Showing 243001 words to 246000 words out of 294767 words

Chapter 82 - Gudun Kaddara Book 2 Hausa Novel Complete

Jikarta khadeeja diyar uncle bashir ta waiwayo tana kallon bibin

"Lafiya bibi?"

"Kinga kiramin hamidou ko hamdiyya,banga ta zama ba" ta fadi a dan rude. Ajiyar zuciya khadeeja ta saki tana lalubowa Bibi number aba. Cikin rashin sa'a a kashe wayar, dubanta khadeeja tayi

"Bibi a kashe yake wayarsa"

"Kiramin hamdiyya" ta fada idanunta akan wayar kamar zata fada ciki.

Sanda ama din ta gama komai take shirin shiga kitchen ta samu tanja ta duba abinda za'a dafa da safen wayarta dake hannunta ta dauki kuka. Ta danyi mamakin kiran bibi a lokaci,don bata saba yin hakan ba saida dalili muhimmi.

Dakatawa tayi tana daga kiran,hankalinta dukka akan bibi din

"Barka da safiya bibi"

"Barka kadai hamdiyya....kowa lafiya ko?"

"Lafiya qalau alhamdulillah" ta bata amsa cikin girmamawa

"Amma nace....me ya samu sultana?"

"Me ya faru bibi?" Dan ajiyar zuciya ta saki hankalinta yadan fara kwanciya,da alama iya shegen sultanar da tabararta ne ya motsa

"Naga kiranta,dana daga kuma sai naji ta sakarmin kuka 'yar banten uba" murmushi me sauti ama ta saki duk da batasan me ya farun ba amma don ta kwantarwa da bibi hankali,saita fara takawa tana wucewa kitchen saboda nutsuwar data samu

"Ban sani ba bibi......bansan me ya sameta ba,don bamu kwana tare da ita ba,tana can tare da aliyyu"

"A'ah ikon Allah,aliyyu kuma?" Bibi ta tambaya zuciyarta na fatan Allah yasa abinda take hasashe ne

"Eh aliyyu.....jiya dare ne yayi,naso kiranki na gaya miki abinda ya faru"

"Daina yimin kwana kwana ke hamdiyya,me ya faru?" Tana dan jin nauyi ace ta fitowa da ama baro baro abinda ya faru,don haka a sakaye tace

"Aliyyun ya sake yiwa aba laifi ne.....don haka yace ya dauki matarsa su bashi gidansa" maganar tadan yiwa bibi sarqaqiya don haka tace

"Wanne irin shirmen banza ne wannan?,da aliyyu yayi laifi itama sultanar laifin me tayi da zai hadasu?" Rasa me zata cewa bibi tayi,sai kawai ta miqawa tanja wayar.

Tanja na dariya ta karba ta saka wayar a kunennta tana gaida bibi

"Dakata da gaisuwar nan......nasan iya shegen aliyyu da kafirin taurin kai da zuciyarsa,sun bashi marainiyar Allah Allah yasa ba wata uban yake mata ba ta kirani da safe tana min kuka......tanja gayamin wanne laifi aliyyu ya sake yiwa hamidou ya koreshi?" Dariya kaman tanja tayi me,ta dakatar da ita da qyar saboda masifa da bibi ta fara

"Ki kwantar da hankalinki bibi,kawai aliyyun naki ya rantse ba zaki bar duniya ba sai kinga 'ya'yansa da sultana turmus......juna biyu aka samu,kun samu qaruwa ko kuma ince mun samu qaruwa" qirji bibi ta dafe tana zaro idanu waje,saidai kuma fuskarta lullube take da murmushin data jima batayi irinsa ba

"Saboda ma'aiki tanja?,kada kisa na biya miki umara fa a banza?"

