Showing 138001 words to 141000 words out of 294767 words
Chapter 47 - Gudun Kaddara Book 2 Hausa Novel Complete
Ya jima sosai a bandakin sannan ya fito,sanye da gajeran wando zalla abinda ya sanyata sake cusa kanta tsakanin cinyoyinta tana jin wani bacin rai da weakness suna ratsata. Baice da ita komai ba ya isa ga windows din dakin dukka ya sauke labulayen,abinda ya qarawa dakin duhu kenan,ya isa ga makashin qwayaye dukka ya kashesu,sannan ya qarasa saman gadon a matuqar kasalance yabi lafiyarsa yana cewa
"Zan huta na wasu mintuna daga bisani na kaiki.....ki kwanta ki huta kema" ya furta yana tattare pillows din saman gadon ya matsesu gam a jikinsa yana sauke numfashi a wahale.
Bata amsa masa ba,hakanan bata motsa ba,taci gaba da rera kukan bacin rai a hankali. A qalla mintuna ashirin da daukan shirun da dakin yayi,wayarta data watse a gefe ta soma haske. Kaman ba zata daga ba sai kuma ta miqa hannu ta janyota
"Ama ta" shine sunan dake yawo saman screen din. Riqe kukanta tayi da kyau tama share hawayenta da bayan hannunta sannan ta daga kiran
"Karki jima sultana sosai,ki dawo da wuri ki fara hada kayanku,kwana biyu kawai ya rage mana zamu koma" kamar bushara haka taji maganar ama,ta bude idanunta da suka jiqe da hawaye tana hangensa daga inda take a zaune,wani irin farinciki ya soma mamaye damuwarta,lokaci yayi da zata sake masa nisa,nisan da idan tayishi ba zata sake bashi daman zuwa kusa da kta ba bare ya dinga walagigi da rayuwarta yana mata Iko yadda ranshi yakeso ba
"In sha Allah ama" har ama din ta buda baki zata tambayeta inda ta tsaya don yasmine tace bata qarasa ba sai kuma ta fasa ta yanke kiran. Wata wawiyar ajiyar zuciya ta saki fuskarta na kallon sama
"Alhamdulillah" ta samu kanta da furtawa,tana ji a nan kusa zata yakiceshi ta huta. Bashi da communication me kyau da ama bare aba ballantana ya isketa a inda take din. Sai ta miqe a hankali ta taka zuwa qofar toilet din tana ji har jikinta da zuciyarta ta samu qwarin gwiwa.
_ba'a nan naso tsaiwa ba,amma yanayin yazo a haka,in sha Allah idan na samu yadda nakeso hutun zai kasance asabar da lahadi ne zuwa litinin kawai,daga nan zamu dora_
_da alama qullalliya sultana ke shirin qullawa maina ta hanyar amfani da ama ba tare da ama din tasan da haka ba,shin ya zata kasance?_
_ayi sallah lafiya cikin aminci,ubangiji ya maimaita mana ya karbi ibadunmu ameen ya hayyu ya qayyumu_*_GUDUN ƘADDARA_*
*H U G U M A*
BOOK 02 PAGE page 72
Alwala ta daura ta goge fuskarta da kyau cikin toilet din,ta fidda powder da bata rabo da ita ta shafa,ta kuma gyara lips dinta. Har cikin zuciyarta tana jin sanyi,bacin ranshi kuma ya ragu sosai,tunda tasan kwanaki biyu rak suka rage mata tayi adabo dashi.
Tayi zaton data fito zata sameshi a shirye ko yana ma shirin su tafi din,maimakon haka samunsa tayi a kwance lakadan abinsa,kamar ma wanda ke bacci. Ta saci kallonsa sai tayi hanzarin kauda kai,saboda ta tunashi da shegen saurin karantar mutum. Taci alwashin ba zata ce dashi komai ba,don haka ta koma saman kujera ta zauna,ta fidda wayarta daidai sanda take ringing kira ya shigo.
