Showing 219001 words to 222000 words out of 294767 words

Chapter 74 - Gudun Kaddara Book 2 Hausa Novel Complete

mata da yaran,ta shiryasu tsaf suka haye gado tayi musu sallama ta fice.

Sama sama takejin qananun hirarrakinsu,wani shirme na yarinta wani kuma fal quruciya,tana zaune kawai tana dafe da kanta saboda yadda madarar data sha din ke taso mata,tanata qoqarin ganin ta danne aman da takeji,amma daga qarshe sai da yaci galaba a kanta.

Da sassarfa ta miqe ta wuce bandaki tana yunquri,abinda yaja hankalin batoul da benazeer,dukka suka miqe saman gadon suka zauna suna kallon juna, sukayi carko carko suna jiyo nishin yunqurin amanta,sai kuma suka sauka kusan lokaci guda suka nufi bandakin da gudu gudunsu.*_GUDUN ƘADDARA_*

*H U G U M A*

BOOK 02 PAGE 117


Sai data amayar da duk abinda yake cikinta tas,ta dafe sink tana fidda numfashin wahala

"Sannu mummy....." Taji muryar batoul,wanda tana waiwayowa benazeer itama ta jeho mata tata tambayar

"Mummy dama baki da lafiya?" Yadda suka rutsata da idanu haka itama take kallonsu,tama rasa amsar da zata basu,sam ta mance suna cikin dakin. Numfashi ta sauke ta juya tana kuskure bakinta hadi da wanke fuskarta,sannan ta tako ta kama hannuwansu suna fitowa daga bandakin.

"Lafiyata qalau,bana dan jin dadi ne"

"Na kirawo ama sai mu tafi asibiti?" Batoul ta tambaya fuskarta na nuna damuwa sosai. Kai ta girgiza da sauri

"Kada wanda ya gaya mata koda gobe da safe ne,ai naji sauqi,ku koma ku kwanta maza". Sai data tabbatar sun kwanta din sannan ta koma saman sofa bed ta nade da wani blanket din daban. Ta cure sosai waje daya saboda sanyin da takeji yana ratsa qasusuwanta,ta kwantar da fuskarta saman cinyarta tana lumshe idanunta. Sosai takejin wani kewa yana ratsata,tana jinta incomplete tun daga zuciyarta zuwa gangar jikinta.

Allah ya taimaketa washegarin ba wanda ya tayar da maganar cikin yaran,saidai ta lura gaba daya sun damu,bini bini idanunsu yana kanta. Batason dorawa ama damuwa me yawa a kanta,don haka sai taqi zaman falon gaba daya ta tattare a bedroom. Hakan ya taimaka mata sosai,don dama jikinta bata jin wani qwari da zata iya dogon zama ko hira cikin mutane. Ranae ta kira bibinta,sun jima suna hira da bibi din,doguwar wayar da suka dade basuyi irinta ba. Maganar bibi ta qarshe da ita ta kashe waya tana juya maganar cikin ranta

"Daga ke har aliyyu har yanzu babu wanda ya yiwa kansa fada?" Dan jim tayi tana hade fuska kaman bibi tana wajen. Itakam zancan aliyyu ya isheta,har yanzun basusan zai iya sanya qafa ya tsallake yayi tafiyarsa ya barta ba?,har yanzu basusan bai dauketa a bakin komai ba?,basusan har yanzu bayajin komai don ya tafi ya barta ba?.

"Wanne aliyyu?" Ta tambayi bibi.

"Qaniyarki ja'irar banza ja'irar wofi" bibi ta fadi tana watsa hannuwa kaman zata kamo sultana

"Kubar ganin kunyimin nisa daga ke har maina din zan sanya a maidomin ku gabana nayi maganinku.....kina jina ko?"

"Allah ya baki haquri" kawai ta fadi a sanyaye,tunda dai tsahon zamanta da bibi ba zata iya tuna sanda ta zageta har haka ba. Ji tayi bibin ta kashe wayarta don haka itama ta aje wayar tana maida kanta saman filo hadi da fidda numfashi,ta lumshe ido tana jin zuciyarta tana mata suya sosai. Kaf matsalar rayuwarta maina ne,kuma still dai har yanzu shi dinne,batasan me yasa ya tsayewa rayuwarta har haka ba......ta fara gajiya itama,tana buqatar hutu a rayuwarta gaba daya.

Zuwa yanzu ta fahimci ko taqi ko taso yanason zamewa rayuwarta jarrabawa,wata jarrabawa da babu yadda zata iya shallake mata. Abinda takeji a kwanakin nan dukka yana son sauya tunaninta.....duk yadda takai ga kafiya da sauya ma'anar tunaninta tana ji a sannu a sannu komai yana canzawa,tana jin tana qaryata kanta da kanta,uzurorin da take bawa kanta da kanta game dashi tana jin zuwa yanzu zuciyarta ta daina gamsuwa ta kuma daina karbar uzurin sam.

