Showing 24001 words to 27000 words out of 294767 words

Chapter 9 - Gudun Kaddara Book 2 Hausa Novel Complete

zai sake dawowa ya kashe lokaci wajenta.

Rashin maganarta ya fara tabashi,tsahon zamanin da aka haifi sultana bata taba zaman minti.biyar bakinta shuru ba,koda bata da lafiya bata lamunci zaman kurum ba,abun ya soma ganin ya wuce tunaninsa,yadda takebin kowa da komau da idanu,tana iya yin kwanaki koda nawa ne a hakan ba tare da buqatar canjin yanayi ba, kodon haka a kwana na takwas ya sanya Dr chafa'atou a gaba yace lallai ayi mata gwaje gwaje ko bayan idanunta da ya kusa nakasa mata qila ya shaqe mata mafitar maganarta ma,don wanda yayi hakan babu abinda bazai aikata ba.

Dan dariya maganar ta bawa Dr chafa'atou,itadai tasan lafiya gurin yake,zallar daya daga cikin illolin da irin wadannan abubuwan suke haifarwa ne kawai data tsinci kanta a ciki. Don dai hankalinsa ya kwanta ta sanya akayi mata gwaje gwaje,kuma komai ya fito normal,ta bashi gwajin tana cewa

"Kulawa ta musamman kawai take buqata aci gaba da bata,don kamar depression ne take ciki har yanzu,komai zai wuce in sha Allah,a yawaita faranta mata ranta da dukkan abinda akasan tafiso,tare da qauracewa furtawa ko tuna duk abinda zai sakata a damuwa". Lafiyar tata da aka tabbatar masa tayi masa dadi,sai ya qara adadin lokutan zuwansa,ya zauna yayita janta da irin hirarrakin da a baya yasan tafiso. Kafin wani lokaci dakin asibitin nata ya cika da kayayyaki,kama daga teddies chocolates,madararta,games kala kala da tarkacen kayan computer. Komai saidai ta bishi da ido,yadda zai gwada mata ya aje shi a wajen bata sake tabashi. Tana jin bata qaunar komai,bata buqatar komai,hakanan komai bai bata sha'awa,inda zasu gane su qyaleta ita daya cikin daki,kowa kada ya kulata,kowa kada ya tanka mata da hakan zaifi faranta mata. Don kusan kowa ta gani da ya danganci gidansu bata ganin komai tattare dashi sai ALIYYU MAINA,suna Mafi girman da ta yiwa mafifiyar tsana,sunan da inda tana da hali da daga rana irin ta yau ta shafeshi a doron duniya,halittar da takejin a rayuwa babu halittar data cancanci azaba irinta.

Sannu sannu komai bai canza ba illa ciwukan jikinta da suka warke din,kumburin fuskarta ya sabe dai dan tabbai masu launin pink,hakanan dinkin qasanta ma ya hade kasancewar akwai quruciya tattare da ita,sannan kuma ama ta tsaya tsayin daka tayi bata kyakkyawar kulawar da banda ciwon dake cikin zuciyarta da babu abinda zai hanata mulka qiba. To a maimakon qibar sai wata mummunar rama da tayi mara kyan gani.

Kwanansu ashirin cif Dr chafa'atou ta tabbatar da samun lafiyarta ta kuma rubuta mata sallama tare da bawa ama qarin shawarwarin yadda zata ci gaba da kulawa da ita don a samu rayuwarta ta koma daidai kamar ta kowa.

Motoci biyu ne cikin motocin gidan iyalin mayak'i sukazo daukarsu. Karon farko da ta fita daga asibitin tun ranar da ta kawo sultana. Tun dava randa ta koma ta wanke zanin gadonsu bata sake barin asibitin ba,don duk inda zata motsa sai taga kamar sultana zata rasa wata kulawar,kamar sultana zata buqaceta,kamar wani abun zai samu sultana din kafin ta dawo.


