Showing 78001 words to 81000 words out of 294767 words
Chapter 27 - Gudun Kaddara Book 2 Hausa Novel Complete
rungume da dardumarta take fitowa daga masallacin. Idanunta sun tasa sun kuma yi jaa saboda yawan kukan da tayi a gaban ka'aba. Rabin kanta sarawa yakeyi saboda abincin da bataci ba wunin yau din gaba daya sai zam zam data dinga sha sosai kaman ba gobe.
Sanye da baqar jallabiyya yake takawa a farfajiyar wajen. Tsahonsa bayananne ne,hakanan nannadaddiyar sumarsa.
Bata lura dashi ba kamar yadda shima din da alama bai lura da ita ba yana cikin gaggawa ne,wannan yayi sanadin da saura kadan kafadunsu su hade waje guda,abinda ya sanya sultana janyewa gefe zuciyarta na wani irin mahaukacin bugu saboda qamshin turarennan da hancinta ya shaqa qwarai da gaske fiye da yadda take jiyo qamshin daga nesa a mabanbantan gurare..........qamshin yaja hankalinta ta waiga a hargitse tana duban wanda ya giftata din........
*_GUDUN ƘADDARA_*
*H U G U M A*
BOOK 02 PAGE 42
Rufewar da idanunta sukayi,da kuma irin bugun da zuciyarta keyi ya sanya idanunta suka nuna mata shi a matsayin maina,daga bisani kuma a hankali ganinta ya washe,ainihin kamanninsa suka fito mata
"Sannu ko?,yi haquri don Allah" ya fada yana daga Mata hannu da sassauqar muryarsa dake bayyana zallar sauqin kansa,ya bata haqurinne da hausa kawai don baya tsammanin ko kadan zataji me zaya fada,don kuwa koda alama batayi masa kama da launin jinsin hausawa ba. Kanta ne yayi wani mummunar sarawa,sai data sake matsawa nesa kadan dashi sannan ta gyada kai tana furta
"Ba komai" a wahale sannan ta juya da sasarfa tana barin gurin,don ko kusa bata qaunar sheqar qamshin wannan bala'e'en turaren
"Uhmm......nace ba,don Allah ko zan iya sanin masaukinku?" Taji ya fadi a bayanta bayan ta baro wajen sosai,don tayi tsammanin ma inda suka tsaya din daga nan ba lallai ka hangoshi ba. Muryar tasa ta sanyata waiwayowa sai suka hada ido. Kai ta girgiza masa alamun a'ah,sai ya marairaice yana ci gaba da binta
"Don Allah,kada kice a'ah" hannuwanta dukka ta sanya tana dage doguwar rigarta tana kuma qarawa qafafunta karsashin yin sauri,don burinta ta tsere masa daga wajen. Ba abinda yake sake hadsasawa zuciyarta sai wani irin bugawa
"Please" ya sake fadi ba tare daya dakata da binta ba
"Ka daina bina,nan din waje ne me alfarma"
"Na sani,ni dinma alkhairi nake nufinki dashi,bata yadda zan miki magana a nan kuma zuciyata sharri ne a cikinta game dake"
"Na gamaka da girman gurin da wanda ake bautawa a wajen ma dakata" ta sake fada daidai sanda ta hangi goumar yana nufo wajen,yana riqe da hannun BATOUL tana bashi labari,shima kuma da alama dukka hankalinsa yana kan batoul,saidai hango sultana da wani na biye da ita ya sanyashi dauke dukka hankalinsa a kan yarinyar ya maido kansu batoul.
Bata fasa sassarfar tsere masa idanunta nakan fuskar Goumar data tabbatar sai yayi mata shishshigi,kaman yadda bai fasa binta yana mata magiya ba,hakanan goumar bai fasa nufosu ba fuskarsa da idanunsa na nuna wani irin emotion.
