Showing 216001 words to 219000 words out of 294767 words

Chapter 73 - Gudun Kaddara Book 2 Hausa Novel Complete

Kayan wankansu harda towels da bathrobe da brushes dinsu ta sanya tanja ta hado musu suka wuce dakin.

Zaune tayi kawai tana kallonsu,sunata zuba mata surutu,har zuwa sanda bacci ya daukesu daya bayan daya. A gaba ta sanyasu tana kallon fuskokinsu, fuskarshi take gani cikin tasu,dogayen yatsunsu irin nasa,harma da tsagar kyakkyawan labbannan nasa.

Sai da tayi alwala sannan ta haura gadon,ta tofesu da addu'o'i ta shiga tsakiyarsu ta kwanta tana jansu cikin jikinta sosai. Numfashi ta fesar me sanyi,tana jin relief sosai cikin qirjinta,ta lumshe idanunta tana jin dumin jikinsu yana shiga jikinta.*_GUDUN ƘADDARA_*

*H U G U M A*

BOOK 02 PAGE 115


Kafin takwas dukansu sun shirya,suna dining ita da yaran,tsaye kawai tayi tana duban abincin,babu abinda ya kwanta mata a ciki,tana kallon su benazeer sunata lodawa cikinsu,da yake ba laifi basa wasa da abinci,wannan ya sanya kullum qibarsu suke,ga gata ga cima me kyau,ba abinda ya damesu sai qiba da fari da suke sake ajewa,kubul kubul dasu,wani lokaci takanji goumar yana tsonakarsu

"Kumatun benazeer ko na batoul zamu cire mu saida mu siyo Sweet ko chocolate?" .

"Ya kike a tsaye kuma uwar dakina?" Tanja data fito zata aje ruwan zafi ta fada tana kallon sultana. Dan yamutsa fuska tayi

"Banajin cin komai wallahi tanja"

"Ashsha.....hala bakijin dadi ne?"

"Wallahi bakina ba taste ma kwata kwata"

"Ai da kinyi magana tun dazun sai a dafa miki abinda kikeso" tanja ta sake fadi tana duban sultana

"Nifa da zan samu wainar fulawa irin na jiya ko dumamamme ne ci zanyi" Batoul da benazeer ne suka bushe da dariya suna duban sultana din

"Mummy dumamen kalallaba fa?,tabdi......ga abinci sabo Allah mummy yayi dadi kici kiji" kai ta kawar tana dan hararar benazeer dake kora wannan jawabin

"To ki bada minti goma mana ayi miki ki tafi dashi,akwai komai ai" agogonta ta kalla,sai taja kujera ta zauna tana cewa

"Da kuwa naji dadi...... benazeer kubu school bus,gobe idan Allah ya kaimu saimu fita tare" ba haka sukaso ba,don sun saka rai sosai su fita tare da ita,amma haka suka gama sukabi motar makaranta.

Sau uku ana dora mata camera ana saukewa. Tayi shuru tana jin bugun zuciyarta yana qaruwa,fuskarsa kawai take mata yawo cikin qwayar idanu,da kuma maganar da ya gaya mata darensu na qarshe

_please,ko yaya ne ko menene sultana....ki taimakeni ki rufamin asiri ki killacemin kanki,i swear bazan iya dauka ba,zuciyata me rauni ce a kanki bazan iya jurewa ba naga wani ko wasu suna kallemin ke_. Kalamanne suka dinga mata amsa kuwwa cikin kunnuwanta,sai da tayi da gaske sosai sannan ta samu ta gabatar da shirin.

Shirin ya qayatar kamar kullum,saidai gaba daya yau din ta rasa farincikin da take samu duk sanda ta gama program dinta successful,hatta da wayoyin mutane da aka saba ana dagawa cikin shirin yau bata samu dagawa ba,tana gamawa tasa sukayi off din camera ta kuma wuce zuwa office dinta.