Kanta ta sake gyarawa tana goge qwallar data ziraro mata,sai taji an turo qofar ana shigowa.

A hankali ta juya bayan ta sake goge danshin idanunta da kyau. Ama ce,idanunta dukka akan sultanar,hakan ya sanya sultana yunqurin tashi ta zauna sosai.

"Yau duka na jiki shuru baki fito ba,na tambayi yara suncemin kina kwance tun safen?,anya kuwa sultana?" Ta qarasa tambayar tana samun waje dab da sultana din ta zauna. Qasa tayi da kanta,zuciyarta nason karyewa amma tana bawa kanta qwarin gwiwa

"Jikina ne ba qwari,amma lafiya nake" dubanta kadan ama tayi tana qaryata zancanta,don ko kusa ko alama bata gamsu ba. Yadda take ramewa yafi komai daukan hankalin ama din,wasu dabi'u nata da yawa sun sauya,saidai hankalinta ya kasa kaiwa inda zuciyarta keson kaita,saboda tana da dalilai da ta tabbatar hakan bazai kasance ba

"Dama ta yaya jiki zaiyi qwari kinqi abinci?, bari aliyyu ya dawo maganin cin abinci xan sanya ya rubuta miki,idan ma ulcer keson hanaki cin abinci,kina fita aiki sannan kuma ba zaki zauna kici abinci ba?". Kai ta daga ta kalli ama sai kuma ya sauke,kiran sunan aliyyun ya haifar mata da wani abu a gangar jiki da zuciyarta,kamar akwai tambayar da takeson yiwa ama din amma ta kasa. Rasa me zatace da ama din tayi,har tayi mitarta ta gama ta miqe

"Ya kamata ki fito hakanan,shima zaman kadaicin kashe jiki ai yakeyi tunda ba wani aiki kike yi ba"

"To" ta amsa mata a sanyaye.

Numfashi ta aje,har ga Allah batason fita bare su hadu da ayana,amma dole ta daure ko don cika umarnin ama.

Toilet ta shiga ta sake wanka wai ko zataji dadin jikinta,ta sauya kaya zuwa wasu riga da skirt na material marasa nauyi,ta sanya dan siririn Gyale ta lullube sumarta data hade cikin wani qaramin band.

Sosai fuskarta ta fito fes,tayi fayau da ita,ta sirance sai mugun haske data qara,kayan sun amsheta qwarai da gaske,duk kuwa da cewa ba wani kwalliya ta yiwa fuskartata ba,sai sassanyan qamshin turaren da jikinta yake fiddawa daya dade da kama fatarta.

Su biyar ne cikin falon,ama benazeer batoul goumar uban gayya,sai tanja dake zaune daga gefe tana gyara lettuce da zata yiwa ama hadin salad dashi.

Fuskar kowa ta kalla,sai taga kaman kowa din cikin farinciki yake,kamar kowa yana cikin walwala banda ita,kamar ita kadai ta rasa walwala cikin gidan.

Sannu da gida ta yiwa tanja da tun safe basu sake haduwa ba,ta amsa tana dan duban sultana din,don ita kanta tana ganin rama a tattare da ita. Tana zaune suna dan hira da tanja jifa jifa,tayi hakanne don ama din taji dadi ta sake bawai don tanason hirar ba.

"Hadin salad za'a yi mana?"

"Ko kina sha'awa a hada dake?" Tanja ta jefa mata tambayar tana jin tausayinta qasan ranta.

" A haka dai sai nakejin ya burgeni,amma ban sani ba ko zan iya ci?,cikin nawa dai kaman ulcer keson cushemin shi" ta fadi tana dan yamutsa fuska. Murmushi kawai tanja tayi tana girgiza kai

"Bari na kammala saiki gwada ci din" ta bata amsa ba tare data kalli fuskarta ba.

Tsaf ta gama hadin salad din ta kawowa ama,ta isa gaban sultana ta aje wani dan bowl din tana cewa

"To bismillah"

"Na gode" ta amsa tana jin dadin yadda tanja ke kulawa da lamuranta,sosai take qaunarta qauna ta fisabilillahi.

Zamowa tayi daga saman kujerar ta zauna sosai a qasa,ta bude bowl din zata fara ci dan neman rigimar ya sako benazeer da batoul daga bayansa wadanda yakewa doki

"Kuje ku taya mummy twins cin abinci"


"Aah suzo ga nasu" tanja tayi saurin tarewa. Dariya ya saki yana fadin

"So nayi ki barsu suci tare,ita matar nan mafa bansan meye yake damunta ba,kunyace ko Kara?,wai sai taqicin abinci da yaran nan?" Harara ta gasa masa don bata da bakin magana a wajen tunda ama tana nan. Tanja ce tayi dariya

"Kaidai anyi babban kwabo goumar,baka girma da jaye jayen rigima?,lallai saita kulaka kunyi?" Dariya ya sake saki yana jawa yaran kwanon salad din,don shi bai dameshi ba..