*_KWANKWASON JIMINA_*

*_TSUTSAR NAMA_*

*_AMEENATOU_*

*_GUDUN KADDARA_*

_DUKKA AYARIN LITATTAFAN KUDINSU YA KAMA KAMAR HAKA_*

LITTAFI DAYA_400
BIYU_800
UKU_900
HUDU_1200

_IDAN TA BANKI NE ZAKI SANYA KUDINKI A WANNAN ASUSUN_

6019473875
Musaa Abdullahi safiya
Keystone bank

_ANTAYA SHAIDAR BIYANKI ZUWA GA WANNAN NUMBER_

09166221261


*Masu tura katin waya ko vtu kuma kai tsaye wannan number zaku tuntuba*

09134848107

*Maqotanmu kuma al'ummar qasar nijer zaku tuntubi wannan number dinne kai tsaye don biyan naku kudin*

09033181070


*ZAFAFA FAMILY na maraba daku*

*_GUDUN ƘADDARA_*

*H U G U M A*

Book 02 page 13
______________________________

*_Shin kin isa mace?,don magana akeyi ta ISASSUN MATA_*

*_SUTURA ABAR TUNQAHO_*

*_Ado da kwalliya shine cikar 'YA MACE_*

_Magana akeyi ta_

*UMMU MAHNOOR LUXURIES*

*UMMU MAHNOOR LUXURIES*

_GIDAN QAWA ADO NA KECE RAINI_

*_INA AL'UMMAR KADUNA ABUJA SULEJA DAMA NIGER......HAR MA FADIN NIJERIA GABA DAYA_*

*_KIN SHIRYA FITA KUNYA?_*

*_MAZA HANZARTA KI LALUBI KALOLIN SUTURAR DA TA DACE DAKE,KAYAN ADO MASU_*

*KYAU*

*QUALITY DA DAUKAN HANKALI*

*LACES NE,SHADDA CE,ATAMFOFI NA 'YAN QWALISA*
*GA KUMA DESIGNERS TAKALMA DA JAKANKUNA NA ALFARMA DA FITA KUNYA*

*_ZAKU IYA SAMUN MAMALLAKIYAR KAMFANIN KAI TSAYE TA WANNAN NUMBER WAYAR_*

08135142610

*INSTAGRAM* UMMU_MAHNOOR_LUXURIES

*FACEBOOK* MUSA GARBA SHIFA

*_Ga wadanda ke cikin garin abuja kuma zasu sameta kai tsaye a_*

*_system property Nefelix estate,near amasco,galadimawa roundabout_*

*_KARKI BARI A BAKI LABARI,KARKI KUSKURA KI ZAMA 'YAR KALLO_*

*TASTED AND TRUSTED*👌👌👌
______________________________




Cikin jikin ama din take kwance luf,ga duk wanda yasan sultanan zai iya rantsuwa a yanzun ba ainihin sultana da ya sani bane,ta koma wata maras kuzari ko kadan,so silent,tana daukan lokaci me tsaho kafin ka tsinci kalma guda daga bakinta.

Bibi batasan da dawowarsu ba sai da suka isa farfajiyar gidan. Dukkan ma'aikata dake da duty da safen suka marmatso suna musu barka da zuwa tare da sakeyi mata sannu da jiki. Sannu da jikin da takejin kamar da gayya akeyi mata ita,duk wanda yace mata ya jiki maimakon taji dadin hakan sai wani bacin rai ya lullube.

Ama na fiddota bibi ta qaraso,ta sanya hannu ta taya ama fiddo ta

"Ki kwashe duka kayan ki shiga dasu ciki,wadanda keda buqatar gyara kuma a gyarasu don Allah" ama ta waiwaya tana riqe da sultana ta yima tanja umarni

"An gama ranki ya dade" ta fadi a ladabce sannan ta zagaya bayan motar tana yiwa modu driver maganar ya buda boot din.

"Sannu" bibi ta fada wadda ke riqe da hannun sultana daya. Kai kawai ta gyada mata bata iya kallon qwayar idanunta ba.

Sun taka har veranda din bibi da zata sadaka da ainihin qawataccen falon dattijuwar. Taku daya tak sultanan zatayi ta sanya qafafunta cikin falon,har ta daga qafar sai kuma ta maida ta sauke tana ja baya kadan tamkar wadda ta hangi wani shamaki a gabanta.

Daga bibin har ama duban fuskarta sukeyi,fuskar data sauya lokaci daya tana fidda wasu irin emotions dake nuna zurfin abinda ke danqare a zuciya

"Mu qarasa ciki sultana" bibi ta fadi tana dubanta. Sake girgiza kai tayi a karo na biyu,sai kuma ta juya da hanzari da qaramar sassarfa,tafiyar da tana yinta ne kawai amma iska ke barazanar bugar da ita daga hagu zuwa dama,sai ama ta take mata baya,sannan cikin hanzari ta sha gabanta gudun kada ta isa farfajiyar gidan kuma wani abun ya faru ta tara musu 'yan kallo.