"Bibi na taba yi miki irin wannan wasan?" Tunda tanja take da bibi bata taba jinta tana guda ba,yau sai ga bibin ta taqarqare tana zankada guda. Khadeeja dake zaune a gefe batasan meke faruwa ba tayi sakato tana kallon bibi

"Dan halak kenan.....ah.....ai nasan za'a rina,ina idanun wannan tsohon nasa wanda yayi gadon kafirin taurin kai a wajensa,yanxu ya yarda da cewa ja'irin yaro ya haifa ko wanda ya fishi kafiya da iya shege" kalaman sunyi matuqar bawa ama da tanja dariya,don ama ma juyawa tayi tana barin kitchen din,don tasan bibi yanxun nan zata baro maganar da zata kasa hada ido da tanja idan batayi wasa ba

"To amma banda ja'iri ne me juna biyu meye zakayi mata da farar safiya haka ka sakata kuka?, bayan lallashi take buqata?,bari na kira ja'irin naji" bibi ta fadi cikin zumudi tana katse kiran.

"Kamomin yayanku haidar maza maza hadeeza". Itadai khadeeja nata cika aiki,haka ta maida akalar nemanta number maina da bibi tayi saving da ALIYYU PARIS.

Sosai iskar wajen ke masa dadi tana kuma ratsa dukka qofofin shan iska dake jikinsa. Yawan furanni da koreyen tsirrai dake wajen ya sake sakawa zuciyarsa tayi fresh. Zamantowarsa likita daya jibanci abinda ya shafi fannin zuciya yasa yake da hanyoyin da zai samawa zuciyarsa yanayin da zai iya bashi nishadi har zuwa qarshen wuni. Duk yadda ya kebe kansa daga gareta don ya samu cika alwashin da ya dauka kansa a kanta hakan bai hana zuciyarsa jinta cikin matsanancin kewarta ba. Iya qamshinta kadai yakan haifarwa da zuciyarsa wani mummunan tabo,duk sanda zaya kalleta sai ta yiwa zuciyarsa illa,baisan adadi ba......baisan girma da nauyin mizanin son da yakeyi mata ba.

Sassanyan sarewar dake a mazaunin ring tone na wayarsa ta fara busawa. Yana shirin dagawa matashin da isowarsa qofar gidan kenan ya soma neman izinin shigowa yar harabar gidan.

Da hannu maina ya masa nuni,sai ya cire sakatar yana qarasowa cikin nutsuwa.

Hankalinsa nakan duba number waye yayi kiransa matashin ya qaraso. Baqin fata ne da zaiyi wuya ya wuce mallakin qasata Nigeria,saidai ko a idanu baiyi kama da matasan hausa fulani ko kanuri ba.

Tsaf tsaf yake cikin shigar qananun kaya,tun daga nesa kadan ya fidda takalman qafarsa,yana goye da jaka ya qaraso inda maina yake.

Abdulhamid kenan,dan asalin qabilar igala dake aikin kula da gidan gaba daya,duk bayan kwana biyu shike zuwa ya gyare gidan gaba daya banda bedroom dinsan nan qwaya daya tak,shike kula da dukka shukoki da furannin da suka qawata harabar gidan kowacce rana.

Da harshen turanci ya fara gaida maina,cikin qasan zuciyarsa yana murnar ganin ubangidan nasa da alama a nan ya kwana. Cike da mutunta dan adam ya amsa masa

"Ka fara da gyara nan harabar,idan ka gama kayimin magana nayi maka iso ciki don yanzun akwai matan aure a ciki......" Fara'ar abdulhamid ya qaru,yanason ya tambayi maina

"Oga kayi aure ne?" Amma kuma yana tsoron tambayar,tunda yasan halinsa sarai, mutum ne da baya jurar shishshigi. A girmame ya amsa masa yana miqewa don kama aikinsa,daidai nan kiran bibi ya sake shigowa a karo na uku kenan bayan kiran farko datayi masa

"Wannan tsohuwar Allah yasa dai lafiya" ya fadi can qasa yana motsa labbansa tare da gyara zamansa yana daga wayar.