Sosai ta dinga jin dadin potatoe salad din,sannu sannu sai gashi ta cinye tas ta riga kowa ma cinyewa.

"Ko a qara miki?" Tanja ta tambayeta,kai ta girgiza

"Na gode tanja ya isa haka alhamdulillah" daidai lokacin ayana ke fitowa daga dakinta.

Riga da wandone a jikinta,wandon yana da fadi amma kuma rigar me hannun vest ne, kunnenta maqale da earpiece tana amsa waya.

Sai wani kwantar da murya takeyi cikin tsananta ladabtarwata,kallo daya goumar da sultanar sukayi mata suka dauke idanunsu,yayin data nufi ama kai tsaye tana fadin

"Am sorry yaaya....... a'ah wlh,am sorry ya haidar.......ga ama din" ta fadi tana miqawa ama wayar da dama earpiece din. Cire earpiece din aman tayi ta karba wayar

"Wai yanata kiran wayarki baki dauka ba,nace may be kin barta a bedroom ne" ayana ta fadi cikin jin alfahari idanunta suna satar kallon sultana.

Kau da kai tayi kaman batasan me ayana ke fadi ba,saita maida hankalinta kan labarin abinda benazeer tayi jiya da tanja ke bata,ta sanyawa fuskarta dariya sosai kamar tana jin nishadi ko fahimtar abinda tanja ke fada,saidai duka ba wannan ba,ba abinda take fahimta sosai game da abinda tanja din ke fada,amma kuma batason maida hankalinta daga sashen da ayana ke zaune.*_GUDUN ƘADDARA_*

*H U G U M A*

BOOK 02 PAGE 118


Tsam ta miqe daga wajen sanda ta fahimci akwai wani abu qasan ran ayana,kuma dashi ta fito

"Wardrobe dina nakeso na gyara tun last week tanja....bari naje na duba"

"Da kin barshi uwar daki,ke da bakya jin dadi sosai?"

"Qyaleta tanja,daki takeso ta gudu,ta shiga ta shirya kema ki shirya kuzo muje wani guri,na samo mana wani guri me kyau....... daughters aje a zabo kayan fita me kyau" ya qarasa maganar yana kallon benazeer da batoul. Wani wawan tsalle suka buga sukayi daki da gudu daya nabin daya,su dama ba abinda sukeso irin suji uncle goumar yace za'a fita,sunsan ranar sai sun qurewa yawo har illa ma sha Allah.

Haka nan taji maganar goumar ya mata dadi da yace ta shirya su fita,yau din ba harara ba tsokana ba tsiwa,ta shiga ta shirya din kamar yadda goumar yace.

Tayi kyau cikin tsadaddiyar abayar tata,daya daga cikin abayas nata da take ji dasu saboda yadda takejin dadinta a jiki idan ta saka. Ta samu ayana a falo kusa da ama,waya take dannawa amma zuciyarta fal da bacin ran yadda goumar din sam bai dauketa da wani daraja ba,baya bata dukkan girman da take buqata ace ya bata ba,ta fahimci goumar din yana da kusanci da maina da yawa,ya kamata ace ita yake dama dama da ita bawai sultanar ba

"Sai illa ma sha Allah kenan ko?" Ama ta fadi tana kallonsu. Murmushi sultana tayi,itama kanta tasan yau sai inda man goumar ya tsaya,yana da son zuwa park park kamar baya gajiya,kamar kuma baisan zafin kudinshi ba. Sallama sukayiwa ama dukkansu suka fice suka barta daga ita sai ayana daketa baqin rai.

Suna tafe a hanya amma zuciyarta tayi nisa wajen tunanin da abinda yake haifar mata dashi illa bacin rai. Meye hadinsa da ayana?,yana waya da ita kenan?,yana kuma kiranta?,yana kiran kowa ma na gidan banda ita?,ita daya tak?,to me hakan yake nufi?,hakan yana sake tabbatar mata da abinda ke saman harshensa yake kuma furta mata ba shine cikin zuciyarsa ba......bata da wani sauran amfani a wajensa sai na biyan buqatarsa?,a yanzun yayi nesa da ita,bashi da wata buqata don haka bai da amfani kenan ya nemeta.....indai hakanne ya tabbata baya sonta.....baya kuma qaunarta,wannan muguwar tsanar da yayi mata tun a farkon tarayyarsu tana nan zuciyarsa babu abinda ya kankareta. Yana da buqatar kowa amma banda ita,saboda ita din bata kai ba,bata kuma da matsayin komai cikin rayuwarsa.

