Showing 261001 words to 264000 words out of 294767 words

Chapter 88 - Gudun Kaddara Book 2 Hausa Novel Complete

sanya ran tace wani abu itama shuru, kosu aminata da take sanya ran samun wani information daga garasu duka satinma basuyi waya ba, don sun shiga cikin sabgar bikin najma gadan gadan. Abinda ya sake rikita mata lissafi kenan, dai dal da goumar jira takeyi taga kiransa koda kuwa tsokanarta zalyi
amma dif. Lissafinta ya fara bata kada dal ace kowa goyon bayan abun yakey!?, kada dal ace dukkansu sunyi hadaka wajen boye mata abinda komai sun goyi bayan maina dinsu?.

Yana zaune bayan motar hayar da zata migasu airport yana amsa waya, saidal fitowarta kuma ta fusgi hankalinsa. Tayi masa wani irin kyau da ya sanya ya gaza dauke idanunshi daga kanta, har ta iso bakin motar ta bude ta shiga a hankali.

sau biyu kafin su isa sardauna da suhall na kiransa, abinda ta fahimta ma kamar gaba daya zasu wuce, kamar Jirginsu daya kenan dasu?, turgashi ta fada gasan ranta tana jin wani zafi yana taso mata.

Wayoyinsa yakeyi har zuwa sanda suka isa airport din. Dan dakatawa yayi kadan yana qarewa zirga zirgar jama'a dake wajen kallo. Akwai mutane da yawa dake kai kawo, alamun cewa yau din akwai matafiya masu yawa dake tafiya wasu kuma suke dawowa kenan.
Ajiyar zuciya ya dan saki, har cikin ranshi yana jin kishi yadda zasu fita haka. Yayi imanin idanu ne zasuyi yawa a kanta, shi kansa yau din shigarsa tayi masifar tafiya dashi, yana jin wani irin kishi har tsakiyar zuciyarsa.

Ta motsa zata bude motar ta fice ya furta

"Wait" da sauri yana kama hannunta ya rige gam cikin nasa ba tare da yasan yayi hakan ba yana tsaka da neman number din goumar.

"Eh mun garaso.....zo don Allat" daga haka ya kashe wayar yana gogarin kulleta.
Idanunta ta sauke saman
dogayen yatsunsa da suka ratsa
nata hannun. Komai nashi ta kalla masu kyau ne, kaman yadda kusan komai nasa shi su batoul suka debo.
Janye idanunta tayi don kada ya kamata tana kallonshi, bugu da gari kuma wani irin kishinsa taji yana
motsa zuciyarta.

Saida goumar ya iso ya fidda luggage dinsu sannan ya bude ya fita, ya zagaya ya bude mata ya bata hannunsa yana rige hannunta
cikin nashi sannan ta fito.

"Biyomu a baya" ya bawa goumar umarni, dariya ta tasowa goumar din ya gintseta. Abun ya motsa kenan, kishin aliyyu ba sabon abu bane ga duk wanda ya sanshi, ya kirashi ne kenan saboda yayi musu bodyguard?, goumar ya raya a ranshi.
Tun kafin ta garasa shiga departure lounge ta Jiyo muryan benazeer da batoul.

Tadan saki boyayyen murmushi, yau kam tasan kowa zia shigesu da surutu.....ba sukuni yau za'a nijer?, bibi taga ta kanta a hannunsu.

Su suka fara ganinta, suka bar komal suka rugo zuwa wajenta, wanda dab da zasu iso maina yayi hanzarin shiga tsakaninsu da sultana yana daga hannu
"Be careful mana BB, ban hanaku irin wannan welcoming din ba......ku taho a hankali" ya fada yana nuna cikinsa. Dariya yaran suka ayalqyale dashi sannan suka sassauta gudun zuwa sassarfa

"Good girls" ya fada yana matsawa daga tsakaninsu.

Wani irin kunya ce ta kamata ganin akwai jamá'a da yawa a wajen, saugin abun kusan da yawansu ba yaren sukeji ba, tabbas da a nijer ko Nigeria hakan ya faru sai ta kusa faduwa saboda idanu, saidai duk da hakan tana jin kaman akwai idanuwa a kanta.
Ta canka daidal, idanunta
basu zame ko ina ba sai kyakkyawan gani da sukayi saman fuskar laila da ayana, kowaccensu saman kujera daban, suna kuma rige da wayoyinsu a hannunsu amma dukkansu idanunsu yana kanta.