Ta karanci abinda ke fuskar Goumar,kaman ma a fusace yake ainun,yau kam sai tayi maganinsa taga idan akwai abinda zai iya,don haka suna zuwa dab dashi ta dakata,ta kuma karantawa matashin Address na hotel harda number dakinta
"Na gode sosai,sunana suhail kefa?"
"Sultana" ta fadi a taqaice tana juyawa ta rabe goumar ta wuce.
Sai data fara nisa da gurin suhail ya maida dubansa ga goumar da yayi tsam ya zuba masa wannan idanun nasu me matuqar kwarjini da haiba irin na maina,idanun buzaye dake da wani irin sirri da kuma launi na daban.
A idanu suhail yaga suna kamanceceniya da sultana,saidai shi din baqi ne sosai kuwa akan kalar fatar sultana dake jazur kamar ta fito daha yankin larabawa,wannan kama da ya gani yasa ya miqa masa hannu yana fadin
"Assalamualaikum" girman kalmar da sanin ma'anarta kadai ya hana goumar qin miqa masa hannu. Ya bashi hannun,saidai kuma ya bar masa saqo yana fadin
"Ita din matar wani ne,kada kayi gangancin shiga gonar da ba taka bace,kada kuma kayi yunqurin keta dokar Allah" sosai sai jikin suhail yayi sanyi,amma a yadda karo daya yake jinta cikin kowanne sassa na zuciyarta daga kallon farko,sai yaji kalaman goumar basu shigeshi ba
"Ni jikina sam bai bani haka ba,idan ma kai din rival ne saidai nace maka kayi haquri na riga na kamu,ma'assalama" ya fada yana yin gaba.
Tun daga ranar sai goumar ya dauke mata wuta tsaf,ta daina ganin koda haqoransa,itakam hakan yafi mata dadi,don dama so take ya fita a sabgarta kuma ya fita din,takance a ranta
"Aikin banza aikin wofi,koshi wanda kakeyin abun saboda shi bai isheni kallo ba,bai kuma isa yace zai damu rayuwata ba bare kai"
Suhail kuwa tasha ganinshi a hanya ko cikin masaukin nasu da alama ita yake nema,saita bace masa kota koma har sai yabar wajen. A daidai lokacin lokacin ubangijinta kawai take dashi,ita kanta cikin zuciyarta taji nutsuwa da gamsuwar lallai tayi ibada iya yadda ubangiji ya bata iko,fatanta kawai ta zama karbabba,muddin kuwa ta karbun tayi imanin zata cimma dukkan nasara da kyautatuwar rayuwa.
Sati uku sukayi suka koma Paris ta rungumi karatunta,wanda babu abinda take gani sai budi da nasara,duk wani nasibi da budi data roqo akan karatunta tana ganinsa,karatun tamkar ana buda kwanyarta ana zuba mata shi,nan da nan kafin ma su kammala ajin farko sunanta ya fara yin fice cikin makarantar tsakanin dubban dalibai dake department dinsu.
Duk yadda takai ga janye jikinta da rashin son jama'a sai Allah ya bata farinjini sosai cikin makarantar,kowa ta zauna dashi dai ya qaunaceta,duk da miskilancinta bata iya wulaqanci ba sam,sannu sannu sai gashi ta fara dan sakewa da jama'a. Koda ba zatayi mu'amala dakai ba amma zata maka murmushi saman fuskarta,wannan sai ya sake zama abun burgewar jama'a a wajenta.
Tun wannan zuwan da sukayi sai zuwa umrar ya zame musu tamkar jiki kamar yadda aba yayi mata alqawari. Abun sai ya zama kaman ya tsara musu kanshi da kanshi,duk sanda suka samu hutun makaranta ita dasu benazeer to a saudiyya suke yin abinsu,suyi wata guda suna ibada sannan su dawo kuma a soma shirye shiryen komawa bakin karatu.
