Showing 114001 words to 117000 words out of 294767 words
Chapter 39 - Gudun Kaddara Book 2 Hausa Novel Complete
yanzu ya sakarmin diyata" ajiyar zuciya kawu ya fidda,ya sani shima aba din ba baya bane wajen taurin kai da kafiya,yasan kuma tunda ya kafe din saukeshi daga abinda ya niyyata din sai babban abu
"Ta yaya zaka ce haka?,bayan yace shi bazai iya sakinta ba?"
"Idan bazai iya sakinta ba ai kawu ita ba sonshi takeyi ba" ido maina ya lumshe yana ganin qiyayyarsa quru quru cikin idanun aba,wanne irin abune haka?,duk yadda yakai ga son sultana baya jin zai sota kamar shi din,gudan jininsa,kuma dansa na fari da ya fara mallaka a duniya
"Waye ya gaya maka?......ke sultana......karki duba girman laifin mijinki,kada kuma ki duba mu mu dukkanmu da muke a nan wajen,aliyyu mijinki ne,kuma uban yaranki da a yanzun baku da kamarsa,kina son mijinki ko kuwa a'ah?" Duk wanda yake wajen yasan cewa kawu yayi tambayar ganganci ne saboda bashi da masaniyar yadda sultana ta dauki maina.......a wajen maina din kuwa,ji yayi kamar ya maida tambayar data fita a bakin kawun......don ya sani abune me wuya yaji abinda yake da muradin ji din daga wajenta
"Bana sonsa kawu......na rantse da Allah bana sonsa" ta furta muryarta tana rawa,fuskarsa na tsakanin dankwalin data warwareshi tana tsane siraran hawayen dake sauko mata.
Saukar wani abu me tsini yaji tsakiyar zuciyarsa kamar saukar mashi,kalaman nata yaji sun matuqar yi masa girma a zuci da gangar jiki gaba daya. Kalmar QIYAYYA ba qaramar kalma bace dake raunatar da mutum gaba daya, qiyayyar ma kuma da aka sanar da ita cikin bainar jama'a,a gaban idanuwan mutane,ba mutum daya ba biyu ba,iyayensa da yaran cikinsa,ya ilahi wannan wanne irin qiyayya ne?,bazaici darajar koda mutum daya a wajen ba!? .
"Shikenan,duk da kince baki sonsa amma hakan bazai sanya ayi gaggawar cewa ya sakeki ba sultana,ki sake nazari,kowace mace na iya fuskantar irin wannan bacin ran,amma bayan zukata sunyi sanyi ana iya fahimtar juna"
"Sai yaushe zuciyata zatayi sanyi?,sai yaushe zan fahimci maina?,bana jin hakan zata kasance har abada,kullum tsanarsa ninkuwa takeyi cikin raina,kullum burina na bude idanuna naga nayi nesa da rayuwarsa shima yayi nesa da tawa,kullum neman hanyar da zata qara nisantani dashi nakeyi" abinda ta fadi kenan cikin zuciyarta tana dunqulewa waje daya sabon kuka yana kubce mata
"Kawu,inda za'a dubi rayuwarta ayi mata adalci shine......ya bata takardarta tukunna,duk wani fahimtar juna da ake buqata a sameshi daga baya"
"Yaaya..... inaga ayi haquri a gwada maganar kawu tukunna" oncle umar ya fadi yana duban aba cikin girmamawa
"A'ah,ku rabu dashi,ai dan kanshi ne,sai yayi yadda yakeso kaman yadda zuciyarsa takeso" muryar bibi data shigo afujajan ta fada,wadda almu ne ya isketa cikin gida ya shaida mata saqon oncle umar,kuma tazo akan gaba.
Gurin zama suke qoqarin bata amma bata bi ta kansu ba,sai data dangane da kujerar dake gaban aba ta zame ta zauna a qasa a gabansa tana kallonsa
"Kafin ka kashe wannan auren inason ka fara kasheni ne hamidou kaman yadda na taba gaya maka" ta furta kanta tsaye da qarfin gwiwarsa.
