Showing 186001 words to 189000 words out of 294767 words

Chapter 63 - Gudun Kaddara Book 2 Hausa Novel Complete

yadda tayi qoqarin kaucema qaddarar haduwa dashi hakan bashi samuwa. Lallabawa takeyi ya fice gurin lafiya lau ba tare daya daura mata jinyar ciwon jiki ba(nace gulmammiya,anaso ana kaiwa kasuwa).

"Koma ki zauna" ya fadi sanda ta ajjiye abincin a gabansa,yana zaune sosai saman dan center carpet dan madaidaici da aka qawata office din dashi. Dubansa tayi kaman zata saki kuka,to amma yadda yake dubanta ya sanyata zamewa ta zauna sosai a a gabansa.

"Oya.....saka hannunki....", Ya bata umarni yana tattare dogon hannun shirt din suit dinsa,ya sanya nasa hannun cikin abincin ya fara kaiwa baki a nutse. Kasa motsawa tayi,cin abinci tare dashi cikin kwano daya wani tsohon al'ada ne data manta rabonta dashi,batajin zata iya sam,don haka taci gaba da duban kwanon sanda yake kai abincin cikinsa hankali kwance. Wani mugun nishadi ne ma yake saukar masa,duk sanda zasu kasance qarqashin inuwa daya kaman hakan,yakanji kaman ya tsaida lokaci ya hanashi motsi,abinda ya kasa bawa kansa amsa har yanzu shine,wai dama can wannan matsanancin son yakewa sultana?,ko kuma bayan faruwar wancan abun a wancan lokacinne mahaukaciyar soyayyarta ke yagalgalashi?.


_KWANKWASON JIMINA_*

*_TSUTSAR NAMA_*

*_AMEENATOU_*

*_GUDUN KADDARA_*

_DUKKA AYARIN LITATTAFAN KUDINSU YA KAMA KAMAR HAKA_*

LITTAFI DAYA_400
BIYU_800
UKU_900
HUDU_1200

_IDAN TA BANKI NE ZAKI SANYA KUDINKI A WANNAN ASUSUN_

6019473875
Musaa Abdullahi safiya
Keystone bank

_ANTAYA SHAIDAR BIYANKI ZUWA GA WANNAN NUMBER_

09166221261


*Masu tura katin waya ko vtu kuma kai tsaye wannan number zaku tuntuba*

09134848107

*Maqotanmu kuma al'ummar qasar nijer zaku tuntubi wannan number dinne kai tsaye don biyan naku kudin*

09033181070


*ZAFAFA FAMILY na maraba daku*🫂🫂🫂🫂🫂*_GUDUN ƘADDARA_*

*H U G U M A*

BOOK 02 PAGE 99


"idan kika bari na rigaki gama cin abincin nan.......dura zanyi miki" ya fadi yana kada yatsansa dan manuni. Itakam a yanzun ko meye yace zaiyi zai aikata ta sani,don haka ta rufawa kanta asiri ta matso,ta sanya hannu ta dauki spoon. Hannunsa ya miqa ya karbe yana fadin

"Um um......yau da hannu zamuci,mu samu albarkaci junanmu" cikin ranta ta tabe baki

"Wanne albarka mutumin da yake da side chics dinsa?" Ta fadi qasan ranta

"Me kika ce?" Ya jefa mata tambayar yana tsareta da idanu

"Ba komai" ta fadi qasa qasa tana tura baki gaba. Murmushi ya saki,lallai da gasken tsoro ya sanya ta fara gyara wasu abubuwan,ya sani akwai abinda tace,amma shakkar tasa ya saka ta kasa fadi masa a sarari,wanda inda ada ne ya tabbatar zata fadi mashi ne,ko meye zaiyi saidai yayi.

Koda ya gama sai ya koma da baya yayi relaxing yana kallon taunarta,idanunsa can qasa,ba zaka taba kawowa ita din yake kallo ba. Wayarsa ya jawo sanda ta fara ringing,ya saki murmushi ganin sunan goumar,yana dagawa muryar benazeer da batoul ne ya soma masa sallama.

