Showing 42001 words to 45000 words out of 294767 words
Chapter 15 - Gudun Kaddara Book 2 Hausa Novel Complete
tafi tsana a duniya,qamshin da batajin ko da tana kwance ne a kushewarta muddin qamshin zai gitta ta gurin zata iya jiyoshi,qamshin da jikin mutum daya ta sanshi,ta kuma yi masa mummunar hadda me wuyar mantawa a baqar ranar da tayi silar jirkita dukka farinciki walwala da tarin mafarkan data tanadarwa rayuwarta.
Tsam ta miqe tsaye dukka jikinta yana rawa,ta ware idanunta tana duban kowanne sashe na wajen. Ba kowa,bata ga kuma kowa ba,hasalima kaf wajen kamar ita daya ce baqar fata,sai kuma ama data shiga ciki.
Dafa kafadarta taji anyi,abinda ya sanyata wani irin bahaguwar juyowa,sai idanunta ya fada cikin na ama. Kallon kallo suka tsaya yiwa juna,ama tana kallonta cikin mamakin abinda ya firgitata daga shiga ta fito bayan wajen safe yake,yayin da ita kuma razanar da tayi da kuma tuna mata da mummunar ranar da sanadiyyar wanzuwar qamshin ya haifar mata ya sanya zuciyarta raurawa,kawai saita aza fuskarta saman kafadar ama ta saki siririn kuka.
Tasan dama akwai sauran qunci cikin zuciyarta,wanda babu wata hanya da zata samu sassaucinsa saita hanyar kukan,don haka batace komai da ita ba,ta jata jikinta sosai tana bubbuga bayanta,har sai data nutsu don kanta sannan ama din ta maidata saman kujerarta,ta kuma tura mata daya daga cikin nau'in abin shan da shima akan dace ya zaunawa cikinta.
Bata tambayeta ba hakanan batace mata komai ba sai da taga tana diba da kadan da kadan kamar me ciwon baki tana sha sannan ama din tayi gyaran murya tana gyara zamanta
"Next month zamu koma asibiti,zan tambayeshi wacce rana ne zaki haihu,zakiji in sha Allah,amma kinsan zai iya ce miki ba yanzu ba?" Da sauri ta daga kai tana wulqa idanu,idanun nata cikin na ama, fuskarta ta narke sosai cikin nuna zallar fargaba. Sai ama ta dage mata dukkan girarta
"Eh mana,ya hana wannan koke koken,sannan yace ki dinga daurewa kina cin abinci sosai haka ne?" Kai ta gyada mata a hankali
"To me kike tunanin zai faru idan mukaje ya gwadaki yaga babyn baiyi girman da zaki haihu ba?"
"Zanci ama,don Allah kice masa kada yacemin ba yanzu ba,bana iya bacci ama,bana iya komai,dukana kawai yakeyi a ciki na,kullum dare a zaune nake....." Ta qarasa fada tana saka tafin hannunta guda tana share sabbin hawayen dake sauko mata. Tsananin tausayinta sai da ya sanya ama din taji qwalla sun sauko mata amma ta daukesu cikin dabara,saita miqa hannu tana dan bubbuga bayanta cikin dabara.*_GUDUN ƘADDARA_*
*H U G U M A*
Book 02 page 22
Ganin ta zage tasha abun sosai sai ama ta yanke shawarar su qara nisan zango a tafiyarsu don ya saukar mata sosai,kada su koma gida da wuri ya dameta ko ya sanyata amai.
Cikin salon jan hankali ama ke bata labarin Germany,har zuwa sanda sukazo giftawa ta wani baby shop. Har sun gota amma ta tsaya,sai a sannan ta tuna babu koda qyallem handkerchief da ta siya da sunan kayan haihuwa. Juyawa tayi ta dubi sultana
"Mu shiga nan ki jirani nayi siyayya" bata musa ba ta sanya kai tana biye da ama din.