"Subhanallahi" kawu dasu oncle umar suka fadi,yayin da aba ya zame qasa kusa da ita babu shiri ya zauna yana dubanta a matuqar ladabce
"Bibi.....me yasa kk irin wannan maganar?" Kafin ta sake cewa komai oncle umar ya dubesu
"Goumar......ka dauki benazeer,maina dauki batoul ku wuce ciki" tuni goumar ya gaji da ganin wannan tashin hankalin dama,don haka a gaggauce ya miqe ya dauki benazeer,ya miqawa batoul hannu,ga mamakinsa saita maqale kafada tana sake dafe maina tana kallon fuskarshi. Wani siririn murmushi ne ya subuce masa duk da yanayin da zuciyarsa take ciki,ya miqe a nutse ya dagata bisa kafadarsa,sai benazeer itama ta zame daga hannun goumar tana jin kishin bai dauketa ba,ya duqa a tausashe ya azata saman daya kafadar tasa ba tare da yaji nauyinsu ba sam sam suka fara takawa suna barin dakin oncle umar da issoufou da kawu suka bisu da kallo kowa tausayin yadda qaddara ta samar dasu tana ratsashi
"To eh mana...... tunda muke da ubanku har yabar duniya ban taba yaji ba bare akai ga batun saki,hakanan tunda na kafa zuri'ata ba'a taba sakin kowa ba a cikinta......sai yanzu za'a fara daga kan maina da sultana?,su zasu kafa baqin tarihi cikin zuri'ata?" Maganar saita zafafi sultana dake zaune a tsakanin kujeru,wato a nan bibi tana nufin tayita dakon aurensa?,ko tana nufin taci gaba da zama dashi?, abinda har abada bata jin zata iya koda a mafarki kuwa,a taqaice dai kaman ma goyon bayan mainan takeyi?,ta manta dukkan wasu azabu da wahalhalu da tasha?,ta manta da qyar ta samu rayuwarta ta daidaita?,da qyar ta tsira da ranta?,ranta ya sake baci sai ta miqe tsam tana barin wajen tana raba hanya.
A nutse yake takawa dauke da yaran,kunnuwansa sunata jiye masa surutun da suke zubawa su da goumar,alamun sabo da shaquwa me qarfi na nunawa a tsakaninsu.
Abubuwan da suka wanzu a yanzun ne kawai ke kai kawo a zuciyarsa,tunda suka fito daga dakin ya kasa furta koda kalma guda daya,sai kunnuwansa dake tsintar surutan yaran.
Haka kawai yaji gidan ya quntace masa,yana buqatar nutsuwa da kuma kadaicewa,yanason ya kalli yaransa son ranshi,yanason ya sake sosai da yaransa wanda yasan muddin cikin gidanne bazai yiwu ba,da wannan tunanin sai kawai ya wuce parking lot na gidan,kafin su qarasa kuwa sunsha kallo shi da yaran,sunyi wani kyau a jikinsa,sai a sannan kamanni kadan kadan suke bayyana tsakaninshi dasu da suka jera dashi.
BMW dinsa ya bude,ya kuma bude gidan baya ya saukesu suka shige suna murna,kamar wani sakarai yayi tsaye yana kallonsu har suka gama shiga ya rufe musu qofar,ya koma mazaunin driver ya shiga,daidai sanda goumar ya bude seat din kusa dashi ya shige shima.
"Me yasa kayimin qarya?,me yasa ka boyemin kyautar da Allah yayimin?" Ya jefawa goumar tambayar ba tare daya kalleshi ba yana qoqarin tayar da motar. Kallonsa goumar yayi sannan ya maida dubansa gaban motar
"Bai kamata zuciyarta ita kadai ta wahala ba,bai kamata ace ita daya tasha wannan azabar ba......taci wahalar da babu wanda ya zatar mata rayuwa,duk wani information da nake baka kana jina ne kawai,amma bahaushe yace gani ya kori ji......banda wasu dalilai.......banda kuma wasu hujjoji tabbas bazan bari ka dawo ka sameta da aurenka ba...... tabbas da na......"
"Goumarrrr!!!" Ya kira sunansa da wani irin sauti me qarfi. Waiwayowa goumar yayi yana dubansa,idanun nan da suka sauya launi tun dazun yanzun sunfi haka jirkicewa, murmushi can qasan zuciyarsa ya qwace masa,yana sane ya gaya masa hakan, yanason ya motsa masa zuciyarsa da kyau a kanta,yana kuma son shima ya dandani koda kadan cikin quncin da zuciyarta ta wanzu akai. Duk yadda yake takurata yake tsokanarta......amma yana jin babu dadi da yanayin da haidar din ya sanyata ciki
"Karkayi tunanin don kana dan uwana..... kuma ka yimin wata rana hakan ya baka daman shiga gonar da ba taka ba" yayi maganar fuskarsa nayin jaaa. Qaramin murmushi goumar ya sauke,sai ya sanya hannu ya bude murfin motar ya zura qafafunsa waje sannan ya waiwayo yana kallonsa
""Ban fada da zummar cin zarafi ba,Allah ya baka haquri" daga haka ya fita a motar salin alin ya rufe masa. Kaman jiran fitar nasa yakeyi ya bawa motar wuta,ya juya kanta da zafi zafi ya nufi gate yana sakewa security horn,cikin iya aiki da cika umarni suka bude masa gate din ya fice da mugun gudu har yana cin taya.
