Showing 222001 words to 225000 words out of 294767 words

Chapter 75 - Gudun Kaddara Book 2 Hausa Novel Complete

ta rusuna tana gaidata

"Sai ina?" Murmusawa kadan tayi

"Zan leqa office.....zan rage wasu ayyukan"

"Allah ya taimaka.......amma sultana......kina kallon kanki a madubi kuwa?" Ama tayi mata tambayar yau kai tsaye idanunta cikin nata. Jikinta sultana ta kalla sannan ta maida dubanta ga ama din

"Me nayi ama?"

"Bakiga yadda kike qashin wuya ba?,ko baki fuskanci kayan sawarki sun fara miki yawa ba?". Gyara yafen mayafinta tayi tana dan jingina da kujera saboda yadda takejin kaman iska zata kayar da ita saboda yadda take jinta fayau,ta rasa me zatace da ama din

"Allah ya tsare" aman ta bita dashi. Tanason ganin iya gudun ruwanta ne,yaro baya qarya amma ba zata gasgatasu kai tsaye ba,saidai kuma shi ciwo ai ba'a isa a boyeshi ba.

Jikinta a sanyaye ta fita,ta tayar da motar tana jin zuciyarta na karyewa idanunta akan gidan data fuskanci ko budeshi ma ba'a yi,alamar me gidan yayi nisan kiwo kenan. Sai kuma ta dauke idanunta da sauri tana jin haushin kanta da kanta. Don meye zata tsaya tana kallon gidan mutumin da bai damu da ita ba?,bai damu data rayu ko ta mutu ba?,farincikinsa ba damuwarsa bane sai biyan buqatar kansa kawai da ya sani?.

A guje ta tashi motar tana ficewa a layin tare da tilastawa hawayen da yake qoqarin digowa komawa inda ya fito.

Sosai ta dinga qoqarin sakewa cikin ma'aikatan wai koda iya na yau ne kawai ko zata samu sassaucin abinda takeji,saidai kuma kome takeyi tana jinta ne sama sama kaman me tafiya akan iska. Qarfe biyu na azahar ta samu taci chips da kaza sai dan black tea kadan,zuwa qarfe uku taji dukka dauriyarta ya qare,do haka tayi musu sallama ta wuce gida.

Ta ajjiye motarta a inda sukan bar motocinsu,ta bude motar ta fito idanunta akan motar aba tana mamakin ganinsa yau a gida haka da wuri. Tun zuwansu qasar aba bai fiya zama a gida ba,harkoki ne kawai suketa bude masa,wani lokacinma yana cikin paris din amma wani garin,sai yayi kwana biyu a can kafin ya qaraso gida.

Kauda wannan tunanin tayi ta fara takawa zuwa qofar gidan. Sau biyu rak ta danna bell aka bude. Batoul ce,hannu dumu dumu da cream na cake. Ko ba'a gaya mata ba tasan yau ranar zuba fitinarsu ne a gida,me daure musu qarqashi aba yana gida.

Da sallama ta shiga falon,amma ragowar sallamar ta maqale mata saboda warin tafasar shinkafa daya taso daga kitchen ya iske hancinta. Ta hadiye wani abu da qyar,yawu kuma ya cika mata baki sai taji kanta na neman juyawa,dole ta samu kujerar da tafi kusa da inda take ta zauna tana tunanin yadda zata hadiye yawun bakinta saboda ama dake wajen. Idanunta ta runtse da qyar ta hadiye,sai ya tsaye mata a qirji ya soma taso mata,ya kuma hadu da warin dahuwan shinkafar ya soma dagula mata lissafi.

Cikin minti daya amai ya fara taso mata,wannan ya sanya a gaggauce ta miqe tana fadin

"Bari na sauya kaya nazo mu gaisa da ab......." Bata iya qarasawa ba wani irin jiri ya maidata ya zaunar

"Subhanallahi" ama ta fadi da hanzari tana yowa kanta,qasan ranta tana godewa Allah da ya sanya ba'a qasa ta fadi ba

"Sultana.....kina jina?" Ama din tana rufe baki zazzafan amai ya taso mata.