Koda tasha gabanta kuka take haiqan qirjinta na dagawa,zaka tsammaci gasar tseren gudu ta shiga. Kamo hannunta ama tayi da kyau ta damqe cikin nata hannun,bata manta da bitar da Dr chafa'atou tayi mata kafin barowarsu asibitin,don haka cikin tausasawa ta tambayeta

"Ki kwantar da hankalinki ki nutsu,u r safe,maina bai isa ya miki komai ba,yanzu ke 'yar gatan bibi da ama ce,ga aba oncle omar oncle bashar ma" kai take jijjigawa,sannan cikin muryar kuka tace

"Bazan shiga ba ama"

".....akwai abubuwan da zasu iya kada hankalinta su kuma firgitata,kamar wajen da abun ya faru,abubuwan dake zagaye da ita sanda komai ya faru da sauransu,so ayi qoqarin goge da kauda komai don kwanyarta ta samu cikakken waraka....." Ama ta tuna maganganun Dr chafa'atou.

Ajiyar zuciya ta sauke tana jinjina kai

"Is okay ya isa,muje sashena,zaki zauna a dakina?" Idonta ta runtse hawayen dake maqale ya qarasa gangarowa,saita daga kanta a hankali tana ayyana ashe akwai ranar da zata guji rayuwar kusa da bibinta?,bibinta abar qaunarta?,ashe akwai sanda zataji gwara rayuwa nesa bibi?.

Batayi yunqurin maidata sassan bibi ba ta wuce da ita kai tsaye nata sashen,saidai bibin na biye dasu,don tana kai sultana dakinnata ta barta da daya daga cikin masu aikinta,ta kuma dawo falon don ta sanya a kwaso sauran kayanta dake dakinta can sassan bibi saiga bibi din da kanta.

"Wani abunne kuma hamdiyya?" Yadda bibi tayi tambayar a sanyaye sai tausayinsu su dukka ya kamata,a yau maina ya zama silar nesantarsu da juna duk da irin son da sukewa juna

"Ba komai bibi,zauna na miki bayani" a nutse ta fahimtar da bibin,ta kuma fahimta duk da fuskarta ya nuna lamarin bataso ya kasance haka ba,amma a yanzun samun cikakkiyar lafiyar sultanan da dawowarta hayyacinta shine gaba da komai.

Kafin yammaci komai na sultana ya koma sassan ama,ta fidda komai nata daga dakin ta sanya an sauya mata daki,ta barwa sultana wannan. Zuwa magariba komai ya kammala.

Da kanta bayan ta kintsa ta dawo ta saka sultana a gaba tayi wanka,ta bata kaya ta sauya sannan ta sake tusata sai data ci abinci. Abinci ne lafiyayye da tasan zai sanyata ta ciko ta kuma tada komada. Tana da buri da fatan nan da sati daya kacal ma sultana din ta sauya ta fara komawa sultananta ta asali.

Ko na minti daya ama bata barinta ita daya bare tayi wani tunani da zai hatsinata. Bayan sallar isha'i ta sanya bilki ta fiddota ta zauna falo kaman kowa.

Dai dai lokacin aman tana zaune saman daya daga cikin kujerun falon. Tab ce a hannunta tana duba hotunan kayayyakin dake cikin container dinta data sauka wadda bata samu nutsuwar dubawar ba sai yanzu,saidai rabin hankalinta na ga wayoyinta wai ko zataga gilmawar wani abu da ya shafi maina. Ita kanta ama din ta fada tayi fayau,amma wannan kyan dai da gayun nata yana nan. Ko a yanzun wani cotton material ne a jikinta da aka yiwa budadden dinki,dogon hannu ne saidai an tsagashi ta sama har kusa da damtsenta. Qafafunta na harde guri guda,saddi yana zaune daga qasa kusa da qafafun na yana tattare mata wasu takardu. Tunda taji alamun tahowar bilki ta shinfidadden marbles din dake malale a dukka ilahirin sassan ta dauke hankalinta daga tab din ta maida inda suke nufowar don taga sultanan tayi wankan kwanciya ta kuma sauya kayan kamar yadda tace mata tayi.