A handsfree ya sanya wayar yana fitar da murmushi,muryarsu fes cike da doki da zumudin mahaifinsu. Hira suke masa sosai hayaniya hadi da shirmensu,ya sakankance sosai ya biye musu

"Daddy munyi missing naka,uncle goumar yace mu tambaya zai kawo mu office dinka?" Tsaiwa tayi da hadiyar lomar tana kallonsa qirjinta nadan bugawa,ko kusa ko alama batasan kowa yasan suna tare,kowa dinma irin goumar?,ta tabbatar daga ranar ta kade daga ita har ganyenta,kai wala'alla ma bakinsa bazaiyi shuru ba saiya gayawa ama, itakam ai da ta kade,da wanne ido zata kalleta?.

Shima din ita yake kalla,kuma salon kallon da yakeyi mata tamkar yana jefa mata tambayar na basu izinin zuwa?ne a fakaice.

Rau rau tayi da idanunta tana tsame hannunta daga abincin,sai ya zame idanunsa yana cewa

"No kuyi zamanku,nayi alqawari anjima kadan zamu kasance tare" ihun murna suka saki,yanata sakin lallausan murmushinnan nasa kafin daga bisani yace su bawa goumar wayar.

Magana sukayi kadan sannan ya kashe wayar,ya miqe ya nufi inda suit dinsa take ya saka,ya maida takalminsa,yana daura agogonsa ya dubeta

"Zaki wuce gida yanzun......daga yau kuma duk sanda kika sake fita bada izinina ba......" Sai bai qarasa ba ya maida kansa ga daura agogonsa.

Afakaice ta harareshi,kaman yaji hakan cikin jikinsa sai ya waiwayo,saura kadan su hada idanu tayi hanzari dauke kanta ta maida ga agogon bangon office din nata.

Lokacin yayi daidai da sanda yarinyar tace zata iso paris,hakanan taji wani abu ya tsaye mata a wuya.....lokacin tashinsu daga aiki da saura,don meye don zaije ya dauko wata can daban zai matsa mata tabar office yanzu?, bayan ya hana mata yin duk wani aiki,har yanzu program din da zata next week bata shirya komai game dashi ba,saboda ya hana mata sakat,ya hanata motsi,ya kuma hanata nutsuwar da zatayi aikinta.

"Are you with me?" Ya tambayeta yana qoqarin daukan wayarsa. Wani tunani da yazo mata ya sanyata miqewa ba tare data kalleshi ba

"Zanje na danyi submitting wani abu,bazan wuce minti biyu ba" ta fadi tana jin dacin yadda wai saita nema excuse a gurinsa kafin tama fita

"Hope ba wajen namiji bane?" Tambayar ta quleta,sai taji kaman kada ta amsa masa,amma tana tsoron hukunci,don haka ta gyada masa kai kawai.

Sai data tsaya tsaf ta maida komai nata inda yake sannan ya barta ta fita din. Qwafa taja bayan ta fita tana cewa

"Ai idan kasan wata bakasan wata ba" office na qarshe a lobby din ta shiga,tasamu baturiyar matar cikin aiki kace kace,amma kasancewar suna girmamata saita tsaida komai ta saurareta.

Dan qaramin hutu ta buqata a kwanakin,ta basu uzurin tanason ta shiryama next program sosai a gida,don mamanta ita zata taimaka mata da wasu research akan culture din da zasuyi magana akai. Ba wani damuwa ta tura request akan buqatarta,ta kuma bata dama a take ta rubuta letter ta tura,sukayi sallama ta fita a office din.

Fes takejin ranta sanda ta baro office din,kome zaiyi daga nan zuwa gida ba zataji haushinsa ba,don tasan abinda ta shirya din shi daya zai mata maganinsa.

Ko a cikin motar yaga ta saki fuskanta sosai,bata damu kaman yadda take damuwa wancan lokacin ba idan ya yanke zasu wuce gida tare a motarsa.

Duk da hankalinta ya dauke daga kanshi,amma lokaci lokaci sai ta dinga duba agogon hannunta,abu daya ranta dai keci gaba da bata zayaje daukota,tanaso tayi tsaki amma tana gudun yinsa a sarari.