Ta riqi karatunta gam da matuqar muhimmanci,tana bashi dukkan lokacinta,saidai kuma hakan bai hanata ibada ko koyon wasu abubuwa da suka shafi rayuwa ba wandada tasan tana da naqasu ta bangaren,kaman koyon girke girke,hanyoyin kula da kai da kuma gyara kai da wata balarabiyar oman ke koya musu. Macace me baiwar sanin ilimin halittar diya mace,shiga ajin matar ya faranta mata ainun,don ya sake maidata wata irin 'yar gayu..... mace me aji,irin macen kuma da tasan kanta ciki da waje. Sai a sannan ta karanci ama cikin hikima. Wato ita ama ba'a banza ba ta fita daban a zuciyar aba,duk da cewa aure qaddarar wasu mazajen ce,to amma bata tunanin tana cikin qaddarar aba,wasu abubuwan ma da yadda take kula da rayuwarta da kuma kanta dukka sai yanzu hankali da ya game sultanan take karantarta,wasu abubuwan tayi qoqarin daukesu,wasu kuma su bata kunya.
Abinda bata sani ba ama din ta fita zurfin nazari sanya idanu da qwaqwqwafi,tuni ta fahimci sultana,sai bata nuna mata ba,amma itama saita sakata a nata ajin na yadda mace zata amsa sunanta mace a idanun mata 'yan uwanta dama maza abokan cudayyarta. Ta sake salute na ama,ba banza ba ta sake fita daban da faccalolinta,tun tale tale komai na ama dabanne,she's so classy,har kuma a yanzun dabi'arnan tana nan,shekaru da fara zuwan girma bai sanya ta canza ba.
Ta zame mata mentor sosai ta fanni da dama,ita kadai data kalla ya sake sanya mata sha'awar koyon girke girke iri daban daban. Ama din kamar half cast za'a kirata,uwa uba kuma ita din tayi zaman qasashe tun zamanin quruciya har zuwa yau,wannan ya sanya ta iya nau'ikan abinciccika kala daban daban,kuma da kadan da kadan sai da sultana da iya da yawa daga cikinsu.
*_KOMAI NISAN DARE gari zai waye_*
Cikin babban dakin taron dake mallakin makarantar,cike yake da dalibai irinsu sultana dake murnar amsar sakamakonsu na kammala karatun aikin jarida fanni daban daban,sai kuma manyan baqi iyaye da 'yan uwan daliban dake qasashe da kuma garuruwa daban daban cikin paris da wajenta.
Tana sanye da academic regalia data dora saman wani tattausan lace da ya lashe kudade masu ciwo da ama ta siya mata,ta kuma bayar akayi masa dinki me aji. Lite make-up ne a fuskarta wanda zaka iya rantsuwa da Allah ba komai saman fuskarta saboda nutsuwa da kwanciyar da kwalliyar tayi a saman fuskartata.
Tun daga takalmin qafarta har zuwa mini handbag da medium mayafinta idan akayi lissafi a qalla zasu tada jari me qarfi ga wani. Komai nata me sanyi da tsari,kaman yadda halittar ta take da daukan hankali da saukar da wani irin nutsuwa.
Siririn kwallin da aka sanya ma fararen qwayoyin idanunta da kuma red lipstick da ta shafa ya fidda mata wata haiba da kwarjini na musamman.
Tana zaune a inda aka tanada saboda dalibai,amma gaba daya hankalinta yana kan batoul da benazeer da aka yiwa kwalliya sosai cikin wata red gown da tayi masiiiifar kwanciya a lafiyayyar fatarsu da hutu da gata ya jiqa sosai. Sai kai kawo sukeyi suna 'yan guje gujensu tsakanin mutane,duk kuma inda zasu gifta din sai sunja hankulan mutane. Wasu su jasu suyi hotuna,wasu su basu qananun gift da ba'a raba baturen mutum dasu.