Tun tana amayar da chips da naman da taci har ya zamana yunqurin kawai takeyi cikin babu uban komai,sai yawu da wani irin yellow din abu dake fitowa. Fara fita hayyacinta tayi,don qirjinta ya riqe sosai da kalar yunqurin da takeyi,ama ta fahimci haka,tasa hannu ta dafe mata qirjin da kyau hankalinta a mugun tashe tana mata sannu.

Sai data galabaice gaba daya sannan yunqurin ya tsaya,zuwa sannan kowa yana tsaye saman kanta harda aba dake can daki. Benazeer da batoul ma na tsaye a gefe suna sharar qwalla,haka nan goumar da shigowarsa kenan yana tsaye shima,sai ya jawo yaran hana shafa kawunansu.

Daga idanunta har fuskarta dukka sunyi jajur,hawayen da batasan na meye ba ya tsinke mata. Tanja ta kawo roba da ruwa ama ta riqe mata ta kuskure bakinta. Haka kawai gaba dayanta take jinta a tsarge,ta gama tanja ta karbi roban ta wuce don ta zubar.

"Sannu sultana......nakega hamdiyya taje taga likita mana ko?"

"Eh in sha Allah aba" ama ta fadi jikinta a sanyaye,hankalinta kuma yana rabuwa gida biyu. Aba ne ya fara juyawa yana komawa ciki tare da qara yi mata sannu,sai ama ta kalli goumar

"Jasu ku koma ciki......tanja duba mata wasu kayan ta cire wadannan,ki dafa mata madara ki kawo ta fara sha tukunna kafin na yiwa asibitin waya" dukka suka amsa mata suna juyawa ciki,sai falon ya zama ba kowa daga ita sai ama din.

Sai da ama ta qare mata kallo sosai,irin kallon da ake kira da kallon qurilla,kallon data jima bata yi mata irinsa ba,sai take ganin kamar sultana ce a gabanta ta shekaru shidan da suka shude,sultanar dake laulayin cikinsu benazeer,amma a yanzun ya za'a yi hakan ta kasance?,bayan ta bada tazara tsakaninta dashi tazara me tsahon da wanda ke nesa ma ya shaida haka bare su da suke a kusa.

"Zan tambayeki,ruwanki ki gayamin gaskiya ruwanki ki boyemin kaman yadda kiketa rufata tunda baki daukeni uwa ba" ama ta fadi tana zama kujerar dake kallon tata.

Hawaye ne ya balle mata da jin abinda ama din ta fada,ta sani tabbas ba zataji dadi ba,ta tambayeta yafi sau shurin masaki akan lafiyarta,amma kulluma amsa daya take bata lafiyarta qalau.

"Already yara sun gayamin,kullum baki da lafiya a haka kike kwana,kwananki nawa kina wannan aman?"

"Bai wuce kwana biyar ko shida ba" ta fada da shagwababbiyar muryar nan data tunawa ama cewa sultanar bibi ce fa har yanzu,a wasu dabi'u nata basu canza ba,wasu halaye nata har yanzu suna nan

"Shine kika gwammaci ki xauna a haka kiyita fita aiki kamar wadda aka gaji da ita ko bata da gata?" Ama ta jefa mata tambayar tana tsareta da ido ranta yana baci. Tana dauka a ranta cewa sultana dolenta ce a rayuwa gaba daya,tana ji a jikinta kamar itace ta tsugunna tayi naqudarta,bataso ko qaunar dukkana abinda zai cutar da ita,kaman yadda bataso ace sultana tana boye mata komai.