Kama ko yaushe ya tsaya daga farkon street din nasu ya bude ya fito ya zagayo inda take zaune yana miqa mata key din

"What do you want to me to do to you tonight?" Ya tambayeta yana dage masa girarsa guda daya hadi da kashe mata ido. Wani abu ya zubawa gangar jikinta,saboda tsananin kusancin dake tsakaninsu yayi yawa,abinda take gani kuma a idanunsa yana son shallake yadda ta daukeshi

"Ki gayyaceni mana yau dai daya da kanki please madam" ya sake fadi yana sassauta mata murya da salon dake narka zuciya.

Saura kadan ya dauke mata numfashi da wani irin tsananin kunya da kuma nauyi daya saukar mata. Ya fahimci ne taji,don haka ya miqe daga durquson da yayi ta jikin window din yana watsa hannayensa gami da dage girarsa sama

"I don't know what's wrong with me,am so addicted to you.....see you tonight" ya fadi da tataccen turancinsa tamkar baisan wani abu waishi yaren faransa ba. Takowanne bangare gwanine,Allah ya bashi baiwar harshe qwarai da kuma salon sarrafa kowanne harshe,idan France yakeyi zaka zaci shine kadai yaren da ya sani,hakanan idan ya juya English.

"Tonight?" Ta maimaita kalmar bayan ta soma gangara motar sosai cikin layinsu. Kai ta gyada murmushin mugunta yana qwace mata

"You will see tonight kuwa" ta sake fada qasa qasa.

Hannayensa ya saki yana juyawa zuwa inda matashin ya aje masa motarsa kamar kullum. Daidai nan wayarsa ta dauki flute ringing me sanyi. Ranshi yadan hade kadan,sai kuma ya daga kiran yana sanyawa a kunnensa.

"Almost over one hour ina jiranka yaa haidar.......bakasan na iso ba ko?"

"Me yasa kika taho laila?,aunty din tana Paris dinne?" Ya tambayeta don baiga ta inda zai bari tayi masa masauki cikin gida ba.

Ajiyar zuciya ta saki,har yanxu tana jin dacin maganar da matar data daga wayanshi dazu ta gaya mata,so amma yanzun ba muhallin da zata tambayeshi bane

"Tacemin yau suna hanya in sha Allah,so ko zakamin alfarmar zama cikin gidanka na wasu awanni kafin su iso?" A yadda sautin nata ya fito ya nuna kaman wani abu ya sosa zuciyarta. Sardauna da daddy sune mutanen daya tuna,ya kuma tuna halacci da gudunmawar da suka taka a rayuwarsa

"Ki tsaya a wajen,zanzo nayi picking naki"

"Alright, thank you" ta fadi. Ya sauke wayar tausayinta yana dan kamashi,shi da ita dukka yana tunanin jirgi daya ne yayi jigilarsu,son maso wani da hausawa ke kira da qoshin wahala,ya juya a nutse ya koma matar yana tayar da ita idanunsa kan hanyar da sultana ta wuce.

Daure da babban towel da kuma qarami ta fito daga toilet. Haka kawai tunda ta dawo gidan gaba daya hankalinta yana kansa,duk kuwa da cewa duka duka basu zarce awa biyu da rabuwa ba. Duk bayan wasu mintuna sai ta tuna da kiran LAILA. Sunan da ma yarinyar gaba daya sun tsaye mata a rai,tayi masifa tayi fada ita da zuciyarta dama ranta gaba daya kan shiga shirgin da bai shafeta ba amma abun yaqi barin zuciyarta.

Tanata ture tunanin tana shirya kanta cikin wani sassanqan material,so take tayi keeping kanta busy yau sosai,tanason ta zauna cikinsu ama da yaran ta basu lokacinta,daga magrib zuwa ishai kuma tana sanya ran ta qarar dashi wajen binciken al'adun qabila daya cikin tarin qabilun Nigeria wato qabilar KANURI.

Fes fuskarta ta fita ta tsakiyar turban cap data sanya fara qal,ta matsa jikin bed Side drawer dinta dake daura da window dinta,haka kawai sai taji sha'awar bude window din.