Guri ta sanya ma'aikatan gurin suka bawa sultanan tace tayi zamanta,gudun kada tace tazo ta tayata zabe taje ta jangwalowa kanta,qilu ta jawo bau.
Sosai ta nutsa cikin shagon,ta dinga zaben kaya designers masu tada da sukaja pounds sosai. Samun kanta tayi da daukar duk abinda ya bata sha'awa,musamman kayan baby girl.
Har yanzu akwai wannan qawa zucin a jikinta da kuma zuciyarta,har yanzu tanason baby girls,don dai kawai lokacin haihuwarta ta fuskanci ya wuce ne.
Sanda ta shiga bangaren overalls 'yan ubansu,saita tsinci kanta da zaben komai pink,haka kawai cikin zuciyarta taji tana da burin inama ace babyn ya zama mace?, murmushi ya subuce mata ba tare data shiryawa hakan ba.
Daidai bangaren teddies ama ta ajeta. A nutse takebin wajen daki daki da kallo,komai na wajen me kyau ne,alamu dake nuna cewa komai na cikin shagon zaiyi tsada kenan.
A hankali wani tsohon emotion nata ya fara taso mata. Nini dinta ta fado mata wadda har kwanan gobe batasan inda tayi ba. Allah ya zuba mata qaunar teddy,duk da wannan emotion din nata yaso mutuwa murus daga gangar jiki harma da ruhinta.
Har ta zare idanunta daga kansu sai hankalinta ya fusgo mata wata kyakkyawar pink teddy. Maida dubanta tayi,ta miqa hannunta tana shafata. Sosai jikin teddy din yayi mata,haka ma fasalin da akayi mata
"Ki dauka idan tayi miki" ta tsinci muryar ama daga bayanta. Da sauri ta waiwaya ta kalli ama dake riqe da wani babban kwando da ta cikashi taf da suturu,saita maida dubanta ga fuskar ama din tana girgiza kai alamun a'ah,sannan ta miqe a hankali da zummar barin wajen. Da kallo ama ta rakata sai kawai ita ta saka hannu ta zaro teddy din ta jefata a kwandon kayan. Har tayi gaba ta dawo da baya,ta zake zabar wasu guda biyar suka zama shida cif,sannan ta wuce wajen lissafi.
Mamaki ne kawai ya kashe sultana sanda taga uban kayan da ama ta diba,ashe kwandon hannunta na daxun sauran kayanne kawai. Kamar ba da guminta take neman kudin ba,ta zare Pounds masu ciwo ta biya kudin kayan tas,sanann ta bada Adress din inda za'a kai mata suka fice abinsu daga shagon.
Har ranta bataji komai ba,jinin maina ne kuma tsatsonta itama.......inda ana kyautar rai tabbas zata iya sadaukarma ahalinta,xata iya komai domin jininta,ita a yanzun ma da kwanakin cikin ke qara nisa sai takejin zumudi qauna da kuma soyayyar abinda ke cikin na sake kamata,taji ta dokanta da son ganin abinda ke cikin sultana din,ta matsu ya iso duniya.
********Sake duba agogon dake daure a tsintsiyar hannunta ama tayi,mamaki ya sake kamata,me sultana din keyi shuru bata fito ba har yanzu?,bayan tasan inda zasuje din da kuma muhimmancin wajen.
Kamar ta aika tanja sai kuma ta fasa,ta miqe tana ajjiye medium veil din hannunta mahadin doguwar rigar jikinta ta gyara zaman agogon hannun nata tana wucewa dakin sultanan.
Zaune ta sameta saman stool a gaban madubi,daure take da babban farin towel,sumar kanta na nannade tsakiyar kanta. Tuni ta jima da zama qazama ta wannan fannin,bata yarda da abinda zaya taba mata kanta duk qanqantarsa,sai ama tayi da gasken gaske sannan ake wankeshi a kuma maidashi yadda yake.