Saman table dinta ta dora qirjinta zuwa kanta tana maida numfashi,tana jin zuciyarta kamar an rataye ta cikin wani kurkuku,ta dinga fesar da numfashi tsahon rabin sa'a sannan ta samu ta maida hankalinta waje daya.

Muguwar yunwar da takeji kaman an mata satar 'ya'yan hanjinta ya sanyata miqewa dole,ta shiga toilet ta wanke hannunta ta kuma dawo ta zauna ta jawo flasks din wainar ta soma ci. Ita kanta sai data kammala sannan tabi kwanon da kallo,tanata tantamar ita ta cinyeta duka yawanta?.

"Kece mana" ta bawa kanta amsa,tunda dai ita kadaice a falon bare tace da wani sukaci.

Ta wanke hannunta kenan ta dawo zata zauna akace mata tana da baqo,mamaki sosai ya kamata,ta tabbatar ba shi bane......don bai taba neman izini wai don zaya shigo office dinta ba,saidai kawai ta ganshi gaba gadi,ta qaraci lissafinta kaf ta rasa gane waye,sai kawai tace a barshi ya shigo.

Goumar ne cikin shigar suit,sanda yake sallama daga bakin qofar office din sai taga yana juye mata maina. Ta tsareshi da idanu,har sai da yayi ciki ciki da idanunsa sannan yace

"Madam......stop starring at me.......ba oga maina bane,wannan baqin buzu ne,angon najma......" Maganarsa tayi tasiri qwarai wajen ankarar da ita ta dawo sautinta,akwai similarities sosai na wasu abubuwan tsakaninsa da maina,amma saita dake ta kums murje idanunta tana watsa masa harara

"Waye kuma maina?,sannan waye baqin buzu?,duk ba wanda na sani a cikinsu, Mr disturber me ka biyoni office kayimin?" Dariya sosai ta taso masa,komai wahala bata rasa confidence wanda yake ta'allaqe da tsananin taurin kai da kafiya da take dashi.

"Zuwa nayi na taimaka miki na daukeki mu dauko yara mu koma gida.....naje gidan naji shuru,ba abokiyar rigima ba kuma yarana.......maimakon ki fara tambayata ma saukar yaushe saiki soma min masifa da tsiwa......ke wannan yarinyar anya zaki iya riqe miji kuwa?,kada halinki fa ya sanya ayo miki kishiyoyi tun bakici talatarki da laraba ba". Idanunta kamar xasu fado ta watsa masa su

"Me aure akewa kishiya ai,kuma wadda keson miji ke kishinsa...kumsma wai don Allah nace ina buqatar taimako?"

"Oh.....really?,ashe bakisonshi har yanzu ko?" Yayi mata tambayar yana kafeta da idanunsa. Amsar da zata bashi taji ta mata nauyi,ta kuma tsargu iyakar tsarguwa. Kodai yana sane da yadda mainan ke biyo dare ya turmusheta?,da kuma sakin layin data taba yi?.

"Ta ina?" Ta yiwa kanta tambayar,saboda ta sani sam maina baya layin maza masu bayyana sirri,sirri koda yaro qarami ne yayi dashi babu meji bare nashi,sam ma bame surutu bane bare ace garin yawan maganarsa ya tonawa kansa asiri,yanzunne rashin maganarsa ma ke dan raguwa saboda yanayin rayuwa da kuma gwagwarmaya da mutane.

"Tunda baki sonshi zamu sanya ya auro wadda ke sonshi....."

"Stop it" yaji an fada ta cikin Bluetooth din kunnensa,sai ya miqa hannunsa yadan tabashi kadan murmushi yana qwace masa.

"Taimako kuma tsakanina dake ai ya zama dole tunda qanwata kike" ya qarasa fadi yana shiga sosai cikin office din. Fara tattara mata kayanta yayi,saita kasa hanashi don gaba daya jikinta a mace yake,ji takeyi ma kaman tace ya matso da motar cikin office din kawai ta shige,tsiwarta dukka ta qarfin hali ce kawai,taji dadin zuwan nasa sosai,to amma fa wannan halin nasu ita da goumar sai an rabashi sannan zasuji dadi.