A nutse ta miqa hannunta ta yaye labulen,ta kuma sake zura hannunta ta janye glass din. Fes ta cikin window din take hangar gidan,gidan da take da tabbacin cikinsa yake rayuwa. Tana qoqarin sakin labulen motarsa ta tsaya qofar gidan,sai ta samu kanta da gaza sauke hannun nata, idanunta tamkar wadanda aka yiwa majanyi suka bi qofofin motar da kallo,dai dai sanda shi da laila dukka suka fitowa daga cikin motar, suhail ya bude back seat shima ya fito. Da qasaitaccen takunsa yabar jikin motor din,ya haura zuwa qofar gidan ya saka key ya bude gidan,ya tura qofar sannan yaja da baya yana bata hanya. Takowa tayi cikin murmushi, zuciyarta yau din tana mata wani dadi,yau itace ya haidar din da kansa ya daukota daga airport?,bayan haka ma sai daya biya da ita wajen cin abinci taci abinci ya taho mata da takeaway wai don kada taji yunwa,zata iya mantawa da wannan ranar kuwa?. Anya ba nasara da sa'a bane ya kawota paris?,kodai da gaske hasashen da Sara tayi mata zai tabbata?,zata jarraba......tana fatan dacewa.

Sanda ta saka kai gidan ya mara mata baya labulen ya subuce daga hannunta,tayi qas da kanta tana son gayawa kanta da kanta da sabganta bane,ba abinda ya dameta bane,ta soma qoqarin buda kwalin turaren amma sai ta fahimci hannuwanta rawa sukeyi,taja wani dogon tsaki a matuqar fusace,ta miqa hannu tana maida window din ta kullesu gam ba tare data sake bari idanunta sun kalli gidan ba

"Bazan sake budeshi ba har mubar Paris" ta gayawa kanta da kanta a fusace tamkar wani ne yayi mata.

Gagara bude turaren tayi don hannuwanta sai tajisu kamar an bugesu,cilli tayi da turaren saman gadon,saita koma saman madubinta ta fesa wanda ya samu kawai,ta dauki wayarta tana fita a dakin can qasan ranta tana qoqarin controlling kanta da kanta,don bataga abun damuwa ba a abinda ta gani,meye sha'aninta a ciki?.


_KWANKWASON JIMINA_*

*_TSUTSAR NAMA_*

*_AMEENATOU_*

*_GUDUN KADDARA_*

_DUKKA AYARIN LITATTAFAN KUDINSU YA KAMA KAMAR HAKA_*

LITTAFI DAYA_400
BIYU_800
UKU_900
HUDU_1200

_IDAN TA BANKI NE ZAKI SANYA KUDINKI A WANNAN ASUSUN_

6019473875
Musaa Abdullahi safiya
Keystone bank

_ANTAYA SHAIDAR BIYANKI ZUWA GA WANNAN NUMBER_

09166221261


*Masu tura katin waya ko vtu kuma kai tsaye wannan number zaku tuntuba*

09134848107

*Maqotanmu kuma al'ummar qasar nijer zaku tuntubi wannan number dinne kai tsaye don biyan naku kudin*

09033181070


*ZAFAFA FAMILY na maraba daku*🫂🫂🫂🫂🫂*_GUDUN ƘADDARA_*

*H U G U M A*

BOOK 02 PAGE 100


Fitowarta ta musu dadi sosai,suka sanyata a tsakiya da karadinsu da basa gajiya. Duk da shuru shurun batoul amma benazeer tanason koya mata surutu.

Jinsu kawai takeyi,amma sai takejin hankalinta da tunaninta baya tare dasu.

"Mummy yau kiyi mana kwalliya.......daddy yace zaizo mu fita dashi......me zamu siyo miki?" Batoul ta tambayi sultana tana kallon fuskarta.

Dan kallon yarinyar tayi fuskarta tana tuna mata da tashi fuskar,yadda yayi bacci saman cinyoyinta dazu lakadan kaman bashi ba......amma kuma yanzun sai gashi yana shiga da wata macen cikin gidansa shi da wani.

"Ba komai batoul" ta fadi tana shafa kan yarinyar zuciyarta tana karyewa.

