Showing 249001 words to 252000 words out of 294767 words

Chapter 84 - Gudun Kaddara Book 2 Hausa Novel Complete

Fes ta zubewa ayana fararen idanunta masu kyau da daukan hankali,cikin wani nutsuwa kuma ta miqa mata hannunta tana fadin

"Ki yiwa ama godiya da ban gajiya......ki kawo basket din kina iya juyawa daga haka". Baisan sanda yaja da baya yana zuqar wata iska yana fesarwa ba. Zai iya cewa ya dauki shekaru masu tsaho baiga abinda ya burgeshi irin wannan salon nata na yau ba,ji yakeyi kaman zai narke a wajen,yau shine sultana ta birkice haka cikin qasa da mintuna a kanshi?.

"Dukkanmu mun gaji kuma hutawa muke da buqata" ta qara mata da bayanin ganin ta xube mata itama idanu tamkar bata da niyyar bata kwandon.

Maina ayana ta kalla,sai ya dage dukka kafadunsa alamun ba ruwanshi,yana nufin kenan ya goyi bayan matarsa?,ya goyi bayan abinda tace?. Kafin ta dawo daga wannan radadin horn din motar goumar da yake a fusace kan sakashi fitowanbda tayi a daren da shegen nacinta ya cika wajen,a matuqar sanyaye ta miqa mata kwandon ta kuma sauka da dan sassarfa tana barin qofar gidan,yayin da sultana ta karba tana kuma takawa a nutse ta shige falon tana jin wata izza tana ratsata gami da wani qarfin zuciya tare da alfahari.

Tana isa falon ta dire kwandon,taja wani mugun tsaki kamar zata cire harshenta, zuciyarta na mata zafi sosai. Ta fita daga harkar ayana,ta baro musu gidansu amma ba zata barta tayi jinya ta raini cikinta cikin salama ba?,da wannan bacin ran ta wuce bedroom ko tsayawa ta gaisa da goumar batayi ba.

Bacin rai fal zuciyarta ta maida qofar ta saka key don batason ma ya shigo yaga wani sauyi tattare da ita. Ta soma zare kayanta da takeji sun isheta,har yanzu ranta yana suya,ta shiga bandaki ta tara ruwa ta shige bathtub.

Tana ta jin knocking dinsa har ta gama wankan ta fito. Sanda tana shiryawa dinma taji knocking dinsa,amma ta basar kaman bata ciki. A nutse ta gama shiryawa cikin tattausan kayan bacci riga da wando masu gajeran hannu,saidai kuma sun sauko sun rufe mata jikinta sosai. Yunwa takeji kaman kaman me amma kuma batason bude qofar. Qaramin tsaki taja,abinda takeji a zuciyarta tafi tunanin mode swing ne kawai ke damunta irin na ciki,ba zata ce ba don ba zata iya tantance komai ba akan cikinsu benazeer. Cikine da yazo mata da wata irin wahala da damuwa da bazata taba mancewa da ita ba.

Cikinta ta shafa tana sake jin ba komai a ciki. Knocking ta kuma ji yayi amma sai tayi biris,da gaske haushinsa takeji sosai,duk da bata da wani dalili da zata bayar akan hakan.

Wayarta dake gefe ce ta fara haske,ta waiwaya tana dubanta,kamar kada ta daga sai kuma ta miqa hannu ta daga ta sanya wayar a kunnenta

"Idan kika sake na sake knocking qofar nan sai ranki yayi mummunan baci" ya furta da husky voice dinsan nan dake da ban tsoro a yawancin lokuta.

Rau rau tayi sai kuma ta ajiye wayar,ta miqe tana nufar qofar ba tare data damu da lullube kanta ba. A hankali taja qofar baya,sai ta maqale a bayan qofar kaman yaron da ya yiwa mamanshi rashin gaskiya. Wayace a kunnensa wadda yanzun akayi kiransa,sunan sardauna kuma daya kira ya bata tabbacin dashi suke wayar.