Kasa bata amsa tayi,sai qasa da tayi da kanta tana matsar qwalla. Tanja ta qaraso da kayan,ama tace da ita

"Bata ta shiga dakina ta canza ta fito,ki cewa goumar ya dauko mota,yabar miki su benazeer muje mu dawo"

"Tom" tanja ta fadi tana juyawa,can qasan ranta tana jin dadi da Allah ya kawo dalilin da dole aje asibitin,ita kanta kawai dai tana addu'ar Allah yasa a kurkusa ama din ta tursasa aje din,siririn murmushi ya kubce mata tana jin farinciki sosai,tana kuma ayyana drama da za'a yi a gidan nan gaba kadan.*_GUDUN ƘADDARA_*

*H U G U M A*

BOOK 02 PAGE 119


A gida suka bar yaran da tanja,sun yarda sun xauna ne saboda aba yana gidan. Ita da goumar da ama ne kadai cikin motar,sai motar ta dauki shuru,wannan dalilin ya sanya goumar danna fefan waqensa na soyayya yana bi kadan kadan. Idanunta ta lumshe tana jin kalaman dake fita daga ciki kamar da ita ake,can qasan ranta kuma tana jin wata fargaba haka kawai game da zuwansu asibitin.

Kai tsaye emergency suka amsheta,don jikinta yayi weak sosai,duk da ba wani galabaita tayi na fitar hayyaci ba,to amma qasashe ne da basa wasa da lafiyar mutum,hakanan ciwo komai qanqantarsa suna bashi kulawa ta musamman.

Drip suka fara sanya mata don qarfin jikinta ya dawo,ba'a jima da saka mata drip din ba wani nannauyan bacci yayi awon gaba da ita. Ama na gefanta goumar na daya gefan,yana danna wayarsa a hankali kiran maina ya shigo.

Disconnecting na wifi yayi sannan ya daga kiran yana miqewa tare da dosar hanyar fita.

Cikin girmamawa goumar ya gaidashi

"Lafiya Lau,ya akayi yau banji BB ba?"

"Bama tare ni nan ina asibiti" saman center table din dake gabansa ya miqe qafafunsa yana zama sosai

"Asibiti?,waye ba lafiya?" Yayi tambayar cikin tsananin kulawa yanayin fuskarshi yana canzawa

"Mummyn twins"

"Ya salam" ya dora da fadi goumar yana ajiye bayaninsa. Hannunsa ya aza saman sumarshi yana shafawa,har cikin zuciyarsa yana jin damuwa sosai

"Kada kacemin damuwa ce?" Dan murmushi kadan goumar ya saki

"Gayen nan yasan takan d'ana tarko" yayi gulmar maina qasan ranshi

"To akwai damuwar ma dai.....amma basuyi gwaji ba,naji likitar tace sai drip din da aka sa mata ya qare"

"What?,drip?" Ya tambaya a dan rude

"Yayi worst ne jikin?" Ya sake jefawa goumar tambayar muryarsa na nuna damuwa ainun.

"No,bawai tsanani yayi ba,jikinta yayi weak ne sosai......"

"Kaga goumar ya isa haka......gobe inajin zan biyo jirgin yamma,kazo da Allah airport ka daukeni......komai ya kamata yazo qarshe hakanan"

"Yes sir" goumar ya fadi da girmamawa,amma kuma yana danne dariyarshi qasan ranshi. Ya jima baiga masoyan dake bawa juna punishment irin maina da sultanar ba. Kowa a cikinsu yana ji a jikinsa,amma sunqi bawa jikkunansu da zuciyoyinsu hutu,to aqalla dai har gwara maina din,yana son ya matsa gyada ne tayi mai koda bata shirya ba

"Please ka kula da ita..... banason ayimin ganganci da mata koda wasa"

"An gama big bro" ya fadi murmushin da yake boyewa yana fita a dole.

"Kana cikin hankalinka?" Maina din ya fadi a dake,take goumar ya shiga nutsuwarsa don yasan abinda tambayar tasa ke nufi

"Afwan yaa haidar" ya fada yana daidaita nutsuwarsa,akan haka sukayi sallama ya juya ciki.