Batakai ga lura da wannan ba idanunta suka sauka kan fuskar sultanan,wadda gaba daya manyan fararen idanunta ke kafe waje daya a falon,sai kuma a hankali a hankali ta soma tsaiwa kafin taja da baya da gudu kuma ta koma ciki da sassarfa kuka yana qwace mata.

Kwata kwata ama batasan da shigowar aba ba sai data waiwaya tana duban abinda ya sanya sultanar razana da kuma komawa cikin. Babban hoton maina ne. Sanye da wasu kaya na asalin buzaye, kayansu na gargajiya,kanshi yasha nadin rawani irin nasu fari qal,kamar yadda ainihin kayan suke baqaqe ne da adon farin zare.

Hoto ne da ama din ke masifar so,saboda ya fita aininun,ya kuma fidda kamannin maina da baiwar zallar kyau da Allah yayi masa,kyawun dake cakude da quruciya da tashen shekaru.

"Kai saddi!,zo ka cire hotonnan" aba ya furta cikin kakkausar murya wani abu me zafi yana gilmawa ta cikin idanunsa. Ba musu saddi din ya miqe cikin sanyin jiki bayan ya ajema ama takardunta,ya nufi hoton yana jawo wani stool me kyau dake gefe wanda aka azama decoration flower,ya sauke flower din ya taka saboda tsahonsa bazai kai ba,maina dinne da kansa ya kafa hoton bayan an wankoshi,naira dubu talatin da biyar ama din ta bayar akayi mata shi.

Qasa ya saukeshi kamar yadda aba ya buqata,yana tsaye daga bayan saddi din ya sake cewa

"Juyashi ya kalli bango" juyashin yayi kamar yadda ya buqata,sai ya sake kallonsa

"Duk wani hoton aliyyu dake sassannan komai qanqatarsa a fiddashi,banaso na sake gani" ya fadi yana nuna saddi da yatsa kamar shine me laifin

"To aba" ya amsa masa cikin ladabi. Bai sake cewa komai ba ya juya yana wucewa qofar da zata sadashi da gefansa,sai sannan ama tayi qarfin halin cewa

"Sannu da zuwa"

"Yauwa" ya bata amsa yana dan dubanta kadan kafin yaci gaba da tafiya.

Rasa waye zatabi tayi cikin aba da kuma sultana?,daga qarshe ta yanke shawarar bin sultana din,don a yanzun ita keda cikakken buqatar a rarrasheta,aba kam batasan meke yawo a kansa ba,alamu sun nuna kamar ma dai ita yakewa kallon maina. Kallon saddi tayi daketa aikin bi yana kauda hotunan maina din, fuskarsa shima ta nuna yadda zuciyarsa ke masa rashin dadi,sai kawai ta fasa maganar ta juya tana fita a falon.

A takure ta sameta,fuskarta tsakiyar qafafunta tana rusgar kuka,wannan karon harda marayan sauti dake fita daga muryartata. Duk sanda taga kuka ya barke mata irin hakan tana narka zuciyar ama,tasan cewa yau koda da wayonta maina yayi mata haka dole taji abun har zuciyarta,koda tana sonshi,balle ita din da ta tabbatar babu komai tsakaninta da maina din sai ADAWA DA GABA DA KUMA TAKUN SAQA.

Qarfe goma harda rabi tabar dakin bayan bacci ya dauketa bayan ta gama koke kokenta. Ta fahimci bawai hotunan maina ba kawai,hatta da sunansa bata qaunar jin wani ya furta koda bawai ana nufin shi aliyyun ba.

Tanason shiga ta iske aba,amma sai zuciyarta tafi karkata da ta tafi dakin maina din.

Iya qurar dake jikin handle din qofar dakinsa kadai ta isheka amsar cewa yayi nisa da wajen,nisan da ko qofar dakin da alama babu wanda ya sake tabawa bare a samu sassaucin qurar dake sauka.

Ga mamakinta key din dakin yana maqale a jiki. Hannu tasa ta murza ta tura qofar ta shiga. Da idanu tabi falon nasa da kallo,falon da baya rabo da tsafta,falon da baya rabo da qamshi,falon da ko yaushe cikin qyale qyale yake,amma a yanzun qura ta soma samun wajen zama.