Idanu ya watsa mata sannan ya qarasa shigowa da kwanukan abinci,ya qarasa kan qaramin rug din dake dakin ya tsugunna yana fidda komai wayar tana maqale a kunnensa. Sai daya zuba komai kaman yadda ya saba mata sannan ya koma ya zauna,ya sanyata a gaba yana kuma ritsata da idanun nan nashi bayan ya dora qafarsa daya akan daya yana mata magana da idanu. Ta fahimci sarai abinda yake nufi,amma duk sai taji abun bai mata armashi ba,ta zauna tsakiyar rug din ta jawo plate din ta soma juya abincin.

Biyu uku taci taji duka bai mata taste ba,ta langabe wuya tanason sakin kuka. Wai me yasa komai nasa yake mata daidai da ra'ayinta?,me yasa komai yayi mata sai taji ya dace da ita?,idan ita tayi kuma sai taji totally wrong?. A jiya da ya kasance shine yake bata abincin sai taji yafi tafiya yadda ya kamata,yafi kuma dadi taste dinsa ya banbanta da wannan,amma a yanzun da takeci da nata hannun komai ma baiyi mata ba,anya kuwa ba sihiri ya fara ta'ammali dashi ba?,ta yiwa kanta da kanta tambayar da tasan hasashe ne kawai mara dalili.

Duk sanda ta tsaya sai ya kafeta da idanunsa,dole haka ta dinga qoqarin ci har sai da ya tabbatar iya abinda zata iya ci kenan.

Wayar ya kashe ya saka a aljihu,sannan ya zamo a hankali ya tattara kwanukan ya fice dasu.

Ci gaba tayi da zama a wajen ba tare data motsa ba,tsoron tafiya ma takeyi ta kwanta gaba daya,don ta tabbatar a yadda wata irin kasala ke lullubeta zaiyi wahala bataji tana buqatar wannan hugging nasa dake bata wata irin nutsuwa ba.

Cikin ranta ta samu kanta da tuhumar

"Me yakeyi bai shigo dakin ba har yanzu?" Tana duban agogo,a qalla ta share mintuna kusan talatin a zaune,dole ta qarfafa jikinta ta wuce zuwa gado tana rage hasken wutar dakin tare da laluben me zatayi da zai dauke mata kewa?.

Komai ta dauko sai taji baiyi mata ba,kaman jiya duk idanunta kunnuwanta nutsuwarta da motsin da duk zataji tana bibiye dashi. At last ta yaye bargon,tana jin maqoshinta ya bushe,ruwa take da buqata me sanyi kadan. Ta laluba inda ya saba aje mata ruwa tsakanin jiya da yau ba komai wajen, zuciyarta tadan karaya,sai taji kaman yanason sake ninka halinsa na daina damuwa da al'amuranta.


_KWANKWASON JIMINA_*

*_TSUTSAR NAMA_*

*_AMEENATOU_*

*_GUDUN KADDARA_*

_DUKKA AYARIN LITATTAFAN KUDINSU YA KAMA KAMAR HAKA_*

LITTAFI DAYA_400
BIYU_800
UKU_900
HUDU_1200

_IDAN TA BANKI NE ZAKI SANYA KUDINKI A WANNAN ASUSUN_

6019473875
Musaa Abdullahi safiya
Keystone bank

_ANTAYA SHAIDAR BIYANKI ZUWA GA WANNAN NUMBER_

09166221261


*Masu tura katin waya ko vtu kuma kai tsaye wannan number zaku tuntuba*

09134848107

*Maqotanmu kuma al'ummar qasar nijer zaku tuntubi wannan number dinne kai tsaye don biyan naku kudin*

09033181070


*ZAFAFA FAMILY na maraba daku*🫂🫂🫂🫂🫂*_GUDUN ƘADDARA_*

*H U G U M A*

BOOK 02 PAGE 133



Kamar me sanda take takowa zuwa falon gidan,hannayenta rungume a qirjinta idanunta kan saitin fridge din tana mamakin ganin cups da ruwa da drink ragowa saman center table din falon.

