Showing 279001 words to 282000 words out of 294767 words
Chapter 94 - Gudun Kaddara Book 2 Hausa Novel Complete
gefe suna hirarsu da kusan rabi quruciya ce a ciki,ranar bikin oncle goumar kaza,ranar bikin oncle goumar kaza.
"Nasan duk maganar da aba zaiyi maka iri daya ce da tawa ko shigenta......dani da aba duka duka ina kyautata zaton watanni bakwai suka rage mana mu gama zaman Paris mu dawo nijer ko Nigeria......akwai dukiyarka a hannuna me tarin yawa da tafiyarka ta kawo rashin baka ita......inason na damqa maka komai naka,saddi da almu suma inason na sakar musu harkokin dake hannuna,saboda haka horar dasu yana wuyanka,saika tsara yadda komai zai yiwu" shuru yayi yana jin nauyi na sake hawa kanshi.
Bai samu ganin aba ba,bai kuma fiya son dogon zaman ba saboda yasan yanayin sultanar,ta zama wata me masifaffen son jiki,duk wani motsinta tafi ganeshi a jikinta,don haka suka yiwa ama sallama bayan ya aika batoul sukayi kiranta cikinsu najma.
"Bloodline" ta kirashi a shagwabe sanda zai tayar da motar
"Ya akayi?" Ya tambayeta
"Nayi missing su BB,don Allah ko zamuje dasu?" Wuyansa ya karyar,yasan abune me wahala ama ta bada su
"Don Allah muje ka rakani na roqi ama ta bamu su" shuru ya danyi sannan ya furzar da iska daga bakinsa
"Okay...... let's go" ya fadi yana fita a motar.
Tun kafin su isa sassan aman ta koma bayanshi ta boye,tana biye dashi kamar mara gaskiya,yana karance da ita tsaf,yana boye dariyarsa har zuwa sanda suka isa cikin falon nata.
A inda ya barta a nan ya sameta,ta daga idanu tana binsu da kallo yadda suka dawo daga fitarsu ga sultanan biye dashi a baya
"Lafiya?" Ta tambaya tana duban idanunsu. Bayansa ta sake komawa ta lafe sosai. Idanun aman sukayi masa nauyi da kwarjini,yadan shafa sumarsa dake kwance lub saman kanshi
"Dama..... batoul da benazeer mukeso a bamu......."
"Naku ne dama?" Ta katseshi tun bai qarasa ba
"No ama......bawai duka ba,aro ko soulsis?" Ya fadi yana waiwayen sultana dake boye a bayanshi. Rigarsa ta riqe ta baya tana sake buya,sai dariyar dole taso kubce masa amma ya danneta da qarfi. Wato a fakaice wayo tayi masa,ta turoshi neman alfarma saboda ita ba zata iya ba.
"Ina sultanan?,kin manta dama kince kin bani halak malak...... batoul da benazeer ba naku bane,ba aro ba dani,Allah ya bamu alkhairi" ta fadi tana miqewa ta dauki wayarta
"Salon daga haka ku riqemin 'ya'ya...." Ta qara fada da salon mita tana wucewa ciki.
Sai data tabbatar ama tabar wajen sannan ta fito daga bayanshi tana kallonshi ido a narke. Hannayensa ya watsa yana dage kafadunsa duka biyun gami da tabe bakinsa alamun nayi iya yina,yadda ta karyar da kai saita sake bashi dariya,ya bude mata hannayensa ta shige,ya dora hannunsa gadon bayanta yana shafawa a hankali,kafin ya saka hannu ya sureta gaba daya yana fadin
"Ga wasu Allah ya bamu,muje muyi rainonsu soulsis.......wancan na ama ne halak malak ba aro ba dani" dariya ta saki
"Na yarda......don da kaina na bayar.......amma a saukeni please kada muci karo da aba"
"Yau duka da kanki kike tattaki,ba zaki sake taka qasa ba sai gobe in sha Allah" ya fadi yana bata kiss a goshi.