Ko data duba sai taga kiran yasmine ne still
"Ya salam" ta furta cikin damuwa,don batasan amsar da zata bata ba
"Oya..... bani wayar nan" muryarsa can qasa kaman wanda yasha wani abu ya ratsa kunnenta. Tadan tsorata don ta tsammaci bacci yakeyi,amma sai ta tada kai tana dubansa. Bai ko kalli wajen ba,amma hannunsa suna saitinta yana jira ta kawo din.
Har tsakiyar zuciyarta taji zallar raini kawai yayi mata,banda haka meye hadinsa da wayarta dama ita kanta da zai dinga qoqarin control dinta da komai nata
"Kada na maimaita fa?" Ya furta har yanzun muryarsa da wani mugun laushi. Bacin rai ya kawo mata iya wuya,ta motsa qaramin bakinta da niyyar masa tsiwa kuma saita maida dukka maganganunta ta hadiye,don tasan furtasu bazai haifar mata da d'a me ido ba,kuma a wannan wajen da suke komai ma zai iyayi mata babu me ganin laifinsa. Wannam tunanin ya sanya ta tattara duk wata tsiwa tata da bacin ranta ta hadiye,ta kuma yunqura a nutse tana isa inda yake din.
Wayar ta miqa kamar yadda ya miqa hannunsa ba tare da tace masa komai ba,tana kuma qudurcewa a ranta ba zata ce masa ta iso ba,duk sanda ya juyo ya ganta.
Hannunta da aka cafka ya sanya zaren tunaninta katsewa,kafin ta sake tuna komai ya jawota zuwa saman gadon ita da wayar gaba daya.
Birkitota yayi sosai yana zare wayar a hannunta ya danna switch ya kasheta,idanunsa a lullumshe muryarsa na dauke da wani irin lallausan amo yana cewa
"Ba zuwa nayi kawai na kashe kudin daki kina niamy ina marad'i ba.....dole ki tayani hutawa,bacci nakeji sosai.......baccin da kikayi shekara da shekaru bakya barina inyisa cikin nutsuwa.......duk sanda na jefar da kaina na kwanta to tabbas sai wannan muryar taki me cike da tsiwa ta biyoni har cikin mafarkina tana sake jaddadamin abinda ta gayamin a baya......zaimin fyade.....Allah ya isa ban yafe ba...... it's so annoyed" ya qarashe fadi da salon muryartata sannan ya cusata tsakiyar qirjinsa a tausashe yana maida hannuwansa ya lullubeta da kyau.
Wani irin abune taji ya mamayi dukka ilahirin jikinta wanda ya haifar mata da tsatstsafowar gumi ta kowacce kafa ta jikinta
"Innalillahi wa inna ilaihi raji'un" ta furta jikinta yana rawa,wani irin tashin hankali yana rufto mata
"Shshshsh!" Ya fadi da qaqqarfan sauti yana dora yatsansa saman lips dinta,wanda a sannan fuskokinsu sunyi matuqar kusaci da juna. Ji tayi kaman zata shide sanda ya busa.mata iskar bakinsa a fuskarta,iskar dake dauke da qamshin mint na mouthwash ne kona meye bata sani ba.
Dukka qarfinta ta tattaro ta turashi baya,sai ya ware lion eyes dinsa yana kallonta
"Ehnnm......bance miki fyade zan miki ba dama?,yanzun wa zaki kira cikin wadanda ke tare miki?,uhmmm?" Ya sauke maganar yana duban tsakiyar idanunta dake kawo gudunmawar hawaye. Labbanta rawa suke tanason fidda maganar dake zuciyarta tare da qoqarin qwatar kanta,sai kawai ya saki siririn murmushi ya maida kansa ya kwanta bayan ya tabbatar ya zagayeta da hannayensa. Ya barta taci gaba da yunqurin qwatar kanta,bai hanata ba bata fasa ba har sai da dukka qarfinta ya qare,yayi amfani da wannan damar ya jata jikinsa sosai,sai ta fashe da kuka ganin babu sauran wata dama data rage mata kenan,bata da sauran zabi sai hada numfashi dashi,ba wata mafita ko garkuwa saita hada gangar jiki dashi,abinda bata sake mafarkin faruwarsa ba,abunda take gani bazai taba hadata dashi ba har qarshen numfashinta. Wanne irin tsaurin ido gareshi haka.,wanne irin taurin kai da kafiya ce dashi da har ya ya iya zare duk wani tanadi data yiwa haduwarta dashi?,ya yake neman rusa komai ya kuma ci galaba a kanta?. Abune da ba zata taba bari ya faru ba yayi iya yinsa na yau ne kadai,saidai duk yadda yakai ga qwarewarsa wajen yaudara bai isa yakai inda yake hari ba.