Wannan tunanin ya haifar mata da illa sosai cikin zuciyarta,ya kuma ji mata rauni me nauyi da radadi. Har cikin zuciyarta ta dinga ji eh yes da gaske bata da sauran amfani cikin rayuwarsa saina ssuke sha'awarsa......da gaske baya da buqatarta bata da muhimmanci sai idan zai sauke lalurarsa. Ta dinga goge hawayen da yakeson kunno mata kai,tanata qoqarin hadiye karyewar da zuciyarta tayi don kada ta ragema su benazeer da tanja jin dadin fitar,ta kuma sacewa goumar gwiwa wanda ta tabbatar ya qirqiri fitar ne musamman saboda ita. Koda bai fada ba dukka ayyukansa sun nuna haka. Goumar din dan uwa ne daya da daya,a baya da suke yawan samun sabani da kuma tsonakar juna bata taba zaton akwai ranar ra zatazo zai zame mata wani jigo kuma masharar hawaye kuma me qoqarin dauke mata damuwa ba.

Duk da quncin da zuciyarta ke ciki tayi qoqari ta danne, guraren cin abinci uku ya kaisu,amma sai a guda daya ta zabi abu daya,da qyar ta iya zabar abu daya taci,shima bata kammala ba taci gaba daya ya fita a kanta. Sosai zuciyarta ta dinga tashi,ta dinga yatsina fuska saboda yadda yake taso mata

"Lafiya uwar daki?" Tanja ta tambayeta. Daidaita kanta tayi qoqarin yi sannan ta amsa

"Abincin na yake min yawo"

"Anya uwar daki?,lafiyar nan taki da sauqi fa,ni banga kinci komai ba tunda mukazo sai abu daya,shima kince yana damunki,anya ba zakije asibiti ayi cakin dinki ba a dubaki da kyau?" Kai ta mirginar gefe,ita kanta batasan abinda yake damunta ba,saidai kawai tasan bata jin dadin komai ma,hakanan rayuwarta take jinta ta zama upsidedown. Bata iya baiwa tanja amsa ba,amma kuma maganarta ta tsaye mata a rai.

Sosai goumar yayi yawo dasu,basu koma gida ba saida suka gaji tubus. Sunga gurare da dama wanda tun zuwansu Paris basu taba zuwa wajen ba. Ita kanta taji dadi,duk da yadda kasala ta dinga mata cikas,wasu guraren ma zamanta takeyi a mota su shiga su fito su taras da ita zaune. Daga qarshe goumar ya gaji ya kalleta cikin salon tsokanar nan tashi

"Ke ba qiba kika qara ba ba komai ba amma kin koyi wani son jiki mara dalili?" Yayi maganar da son tsokanota. Murmushi kawai tayi ta dauke kai,taqi ce masa uffan,ganin hakan ya sanyashi shima bai sake cewa komai ba sukayi gaba,daman wani ice cream ya kawosu siya su wuce.

Suna komawa yau kam ko wankan dare basuyi ba,banda sultana din da ko ina yake mata ciwo,ta hada ruwa me zafi tayi wanka sannan ta kwanta. Saidai kuma kwanciyar batayi nisa ba zazzafan amai ya taso mata. Kaman jiya dukka yaran suka tashi,sukayi carko carko. Ta gama ta fito ta samesu yau harda hawaye

"Kuje ku kwanta,banaso ku tayarwa da ama hankali,zansha magani gobe in sha Allah" da haka ta lallabasu.

Kwanaki uku kenan duk dare da kuma safiya sai tayi wannan asababben aman,ta kuma hana yaran su gayawa ama,tana ganin ulcer dince kawai tazo mata da wani salo na daban,don komai da takeji a jikinta na alamu ulcer yana kawo hakan,tayi duk wani qoqarin ganin ta daina wannan aman ta kuma samu energy a jikinta amma haka ya gagara.

********Kamar kazar da qwai ya fashewa a ciki haka ta fito daga dakin nata,tana sanye da doguwar riga ta atamfa data bude sosai daga qasa. Shiga ce da ba kasafai ta fiya yinta ba,amma kuma duk sanda tayin tana bala'in yi mata kyau a jiki sosai.

Medium mayafi ta yafa saman kanta, daga takalmin qafarta har hand bag dinta dukka designers ne daga kamfanin Hermes. Ko mace 'yar uwarta idan fa kalleta dole yanayin adonta da kamewarta ya burgeta bare namiji,tayi wani irin kyau saidai sirancewa da tayi da haske data qara.

Idanunta akan fuskokin benazeer da batoul dake kwance saman cinyar ama,sanda ta fito ta fuskanci akwai abinda suke gaya mata,amma fitowartata ya sanyasu yin shuru suka bita da idanu kaman yadda itama ta bisu da ido. Abinda bata lura dashi ba ama itama kallonta takeyi,har ta qaraso


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login