Kaman yadda yace din kuwa bai barta ta sake taka ko ina ba,sai daya tabbatar ya gama mata dukkan abinda ya kamata,yana shirin ja mata duvet ta riqe hannunsa
"Uncle maina....." Tayi kiransa da wani tsohon suna da take kiransa shekarun baya. Idanunsan nan dake kasheta ko yaushe ya daga ya kalleta
"Me yasa ba zaka barni nayi hidima cikin gidana ba kamar kowacce mace?,bakaso na samu irin ladan da kowacce mace ke samu cikin gidanta?,zuciyata ba zata nutsu ba,inason naga ina hidima maka da hannuwana kaman yadda kake yimin" Murmushi ya saki,sai ya koma sosai ya zauna saman gadon
"Zakiyi soulsis.......but a yanzun lafiyarki ita muke da buqata,beside ma......hidiman da kikeyi tafimin kowacce kalar hidima muhimmanci"
"Wacce kenan bayan bana komai?" Ta tambayeshi tana ware masa fararen idanunta. Qasa qasa ya gaya mata wani abu daya sanyata jin matsananciyar kunya,ta danna kanta cikin pillow tana cewa
"Allah bloodline......wai baka Jin kunyata?,kana manta wace ni?,babynka dinnan fa daka raina.....baby sultanarka?"
"A nan wajen duka wannan abubuwan da kika lissafa mantawa nakeyi dasu......bana iya tuna komai" ya bata amsa yana dariya hadi da wucewa toilet.
*********Gadan gadan aka shiga hidimar bikin goumar,komai ya hanata zuwa,qiri qiri saidai taga komai ta waya. Bata samu ya barta ta taka gidan bikin ba sai ranar kamun amare,a ranar ma aba ya buqaci ganinsa,ya barta cikin gidan suka fita shi da aba din.
Ganin har lokacin tafiya gurin kamu yayi bai dawo ba sai wanann ya bata dama ta bisu abinta hankali kwance.
Sunje gurare da yawa shi da aba din,ya kuma nuna masa kadarorinsa da yawa wanda shi mainan baisan mallakinsa bane. Qauna irin ta d'a da mahaifi ta dinga zaga jininsa,dukkansu shida ama sunyi fushi dashi ne a baki kadai,amma tsahon shekarun suna tattala duk wata kadara da sukasan tashi ce,hakanan zuciyar tana damfare da tunaninsa.
Duk tsahon awannin da suka dauka da aba amma zuciyar da hankalin suna tare da ita, kowacce daqiqa idan ya samu chance sai yayi kiran wayarta,amma ta shiga tanata ringing bata dauka ba,don already ma a gida tabar wayar. Bata sani ba,ciki ne ya jawo haka?,ko tsohon tsimi ne ya tashi,haka siddan yau din taketa murna zata shiga taron mutane da yawa cikin family,abinda ya dade da mutuwa daga cikin ruhinta,ta kuma dade da ajjiyeshi tare da cireshi daga tsarin rayuwarta gaba daya.
Zuwa wani lokaci haqurinsa ya qare,ya daina gane abinda aba yake fadi sosai,Allah ya taimakeshi wani abokin aba din ya buqaci ganinsa,ya matsa ya basu guri,sai kawai ya wuce inda ya ajjiye motarsa ya shiga ya nufi gida.
Kaf gidan aka duba mishi ita bata a nan,daga qarshe matar oncle issofou da ita daya ta rage a gidan maman najma din ta gaya masa sun wuce wajen taron tare.
Ajiyar zuciya ya saki me nauyi yana jin kishinsa yana motsawa,ji yakeyi kamar kowa na wajen ita zaiyita kalla,kamar kowa hankalinsa zai zama a kanta ne,ya tayar da motar da zafin nama yana fita a gidan,yana jin kamar yayi tsuntsuwa ya ganshi a wajen.