_nikam nace mmmm🤐
Tun tana lissafa minti biyu biya har goma sai gashi ta tafi lissafin awa daya,sannu a hankali awar tana shudewa tana zarcewa awa ta biyu. Idanunta fes tana zagaye da cikin dakin tana muma biye da fitar numfashinsa da kuma bugun zuciyarsa. Ko yaya ta motsa da zummar zare kanta sai taji ya sake maqaleta da kyau,murya can qasa kuma ya furta
"No" har abun ya fara bata tsoro,a qa'ida ya kamata idan baccinsa yayi nisa dukkan gabbansa su saki ta yadda zata iya zare kanta,amma nasa qawa zucin bai bar hakan ya faru ba.
Tayi kuka tayi kuka har dantsensa daya dora kanta akai ya jiqe,idanunta dukka suka tasa saboda tsabar bacin ran da takeji cikin ranta,ga wayarta daya kama ya kashe mata,tsoronta daya kada hankalinsu ya tashi da neman inda take tunda dai ita bataje gidansu aminata din ba,sannan kuma bata koma gida ba.
Dai dai sanda muhtarin sallar la'asar ya shiga ya motsa. A hankali ya bude zagayyayun idanunsa da duka qara girma suka. Dan kada kadan ya zubesu akan fuskarta. Kamar an qara mata qarfi saboda yadda zuciyarta ta motsa da rainin hankalinsa,shi ashe ma baccinsa yakeyi da gaske?. Sanda yake qoqarin tashi saita rigashi tashin,tana tunanin shammatarsa ne batasan miqewa shima zaiyi ba. Tsam ta miqe tana gyara dankwalinta da mayafinta,sai ya miqe a nutse ya zauna ya zuba mata idanunsa. Can qasan ransa dariya ce sosai take kamashi,yasan ya gama da ita,wannan din wani assignment ne ya bawa zuciyarta da gangar jikinta,ya basu wani aiki ya kuma ajjiye musu wani yanayi da zaiyita kai kawo cikin kwanyarta koda batason hakan.
Abu na biyu yadda taketa wani gyara jikinta tana gyara yafen mayafinta tamkar wadda taga wani muharraminta. Taurin kanta da yadda har yanzu take masa kallon ba mijinta ba yana burgeshi,don yana hango ranar da zai sanyata ta qaryata hakan da kanta,ba da bakinta ba,zata qaryata ne tun daga qasan zuciyarta har ya bayyana a dukka ayyukanta.
Kau da kansa yayi kaman baiga abinda takeyi ba ya miqe a nutsensa ya wuce toilet yana boye dariyarsa,ya azawa fuskarsa wata muguwar daurawa da cin mur.
Har ya fito ya maida rigarsa ya dauki key zai fita tana zaune,sai da taga da gasken yayi hanyar fita sannan tayi hanzarin miqewa
"Ina zaka tafi ka barni?" Tayi masa tambayar wadda a zahiri murya da fuskarta dukka sun juye sun koma kalar shagwaba,irin tsohuwar shagwabar nan tata da take tatawa sanda take ganiyarta,yayin da can qasan zuciyarta kuma ba shagwabar bace. Wata tsana da haushinsa ke yunqurin hallaka zuciyarta. Muryartata saita kashe masa jiki gaba daya,ya daki handle din ya tsaya sosai yana kallonta,kaman zaiyi magana sai wani abu ya fado a ransa,sai yasa hannu yaja qofar ya rufe yayi gaba. Duk taku daya kunnuwansa na cikin dakin yana wani murmushin mugunta,zayaso wannan LOKACIN ya qaraso,sanda zai dafa zuciyarta da gangar jikinta da soyayyarsa,yana tausaya mata,daga mata qafan da yakeyi a yanzun yana yinsa ne kawai saboda yanason ya fara sauke zafin kanta da kuma zafin fushin da zuciyarta ke ciki a kansa.