_KWANKWASON JIMINA_*

*_TSUTSAR NAMA_*

*_AMEENATOU_*

*_GUDUN KADDARA_*

_DUKKA AYARIN LITATTAFAN KUDINSU YA KAMA KAMAR HAKA_*

LITTAFI DAYA_400
BIYU_800
UKU_900
HUDU_1200

_IDAN TA BANKI NE ZAKI SANYA KUDINKI A WANNAN ASUSUN_

6019473875
Musaa Abdullahi safiya
Keystone bank

_ANTAYA SHAIDAR BIYANKI ZUWA GA WANNAN NUMBER_

09166221261


*Masu tura katin waya ko vtu kuma kai tsaye wannan number zaku tuntuba*

09134848107

*Maqotanmu kuma al'ummar qasar nijer zaku tuntubi wannan number dinne kai tsaye don biyan naku kudin*

09033181070


*ZAFAFA FAMILY na maraba daku*🫂🫂🫂🫂🫂*_GUDUN ƘADDARA_*

*H U G U M A*

BOOK 02 PAGE 130



"aliyyu kana ina?" Itace tambayar da bibi ta fara jefa masa tana wani hade rai

"Ina gidana mana" ya bata amsa calmly.

"Eh ai na sani basai ka gayamin ba, yarinyar mutane da aka baka amana fa ka barta a daki tana kuka?" Yadda take maganar cikin haqiqancewa sai ya bashi dariya,yadan saki murmushi me qaramin sauti yana miqe qafafunsa saman table

"Me haidar yayi mata?,banda soyayyarsa da tayi mata mugun kamu kuma taqi barin zuciyarta ta bayyana hakan?,ki gaya mata ita zuciya ba'a tilastata ta boye soyayyar wanda takeso" ya fadi maganar hankalinsa kwance

"Iyeee......ni kake bawa wannan saqon?" Kafadunsa dukka biyu ya daga yana dariya

"Bani nakar zomon ba,rataya aka bani......kawai ki tuna mata dukka 'ya'ya mazan da suka fito da tsatsonki zafafa ne.......mace bata iya kubcewa soyayyarsu......idan ta manta soyayyar aba da ama ki tuna mata"

"La'ilaha illallahu........aliyyu wai ni kake gayawa magana haka kanka tsaye?,......aliyyu ko kasha wani abunne?" Dariya ta kusa qwace masa,yanason yayi maganin bibi ne gaba daya kuma hankali kwance,don bayason taci gaba da saka baki cikin harkar gidansa,kada a samu akasi wannan tsohuwar soyayyar da takewa sultana ta janyo ta dinga bin bayanta koda kuwa kuskure ta aikata.

"Ba abinda nasha sai giyar soyayya.....bibi ita zanci gaba da sha.....amma shawara bibi,indai bakison ki jini cikin mayen soyayya irin haka.....ta daina kawo miki qarar maina kina kiranshi kai tsaye haka"

"Haidar?,eh lallai,biri yayi kama da mutum" bibi ta fada tana tafa hannu kaman yana gabanta

"Wallahi bata inda sukayi kama bibi,dadinta dai wannan cikin tana nesa bare kice aje a zubar?"

"....aliyyu ai tun ba yau ba nasan tatacce ne kai.......amma zakasan ni ka kwarewa baya,inacan ina hanqilo a kanka na tsaya maka saboda 'yancinka ni ashe ka yimin tanadin cin mutunci" bibi ta fadi cikin jajjabi.

Wannan karon siririn sautin dariyarsa kasa boyuwa yayi,ya saki dariyar yana cewa

"Ba za'a yi haka ba.......kawai shawara na baki bibi ta ta kaina..... Ke kika yimin silar samun wannan alkahirin fa?,duk da dai ba don Allah kikayi ba..... wai kina tsoron kada na yiwa jikarki fyade .....bakisan alkhairi zai zame mata ba"

"Kaci ubanka maina......ubanka nace.......zaka tashi a wajen kaje ka dubo yarinya tana can tana sharban kuka ko sai na ragargaje maka kai dan kusun uwa?" Ta fada cikin hargagi ganin xai kwance mata zani a kasuwa,zai tado tsohon zance. Dariya ya saki sosai wannan karon harda duqawa,ko a ina zata ganshi har ta ragargaje masa kan kamar gaske,matar da qarfin arziqi bai isheta ba.

"Naji me ran qarfe"

"Da ubanka hamidou kake dan baqinciki,yanxu muka fara rayuwa a duniya" tana kaiwa nan ta kashe kiran.