*_second to the last page zamu shiga in sha Allah_**_GUDUN ƘADDARA_*
*H U G U M A*
BOOK 02 PAGE 150
Ganinta cikin jama'a ya tuna mata da baya sosai,ta dinga kallon masu kai kawo da masu taka rawa a wajen tana ayyanawa cikin ranta itama da haka take?,da hama takeyi?. Kunyar kanta da kanta ta kamata,tayi qas da kanta zuciyarta na rawa,zuciyarta na ayyano mata girma da martabar maina a ranta. Ashe duka haka yake hango mata?,ashe haka yakeso ta zama yadda take yanzun?,ashe ciwo yakeji cikin ransa?. Cikin zuciyarta taji wanne sakamako zata yiwa bawan Allahn nan?,dame zata saka masa?,tabbas itama bata sani ba,amma tanaji zatayi iya qoqarinta tuquru,xata sadaukar masa da rayuwarta har zuwa qarshen numfashi kamar yadda shima ya sadaukar mata.
Akwai friends nata da yawa data jima rabonta dasu,wasu ma kwata kwata rayuwa ta sanya ta manta dasu,sai gasu sun hadu a wajen. Kowannensu mamaki yakeyi,kowannens kallon sultana yakeyi
"Sultana hamani mohmoud?" Suke fadi. Duk da da yawansu sunsan a yanzun ita din wacece,Tv show presenter ta qasar paris.
Kowa ya kalli benazeer da batoul ya kalli sultana din sai suyita mamakin idan tace yaranta ne,da yawansu ma qaryatata suka dinga yi,saboda basusan meye ya faru a rayuwarta ba,kawaidai sun tsinci ta daina zuwa makaranta rana tsaka,daga bisani kuma ta bace musu daga nijer gaba daya,sai suka samu labarin bata qasar.
Yadda yaran keta daukan hankulan jama'a a wajen yadan dagi hankalin sultana,saboda sun zama popular a Instagram sosai,babu twins dake tsananin kama da juna dake trending a Instagram irinsu. Tasan ama ta musu addu'a tabbas kafin su fito,amma duk da haka ta sani bakin uwa daban yake,don haka ya kirasu ta jasu gefe ta sake tofesu.
"Wai da gaske sultana hamani ce?,sultanan ya maina?,sultana 'yar madara fa?" Wata qawarsu dijama ta fadi tana dariya ganin zallar nutsuwa da kamalar da sultanar ta siffantu dashi a yanzu. Ta sake zama wata cikakkiyar mace,kwarjini da wani irin zallar kyau lullube da ita. Murmushi ta sakarwa dijama
"Shafa mana kiji,halin fa yana nan raguwa yayi bawai na daina ba" ta fada tana dan gatsina baki. Dukkansu sai suka kwashe da dariya,wannan haduwar ta musu dadi qwarai,don rabuwa ce ta shekara da shekaru ba'a kuma yi zaton za'a sake haduwa ba.
"Nidai ki bani twins dinnan don Allah sultana?" Daya qawar tasu ta fada cikin tsananin son yaran da burgewa.
"Turqashi!"aminata ta fada tana dariya.
"Ba zasu bani ba ko?" Ta fadi tana kallon aminata
"Ko ubansu bai isa yace a bashi su ba bare uwasu bare wani,yara halalin ama ne ama kuwa ko mutuwa tayi inda da hali a hadata dasu" ta qarashe fada tana dariya. Dariya sultana tayi tana kauda kai
"Nidai ba ruwana,Allah yasa ta jiki" kauda kan da tayi saita hango almu yana tahowa. Ya qaraso daf da ita yayi qasa qasa da kansa
"Ya maina yana Jiranki ta waje fa" almun ya fadi yana dubanta. Idanu ta fidda waje,shaf ta mance ma bata gaya mishin zata bisu ba,ta kuma san halinshi sarai. Tsam ta miqe tana ce musu
"Ina zuwa"
"Ki gaida gida dai" aminata dake dariya ta furta
"Don nasan wannan Romeo din naki bazai barki ki dawo ba" harara ta watsa mata
"Sai na gaya masa abinda kika fada" ta furta tana yin gaba
"Ki yiwa Allah kiyi haquri" itama tayi mata magiya tana hada hannayenta biyu waje daya alamar roqo.
A nutse ya daga idanunsa yana duban hanya don yaga kota taho?. A hankali a hankali take takowa kamar me tsoron cin karo da wani abun tsoro,tana tafiyar tana sunne kai da hade jikinta guri guda. Ya zuba mata idanu sosai,sai kuma ajiyar zuciya gami da dariya suka subuce masa ba tare da ya shirya ba.