Kiransun da aka fara yi daya bayan daya ya sanya dole ta haqura da lura da kai kawonsu,duk da tasan idanun aba ama goumar harma da bibi da tayi tattaki tun daga nijer domin ganin yadda gudaliyar tata a yau zata karbi sakamakon da zai bayyanata a cikakkiyar 'yar jarida.
Sanda sunanta ya fita a cikin mic haka ta miqe tana ratsa mutane,kunya gami da nauyin idanuwan da sukayo kanta dukka suka cikata,haka ta dinga takawa cike da nutsuwa har takai saman step din da kowanne dalibi ke tsaiwa tana qasqantar da ganinta.
Idanu sosai takeji cikin jikinta tamkar yawansu ya wuce yawan adadin jama'ar dake wajen kadai. Bayan gajeriyar gabatarwar dake nuna da qwazo da nagartarta,kwanya da kaifin ganewa da take dashi,da kuma kasancewarta daya daga cikin dalibai guda biyar da sukafi kowanne dalibi samun high mark. Ji ta dinga ji kamar zata fadi a wajen,gaba daya qafafunta sunyi laushi hawaye ya cika idanunta. A kowanne bigire na rayuwa data tsaya ba abinda take gani sai haske,wani irin budi take gani a duk matakin karatun data taka,batasan abinda ke nufi da hakan a gareta ba,me yiwuwa akwai hukimar ubangiji da ya sanya qiyayyar karatu me yawa a ranta a baya.
Kuyi haquri dai,ku qara haquri,naso yau na kaiku inda ya kamata aje din,amma yau da gobe ta riqeni,duk da haka ku bini bashi gobe in sha Allah,na gode sosai
*_GUDUN ƘADDARA_*
*H U G U M A*
BOOK 02 PAGE 43
Hannu ta sanya ta amshi certificate dinta,wanda tayi tsammanin bayan ta karba din zata koma ta zauna ne kamar kowanne dalibi......amma kuma a'ah. Kyaututtuka na karramawa ne suka yita fitowa saboda qoqarin data nuna da hazaqa a guraren da suka danyi ayyuka dasu na neman qwarewa watannin da suka wuce da kuma cikin makarantar kanta,kasancewar su mutanene masu girmama mutum irinta,sunason suga mutum me talent qwarai da gaske. Sai ta dinga ji kamar tarihi yana maimaita kansa a hassan Ibrahim gwarzo makarantar da har yau take kewarta,take kuma jin tamkar ta koma can. Makarantar ta zame mata wani mabudi,ta kuma zamewa rayuwarta haske kuma fitila dan jagorarta daga duhu izuwa haske.
Kafin a kammala taron duka ta bata fuskarta da koke koke,sai tissue da ama keta bata tana goge fuskar saboda hotuna da aketason dauka da ita,musamman su benazeer da suka ja hankulan mutane qwarai.
Tana duqe tana qoqarin controlling hawayenta muryar benazeer ta karade hall din ta cikin mic. Da zazzaqar muryarta tayi sallama,sallamar data sanya kowa dake wajen murmusawa,ta kuma saka sultana dagowa da sauri. Tayi dare dare saman step din tana murmushi,cikin yaren france da ya kama harshenta matuqa da gaske tamkar yaren hausa da suke magana dashi yau da gobe a gida ta soma magana
"Ina gaida aunty na.....ina gaida mommy na ama.... oncle goumar....kaka na aba.....sai daddy na.......daddy na ina gaisheka......muna kewarka daddy,yaushe zamu ganka?" Ta qarashe fada muryarta tana raunana.
Tafi wajen ya dauka,yayin da maganar ta doki qirjin duk wani ahalin mayak'i dake a wajen. Sultana kam maida bayanta tayi makarin kujera ta jinginar tana rufe idanunta, qirjinta yana bugawa kusa da kusa. Goumar ya riga ya gama yiwa tunaninsu lahani,ya gama cusa musu wannan tunanin na mahaifinsu wanda batasan yaushe zaibar zukatansu ba.