Kaman ta kwashe sai kuma ta fasa tunda bata sani ba ko shine yake amfani dashi don haka kai tsaye ta wuce side din da fridge din yake.

Ta bude a nutse tana duba ruwan da baiyi sanyi sosai ba,sai ta dinga jin kaman magana qasa qasa. Ta share tana tsammanin daga waje ne,amma kuma sai ta dinga jin kamar dukka muryoyin biyu ta sansu. Ruwan ta aza saman fridge din ta waiwaya zuwa bakin qofar shigowa falon,saita ganta a bude. Ta danyi mamaki tunda ba al'adarsu bane barin gida a bude,ta fara matsawa a hankali da zummar rufe qofar,amma kuma muryar wadda takeji ta sanya gabanta yankewa yayi mummunan faduwa

"Ina sonka......wallahi ina tsananin sonka.....kuma ko yaya ne zan iya zama dakai ya maina..........kaima kuma nasan kana sona......don ba wanda zai dinga respecting abinda baya so"

"Laila......." Ya kira sunanta dai dai sanda sultana ta isa bakin qofar. Shi da lailan ne,tsaye suna fuskantar juna saidai kuma akwai tazara tsakaninsu.

Dukka jikinta ne ya dauki rawa,ta saki qofar a hankali tana nufin juyawa,saidai kuma garin gaggawar barin wajen hannunta yadan daki qofar,sautin da ya sanyashi juyawa ya ganta amma kafin ya gama ganin nata gaba daya ta bace a wajen.

Bai wani kawo abun da komai ba ya maida dubansa ga laila wadda zuwa yanzun ranshi ya soma baci da ita.

"Next week zaki wuce Nigeria,wannan umarnina ne kuma umarnin daddy......duk wannan shirmen da kikeyi banason ki kaini bango,ina respecting sardauna......dole nayi respecting naki......ina girmama daddy......dole na girmamaki don ke din jininsa ne" ya qarasa maganar yana kara waya a kunnensa

"Sardauna kazo ku tafi......zan kwanta sai da safe" ya fadi duka lokaci daya.

"Ba matsala gani a qofar gidan" sardaunan ya amsa masa daidai sanda lailan ke sakin kuka ta kuma nemi wajen zama a wajen.

Wayarsa ya jefa aljihu yana komawa cikin gidan,yana kunyar sardauna,bazai iya ci gaba da tsaiwa har sardaunan yazo ya iske qanwarshi a haka ba.

Har ya gota fridge din ya ganshi a bude,sai ya koma ya cire ruwa guda daya me sanyi ya rufe fridge din yana mamakin barinsa a buden da akayi. Saman kujera ya koma,ya zauna yana bude murfin gorar ya kafata a bakinsa yana shanye ruwan da sauri da sauri.

Tsaf ya gama dashi,yayi wulli da robar yana fidda wani zazzafan numfashi daya gauraya da sanyin bakinsa

"AYANA LAILA" a yanzun sune manya manyan matsalarsa.......dukkansu kuma suna da wata martaba a idanunsa da bazai iya wancakali dasu lokaci guda irin yadda ya dace ba,ANYA KUWA BAZAIYI ABINDA YA DACE A KANSU DUKKA SU BIYUN BA?" ya tambayi kansa da kansa. Wani dan gajeran tunani yayi,sai ya girgiza kanshi

"BA HARAMUN BANE" ya bawa kansa da kansa amsa,amsar data zaburar dashi ya miqe a hankali yana tuna ta leqo dazu,ta kuma juya da gaggawa,don haka ya miqe yana kashe na'uarorin falon ya wuce zuwa bedroom din.

Yadda ya sameta cikin duvet tayi luf sai yayi tsammanin bacci ne ya dauketa,ya zube wayoyinsa ya sake rage hasken dakin,sai ya zare rigarshi ta sama ya shiga toilet yayi alwala.