Ya tuna shekarun baya da idan tayi wani laifi,irin wannan tafiyar takeyi kafin ta kawo gareshi,ko a yanzun da take tafiyar sai ya hango sultana 'yar shekara sha hudu. Gaza jurewa yayi ya fita da hanzarinsa,bata ankara ba taji yayi sama da ita
"Kinaso ki wahalarmin da zuciyata ko?,kinason ki raban wannan kyakkyawar fuskar da wasu?,sai da naji zuciyata kamar zata narke sultana" ya fadi yana ajjiyeta cikin motar. Maqaleshi tayi ta hanashi ajjiyeta,ya daga idanunsa ya aza cikin nata. Ta shagwabe masa fuskar nan da irin nau'in shagwabar dake tafi da hankalinsa
"What?" Ya tambayeta yana jin jikinsa yana saki gaba daya
"Am sorry" ta fada a tausashe. Yatsansa kawai ya dora saman labbansa
"You are already forgiven" ya amsa mata da wani irin shauqi dake fita daga qwayar idanunsa,kanshi yakai a hankali zuwa labbanta da goshinta ya aje mata wani tattausan kiss.
Hanyar gida kawai ya wuce da ita,ta juyar da kanta a hankali tana dubansa
"Bloodline......na dauka zaka barni gidan ama ne,tunda gobe daurin aure?" Idanunsa duka ya waro waje yadan saci kallonta a hargitse
"Bazan iya ba soulsis....." Sai ya fara irga mata da yatsansa.
".......awa daya,awa biyu.....awa uku......awa hudu,har awa nawa?,it can't" ya qarasa fada yana girgiza kai. Bata sake ce masa komai ba,don ita dinma kawai tana sha'awar komawa gidanne,amma tasan ba tabbas ta iya bacci,ta maida kanta saman kafadarsa a hankali ta kwantar tana lumshe idanunta,sai ya sake sauke wata ajiyar zuciya wadda kusan sultana ta saba da jinta,batasan wanne irin ciwo soyayyarta take masa a zuciyarsa har haka ba.
Bai iya sake barinta zuwa gidan bikin ba kwata kwata,suna gida ana bude sabuwar rayuwa,dukkansu sun budewa junansu idanu da wata irin soyayya me tsayawa a zukata,duk dare sai sun fita tadan motsa jikinta,ya kuma kaita guraren da yasan a baya tana da shauqin zuwa cikin nijer,guraren da a baya yake hanata zuwa da kuma kusantarsu,a yanzun shine ya zame mata dan jagora. Duk inda sukaje din sai ta tuna komai,kunya tayita kamata tana sunne kai,sai yayi fuska kawai kaman bai fahimci abinda takewa kunyar ba. Wasu guraren sai hawayen farinciki yazo mata,a yanzun data mallaki cikakken hankalinta,ta kuma samu ilimin addini dana boko isashe sai take ganin cikakken baiken rashin kasantuwar diya mace a wajen.
Da gaske maina yayi mata gatan da ko uba mahaifi iya gatan da zaiyi mata kenan,yayi tsaiwar daka akanta irin tsaiwar da uwa ce kadai ke yiwa diyarta. Daga qarshe guri na qarshe da sukaje,taga yara irinta irinta nata tiqa rawa irin rawar da a baya bata da abun burgewa da takeso taji tana yi sai ita,saita kamo hannuwansa ta sanya cikin nata tana duban idanunshi
"Bloodline......ka yafemin don Allah?" Wayarsa da yake amsa kiran suhail ya ajjiye gefe yana bata duka hankalinsa
"Me kuma ya faru?,kinason sakani a damuwa sultana.....menene?" Sosai idanuntan nan masu sheqi suka hada hawaye
"Nayi maka abubuwa da dama na rashin kyautawa,na kalleka ta fuskar abokin gaba,maqiyina wanda bayason walwalata ko ci gaba na,nayi maka mummunar fassara......na dauki duka qiyayyar duniya na aza maka......bayan dukka gata kakemin,duk duniya kuma bani da masoyi sama dakai......ya maina......ka yafen....."