Sassanyan ajiyar zuciya ya saki sanda yaji fitarsu a office din,ya maida bayansa jikin kujera yayi relaxing yana lumshe idanunsa.

Badai zata daina nunawa duniya bata sonshi ba?,ba zata daina nuna cewa bata damu dashi ba?. Bude idanunsa yayi ya kalli calendar,akwai kusan kwana goma sha biyu a gabansa kafin ya dawo,yana jin kamar yayi tsuntsuwa ya baro komai ya dawo din. Tunda har take nuna komai da zafinta,shima yaci alwashin sai ya sanyata ta kusa haukacewa a kanshi,yayi alqawari sai ya sanyata ta fidda duk wani sirri dake cikin zuciyarta ba tare data iya boye koda abu daya ba. Ya mata dukka dagin qafar da zaiyi mata,a zatonsa zata fidda komai da bakinta,tunda ta zabi ya turara zuciyarta da kyau to shima a shirye yake,har yanxu ya tabbatar batasan ainihin waye maina ba.....but a wannan karon zata gani......yazo qarshe ya kuma kai bango.*_GUDUN ƘADDARA_*

*H U G U M A*

BOOK 02 PAGE 116



To zuwan goumar a wannan karon sai ya zame mata na daban akan kowanne zuwa da ya saba yi,tun suna Austria har zamansu a Paris. Don ita kanta sai ta dinga jin dadin zuwan nasa cikin gidan,kewa ta dinga ji yana debe mata,duk kuwa da cewa bata sanya kai cikin shirmensu da shirginsu da su benazeer,amma dai tana wajen suke bidirinsu. Dole ta soma zaman parlor ganin yadda zaman daki yake neman fin qarfinta,yake kuma neman maidata zautacciya. Bata da ikon zama ita daya sai ta zurfafa a wasu tunanuka na daban da suka shafeshi. Koda tana cikin jama'a ma bata rufa minti talatin bai fado mata a rai ba

"Wai ina ya tafi?,ina ya shiga?" Wannan tambayar itace tafi tsaye mata a rai. Hatta goumar bata taba gani suna waya dashi ba,suma yaran har ama ba wanda taji yayi zance ko cigiyarsa.

Dukka wannan abun sai dare yayi tazo kwanciya sai bacci ya gagareta,suyita fafatawa da idanunta amma tunani yace baisan wannan ba. Sau tari saidai ta hada benazeer da batoul duk biyun ta rungumesu a jikinta sannan take samun sa'idar zuwan bacci. Banda zaman data koya qarfi da yaji a falo ta tabbatar qila da yanxun ta fara samun dimuwa. Sauqin abun daya ayana bata fiya zama a gidan ba sosai,ko tana nan dinma bata fiya zama a falon ba muddin ita da yaran da goumar suna ciki. Abinda ta lura ba wata jituwa tsakaninta da goumar,batasan meye dalili ba,amma gaisuwa itace kadai tsakaninsu. Tayi mamakin hakan kasancewar goumar bame irin wannan halin bane sam,bashi da fada wulaqanci ko qyamatar mutum,amma dai miskilinne shima tamkar yayansa. Ayana din tana da dan daukar kai,don haka ba ruwansa da lamarinta.

*******Da yammacin da yayi dai dai da sati biyu da kwana daya da tafiyar maina din. Suna daga gaban gidan,benazeer goumar da batoul suna dan buga qwallon qafa bame zurfi ba sosai. Ya dage lallai sai ya koya musu,suma din kuma suna so,don haka daga ita har ama sai ganinsu sukayi da Jersey masu kyau da ball dinma kanta.

Baki ama ta kama tana kallonsa

"Kana da daurewa qarya qarqashi uncle goumar,yara mata da football?"