Sosai ya sake darawa da maganar bibi, wai matar data doshi shekara tamanin da wani abu ita ke zancan yanzu suka fara rayuwa. Itama yasan halinta,dole ne ya biyo mata ta bayan gida sannan zai barta ta sarara,idan ba haka ba ya sani tsaf zata buwayeshi ta zuge masa matar da yake ganin ya fara dorata bisa saiti.

Hankalinsa kuma sai yayi dakin,to kukan meye takeyi?,duk wani motsinsa a wajen tana ransa,rana yake so tadan sake dagawa ko zuwa yammaci ya sanyata ta shirya,akwai guraren da yakeso suje a yau din.

Tsaye yayi a bakin qofa yana qare mata kallo,duk wani yanayin jikinta ya nuna emotion na zuciyarta. Boyayyen murmushi ya saki,koda batayi kowanne action ba yayi imani hug take da buqata,ya gani cikin qwayar idanunta,dukka nutsuwarta tana neman barin gangar jikinta

"Allah ka tabbatar da ita a haka .....indai hakan ta kasance wannan juna biyun ya sake xame min Alkahiri kan alkhairi" ya furta a zuciyarsa.

Sallama yayi qasan maqoshinsa,wadda tana jin sautinsa ta waiwayo da sauri,suka hada ido ta kauda kai tana gyara kwanciyarta gami da bawa qofa baya. Batason yaga hawayenta bare ya zargi wani abu. Ya sake sakin murmushin kallonki kawai nakeyi,ya taka ya isa gaban gadon inda ta juyar da fuskarta.

A nutse ya tsugunna a gabanta fuskarta data dan yi ja taba bayyana tarwai cikin idanunsa. Ya tsareta da ido yana kallon zara zaran eyelashes dinta data kulle idanunta taqi yarda ta kalleshi. Kowanne sashe na jikinsa yana muradinta, zuciyarsa kuma na sake narkewa cikin soyayyarta.

Gyaran murya yayi yana dan hade rai sannan yace

"Kukan me kikeyi?,me akayi miki?,idan yunwa kikeji sai sakiyi magana ko?,baki zauna kuka ba.....mema nayi miki?" Jin tambayar tasa tayi kamar wani rainin wayo ne da zallar gatse,tana ganin ya kamata yayi mata abinda ya kamata ba har sai taji damuwa akan haka ba, zuciyarta taso hasala amma wani sashen na zuciyarta yace da ita

"Ke kikace ya nisanceki.....bakison kusancin dake tsakaninku,duk da haka ma ya sammiki dumin jikinsa wanda dashi kikayi bacci,yanxun kuma me zaya yi miki bayan ya tabbatar kin qoshi?". A shurun daya gilma tsakaninsu wayarsa ta dauki wani qarar kiran. Koda ya duba sai yaga ama ce

"Ya salam" ya furta a fili,abinda ya sanyata bude idanunta ta watsa a kansa gabanta yana faduwa,don zuciyar tuni ta raya mata wannan yarinyar LAILA ita ke kiransa,waya sani ma fitan da yayi da zaman da yayi a waje ba tare daya dawo ba ko yana can suna waya ne kaman jiya?.

Idonsa ya nutsar sosai cikin nata,ya motsa jajayen labbansa yana furta

"Qarata kika kakkai wajen al'umma?" Ya qarashe maganar yana dage mata girarshi dukka biyun.

Ya riga ya gama luguguitata zuciyarta ya kuma karyata da salon kallon da yake jifanta dashi,batasan ya akayi ba, cikin narkewa da salon karyewar da take masa magana shekarun baya can sanda tana little sultana dinta ta girgiza masa kai tana turo lebanta na qasa.

Lips din yabi da kallo yana jin kaman ya kamashi ya tsotse saboda yadda ya bashi sha'awa,amma kuma sai ya fuske,yana jiran ranar da zatasan muhimmancin haduwar jikkunansu guri guda qarqashin umarni da kulawar zukatansu da kuma soyayyarsu.