Shafa'i da wuturi yayi sannan ya haa dukka addu'o'insa. Ya jawo wayarsa yana duban numbers dinsu duka su biyun,kamar ya rubuta gajeran saqo ya aika musu,sai kuma ya fasa,ya ajjiye wayar ya kammala shirinsa ya wuce saman gadon.

A tausashe ya jawota cikin jikinsa,saidai kuma ta sanya duka hannuwanta biyu ta nesanta kanta dashi. Mamaki yadan kamashi,yayi zaton bacci takeyi,ya sake kamota don bata wannan yanayin daya fuskanci tafi buqata amma ta sake masa hakan. Sautin kukan da yaji ta fashe dashi ya sakashi miqewa yana kunna bedside lamp.

"Me haka?,me ya sameki?,ar you okay?" Kamar dama tana jiransa ne,muryarta na rawa saboda uban kukan da tayi tace

"Stay away from me!" A kausashe. Idanu ya zuba mata sosai,ranshi yadan motsu

"Ki gogeni daga rayuwarki mana idan zaki iya?"

"Bazan iya ba but i hate you!,baka da aiki saidai mata su dinga binka har cikin gida?,shin ba zasu iya jira ka fita ba?" Dan yamutse fuska yayi maganarta na bashi mamaki

"Bana sonka,kabar rayuwata ta huta" a wannan karon! Yaji dukka wani haquri nasa yakai bango,a wannan karon yaji ya kamata yayi mata me gaba daya!, A wannan lokacin yana jin cewa ya kamata komai yazo qarshe,sai ya soma sauka daga gadon a hankali zuciyarsa na wani irin tafasa,har sai daya kammala sauka gaba daya,sannan ya tsaya sosai a gabanta yana kallonta da dukka idanunsa fes........


_KWANKWASON JIMINA_*

*_TSUTSAR NAMA_*

*_AMEENATOU_*

*_GUDUN KADDARA_*

_DUKKA AYARIN LITATTAFAN KUDINSU YA KAMA KAMAR HAKA_*

LITTAFI DAYA_400
BIYU_800
UKU_900
HUDU_1200

_IDAN TA BANKI NE ZAKI SANYA KUDINKI A WANNAN ASUSUN_

6019473875
Musaa Abdullahi safiya
Keystone bank

_ANTAYA SHAIDAR BIYANKI ZUWA GA WANNAN NUMBER_

09166221261


*Masu tura katin waya ko vtu kuma kai tsaye wannan number zaku tuntuba*

09134848107

*Maqotanmu kuma al'ummar qasar nijer zaku tuntubi wannan number dinne kai tsaye don biyan naku kudin*

09033181070


*ZAFAFA FAMILY na maraba daku*🫂🫂🫂🫂🫂*_GUDUN ƘADDARA_*

*H U G U M A*

BOOK 02 PAGE 134



"Tu m'as dit que tu ne m'aimais pas d'innombrables fois(kin gayamin baki sona sau babu adadi),inajin yanzun ya kamata nayi nesa dake din kaman yadda kika buqata......but zan auri wadanda suke sona......soon in sha Allah" yayi maganar babu hargagi balle fada,saidai kuma shi kadai yasan me yakeji qasan zuciyarsa,meye zaiyi ya burgeta?,me zaiyi da zai sanyaya dukka zuciyarta ta fito masa da zallar soyayyar da taketa boyo qasan zuciyarta?,ya rabu da ita din kaman yadda tace?,ko ya biyo mata ta bayan gida?" Maganganun daya dinga tattaunawa cikin ransa kenan shi daya zaune cikin balcony din gaban gidan.

Duk da yadda dare ya tsala amma baiga hakan ba,radadi sosai yakeji cikin zuciyarsa,baya jin bacci kwata kwata a cikin idanunsa,mode swing ne ke damun sultana kamar yadda ama tace?,ko kuma wannan kafaffen halinne daga zuciyarta?,meye ma ya tunzurata haka?. Ya dinga yiwa kanshi tambayar.