Sanda ya saitu a saman titin batoul ta saqalo hannunta ta wuyansa,abinda ya sanyashi sauke wata ajiyar zuciya me sanyi
"Uncle haidar.....me ya sanyaka hawaye dazun kai da auty?" Tambayar tazo masa a bazata,sai ya dinga juya amsar da zai bata din. Baisan yadda zai gaya mata yadda zaga fahimta ba,hakanan kuma bayason ya mata qarya
"Ko aba ya dokeku ne?,kuma shi ai baya duka,bai taba dukanmu ba" batoul din ta sake fadi sanda benazeer ta zuro hannu tana shafa gashin habarsa dake da santsi cika da kuma baqi sidik.
*_KWANKWASON JIMINA_*
*_TSUTSAR NAMA_*
*_AMEENATOU_*
*_GUDUN KADDARA_*
_DUKKA AYARIN LITATTAFAN KUDINSU YA KAMA KAMAR HAKA_*
LITTAFI DAYA_400
BIYU_800
UKU_900
HUDU_1200
_IDAN TA BANKI NE ZAKI SANYA KUDINKI A WANNAN ASUSUN_
6019473875
Musaa Abdullahi safiya
Keystone bank
_ANTAYA SHAIDAR BIYANKI ZUWA GA WANNAN NUMBER_
09166221261
*Masu tura katin waya ko vtu kuma kai tsaye wannan number zaku tuntuba*
09134848107
*Maqotanmu kuma al'ummar qasar nijer zaku tuntubi wannan number dinne kai tsaye don biyan naku kudin*
09033181070
*ZAFAFA FAMILY na maraba daku*🫂🫂🫂🫂🫂*_GUDUN ƘADDARA_*
*H U G U M A*
BOOK 02 PAGE 61
Kai ya girgiza qaramin murmushi yana subuce masa,ko da basu fada ba,kallo daya zaka yi musu kasan sun samu gata gami da tsantsar kulawa me tarin yawa
"Aba be dokeni ba,autynku nakeso......ita kuma tace bata sona" ido suka hada yaran suna hangame baki,qwaqwalwarsu bata gama fahimtar ainihin ma'anar maganar ba,amma kuma sunsan meye so a suna bawai a ma'ana ba
"Uncle babu kyau,Allah ya hana acewa mutum ba'a sonshi ko?" Benazeer ta furta har tana leqowa fuskarsa. Hannu daya ya sanya ya shafa sumarta yana sake sakin wani murmushin,har cikin zuciyarsa yana jin suna sake zama jinin dake harbawa a zuciyar tasa suna narkewa da kyau
"Ba kyau beenaz......zaki gaya mata ta daina fada?"
"Eh Uncle"
"Kefa batoul?"
