halayya daga gareshi,koma meye dai oho,damuwarshi ne,ita ba wannan ne a gabanta ba,gina kanta takeyi a yanzun,lokaci ne da shekarunta suke dai dai da sanda kowanne dan adam ya kamata ya maida hankali ya gina gobensa,tanason ta sake yiwa rayuwarta ta baya nisan tazara sosai fiye da tazarar da tayi mata a yanzu.
Daren jiyan ya fado mata a rai,tsaki taja,har yanzu haushi da baiken kanta take gani,tana ganin kaman tayi sakaci da har haka ya faru da ita,abun ya maqale mata a rai,tana jin tayi abun kunya da har tayi saken da ta sake hada jiki dashi,yadda akayi yaci galaba a kanta abune da bazata iya tunawa ba,ta sanya yatsanta guda daya a baki tanason second guda daya daya bashi dama ya shawo kanta amma ta kasa tunawa. Dan dukan steering din motar tayi tana tura baki gaba cikin alamun jin haushi tamkar yana a gabanta.
Batayi wani nisa ba can danja ta tsaidasu,ta tsaya kaman yadda dokar qasar yake,tana yi tana duba adadin mintunan da suka rage a basu daman wucewa. Tsaki ta kuma ja,duk shi yaja mata koma meye,wannan lattin batasonshi,bataso ta fara aikinta da saba alqawari da kuma saba lokaci,tunda ta sani,su din mutane ne masu girmama lokaci da kuma alqawari.
Gefan hannun damanta tadan kalla,har ta dauke kai tayi saurin maida dubanta wajen. Maina ne,zaune cikin motarsa hankalinsa kwance,ya manne qwayar idanunsa da baqin eye glasses wanda suka yiwa farar fatarsa mugun kyau. Kallo daya zaka masa kasan cool guy ne a ido,amma a idanun sultana can qasan zuciyarta sai ta furta
"Wicked" sannan ta dannan madanni tana dage glass din side din,don bata qauna ko fatan ya ganta ma,kowa tashi ta fishsheshi,hanyar jirgi daban ta mota daban. Ana sakinsu kuwa taja motarta tana dan qara speed kadan akan na dazu duk kuwa da yadda take tsoron gudu a mota,koda kuwa driving nata akeyi bare ace ita keyi da kanta.
A nutse take dan bin waqar da suka sanyo cikin gidan radio din da harshen faransanci,saita waqar ta dinga tuna mata shekarun baya,sanda tana sultanar bibi,me bala'in son rawa da waqa,me bin duk wani gida da ake shagali walau gida ko hotel. Waqar na daya daga cikin waqoqin da take mutuwar so, murmushi ya dinga kubce mata a hankali tana bibiyar waqar.
Dan speed ta qara ganin ta hau doguwar hanyar nan wadda daga ita zata shiga titin gidan tv dinsu,hanyar ta fiya shuru,ita kuma tun dacan tana da tsoron wajen daya fiya shuru haka.
"Innalillahi wa inna ilaihi raji'un" ta furta tana zaro idanu lokacin da gudun motar ya fara ja baya,ta kuma fara tafiya slow. Dukka idanunta ta fiddo waje ciki tsananin fargaba tana duba ma'ajiyar dake nuna dadin man fetur dake cikin motar. Mamaki ya kamata qwarai ganin cewa wai mai ne ya qare,bayan shekaran jiya aba yayi mata full tank da motar tata.
Bata saku damar kai motar gefan hanya ba ta mace mata,ta sake kiran sunan Allah tsoro da fargaba yana cikata,ta kalli hagu da dama dukka ba motsin kowa sai kukan tsintsaye da iskar dake kada dogayen bishiyun da suka yiwa hanyar qawa.
Hannayenta ta hada waje daya ta karanta addu'o'i ta shafa a jikinta,ta bude murfin motar a darare tana fitowa wai ta duba gaban motar ko zata gane inda matsalar take,duk da cewa ba wani abu data sani akan matsalar data shafi mota,don shi kansa driving ma bata dade da farawa ba,ko ina zata akwai mai kaita akwai me daukota.
Koda ta bude kaman yadda ta zata bata fahimci komai ba,haka ta qarewa wayoyi kallo ta mayar ta rufe,saita jingina da motar zuciyarta na bugawa tana kiran sunan Allah.
Waige waige taci gaba dayi,mintuna kusan goma amma bataga gilmawar kowa ba,ta lumshe ido ta juya da sauri ta bude motar,ta dauko jakarta ta fidda wayarta da zummar kiran ama ko aba ko can tv station din nasu ko akwai wani dauki da zasu iya kawo mata.
Wayam ta gani,babu komai cikin jakar sai dan tarkacenmu na mata da bama rabo dashi,kulle idanunta tayi da qarfi tana cewa
"Innalillahi" tabbas saman dining din ama ta manta wayar. Zuciyarta dukka ta karye,ta koma ta window tana cilla jakar,daidai sanda ta soma jiyo sautin tahowar mota
"Alhamdulillah" ta fadi tana gyara yafen scarf dinta,ta matso bisa titin sosai ta sanya hannu sanda motar ke dab da isowa inda take tsayen,saidai abun haushin wucewa motar tayi. Cikin sarewa ta sake komawa ta tsaya tana fatan samun dauki,cikin sa'a ta sake jiyo wata motar,sai ta sake matsowa tana saka hannu wannan karon harda bayani
"s'il vous plaît, aidez(please help)".