"Mummy to ki shirya muje tare dake mana?,.......ama don Allah ta bimu?" Ta maida tambayar ga ama dake a zaune waje daya,tana karantar sultana din a fakaice,cikin kwanakin tana fuskantar canje canje daga gareta,saidai har yanzun batakai gacin gano sauyin na menene ba

"Na gaji ni bazan iya sake wani fita ba...... infact ma ina da aiki da zanyi na program dina......saikun dawo,tanja zata shiryaku" ta basu amsa tana miqewa don dab ake da shiga lokacin sallar.

Dukansu suka bita da kallo,fuskokin yaran tayi rau rau da alama basuji dadin hakan ba,ama ta kira sunansu tana yafitosu da hannu,suka taso dukansu suka zauna gabanta,saita riqe hannayensu tana dubansu

"Idan mummynku tace ba zatayi wani abu ba ku daina tursasata kunji?,tana fita aiki,kuma tana dawowa a gajiye,kunaso tayita ciwon jiki?" Kai suka girgiza a tare

"Yauwa......yanzun ku yiwa uncle goumar waya ya dawo da wuri sai kuje tare" hakan data fada sai ya saka suka saki ransu,suka suri wayarta suna qoqarin gano lambarsa su kirashi din.

Duk abinda ama din ta fada ma yaran akan kunnenta ne,don tsaye tayi jikin bakin qofarta. Gwiwoyinta sukayi sanyi,tausayinsu taji yanason kamata,ta daga qafafunta da qyar tana wucewa ciki,idanunta akan agogo.

Tanaji a jikinta babu ma lallai ya tuna da yaran tunda wancan laila din tazo,duk zumudin fita dashi din da zasuyi tasan ba lallai ya tuna dasu ba. Ta sake maida idanunta tana kallon window din kamar zata iya hango cikin gidan,saidai kuma zuciyarta ta gargadarta kada ta soma budewa,don haka ta juya tana wucewa toilet don dauro alwala.

Sanda ta fito sai tayi deciding ta kira yaran wajenta suyi sallah da azkar tare,wani sashen na zuciyarta yana gaya mata

"Kinaso kiga baban nasu zaya fita dasu ne?,ko kina son gasgara zarginki?" Tsaki taja tana qaryata wannan hasashen na zuciyarta,sai ma ta fasa fita,ta dauki wayarta ta kira tanja tana tambayar yaran

"Gasunan suna alwala zasu wajen ama suyi sallah"

"Turomin su"

"Tom" tanja ta amsa mata. Fasa shimfida qaramin abun sallarta tayi,ta sanya musu wadatacciyar dadduma,ta sanya ustazah dinta da ya fidda kyan fuskarta ta fuskanci gabas,daidai sannan suka shigo suma kowa sanye da wadataccen hijabi. Fuskokinsu kawai sun sanya zuciyarta yin sanyi,ta lumshe idanunta ta kuma budesu,ta qarasa saman dressing table dinta ta dauko tutarenta,ta matsa dab dasu ta feffesa musu duk kuwa da cewa ko yaushe cikin qamshin suke,don suna da personal turarensu. Hakan ya musu dadi,kuma ya nuna har saman fuskarsu.

"Oya assalaat" ta furta tana maida turaren,duk sai suka matso suka hau saman abun sallar.

Gefen hannun damanta ta tsaidasu suka tada sallar cikin nutsuwa. Kusan a shekarunsu sun iya komai na sallah,koda akwai gyara bazai wuce wasu qananun abubuwa ba,da haka suka kammala sallar,suka daga hannu yadda sukaga tayi sukayi addu'a tare suka shafa.

Agogo ta sake kalla, lokacin dai yanata tafiya,zuciyarta taji ta sake matsewa,sai tayi qoqarin saita kanta ta maida dubanta kansu

"Yaudai karatun islamiyyan kowa zanji" da zumudinsu suka gyara zama,cikin dabara da hilata ta dauke musu hankali da karatun,duk da hakan tanayi tana duba lokaci,har sannan bataji wani motsinsa ba,bata kuma ji ance su fito su tafi daddynsu yazo ba.


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login