Wayarsa kawai ya daga yana nuna mata screen din. Taga sunan ama itama,sai taji dukka ba dadi,bai kamata a irin wanna lokacin daga tahowarta jiya ace sun wayi gari haka ba. Ta tsurawa wayar idanu yayin da shi kuma ita ya tsurawa nashi idanun,sainya saki wayar ya aje mata kawai a gabanta,murya can qasa yace

"Pick" tada kanta tayi sosai saman pillows data jera,saita miqa hannu ta dauki wayar ta daga sannan ta kara a kunnenta.

Sosai ta sakawa ranta wani irin dakiya da juriya. Suka gaisa da ama tanata qoqarin controlling voice dinta da mode dinta

"Hope komai lafiya ko?" Ama ta tambaya daga qarshe jin batace komai ba,hakanan muryarta fresh na wani alamun kuka ko wani abu

"Lafiya qalau ama"

"To ma sha Allah" ta amsa mata tana jin dadin amsar data bata

"Bashi wayar" aman ta fada. Daga wayar tayi daga kunnenta ta miqa masa wayar,ya hada da hannunta ya riqe tsam sannan ya miqe daga tsugunnon da yayi ya koma soman gadon har kafadunta suna gogar nashi,sannan ya sanya daya hannun ya zare wayar ba tare daya saki hannun nata ba,ya hada tafukan hannunsu ya game waje guda yana amsa kiran ama.

A tausashe yake gaida ama din,itama ta amsa masa cikin kulawa,bata iya jin me take gaya masa,amma da to kawai yake amsa mata,gefe daya yana murza tafin hannunsa cikin nata abinda yake sake luguguita zuciyarta da gangar jikinta kenan,yake sake haifar mata da kasala,take kuma jin tana buqatar wani abu da zai lullubeta ya zame mata garkuwa.

Waiwayowa yayi ya kafeta da idanu bayan ya gama amsa wayar

"Ta yaya uncle haidar zai baki skin contact da rana?,idan ba jaraba irin ta sultana ba?" Yayi maganar yana wani tsare gida,bayan shi kansa jikinsa yana da buqatar kusanci irin na jiya.

Tabbas banda kwarjinin da yayi mata,banda ido daya cika mata ba abinda zata huce dashi irin ta kama lallausan gashinsa taja da kyau yadda zaiji zafi har kwanyarsa. Yanzun itace jarababbiya?,to ai a samu jarababbiya tsakanin ita dashi,shi da tsabar maitarsa take iya karantar sirrin dake kwance qasan zuciyarta?.

Dukka qarfinta ta tattara ta saka hannunta zata tureshi,saidai dukka hannayenta ya kama din,ya jata a jikinsa yana bata kyakkyawan dumin jikin da ya tabbatar zai bata cikakkiyar nutsuwa. Sannu a hankali duk ita dashi sai dukayi collapse,kamar kowanne lokaci irin wannan bugun zukatansu sai suka zama kamar abokan hirarsu.



*_B A Y A N A W A N N I_*

Kusan mintuna aqalla goma da yayi zaune cikin motar yana jiranta ko sau daya bai dauke idanunsa daga bakin qofar ba. A hankali ta sake bude qofar ta fito a karo na biyar,fuskarta a hade bacin rai yana dan bayyana kanshi da qananun fushi.

Tun daga yatsan qafarta ya fara qare mata kallo har zuwa girarta. Wannan shine shiga ta biyar da tayi yana maidata. Duk shigar da tayi idan ta fito sai yaga tayi masa wani mahaukacin kyau,tamkar a ranar ya fara ganinta,kamar kuma a ranar ya fara sonta.

Tunda take shiga tana fita ba abinda zuciyarsa ke nanata mamaki a kai. Wai sultanarshi ce wannan?,me wani irin zubabben kamala da nutsuwa me cakude da kwarjini me matuqar yawa saman fuskarta.

Duk yadda kakai ga jin isa idan ta tunkaroka sai kaji wani irin kwarjini ya dakeka..... sultanar da dukkansu a baya ke tsoron zamowarta wata mace ta daban saboda yadda suka qulla alaqa da zumunci me kyau da hotel hotel da guraren sharholiyar


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login