Samun kanta da faduwar gaba tayi, tayi namijin gogarin dauke idanunta daga sashensu cikin nuna sam sam ma bata gansu ba, to amma me sukeyi a nan?, dasu za'a yi tafiyar? ¡dan dasu za'a yi tafiyar me zasuje nijer suyi?, meye alagarsu da familynsu?, indai duka tambayoyin nan akwai amsoshinsu, kuma amsoshin suka zama daidai da hasashenta hakan yana nufin...
...".

Kasa garasa hasashen
da zuciyarta tayi mata tayi saboda wata fargaba da taji ta saukar mata, saita soma takawa a hankali tana budewa benazeer da batoul hannuwanta tana yogarin canza mode nata saboda idanun da takeji suna kewaye da ita.*_GUDUN KADDARA_*
*HUGUMA*
BOOK O2 PAGE 140

Daga ayana har laila babu
wanda bai hangi tsantsar dacewa me girma tsakanin maina da sultana ba. Wani irin matching da ba kasafai aka fiya samunsa tsakanin ma aurata ba. Wasu irin couples da suka dinga daukan hankulan mutane, tun daga shogowarsu airport din har zuwa wait lounge din. Kamannin dake tsakaninsu ita da maina din sai ya zama wani abu na musamman kuma na daban da ba kasafai ake samun irinsa ba.
Tsakaninita da mainan saika rasa waye yaf kyau?, duk da a zahiri nata kyan ya dara nashi, saboda natan ya hadu da ado da gayu irin na diya mace.

Daga laila har ayana ba wanda bai sake duban jikinsa ba... ba wanda baiji ya muzanta ba, ba kuma wadda bataga tarin fifiko dake tsakaninta da sultana ba, wauta ce ko ganganci shiga gonarta?, ko ratsa huruminta?, ko kuma hadakar masoyi da ita?.

Sultanar irin mutanen nan
ne da bangiji ya sanya suna da rabon abubuwa masu tarin yawa a rayuwarsu, kyau ilimi dukiya gata
da kuma miji na kerewa sa'a, ga albarka ya'ya na gani na fada har guda biyu sukutum da guda tunda sauran quruciya sharkaf a jikinta.
Wannan ya sanya duk wanda zai kalli su batoul baya taba kawo cewa su din wai 'ya' yanta ne, kallon gannenta kawai ake musu, don ko zaka kwana kana rantsuwa indai ba da qwaqwawaran hujja ba babu me yarda dakai akan hakan ba, ba kuma wadda bataga tarin fifiko dake tsakaninta da sultana ba, wauta ce ko ganganci shiga gonarta?, ko ratsa huruminta?, ko kuma hadakar masoyi da ita?.

Tsam suka rungume
gafafunta dukkansu, ta saki murmushi a nutse tana shafa kansu.
Sunyi kyau matuga da gaske cikin wandunan jeans da shirt dinsu data dace da wandon. Rafafunsu sanye da rufaffun takalma, komal nasu iri daya ne kuma kala daya ne, ama bata taba yarda koda zaren ya rabasu, don haka hatta agogon dake magale a hannuwansu da kayan adon gashi da aka yima gashinsu ado iri daya ne sak da sak.

Hannuwansa ta rige suna
takawa zuwa rukunin wasu kujerun daban da basa kusa da inda su laila ke zaune, saidal duk da hakan bata jin ta tserewa ganinsu.
Dukka hankalinta ta karkata akan yaran, sunata mata surutu tana biye musu, saidai fiye da rabin hankalinta gaba daya yana kan duk wani motsin maina da su suhail, wadanda tunda suka zauna suke qus qus, ba kuma zatace ga abinda suke tattaunawa ba.

Abu guda daya ne kacal da
zata iya cewa yayi mata dadi,bataga yaje inda su ayana suke ba, haka suma basuje ba, kawal dal zata iya ganin sanda ya daga musu hannu suma suka daga masa, sannan ya samu waje ya zauna cikinsu suhail din.

Hannu takaita shafa
cikinta jin yayi wayam kamar anyi yasa, ta daga agogon hannunta ta kalla, agalla akwai kusan awa guda a gabansu kafin tashin jirginsu, ita kuma bata jin zata iya jurewa har zuwa sanda zasu shiga jirgi a basu in flight meal ba.