"Eh mana ama...... tunda mamansu taqi bamu baby boy......kinga gwara na maida mata yara maza qila tayi zuciya" sanda ya fadi maganar tana zaune saman kujera,ta gama shan kankana kenan wadda tun safe itace abinda ta sanya a cikinta saboda rashin sha'awar cin abinci dake damunta,ga kuma cushewar ciki.

Har cikin qashinta taji wani irin sanyin kunya yana ratsata, maganar tayi mata girman da ya sanya ko kanta ta kasa dagawa

"Na shiga uku..... innalillahi goumar?" Ta fadi cikin ranta kawai tana ci gaba da latsa wayarta tamkar bata a wajen. Ama ma abun ya mata nauyi amma kuma saita saci kallon fuskar sultana din,bata samu nasarar ganin kowanne reaction nata ba,don haka batace komai ba ta juya tana wucewar ciki.

Allah Allah dama takeyi ama din ta juya,ta jefa wayarta gefe tana kallonsa idanunta awarwaje zata sauke masa. Hannunsa ya dora saman lips yana zare mata idanu kamar yana magana da qaramar yarinya

"Wallahi kina cewa tak zan dawo da ama,kuma idan tazo cewa zanyi kema kince kin qosa ki samo mana din......don dai kawai sunqi fahimtar haka su maidaki dakin yaa maina" qamewa kawai tayi tana dubansa,mamaki ya cikata,tayi imanin zai aikata tsaf,ta rasa mw zata masa ta rama,sai ta miqe kawai ta kwashe tarkacenta tana cewa

"qanin maina dinne ai,zaka aikata,in sha Allah sai an qara shekara daya akan ranar aurenka da najma" ta murguda baki tana wucewa dakinta. Tana jiyoshi yana qyalqyala dariya harda kwanciya,batoul da lokacin suka dawo parlor din suna tambayarsa

"Uncle goumar meye?".

Lokaci lokacin tana dan daga kai taga yadda suke buga ball din,sannan ta maida kanta ga system dinta da take research a ciki. Fayau takejin cikinta ba uban komai,amma kuma batason cin komai din,ta kuma soma gajiya da saka tanja ta soya mata wainar fulawa,wanda kullum sai goumar ya tasata a gaba yana fadin

"Ni banga abun dadi a fulawa da mai da albasa ba,salon kwadayi ne kawai wannan,daga yanzu ama na daina siyo fulawa a list na shopping din gidan nan" Bata da amsar bayarwa,don ita kanta tana mamakin yadda ta maqale mata. Ama kuwa da idanu kawai take binta,ba abinda yake damunta irin yadda duk wani kuzari nata ya ragu,ga kuma ramewa da takeyi a tsaye haka kawai, addu'a takeyi cikin ranta, ubangiji ya sanya hankalinta ne ya soma karkata akan mijinta.

Sanda taji dariyar goumar da batoul suna yiwa benazeer dariyar an cinyeta wayarsa dake ajiye gefanta ya dauki tsuwwa,ya saki ball din yazo ya daga wayar yana dubawa,sai ya sanya Bluetooth dinsa a kunne yana fadin

"Good evening bros....." Maida kanta tayi a hankali kan system dinta tana ayyana mintunan da zata tashi a wajen ta shiga ciki koda tsiya ta samu wani abu ta tilastawa kanta cinsa.

Zama goumar din yayi yana amsa wayar,yaran suka dawo gabansa suka zauna suma. A hankali sai zuciyarta da kunnuwanta ke fusgar wayar goumar din. Sannu sannu take bin maganar da yakeyi cikin wayar,gabanta yayi wani mugun faduwa lokacin data fahimci da maina yake magana.

"He's safe dama?,yana ta wani wajen ne?" Ta yiwa kanta tambayar. A hankali sai taji ranta yana baci,duk yadda taso yage kunnuwanta daga jin hirarsu amma haka ya gagara.