Takawa tayi cikin falon ta danyi shawagi,idanunta manne da hotunansa qwaya hudu rak dake maqale a bangon falon. Dauke kanta tayi ta tura qofar dakin gadon nasa wadda itama dai a bude take,barin qofar kuma a bude na sake haifar mata da tunani da kuma kokwanto me yawa.

Dan razana tayi kadan da ganin mutum cikin dakin,amma yana dago fuskarta data fahimci waye saita daidaita nutsuwarta

"Qaraso ciki mana" aba ya fada ganin taja ta tsaya daga qofa yana maida hankalinsa ga gurin da maina ke ajjiye duk wani abu nasa me muhimmanci

"Kema sahunshi kika biyo?" Ya sake jefawa ama tambayar. Ganin yanayin aba din kawai sai ya haifar mata da rauni

"Aba,kwana........"

"Kwana goma sha hudu kenan ba.....babu shi ba dalilinsa,bai nememu ba bai kuma dawo gida ba,ai dama bazai dawo din ba,saboda mu din ba wasu mutane bane dake da muhimmanci a tattare dashi ba,inda muna da muhimmanci muna da kima da martaba tun asali da bai aikata abinda ya aikata din ba,yarinya qarama tsakiyar iyayenta da kakanninta, bashi da asara kota sisin kwabo shi yasa ya tsallaketa ya kuma biyo ya dakinsa ya iya tsaiwa tattara komai nasa me muhimmanci,kinga yabar mana saqo tare da tabbacin cewa kada muce zamu nemeshi,don a yanzun ya zama d'an kanshi bashi kuma da buqatar wasu iyaye".

Kalaman aba daya bayan daya suka dinga dukanta har sai da suka sanyata sulalewa ta zauna gefen gadon maina dake a mulmule sai 'yar qura data sauka akai. Hannunta har dan rawa yakeyi sanda ta kalli wajen taga kaf komai nashi da suka sani me daraja yana adanawa a wajen fes babu komai wajen. Duk da taga zahiri amma zuciyarta taqi aminta da nata zargin da kuma sharhin aba,sai ta fara girgiza kai idanunta suna nuna zallar tashin hankalin dake yawo a jiki da zuciyarta.


*_KWANKWASON JIMINA_*

*_TSUTSAR NAMA_*

*_AMEENATOU_*

*_GUDUN KADDARA_*

_DUKKA AYARIN LITATTAFAN KUDINSU YA KAMA KAMAR HAKA_*

LITTAFI DAYA_400
BIYU_800
UKU_900
HUDU_1200

_IDAN TA BANKI NE ZAKI SANYA KUDINKI A WANNAN ASUSUN_

6019473875
Musaa Abdullahi safiya
Keystone bank

_ANTAYA SHAIDAR BIYANKI ZUWA GA WANNAN NUMBER_

09166221261


*Masu tura katin waya ko vtu kuma kai tsaye wannan number zaku tuntuba*

09134848107

*Maqotanmu kuma al'ummar qasar nijer zaku tuntubi wannan number dinne kai tsaye don biyan naku kudin*

09033181070


*ZAFAFA FAMILY na maraba daku*🫂🫂🫂🫂🫂*_GUDUN ƘADDARA_*

*H U G U M A*

BOOK 02 PAGE 14
_________________________________
_Assalamualaikum warahmatullah_*

*_Kin dade kina neman gurin da zaki siya kaya amintattu masu quality cikin farashi me sauqi?_*

*_ina marabtarku zuwa cikin wannan gida tare da kasancewa da juna,WANNAN GIDANNA HUGUMA CLOSET NA BUDESHI NE SABODA NA BAKU DAMAR SIYAN KAYA MASU KYAU QUALITY DA KUMA SAUQIN KUDI CIKIN AMINCI DAGA GURINA,MASU SIYAN D'AI D'AI DA MASU SARI,NATION WIDE DELIVERY cikin aminci da izinin Allah,Kayan haihuwa na jarirai har zuwa girmansu,ina muna fatan alkhairi ni da ku gaba daya_*

https://chat.whatsapp.com/CKY0xZDtpby6MTkGrPkXLr
__________________________________




"kar kayi haka aba,kaifa uba ne.... kada ka yanke hukunci cikin


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login