Yadda ya zata hakance kuwa ta faru,sulalewa tayi a wajen qwalla masu zafi suna fita mata a fuska,wannan wacce irin baqar rana ce gaba daya a wajenta?,tayi nadaman fitowa a yau,inda tasan wannan ranar zata qareta dashi ne qarqashin daki guda,zata gwammace ta wuni a daki da zazzabi a jikinta,tasan koma meye duk inda za'a je a dawo shi zazzabi kankarar zunubi yakeyi.
Baiyi mamaki ba daya dawo ya sameta a wajen,shima yi yayi kaman bai ganta ba a wajen,ya koma ya zauna ya gama azkar dinsa na yammaci,yana ankare da ita baiga ta tashi tayi sallah ba.
"Ki tashi kiyi alwala kiyi sallah" ya furta yana miqewa sanda ya hangi wani a bakin qofar dakin yana jiran a bude mishi ta cctv din dake maqale a qofar dakin. Bayansa ta ballawa harara siraran hawaye na karyo mata,ta sanya hannu ta daukesu a zuciyarta tana cewa
"Ba za'a yi sallan ba,sai kace da can kaike sakani sallar" amma yana waiwayowa ta kwashe kallonta daga kansa zuciyarta nadan bugawa tamkar tana tsoron yaga tana harararsa ne
"Allah ya kiyaye ni.ba tsoronsa nakeji ba" ta baiwa kanta da kanta amsa cikin fushi.
"Bazan zake maimaita kije ki sallah ba........kawai nasan idan na tashi zan saki kiyita koma ta yaya ne" ya fadi yana bude makararren lunch din da aka kawo musu
"Fashi nakeyi......" Ta furta a dan tsiwace tana tura baki gaba rai bace,na meye zai takura lallai sai yaji sirrinta. Tsaiwa yayi daga abinda yakeyi yana dubanta
"Fashi kaman yaaya?,kina nufin har yanzu baki daina wasa da sallah ba ashe?" Ya fadi seriously
"Menstruation......" Ta furta da sauri harda dan daga murya hawaye na balle mata ganin yana niyyar yi mata mummunar fassara.
Siririn murmushi ya kubce masa duk da bai shirya ba,dama abinda yakeso yaji kenan daga bakinta duk da ya fahimci tun farko abinda take nufi. Waskewa yayi yana shafa tattausar sumarsa
"Oh..... okay,ashe ma a bule kike kiketa wani tutturjemin....." Kasa riqe bacin ranta tayi sai kawai ta rushe da kuka,abinda ya sanyashi boye kansa tsakiyar tafukan hannunsa kenan yana sakin asirtacciyar dariya.
Ya yadda babba babba ne kuma duk wanda ya girmeka ya riga ya girmeka,duk yadda yaketa qoqarin hargitsata dinnan bata fahimci da biyu yake komai ba,sai quruciya da suka sanyata a gaba taketa sake tunzura.
Sau uku yana mata maganan tazo taci abinci taqi,sai ya qyaleta ya bude yaci.nashi,duk da shima din ba wani me yawa bane.
Magariba tayi taga ya daura alwala ya fice,ya dawo yaci gaba da sabgarshi abinshi. Yana haramar fita Isha'i ta sanya masa kuka. Kunya takeji da kuma nauyin dukka jama'ar gidan. Duk duniya duk wanda ya gansu tare babu wanda bazai fassara da goyon bayanta ba kuma tana sane ta biyoshi. Ta tabbatar kuma zuwa yanzun nemanta kowa keyi, musamman da wayarta ke a kashe. Yasan me yake damunta,amma yaci alwashin ba zasu tafi ba har sai ta buda baki ta roqi su tafi, zaiga qarshen gudun ruwanta. Abu daya ke damunsa yadda taqi yarda taci ko tasha komai kaman me azumi.