Benazeer ta kalla tayi gasa
gasa da murya

"Kiramin uncle goumar" amsa mata tayi tana sauka daga saman kujerar, ta kuma nufi inda goumar yake wanda yayi zaune yana waya da najma. Duk motsinta idanunshi
yana kai, zakayi tsammanin baya gani ko baisan abinda ke faruwa ba, saidal har jininsa yana jin ita din priority dinsa ce. Har suka gama
qus qus da goumar ya juya yana laluben hanyar fita don ya sama
mata abinda zata ci din idanunshi a kai, sai yasa hannu ya yafici goumar din.

A girmame ya davo yadan
ranqwafo gabansa

"Ina zuwa?" Ya tambayeshi yana
kallon idonsa

"Mummyn twins ce take jin yunwa, so zan sama mata abinda zataci kafin lokacin tashi".

"Waye ya saka?, ba aikinka bane tafi ka bani guri" ya fada cikin kurari.
Abun ya bashi dariya sosal, don suhail da sardauna dake gefe basuji ma abinda yake gaya masa ba, ya qunshe dariyarsa yana komawa mazauninsa, cikin ransa yana fadin
"Dama nasan za'a rina, ina zaman zamana an jawomin kora da hali".

Dubansa ya malda inda suke zaune din, akayi sa'a Idanunsu suka hadu guri guda. Cikin ido da fuskarta yaga rauni sosal, da gasken gaske take jin yunwa da alama, yadan motsa idanun nasa da wani salo na magana da ido, sai ta dan janye idonta kadan daga kanshi saboda qwayar idanunshi kadai suna sanyata jin abubuwa gasan zuciyarta da take gani bai dace ta ji a kansa ba. Kamar tana zurfafawa tana kuma zafafawar da bai kamata ace haka tayi ba.

A nutse ya mige yana basu excuse ya nufi hanyar fita. Bai wuce minti goma ba duka duka ya dawo.
Kai tsaye ya nufi kujerun da suke zaune bayan ya ja kujera guda daya ya a je gabanta.

"Oya ku matsa mamanku da baby zasuci abinci" yace da benazeer da batoul wadanda sukayi kane kane saman cinyarta. Kai kawal ta daga ta dubesti, batasan me yasa baya kunyar yin zancan cikin da yaran ba kwata kwata, itakam ba zata ya ba, ko a yanzu ma kunyar yadda zata shiga nijer da wani cikin takeyi, bayan tsayin dukka shekarun da kuma irin kai ruwa rana da aka dinga yi tsakaninta dashi, yanzu ta dubiidonsu tace me?, bibi ma kawai tasan ta isheta.

Suna dariya kuwa suka
matsa din, yayin da idanu suka gara yawa a kansu.

Saman gafafunsa ya dora abincin sannan ya bude, ya sanya spoon yana kallonta

"Bismillat" ya fada yana tsareta da idanu. Ya lura kaman bata zama comfortable da cin abinci a gurin ba, don haka ya sake jawo kujerarsa gabanta. Sunyi kusa ainun kamar zasu hade gaba daya, amma kuma hakan ya zame mata garkuwa ya kuma bata nutsuwar fara cin abincin a hankali, har sai data goshi sannan ya janye jikinsa.

Ko a cikin jirgi tana
ankare da komal, saidal kuma ko a tuska bata nuna ba. Lailan da ayana seat dinsu daya, sai suhail da sardauna suma seat daya suke.
Benazeer da batoul suna seat din gabanta.

Kusan shine na garshe, ya garaso a nutse ya zaua seat din usa da nata bayan ya dudduba benazeer da batoul ya tabbatar komai lafiya.

"Akwai wata matsala?" Ya jefawa sultana tambayar yana zaro wayarsa a aljihu don kasheta.

"Alhamdulillah" ta amsa masa tana sake hade ranta, ta fahimci yadda ayana ke yawan waiwayowa tana kallonsu, ta tsani wannan bala in kallon da take dashi wanda batasan meye dallinsa ba.

Sanda jirgi ya daidaita a sararin subhana sal dukka ga jiya da kasala suka saukar mata, ta cure jikinta guri daya bayan ta gama cin abinda zata iya ci daga in flight meal din da duka gabatar musu.

Yana karance da ita,ya kuma fahimceta, ya sanya hannu ya dauko mini blanket ya ware ya lulluba mata. Wannan ya sake kashe mata jiki sosal, ta bishi da idanu, idanuwansu ya hadu guri guda. Ya karanci godiya takeson masa, Itace magale a bakinta, sai ya dauke kanshi a hankali yana maida idanunsa kan screen dake gaban kujerarsa yana duban map da awannin dake gabansu kafin saukarsu a niamy.