Peaceful man ne shi,baya qaunar tashin hankali sam,kuma shidin mutum ne da yake buqatar tattaunawa tsakaninsa da duk wani mutum da suke mu'amala,me yasa ba zata fuskanci halinsa ba?,bayan ita din ba baquwar saninsa bace?.

Yadda ya dinga juyi a waje haka ta dinga juyi cikin dakin. Yanayin yadda yabar mata dakin salin alin ya dinga nuqurqusar zuciyarta. Wani sashen na zuciyarta yana gaya mata bata kyauta ba......wani sashen kuma yana laluben meye tayi na rashin kyautawa a ciki?. Mutumin da ya jawo mata 'yammata har biyu cikin gidanta na sunna?,ta gama da wata saiga wata?,ta tabbatar yasan da zuwansu,me ya hana ya dakatar dasu?,tunda dai yayi waya da sardauna,tabbacin yasan suna zuwa.

Da qyar ya miqe yana komawa cikin gidan saboda wani mugun ciwon mara daya sarqeshi,ga wani zazzabi da yaji yana shirin kamashi,wannan ya sanya ya dinga jin sanyi sosai yana ratsashi har cikin qashinsa.

Daya daga cikin bedrooms din dake gidan wanda baima taba budesu ba yau dole ta sakashi ya bude,yanason bata tazarar kaman yadda tace taji idan har hakan zai dace da rayuwarta.

Bata samu bacci ba har dai dab da asuba,wannan ya sanya ta makara sallar asuba. Sanda ta tashi da idanu ta dinga bin dakin,tayi tsammanin ganinshi a ciki,saidai bataga alamun ma ya sake komowa dakin ba. Jiki a mace ta shiga toilet,ta daura alwala ta dawo ta tayar da sallah.

Duk sai take jinta wani iri,har ta kammala sallar ta koma ta zauna tana lazumi. Duk bayan wasu mintuna sai ta daga kai ta kallo lokaci. Lokaci yanata garawa amma babu motsinsa ko alama. Ta lumshe idanunta tana jin wannan baqar yunwar da take fama da ita duk bayan kowacce awa cikin duniyarta,sai taji hawaye yana shirin zubo mata.

Tun jiya take tauna abun cikin ranta,tanaso ta tantance kyautawarta da rashin kyautawarta. Idan bata kyauta ba ai shi dinma haka,ko banza ko bata hada alaqa dashi ba a matsayinta na jininsa,mai matsayi tamkar Diya a wajensa,uwar yaransa kuma qanwarsa ya kamata ya kaucewa barin kowacce mace shiga rayuwarsu.

Haka ta dinga dakon lokaci,qarfe shida bakwai takwas tara haqurinta ya gagara,yunwa ta cita sosai,haka ta miqe tana maida hijabinta tana layi ta,ta sanya slippers ta murda qofar dakin tana fitowa.

Da qyar ya janyo wayarsa dake vibration saman kanshi idanunshi a rurrufe ya daga kiran ya kara a kunnensa. Abdulhamid ne,ya gaidashi cikin tsantsar ladabi sannan ya shaida masa ya iso.

A qa'ida bayason ya bawa abdulhamid din damar shigowa gidan kai tsaye,don yanzun yasan bashi daya ke rayuwa cikin gidan ba,amma kuma akwai buqatar a tsaftace gidan,uwa uba yasan zuwa yanzun tana da tsananin buqatar abinci. Ciwon da cikinsa keyi da kuma zazzabin jikinsa bazai barshi ya samar mata komai ba,don haka yace dashi murya qasa qasa

"Ka gyara harabar gidan da parlor,kayi da sauri,ka qarasa kitchen ka hada simple breakfast wa madam.....idan ka gama kayimin magana na fito"

"Okay sir" ya


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login