"Eh nima haka uncle"
"Am not Uncle.....am dad" ya furta a hankali yana duban yanayin fuskokinsu ta madubin gaban motar. Sak yaga sunyi suna sake kallon junansu,sai suka kasa fadin komai saboda kwanyarsu kamar tana mamakin maganarsa
"Kun taba ganin daddynku?" Ya sake jefa musu tambayar. A tare suka hada baki wajen cewa
"Eh...." Batoul ta daga yatsanta daya tana cewa
"Amma fa sau daya"
"Nayi kama dashi?" Ya fadi yana nuna kanshi. Tsit suka sakeyi suna duban fuskar nashi ta cikin mudubi su dukka biyun,kowanne kwanyarsa na dawo masa da surar abban nasu da goumar ya taba nuna musu shi har sau biyu
"Kuna kama sosai uncle....." Benazeer ta fadi
"Kaman kai ma" batoul ta sake fada tana Dora hannun a qirjinsa tana qaramar dariya. Shuru yayi shima yana murmushi,zuciyarsa na masa sanyi,komai daya sameshi a baya a yanzun sai yaji kaman bai sameshi ba,komai sai yaji yana sauka masa a zuciya,wani farinciki na ratsashi da kadan da kadan. Kalaman bibi suka dawo masa,ya tabbatar da izinin Allah komai ya kusa zuwa qarshe,kuma tunda bibi na goyon bayan barin igiyar aurensa.......yana da yaqinin shike da nasara...... matsalar aba kuma zata zo masa da sauqi tunda dai da bibi a gefansa,rigima da kuma daru ne yasan zaya shashi
"Sultana fa?" Zuciyarsa da tun dazun take motsawa ta jefa masa tambayar dai dai sanda yake karya kan motar zuwa titin dake dauke da hotels da kuma guest in. Ya gama karantar lamarin sultana,yana da kuma plan guda uku zuwa hudu dukka a kanta,yana kuma kyautata zaton bazai hau dukkan matakan ya sauka babu nasara ba. A yanzu yanaso yayi calling attention dinta ne har ta tsaya dashi,bayan ta tsaya din maganar fatar baki ta hadasu,wannan shine matakin farko da yake da buqata,saidai kuma ya fuskanci shine abu mafi wahala a dukka tafiyar. Tunda yazo qasar ko kalmar A bata taba hadasu ba,ta yaya zai samu ya tsaidata suyi magana shi da ita?.
Kai tsaye ya gama zagayen titin,ya kuma zaba musu hotel me kyau. Bayan sun bashi key bai isa dakin ba,sai daya daukesu suka tafi yawon siyan kayan maqulashe. Ci wannan ci wancan,duk abunda suka nuna sona so sai ya siya musu,haka suka dawo masaukinsu da tsaraba fal,suka yada zango a dakinsu.
Da kansa ya musu wanka,ya kuma shiryasu cikin wasu baby pink din pyjamas masu ratsin maroon sannan shima ya shiga yayi nasa wankan,daya fito cikin irin nasu pyjamas din ya shirya,ya feshe jikinsa da tattausan turarensa ya kuma gyara lallausar sumarsa ya maidata baya,sai ya sanya slipper din da ya siyo,ya kunna musu tv yace zaije yayi sallah,bazai jima ba kada suje ko ina. Su din ba baqin abun bane already sun saba,don haka har yaje ya dawo suna zaune abinsu. Dukka kayan ciye ciyen ya sake baje musu sukaci iya cinsu suka bar na bari,sai ya tattara komai ya dawo ya zauna a tsakiyarsu.
"Kuzo kuga daddynku" ya fadi yana buda wata folder daya adana dukkan tsaffin hotunansu,wasu da yan gidansu wasu da aba ama,wani shi da sultana sanda suna dasawa qwarai.
Kallon hotunan sukeyi suna kuma duban fuskarsa,kaman yadda duk inda akazo wajen da take a ciki sai ya tambayesu waye wannan?sai suce
"Kaine"
"Shine daddynmu" batoul take yawan nanatawa sai ya daga musu kai yana murmushi. Sai da suka gama kalla tsaf sannan yace
"Bari daddynku ya baku labarin mommynku" kwance sukayi a jikinsa fuskokinsu cike da farinciki,sun kanainayeshi gaba daya suna maimaita
"Uncle haidar......kaine daddynmu?" Da alama abun yana bugar da tunaninsu yana kuma basu mamaki
"Baru na kira muku uncle goumar a tambayeshi"
"Yes" benazeer ta fada tana miqewa ta zauna sosai a gabansa gami da tanqwashe qafa,ta kuma tsireshi da idanun nan nata. Sak abun sai ya masa kama da yadda sultana ke masa,ya saki siririn murmushi ya soma laluben number goumar.
Sau uku tana sanya hijab dinta tana zareshi kana sai ta koma ta zauna a wajen data tashi. Ta sake duba agogo,still dai dare yana dada yi,ba motsin benazeer ba na batoul,ta kuma lura tunda ya fita dasu daga falon aba ne. Taga goumar har kusan sau biyu,bata ganshi da yaran ba,sannan bataji kowa yana maganar yaran ba. Idanunta ta lumshe zuciyarta tana bugawa,tun dazun abu daya zuciyarta ke raya mata,kada fa ya gudar mata da yara?,kada fa a sake nemansa a rasa da yaran?,tunda dai shi din mugu ne dama,mugunta bai dauketa a bakin komai ba.
Zumbur ta sake miqewa a karo na hudu zuciyarta na tsunkularta ta maida hijabinta,saidai kuma tana takawa zuwa waje tana tunanin waye zata kaima qara ko ta tuhuma?.