Bazatace ga yadda tafiyar ta kaya, ba kuma zatace ga yadda akayi ba, tadal farka ta ganta kwance cikin air jinsa, ya mata wata irin kyakkyawar runguma data jima tana kewa, wanda kuma tayi imanin wannan hug din data samu shi ya sanya baccinta yin lasting har haka.

Bataso ta motsa har yasan ta farka, don batasan da wanne ido zata kalleshi ba, awa nawa ta share oho...... kamar sunsan me take tunani sanarwa ta fara karade cikin
Jirgin akan isowarsu niamy din.

Tunda ta farka yaji haka
a cikin jikinsa amma shima yagi ya nuna don ta samu nutsuwa da kyau. Hakanan shi shaida ne akan ta samu bacci me kyau na dukka awannin, baccin dashi kansa yayi mamakin yadda ta cinye awannin tana yinsa.

A hankali ta zare jikinta, bai barta ta gama daidaituwa a zamanta ba ya soma qoqarin daura mata belt. Idanunta akan hannunsa sanda yake hakan, hucin numfashinsa da gamshin tattausan turarensa yana ratsa hancinta, take ta ji Jikinta gaba daya ya amsa, sai ta kawar da kanta gefe zuciyarta na gara yawan bugawar da takeyi.
*_GUDUN ƘADDARA_*

*H U G U M A*

BOOK 02 PAGE 141



Kusan tun daga nan bata sake ganin ayana da laila ba,hakanan suhail da sardauna.

Suna zaune dasu benazeer maina din ya qaraso,ya dubi goumar

"Nan da one hour flight din da zashi maradi zai tashi,so ina ganin is better ku zauna jirashi a nan,gobe in sha Allah morning flight muma zamu biyo" ya fadi yana kallon agogon hannunsa.

"Yeah hakan yayi,awa dayan ai kamar yanzu ne" goumar ya fadi yana duba lokaci shima.

"BB......see you tomorrow ko?" Maina ya fada yana duban benazeer da batoul. Qarasowa sukayi suka rungumeshi,sannan suka matsa jikin sultana dake tsaye wadda bata gama fahimtar abinda maina yake nufi ba.

"Gaskiya zan bisu......banason kwana a niamy" sultana ta fadi tana gintse fuska. Waiwayowa yayi ya kalleta sau daya tak,sai ya maida kansa yana ci gaba da tafiya. Sak ta tsaya ranta yana baci,ta waiwaya sai suka hada idanu da goumar.

Da ido yayi mata nuni da ta bishi,tayi kaman bata gane ba,dole ya buda baki

"Why are you like this mummy twins?" Ya tambayeta cikin ranta yana jinjina soyayyar da maina keyi mata. Yadda ya sauka a boss mainan nan tunda ya shaqi iskar niamy kafin sukai ga shiga maradi ya tabbatar inda wani ne cikin shi ko su almu ko su aminata da tuni ya gamu da nasa tashin hankalin,amma da yake shalele ce bai tanka ba yadai soma nuni ne kawai da ido.

Yaran ta kalla taga sun dan zuba mata idanu,kai ta kada,ba zataso ta dinga jayyaya da daddynsu a gabansu ba, zuciyarta a raunace tace

"Ku gaida su bibi kafin mu qaraso" saita qarasa tana tana kumatunsu benazeer

"Kuce nace ta tanadarmin abun dadi" dariya sukayi dukansu

"Allah yasa ta baki,don itama bibi kwadayinta baya barinta ajjiye wani abun dadi"

"Qaniyarku,uwatace dai" ta fada tana dan zare musu ido.

Cikin sabuwa kar din fara BMW ta sameshi a zaune,ta bude baya kusa dashi ta shiga ta maida qofar ta rufe,driver ya tashi motar suna ficewa daga airport din.

Hannunta taji ya kama a hankali ya sanya cikin nasa,yadan matsa har dai da taji zafi,ta saki qaramar qara tana kallonshi bakinta a gaba. Ba ita yake kalla ba sam,hasalima idanunsa suna kan titi

"Taurin kai.....har yanzu wannan halin bai canza ba?......muna niamy zamu wuce maradi gobe.......kina da chance sultana...... Think twice" abinda ya fada kenan da muryarsa da tayi sanyi can qasa kamar wadda yayi jiyya.

Da idanu ta kafeshi,tayita kallonsa ba qaqqautawa,tanason ta tantance me yakeson cewa. Cikin ba zata ya waiwayo suka hada idanu,ga mamakinta sai ya sakar mata murmushi duk kuwa da yadda taga yanayin


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login