Da dan sauri ruwan ke shiga shi yasa yake tafiya da saurin. Ya dubi ama yana tamabayarta ko akwai abinda suke buqata?,sai ta girgiza kai

"Ba komai,ai Allah ya kawo mana sauqi,likitan neighbor dinmu ce,zasu dauki sauran test din da za'a mata,tace saimu wuce gida,gobe idan ta tashi daga aiki zata shigo da result din,idanma akwai wani treatment da zata buqata duk ba damuwa bane" kai ya jinjina ya koma saman kujerarsa ya zauna.

Ruwan yana qarewa ta farka tamkar tare suka tafiya da baccin nata. Likitar nada kirki sosai,ta zare mata allurar tana mata sannu,ta dauki sample na jininta dana fitsari,suka dan sake cewa ta huta duk da taji dadin jikinta sosai da drip din da suka sanya mata,sai kuma yunwa da takeji kaman taci babu, goumar na tsokanarta ya fita na mata abinci

"Kodai mayu ne suka kamata ama?,akwai mayu a qasar masu jajayen kunne?" Ya kalli ama yana tamabayarta. Waiwayowa tayi tana dauke kanta daga kan sultana da taketa nazarta ta jefeshi da harara don iya shegen goumar ba wanda ya bari

"Ka tambayi 'yan qasar idan kaje siyo abincin.....xaka tafi ko so kake muyi dare cikin asibiti?" Yana dariya ya fice,saita maida dubanta ga sultana,tana kallon tafukan hannayenta dake zube kan cinyarta tana lissafa wurudin da takeyi bayan ta idar da biyan bashin sallolin dake kanta.

Gaba daya hannayenta sun dashe,sosai suke nunawa ama alamomi da yawa,saidai har yanzu taqi gamsuwa,ta kalli qafafunta ta kuma sake maida dubanta ga qwayar idanunta,duk abu daya suke gayawa ama,amma taqi gamsuwa sa hakan,daga qarshe ta tattara tunanin ta maidashi baya,ta miqe tana maida qananun kayayyakinsu cikin qaraman jaka tana jiran dawowar goumar,tasan zuwa sanda zata gama cin abincin mitunan da sukace ta qara din sun cika sai wucewa gida kawai.

Kamar kowanne lokaci idan bata da lafiya,kamar kuma kowacce uwa haka ama ta tsaya a kanta. Sanda suka iso gida ta tabbatar tasha maganin ciwon jiki da suka fara bata,tayi wanka da ruwa me dumi sosai,ta kuma saka tanja ta dafa mata madara kaman dazu. Sai data tabbatar tasha,sannan ta sanya aka kawo mata su benazeer kaman yadda aka saba. Don tun daga ranar data fara daukansu su kwanan mata kullum dakin suke kwana,koda wani abu ya dauke mata hankali bata zo daukansu ba,ama zata sanya su taho ko tanja ta kawo mata su. Hakan da ta fara yi da kanta ya yiwa ama dadi sosai,don tsuntsu biyu ta jefa da dutse daya,kuma yadda take dibansu tayata kwana ta tabbatar ruwa baya tsami banza,ta tabbatar akwai wani kusanci na daban tsakanin zukata biyu dakan iya motsawa.

Sunyi rigata yin bacci yaran,sanda ta gama komai ta kwanta daga bayansun kamar yadda ta saba sun jima dayin nasu baccin. Ta rufe idanunta tana sakin ajiyar zuciya,tana jin raguwar ciwon da gabbanta sukeyi mata sosai,saidai har yanzun zuciyarta bataji ta samu sukuni da nutsuwar daya kamata ace ta samu ba.