Tana tsananin kunyar ama ba zata iya tunkararta ba,aba kuwa batason sake assasa qiyayyar da yake nunawa diyan cikinsa qarara a kanta,bibi kuwa ta fara sallama lamarin bibi,duk da bata fito kai tsaye ta nuna tana yi da maina ba,amma kuma ta fuskanci ta karkata gareshi
"Goumar" zuciyarta ta gaya mata, tabbas shi daya ne zaisan inda suke,tunda zuwa yanzu ta fahimci tun asali munafukinsa ne,kamar akwai wata boyayyar alaqa tsakaninsu.
Gidan yayi shuru saboda raguwar 'yan biki,don tun magariba aka kai amare aka dawo,amaren da bata samu daman zuwa kaisu ba. A nutse take taka farfajiyar gidan,zuciyarta na mata fargabar amsar da zataji daga goumar. Har ta nufi hanyar dakunansu sai ta fasa,ta dawo da baya tana nufar bakin gate din farko na gidan. A bakin motarsa ta sameshi a tsaye yana amsa waya da qaramar wayarshi,saita nufeshi kai tsaye tana saita nutsuwarta.
Sanda yaji ana nufoshi waigawa yayi kadan,sai yayi qoqarin yin sallama da wanda ke kan layin dab da sanda ta iso gareshi.
"Ina yara na?" Ta tambayeshi tana shan mur idanunta a kansa. Qaramar dariya ce ta qwace masa,ya gyara tsaiwarsa yana kallonta,kamar ya tsokaneta yace daman kina sonsu har haka?,sai kuma ya fasa kada qilu ta jawo bau,ya hada nutsuwarsa da kyau sannan yace
"Bansan ina suke ba,amma dai sunbi mahaifinsu" haushi kalmar mahaifin ta bata har ta gaza jurewa ta jefa masa wata tambayar
"Dama suna da wani mahaifi ne?" Shigowar kiran wayar goumar sai ya zamana kamar amsar tambayarta,sai ya hadiye amsar da yayi shirin bata ya zaro wayar yana dubawa.
Murmushi ne ya qwace masa,abun yazo masa a dai dai,don haka sai ya miqawa sultana wayar kai tsaye yana duban qwayar idanunta
"Ga mahifin nasu,saiki gaya masa ya dawo miki dasu ko?"
"Kana tunanin bazan iya bane?,ko kana tunanin jiya yau ce?" Ta furta da zafi zafinta tana fusgar wayar daga hannun goumar cikin fushi. Dagawa tayi ta kuma sanya wayar a kunnenta. A nutse yayi cikakkiyar sallama
"Assalamualaikum" ya ajjiye sallamar a hankali,saidai kuma a maimakon yaji muryar goumar sai wannan sautin......sautinnan da bai taba gushewa daga kunnuwa da memory dinsa ba,sautin nan dake tsaye tsakanin zuciyarsa da jinin jikinsa,sautin nan da yayi matuqar kewa.......yake kuma son yaji koda sau daya tak ne ya mamayi qirjinsa da kunnuwansa
"Ka dawomin da 'ya'yana,kada kuma ka yarda komai na cutarwa ya samesu,don baka da hurumin tabamin yarana" idonsa ya lumshe wani abu yana kwarara tsakiyar zuciyarsa,ya tabbatar idan bai tsokaneta ba,bai kuma tunzurata ba maganarta dashi ta qare,don haka yace
"Wadannan kam sun zama nawa,saidai ki haifi wasu" ji tayi kaman ya doka mata guduma saman kai,idanunta suka rufe,tana son yayyaba masa maganganu amma kuma idanun goumar na bisa kanta,batason kuma ta sauka da yawa daga control dinta
"Wannan duka cikin matsalarka ce,nidai na gaya maka ka dawomin da 'ya'yana.......mtsewwe" ta rufe da jan tsaki kaman zata tsinke harshenta sannan ta zare wayar a kunnenta tana miqawa goumar.
Lips dinsa na qasa ya cije sosai yana rintse idanunsa saboda yadda sautin tsakin ya rasashi matuqa. Tsaki?,ta manta yana cikin abubuwa biyun daya tsana?,tsaki da gunaguni?,har cikin ransa yaji saukarsa matuqa,sai ya gaza bude idanunsa har zuwa sanda yaji muryar goumar ta maye gurbin tsakin nata
"Yaa haidar" ya fadi