"Shshshsh.......ya isa soulsis mana....eheennnn......goge hawayen" ta fada yana sarqafe yatsunshi da nata. A hankali ta fara goge fuskarta da bayan hannun nata. Ya saki wani siririn murmushi na gefan baki wanda ya qara masa kyau sosai,ya motsa jajayen labbansa da tattausan muryarsa dinnan ya fara mata wata waqa cikin harshen France. Waqa ce da yake mata tun tale tale,tun tana zanin goyo sanda yake rainonta. Ta tuna waqar fes,ita ta dinga sakata sakin murmushi daga qarshe dariyar kunya ta qwace mata,ta kifa kanta saman table din da suke zaune tana boye qwayar idanunta.
"Sultana na ta zama me wani irin kunya" ya fada a hankali yana dan taba saman qafarta da qafarsa dake cikin socks ta qarqashin table din,saita janye qafartata da sauri tana qyalqyala dariya.
Da gaske wani irin kunyarsa takeji kam,sosai idan yayi wani abu saita dinga gani kaman ba uncle maina dinta ba?,wanda yake kaman uba a gareta?. Inda Allah ya taimaketa......da sun kebe sun shiga da'irar da yakeso saita manta da komai,shima kuma ta dulmiyashi cikin shauqi ta kuma kaishi wata duniya me nisan nisa. Dole ta zage ta karkade duk wani salo na ama da karatun ama,ta kuma sake zurfafa bincike da neman sanin hanyoyin kama miji,kamar yadda taji ama tana yawan gaya mata
"Karki sake kada kuma ki yarda ki zauna haka sakaka,duk soyayyar da mijinki ke nuna miki saikin dinga fadada hanyoyin riqeshi da faranta masa da kawo sabbin abubuwa cikin zamantakewarku,sannan uwa uba addu'a.......kada kiyi sake......ina maimaita Miki kada kiyi sake ki kuma miqe qafa don miji yana sonki ki gaza yawaita addu'a akan Allah ya dawwamar da wannan soyayyar taki cikin zuciyarsa,addu'a takobi ce...... addu'a gata ce.....sannan kuma addu'a tanadi ce"
"Ya Allah ka maida jin aliyyu,ka maida ganin aliyyu,ka maida tunanin aliyyu ya zama SULTANA ce" wannan shine addu'arta a duk sanda ta sanya goshinta qasa.
Batasan tana tsananin kishin aliyyu ba sai yanxu,batasan tana da kishi me tsanani ba sai yanzu,wannan ya sanya addu'arta a kullum
"Ya Allah,ka mallakamin aliyyu ni kadai,Allah ka sanya ni kadaice matarshi a duniya,ni kuma Allah ka bani ikon zama baiwa a gareshi,ya ubangiji kada ka bani iko na cutar dashi ko na tauyeshi cikin haqqinsa,Allah ka kiyayemin jinsa ganinsa da zuciyarsa daga kowacce 'ya mace".
Aba dakeson ya sake ganinsa su qarasa tattaunawa ya sake kiransa,ranar ne suka koma gidan bayan an share biki. Bibi tayita kwasarsu shi da ita tana musu tsiya
"Ji'irai biyu,sun gama yaqin da dauki ba dadi tsakanin dangi,sun hanawa kowa zama lafiya amma sai gasu yau bulunbuqui dasu,kaga idanun ja'irai"
"Bibi......kiyimin ni kadai ki qyale matata ta huta" maina ya fada yana duban bibi. Baki ta riqe tana dubanshi,can qasan ranta ita daya tasan me takeji,ita kadai tasan farincikin da takeji,amma a zahiri saita tamke rai
"Sannu me mata,matar da sai dana saka aka mata tara tara kai da ita?,ni zaka gayawa wai mata?,naci gidanku kai da matar" saita watsa masa daquwa. Qasa yayi da kansa yana dariya,bibi tafi gaban komai a wajensa,ta masa gatan da har ya mutu bazai manta ba.
"Yo ai nima wannan cikin idan aka sauke ni ya kamata a baiwa sannan ku fara tara naku ma" ta fada tana miqe qafafunta wanda suke sake matsanta mata da ciwo,duk kuwa da cewa cikin magani da kulawa kullum ake.