A nutse tare da sallama ama ta shiga dakin,waiwayowa sultana din tayi,hawaye ne shabe shabe kwance a fuskar tata
"Ya salam" ama ta furta qasa qasa. Itadai tunda take bata taba ganin mutumin da kuka baya damunsa ba baya kuma yi masa wuya ba irin sultanar
"Yanzun kuma kukan meye?" Ta tambayeta tana isa bayanta ta tsaya tana duban fuskarta cikin mudubi. Cikinta ta kalla,sai a sannan idanun ama yakai kai,ta yaye towel din dake jikinta,sai turtsetsen cikin a gaba kai kace saura satittika ta haihu
"Menene?" Ama ta sake tambayarta cikin fargabar kada ta bata amsar wani abu ne ya samu cikin
"Fasamin ciki zaiyi ama......sai dukana yakeyi nan da nan" ta bata amsar tana rushewa da kuka tare da nuna mata gefe da gefen cikinta da yatsanta. Ga dariya ga kuma tausayi,da gasken gaske sultana danya ce shataf,babu wani abu data sani dangane da ciki ko haihuwa,uwa uba auta kuma 'yar fari,wautar tata tayi yawa.
Gaban sultana din ama ta zauna tana qoqarin fahimtar da ita cewa alama ce ta lafiyar abinda yake cikinta
"Ni na tambayeshi yana lafiya?,ya mutu mana" ta fada tana buntsuro baki gaba
"Subhanallahi" ama ta fadi tana zaro idanu,don sosai maganar ta daketa, jikinta yayi wani mugun sanyi,tsoro kuma ya shigeta. Kada dai ace zuciyarta ta taso da qeqashewa da qiyayyar abinda zata haifa din kamar yadda ta yiwa mahaifinsa muguwar tsana?. Wannan tunanin kadai ya sanya zuciyarta rawa,bata fatan kuma wannan ya zama qaddararta ta gaba,batasan yadda zata fuskaci wannan qaddarar ba kuma
"Sultana?" Ta kirayeta a sanyaye tana kallon tsakiyar qwayar idanunta. Duban aman tayi amma sai ta janye kallonta daga kanta,karon farko da taji wani nauyi na aman,taji kuma nauyin kallon idanun aman,jikinta itama ya sanyaya,taji a jikinta kamar ta furta wani abu da ba dai dai ba.
"Kinaso muyi fada dake?" Ta sake tambayarta with seriousness. Da sauri ta girgiza kai tana jin zuciyarta tana karyewa
"To kada ki sake fada,kada na sake jin kinyi wannan furucin,akan kowa ma bare d'an cikinki,da yake kwana ya tashi a jikinki,bashi da wata uwa sai ke,ke kadai kika dauki cikinsa kikasan wahalarsa,mu nan dukka tayaki kawai mukeyi kinji ko?" Kai ta jinjinawa aman,sai tayi saurin kauda zancan ta hanyar cewa
"Oya.....tashi ki qarasa shiryawa,idan munje wajen likita saiki kai masa qararsa,zai masa fada nasan,zai daina kuma dukanki" wannan 'yar maganar ta sanyayawa sultana rai,ta kuma miqe din ta shirya tsaf a gaban ama din kamar yadda ta saba shiryawar,ba wani nauyi ko kunya ko digo da takeji nata.
Yauma sai da sukayi tattaki subway,sannan suka hau train zuwa asibitin.
Dr abdur'razaq mansoor,cikakken likita dan asalin qasar Egypt shine likitan dake duba sultana,likita ne me matuqar kirki da kula da addini,yana da tausayi da kulawa sosai. Tun ranar farko da ya fara ganin sultanan tausayinta ya cikashi,ya fahimci yarinya ce qarama sosai da bata gama sanin rayuwa ba.