Kusan jikinta a sanyaye aka kammala taron,saidai dab da za'a kammala din saiga sanarwa daga wani gidan tv kai tsaye suke neman sultana zuwa channel dinsu zatayi interview,suka bata date wanda ya dauki makonni kusan hudu,dai dai da sanda suka kammala wasu gyare gyare na shirye shiryen da suke gabatarwa a channel din nasu. Wannan shine abinda ya wanke mata zuciyarta,farinciki ya kamata sosai,abinda bata taba tunani ba,yau ita sultana wani tashan talbijin dake a qasar turawa ke nemanta da kansu?
"Alhamdulillah" kawai ta dinga maimaitawa tana jin farinciki yana ratsata,ko ta ina addu'arta ke karbuwa,cikin qaramin lokaci buri da muradinta ke dab da cika.
Koda suka koma gida bacci tayi sosai na gajiya,bata tashi ba sai azahar,tana yin sallah ta sake komawa,don duka kwanakin zirga zirga sukeyi don tabbatuwar taron. Bayan sallar la'asar benazeer ta shigo,ta bita da kallon harara sannan ta zaunar da ita. Data fara yi mata fada akan abinda tayi dazun saita sakar mata kuka,abinda ya sanyata sakin baki kawai tana kallonta,sannan kuma cikin bacin rai tace
"Oho.....tun bankai ga dukanki ba?,hala duka kike buqata ko?" Kai ta girgiza tana share hawayen fuskarta
"We missed him mommy,uncle goumar yace yana nan amma bamu taba ganinsa ba,sai a hoto ya taba nuna mana shi sau daya" gabanta yayi mummunar faduwa,da gaske goumar yakeyi bazai bar shiga shirginta ba?,wato har wani nuni yake musu dashi a hoto
"Tashi ki bani waje" ta fada tana watsa mata harara. Har ta miqe sai ta dawo a sanyaye,ta tsugunna gabanta murya a sanyaye
"Kiyi haquri aunty" ta fadi tana mutsuka idanunta da qwalla ke fita. Ido tadan xuba mata na sakanni,tausayinsu su dukka yana ratsata,ita da yaran gaba dayansu ababen tausayi ne,sai itama taji nata idanun sun ciko,ta sanya hannu ta jawota ta rungumeta a jikinta.
Ajiyar zuciya yarinyar ta saki tana yin luf a jikin nata,kasancewar basu fiya samun wannan damar ba,saida tayo controlling nata hawayen don kada ta gani sannan ta sake tana cewa
"Kije wajen bibi naji kaman tanja na kiranki"
"To" ta amsa tana miqewa da dan tsallenta tamkar komai bai faru ba,gashinta dake daure yanaya lilo a bayanta ta fice a dakin.
Binta tayi da kallo har zuwa bakin qofar,sai a sannan taga ama dake tsaye hannayenta goye a qirjinta. Sauke hannuwan tayi ta tako cikin dakin,yau dai sau daya tak taji zata yima.sultana din magana,zafin qiyayyar aliyyu da take gani a idanunta sun fara bata tsoro,tayi tsammanin ilimi shekaru da kuma wayewa sata samu zasu goge komai,koda komai din bai gogu ba tayi zaton xai ragu ainun har ya zamana bai iya bayyanuwa a idanun mutane
"Sai yaushe sultana?,sai yaushe zaki sassautama ranki wannan abun dake qulle cikun zuciyarki?" Karon farko tayi mata tambayar ido cikin ido.
Qasa tayi da kanta,ba zata iya jurar kallon qwayar idanun ama ba,nauyin da dukka ruhi keji akan uwa game da d'anta ya saukar mata. Da alama abun ya zafafi ama a yau tunda har ta magantu,shine abinda sultana ta raya a ranta,kamar ta karanci abinda take rayawar sai ta