"Gasu a gabana ma.......dama tun jiya suke mitan kace zaka sake kira baka sake kiransu ba har sukayi bacci.......BB ga daddy..." Sai ya miqa musu wayar yana sanyata a handsfree,ya matsa gaba yana kwashe ball dinsu da takalmansu da suka zubar hankalinsa kwance kaman sultanan bata wajen.

Fes muryarnan tasa dake da wani irin amo me saurin isar da saqo da kuma tsayawa cikin zukata ke fita ta speaker din wayar goumar. Hira yake sosai da yaransa,irin hirar da kana ji zakasan ba wai yau ya fara kiransu ba daga sanda yayi tafiyar,don sunata tambayarsa abubuwa yana basu amsa. Hira irin ta d'a da uban da suka shiqu,yaran suka dinga dariya suna kwanciya saman grass carfet saboda tsokanar da yake musu.

Kadan kadan taji wani abu yana tsaya mata a wuya,ranta ya dinga motsuwa da kadan kadan yana baci. Kasa jurewa ci gaba da zama a wajen tayi sanda taji ya tambayi ama sannan kuma ya hada da tambayar ayana,ya kuma kashe wayarshi ba tare da ita ya tambayeta ba,saita wuce ciki a gaggauce bata ko waiwayosu ba.

Saman gado ta zube tana qoqarin gayawa kanta kada ta soma kuskuren damuwa dashi,kada ta yarda wani abu me suna damuwa a kanshi ya shiga zuciyarta,meye ma hadinsu?,ya tafi yayi shekara kusan biyar bata damu ba sai yanzu?,me yasa zata damu ne?.

A haka tayi sallar magariba,tayi isha'i,dole bayan isha'i ta fito don neman abinda zataci ganin yunwa na neman halakata,ga wata azababbiyar yunwa kamar bata taba cin komai ba a duniya.

Motsin fitowarta falon yaja hankalin ama,ta daga kai tana binta da kallo bayan ta musu sannu da gida ta wuce kitchen. Sanda ta fito da cup data hada madara da cornflakes sai ama ta kasa jurewa ta kirata.

Qasan carfet ta zauna,don tana jin jikinta dukka ba qwari

"Baki da lafiya sultana" ama tafadi kanta tsaye. Tanaso cewa ama din lafiyarta qalau,don ita bata yarda bata da lafiya ba,amma sai wani mugun rauni ya mamayi zuciyarta,take kuma hawaye ya cika mata qwayar idanu,daga ama din har goumar da yaran dake wajen sai suka zuba mata idanu.

Kallonsu gareta ya sanya ta aro juriya,tana qoqarin shanye hawayen muryarta na rawa kadan tace

"Lafiyata qalau ama"

"Ban yarda ba.....bakiga yadda kiketa rama a tsaye ba kaman kin hadiyi allura?,sai uban haske fau?,ko aba dinku da ba zama yake ba jiya sai da yayi complain kan ramar da kikeyi,ya tasani gaba akan lallai lallai na tambayeki ko kina da damuwa?" Dan shuru tayi kanta a qasa,batasan me zata ce da ama ba,kuma fadin ba komai din ta tabbatar ba zata taba yarda da hakan ba

"Bana iya cin abinci ne ama"

"Me yasa?" Ta jefa mata tambayar tana tsareta da idanu

"Ina tunanin aiki ne da ban saba dashi ba.....amma komai zai warware in sha Allah" ta fada tana jin karayar zuciya sosai.

Shuru ama ta danyi kaman bata gamsu ba,sai kuma ta dubeta

"Rashin cin abinci indai ba da ciwo ba to akwai matsala,ki dinga qoqari kina cin abinci,aiki ba uzuri bane kuma ya zamana harda rama a ciki ma"

"In sha Allah " ta fadi tana jin dadin ta kufcewa tuhumomin ama din.

Tana zaune saman sofa cikin dakin tanja ta shigo


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login