Murmushi ya kamashi amma ya danne,har yanzun halayyar nan ta tsoro tans nan bata barta ba?,target dinsa ya fada a dai dai kenan. Yana sane yadan take motar kamar zai wuce,har yayi gaba sai ya rage gudu,ya danna reverse ya dawo da baya da gudu.
"Alhamdulillah" ta fada tana aje numfashi ganin motar data wuce din ta fidda ran tsaiwarta itama tana dawowa.
Ganin an tsaida motar kuma ba'a fito ba saita soma takawa zuwa gaban motar,duk dadai a tsorace take amma tana da yaqinin qasa ce me aminci da iren iren abubuwa masu cutarwa haka basu fiya faruwa da mutane ba,uwa uba kafin ta fito daga gida tayi addu'a,tana da tabbacin tana cikin kariyar ubangiji.
Yana zaune daga cikin motar yana qare mata kallo son ranshi,idanunsa da kansu suka dinga rusunawa suna budewa,yadda take takowa zuwa gareshin yana sake tada masa wani sabon tsumammen feelings a kanta,tamkar daren jiya dama baiyi komai ba. Yana iya ganinta tarwai,amma ita bata iya ganinsa saboda baqin glass ne dashi. Sanda ta tsaya jikin window din ta masa knocking sai yayi kaman baiji ba,yana ganin yadda fuskarta ta nuna alamun qosawa,ta sake knocking glass din,sai yadan sauke glass din kadan ta yadda zai iya jinta kawai ba tare da taga fuskanshi ba
"Pouvez-vous m'aider? La voiture ne fonctionnait plus(zaka iya taimako na?,motata ce ta daina aiki)" kai kawai ya gyada,ya maida glass din ya kulle. Sak tayi tana tsammanin mamallakin motar na shirin yin gaba ne abunsa,sai taga an bude murfin side din da yake,ya zura qafafunsa ya fito gaba daya.
Baya taja da sauri tana dubanshi yayin da shi kuma ke gyara zaman suit din jikinsa kamar ma bai santa ba. Sake ja tayi da baya sanda ya fara takawa yana nufar motar .
Turqashi!,ita sam batasan shi bane tunda batasan wanne kala ne motarsa ba,tsoro ya hanata motsawa,har ya bude gaban motar ya gama tabe tabensa,ba kuma tare daya kalleta ba yace
"Wannan motar bazai tashi ba yanzu ya tafi hutu,ki nema abun hawa ki wuce" ya fadi yana karkade hannayensa kaman wanda yayi wani abun arziqi.
Tayi zaton zaice mata ta taho suje,amma sai taga yana nufar motarsa,har yanxun kuma bai kalleta ba, sanda ya shige ya maida murfin ya rufe ta tabbatar tafiyar fa zaiyi,saita kalli hagunta da damanta,su kadai suka rage a wajen,dole ta sake matsowa gaba da sauri ta daga masa hannu.
Kaman bazaiyi kowanne motsi ba sai kuma taga yana sake sauke glass din har ya kammala saukeshi tas,idanunsa a kanta,ya sanya hannu a nutse ya zare baqin eye glasses dinsa
"Ya akayi?" Ya jefa mata tambayar yana mata wani irin kallo. Idanunsa sun fiya dafi da yawa,sai ta kauda kanta gefe sannan tace
"Ka qarasa dani bakin hanya...... please" ta qarasa maganar tana jin dacin neman alfarma yau a wajensa. Kaman ya qyalqyale da dariya to amma yanzun ba muhallinta bane,don yana hango yadda roqon ya mata daci. Murya can qasa ya amsa mata yana maida glass dinsa
"Bismillah" yace da ita. Rai a bace ta qarasa wajen motar tata ta fidda kayayyakinta,ta tako cikin nutsuwar nan tata zuwa bakin motar.
Bayan motar take da muradin shiga,to amma kuma tun duniya tana kwance tasan halinsa sarai,dole badon taso ba ta bude gaban motar ta shiga,ta maida murfin ta rufe,ya saki boyayyen murmushi cikin ranshi yana cewa
"Mission accomplished" ya tayar da motar a nutse yana qarawa fuskarsa daurewa,daurewan da ya qara mata wani irin kwarjini daya fitar da ainihin kyanshi.
_su maina sarkin wayo,ina zuwa?_
_KWANKWASON JIMINA_*
*_TSUTSAR NAMA_*
*_AMEENATOU_*
*_GUDUN KADDARA_*
_DUKKA AYARIN LITATTAFAN KUDINSU YA KAMA KAMAR HAKA_*
LITTAFI DAYA_400
BIYU_800
UKU_900
HUDU_1200
_IDAN TA BANKI NE ZAKI SANYA