Yanayin nutsuwar likitan da tausayin da ya gwada ma sultanan ya sanya ama bata boye masa komai ba
"Zan bata kulawa in sha Allah,zata haihu kuma lafiya" a boye ya baiwa ama addu'o'in da zata dinga tofawa sultana din a ruwa,kuma ko sau daya aman batayi fashin tofa mata din ba ba tare da sultana ta sani ba. Duk wani gorar ruwa na gidan da tasan sultanan zata iya sha sai data budesu ta tofa din,daya daga cikin sirrikan abinda ya kawowa zuciyarta nutsuwa ya kuma sake tanqwara ta ya sanya mata dangana.
A irin qasashe dake da ci gaba irin haka,zaiyi wuya kaje ganin likita ka samu cinkoson marasa lafiya suna jiran likita,hasalima lokuta da dama saidai ka samu likitan yana zaune kawai yana hutawa ko wani research da ya danganceshi. Don haka mace daya ce ta fito number dinsu tayi appearing jikin board na office dinsa don haka suka wuce ciki kai tsaye.
Da fara'arshi da kuma sakin fuska ya musu maraba. Ya saba sam sultana bata magana har su gama ganinsa su tafi,amma hakan baya hanashi dan tsokanarta janta da wasa kadan don ta saki jiki da kuma tambayarta yanayin lafiyarta.
Sai da ya gama mata dukka tambayoyin da aka saba,ya nemi jin ko akwai wata matsala da take fuskanta?. Murmushi ama tayi sannan cikin harshen France don sultana din taji ta gaya masa
"Tace dukanta cikin yakeyi,ta gaji dashi yaushe zan karba?" Qaramar dariya Dr abdur'razaq mansoor ya saki
"Yau zamu duba muga me yake faruwa sai a gaya masa ya fito haka momy ta gaji" shi da ama suka dan saki dariya,banda sultanan da take binsu kawai da kallo.
Komai ya hada sannan ya bata umarnin hawa gadon scanning. Karon farko da za'a yi mata scanning din tun bayan wanzuwar cikin.
Kusan daskarewa Dr abdur'razaq mansoor yayi yana ci gaba da yawo da na'urar saman cikinta
"Subhanallah" kawai yake furtawa lokaci lokaci idanunsa qur bisa allon computer din.
Subhanallah din da yake fada ta sanyawa ama fargaba,amma ita dinma saita dinga ambaton sunan Allahn kawai,don tunda taji baice komai ba qila babu buqatar yin maganar gaban sultana.
Yana kammalawa ya danna wani madanni na kiran nurse,ba jimawa nurse din ta shigo,cikakkiyar baturiyar Austria,saidai ita dimma da alama macace me kirki da yawan fara'a.
Cikin harshen German yace da ita ta kaita garden na masu juna biyu,sannan ya sake juya harshen nasa cikin yaren France ya yima sultanan magana. Ba musu ta miqe ta saki doguwar rigarta,ta kuma gyara yafen mayafin nata tabi bayan matar.
Da idanu ya bisu,sai daya tabbatar da fitarsu sannan ya dawo da dubansa ga ama wadda ta tsurawa hoton scanning din dake jikin allon computer din idanu,kwanyarta nason rarrabe mata gaskiyar abinda idanunta ke gane mata.
Hannu kawai ya miqa ya juyo mata da fuskar computer sosai yana kallon idanunta,cikin yaren faransanci yace mata
"Ina tayaku murnan samun 'yan biyu,yarinyarki tagwaye ne a cikinta kamar yadda na jima ina zato" maganar tazo mata a mugun ba zata,cikin hanzari ta maida dubanta ga Dr abdur'razaq. Ya fahimci she was shocked,sai yayi murmushin nan nasa yana dora dukka hannuwansa kan computer din.
Kai tsaye ya canza hoton da take gani zuwa 3D scanner,take fuskokin yaran dake kwance cikin mahaifar sultana din suka bayyana tarwai.