Yana hanyar dawowa masallacin kiran suhail ya shigo,kusan kira na biyar kenan da yayi masa yana shareshi. Sai daya hadiyi wani abu yakai kuma zuciyarsa nesa,yaja numfashi har cikin hunhunsa sannan ya daga kiran
"Ina ka tafi ne haka?,haka ake tarbar baqo a gurinkun?" Ya fadi cikin muryarsa akwai alamun wani abu yakeci
"Komai kake da buqata nasan ka sameshi......wani uzuri ne ya fiddani amma ina hanyar dawowa ko yaushe"
"Uhunn......yayi kyau,banda Allah ya hadani da tsohuwar nan me kirki da kuma dattijuwar arziqi ama haka zaka kwasoni ka yasar ko?......kasha zamanka ma ni na samu abokiyar hira me kirki ba me shegen baqin rai irinka ba......amma kasan wani abu?"*_GUDUN ƘADDARA_*
*H U G U M A*
BOOK 02 PAGE 73
"Nop" ya fada a gajarce don ba abinda ke dawo masa sai kallon da ya dinga bin sultana dashi dazu"
"Na samu komai......amma wannan balarabiyar sister din naka......kasan itace naketa nema tsahon wannan shekarun......tunda na ganta a haram ban sake ganinta ba sai yau a gidanku?,kuma tunda naga ta shige dakin bibi nayi imanin kuna da qaqqarfar alaq......."
"Wait mana......wai me bibi ta baka kasha ne kaketa zuba haka kaman lalataccen famfo?" Dariya suhail ya tuntsire da ita
"Giyar soyayya nasha....... maganar gaskiya ina neman taimakon ka haidar....... I really really love her,na kamu sosai"
"Stop mana suhail.......soyayya kazo neman nijer ko zumunci da aiki ya kawoka?"
"Dukka ukun" ya maida masa amsa muryarsa tana komawa serious. Dif maina yayi yana karanto yadda suhail ya koma magana da gaskensa ba kamar daxun da yake magana da wasa wasa a ciki ba
"Alright......sai ka nema mai taimaka maka,ka kuma nema wata matan ba wannan ba...."
"Why?" Ya tambayeshi a mamakance
"Saboda bazan iya ba"
"Gashi kuma ni ita nakeso.....ita na jima inaso,na ganta kuma saika haramta min ita?" Ido ya lumshe yana jin zuciyarshi kamar zata fashe duk sanda suhail yace masa ita yakeso
"Meye dalilinka haidar?,ko kaima kana sonta?,idan sonta kake hakan bazai hana a bawa wani dama ba,tunda mace allura ce a cikin ruwa ko?."
"U are very stupid suhail,damnit!" Ya furta a fusace yana katse wayar. Sauran kadan yayi cilli da wayar sai kuma Allah yasa ya jefata cikin aljihunsa.
Baisan wanne tsautsayin ne ya kawo suhail nijer ba,amma yayi imanin muddin zaici gaba da fadin wadannan maganganun akan sultana komai zai iya faruwa tsakaninsu.
Bai koma cikin dakin ba saboda bayason ta ganshi a wannan mode din,sai daya zauna na wasu mintuna masu yawa a waje ya daidaita kanshi sannan ya samu qarasawa ciki.
Yana bude dakin kiran goumar yana shigowa wayarsa. Da sallama ya daga kiran goumar din ya amsa
"Ina kyautata zaton tana tare da kai yaa maina right?"
"Yeah,me ya faru?" Ajiyar zuciya ya sauke
"An fara nemanta fa......har an sanarwa aba.....don bataje gidan yasmine ba bare aminata,wayanta kuma switched off,kayi qoqari ku dawo please kafin su ankara kaine ka dauketa,kasan har yanzu