Vibration na wayarta dake saman kanta ya tilasta mata bude idanuwan nata. A mamakance take kallon qaramin agogon dake ajjiye saman bedside dinta tana duba lokaci tare da mamakin waye yake kiranta a irin lokaci irin wannan?.

Wayar ta dauko saita maida kanta saman pillow tana duba kiran. Baquwar number ce,babu ita cikin list na contact dinta,wannan ya sanya ta maida wayar ta ajjiye. Tana ji tana ci gaba da bugawa,duk motsin wayar tana qididdige dashi,har zuwa sanda ta gama vibration dinta ta yanke. Kamar wadda ke jiran ta yanke din saita sake maida idanunta ta rufe,yadda wayar ta dinga burari ya dinga dawo mata akai,bata kammala ba wani kiran ya sake shigowa.

Ba kasafai ta fiya maida kai ga kiraye kirayen da batasan waye ba,amma koda ta sake duba kiran taga dai still wannan number dinne saita gaza ajjiyewa,ta daga kiran ta kara a kunnenta tana daga kwancen.

Wannan husky voice din nashi cikin wani irin softness da ita ya cika kunnuwanta da cikakkiyar sallamar data zare kowanne irin kuzari da yayi saura a jikinta. Tun daga yatsun qafarta har zuwa tsakiyar kanta taji wani abu ya zuba mata yarrr har sai data dunqule hannunta da kyau tana curewa waje daya.

Shuru ya ratsa tsakaninsu,sai ya sake motsa labbansa yana sake maimaita mata sallamar,da alama yana da buqatar amsawarta kenan

"Wa'alaikummussalam warahmatullah" ta motsa labbanta tana furta amsawar da bata da yaqinin yaji ko baiji ba.

Shuru ya sake wanzuwa,saidai kowannensu yana iya jin fitar numfashin dan uwansa ta cikin wayar,abinda ya haifar da mutuwar jikkunansu gaba daya.

Kira ne da bata taba zaton samunshi daga gareta ba,to amma kuma zuciya na gaya mata sai yau zaya nemeta?,dukka tsahon wannan lokacin sai yanzu zai tuna da ita?.

"Hellooo..... sulthana" ya kirata a tausashe muryarsa can qasa fiye da kullum. Ya gama kassara kunnuwanta da fitar sautinsa,don haka ta kasa amsa masa

"Nasan kina jina......kina fushi ko?" Ya jefa mata tambayar. So take tace masa NO don kada ya gano lagonta,to amma yadda zuciyarta tayi wani irin laushi, idanunta suka fara tattara ruwan hawaye sai harshenta ya gaza aiwatar da komai

"Mummy twins" ya kuma kiranta still yana haifar da wani irin amo cikin muryarsa

"Kina buqatata a kusa?" Tambayar data qarasa ruguza dukka sauran qarfin zuciyarta,suka tilastawa hawaye biyowa hanyarsu. Shuru ya sake giftawa,yana iya bibiyar bugun zuciyarta daga cikin wayar da kuma sauyawar fitar numfashinta

"I know you want me.......but i want you to tell me....."

"Okay.... lemme tell you ni tunda ke ba zaki gayamin ba.....i want you and I want you forever" sautin kukanne ya kufce mata,sai tayi hanzarin hanging up na wayar,tayi switching dinta off gaba daya,ta maida kanta cikin pillow tana boye kukanta gudun tashin wani cikinsu benazeer ko batoul.*_
*_GUDUN ƘADDARA_*

*H U G U M A*

BOOK 02 PAGE 120


Abu mafi ban mamaki sai ta dinga jin duk wani qunci daya lullube zuciyarta da kuma zuzzurfar kewa suna sulalewa suna kuma zagwanyewa. Hawayen dai kawai take zubarwa,amma kuma babu wannan quncin da takurar zuciyar.

Sakin ajiyar zuciya ta dinga yi a jajjere,ta mirgina tabar sashen dasu benazeer suke zuwa daya sashen gadon,ta kama pillow ta rungumeshi


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login