Ko ina a jikinta ya dauki rawa,ta sanya hannuwanta dukka biyun tana rufe bakinta,bakin nata dakeson kama sunan Allah amma rawar da yakeyi ya sanya ta kasa,Dr abdur'razaq bai waiwayo ya dubeta ba yaci gaba da mata zooming fuskokin guda biyu da suka zama cikakkiyar fuskar bil'adama,fuskokin da suka cika suka kuma bayyanar da kamanninsu,suna rungume da junansu
"Bacci sukeyi,inda idanunsu biyu zaki iya ganin motsawar kowannensu,kukansu ko walwalarsu"
"Subhanallazi lam yattakiz waladan walam yakun lahu sharikun fil mulki walam yakun lahu waliyyun minazzull" ta furta wasu hawaye masu sanyi suna sauko mata. Tayi tunanin zasu tsaya amma basu tsaya din ba,haka suka dinga sauko mata daya bayan daya. Bai hanata ba Dr,yadai miqa mata tissue yana duba wasu ayyuka nashi har sai da zuciyarta tayi sanyi sannan suka dakata,ta gyara fuskarta ta kuma gyara zaman mayafinta sannan tace
"Amma Dr ina tsoro,ta yaya sultana zata iya haifan tagwaye da kanta?" File din gabansa ya rufe yana dubanta
"Bayanin da nakeson miki kenan,tayi qanqanta qwarai,don ko a yanzun girman da yaran keyi a cikinta ya bani mamaki,nauyinsu da na gani,lallai ita kanta ba qaramin qoqari takeyi ba,kuma tana da jarumta duk raunin nan nata da yawan koke koke,bakinta kuma na tabbatar duk da yawan qorafinta akwai abinda bata iya gaya miki,so ina kyautata zaton cikin yana shiga sati na talatin da shida za'a yi mata CS a cireshi......amma banason ki gaya mata hakan,saboda a yanzun dole a dinga monitoring blood pressure nata,a bata kwanciyar hankali sosai da nutsuwa don komai yazo yadda akeso". Sosai jikin ama ya qara sanyi,ya lura da hakan sai ya bata gwarin gwiwa sosai,qwarin gwiwar da ta sanya taji eh tabbas zasu iya fuskantar komai,kuma komai zaizo ya wuce da qudirar Allah kaman bai faru ba.
A karo na Babu adadi bayan fitowarta daga office din Dr abdur'razaq ta ciro wayarta,kamar kowanne lokaci da idan abu irin hakan ta faru zatayi gajeran tex wa maina
*_KWANKWASON JIMINA_*
*_TSUTSAR NAMA_*
*_AMEENATOU_*
*_GUDUN KADDARA_*
_DUKKA AYARIN LITATTAFAN KUDINSU YA KAMA KAMAR HAKA_*
LITTAFI DAYA_400
BIYU_800
UKU_900
HUDU_1200
_IDAN TA BANKI NE ZAKI SANYA KUDINKI A WANNAN ASUSUN_
6019473875
Musaa Abdullahi safiya
Keystone bank
_ANTAYA SHAIDAR BIYANKI ZUWA GA WANNAN NUMBER_
09166221261
*Masu tura katin waya ko vtu kuma kai tsaye wannan number zaku tuntuba*
09134848107
*Maqotanmu kuma al'ummar qasar nijer zaku tuntubi wannan number dinne kai tsaye don biyan naku kudin*
09033181070
*ZAFAFA FAMILY na maraba daku*🫂🫂🫂🫂🫂*_GUDUN ƘADDARA_*
*H U G U M A*
BOOK 02 PAGE 23
A duk sanda wani abu ya faru sai ta rubuta ta tura masa tare da gargadinsa kan duk inda yake ya dawo. Ko sau daya bata taba samun tabbacin saqon yana isa ba,bata taba ganin alamu na maido amsa ba koda da digo,amma hakan bai hanata aika saqon ba.
Cikin hanya kaf tunaninta na yadda zata sake dauke hankalin sultana,tare da yin handling komai idan lokaci